Free chapter · Read without an account
chapter 17&18
👰👰AMARYAR ZAMANI👰👰
SHORT AND BRIEF STORY
STORY AND WRITTING BY SALMEERT (AUTAR MAMA ,ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♂️🧚♂️🧚♂️)
HAPPY SALLAH ,INAYIMA DUKKAN DAUKAKIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN AN SHA RUWA LAFIYA , ALLAH YA MAIMAITA MANA.
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
FREE BOOK .
PAGE 16&17.
""""""""""""""""""Cikin alamun zaulaya, tana gyara zamanta kan gadonta.
sukuwa ai tafi suka fara suna hayani, kowa na faɗin albarkacin bakinsa .
"Aaaaaah lalle su miji manya "cewar Meerlas tana daka mata duka a bayanta domin ta juya baya ma daga kallonsu.
dauka tayi tana kara kashe murya.
A,A ce ta kalle ta tana kyarkyacewa da dariya sai chan kuma ta kara juyowa tana cewa, "Angona kana lafiya ya gida ya kewata, komai nawa yanan normal ko a kara adanamin su dakyau soon na kusa karɓar ajiya ta ", ta fada tana wani kashe murya da fari da ido.
kwashewa duka sukayi da dariya Meerlas ce tace "sai kace wata kilaki" , ta fada suna taɓawa ita da A,A.
Miemie ce ta juyo tana cewa "dallah kuyiwa mutane shiru kunsan ma ko akan mai muke magana ne , kuma inma kilakince ai mijina nayi mawa", ta fada tana harararsu.
su kuwa ai sun samu abin yi, sai kwatanta yarda Miemie takeyiwa Abdul shagwaɓa , suke.
ba su wani dade suna fira ba sukayi sallama saka makon su AA da suka ishesu da hayaniya.
kwanciya tayi tana tuna kalmar da Abdul ya gayamata,wani kasaittacen murmushi ta saki, mai zasuyi banda dariya sosai suke tsokanarta tun tana yin shiru har suka kureta ta fara basu ansa .
"to wai ke Miemie ya zaki da Yaya Abdul, dan da alama ba karamin mabukaci bane,"
"yarda ko wace mace take daukar mijinta nima haka zan dauke nawa daf".
ta fada da alamar yan rashin kunyar suna kusa.
"wai ai nasan, tundaga wannan gidan naki sai munjiyo ihun ki har nan", suka fada da alamar shakiyanci.
"lalle Yara kunma rainamin wayau kawai sai na saki baki ba kana ihu sai kace wata sakara ai saidai shi ya yi ihu badai niba", ta fada taba wani ya tsina fuska.
"hhhhhhhhhh, mudai ai yan gashi ne, tunda dugu-dugu, zamuzo muyi gashi", Ummi ta fada tana wani irin juyi da rawa.
"lalle Ummi baki da hankali kawai sai in saki cinyoyi inbari har sai kinzo kin gasani, kijima wani iskanci wai a gasani sai kace wata kaza",ta fada tana hayayyakowa Ummi .
ita dai Meernal batace komai ba sai dariya da takeyi musu, suna ta cacar baki, su suna cewa sai sunzo gashi ita kuma tana cewa basu isa ba.
"hmmmmmm, lokacin da Yaya ya cika aiki ya yi miki raga-raga ragas raga fata - fata ai zakiyi bayani".
"nifa bana ma gayyarku gidana duk mai kewata ya kirani waya kuma kar wadda tasake ta kirani da daddare ko da safe don ko kun kirama ba dauka zanyi ba domin lokacin na my love ❤ ne".
ta fada tana yi musu fari da ido.
"aiko sai kin nemaimu ruwa ajallo kin rasa tunda kika ce haka", cewar AA tana gyara kwanciyar kan makeken gadon.
har sunyi shiru sun fara addu'o'i sai Miemie tace "waiiiiii waya ganni da ciki talli-balli", ta fada tana wata irin mahaukaciyar dariya ,suma maganar tata dariya ta basu hakan yasa suma suka dara, fira suka cigaba dayi sai karfe kusan daya tukunna suka kwanta.
*WASHE GARI*...
*YAU CE KUMA RANAR DAURIN AURE*
tunda sasafe suka shirya cikin atamfa hollod mai masifar kyau mai ratsin navy blue da light blue, sosai ta karɓi, jikinsu tayi musu bala'in kyau dama abu ga fararen fata, sosai atamfar tayi musu kyau.
gidan wata makobciyarsu suka shiga da yake itace wadda zatayi lallen Miemien hakan yasa ita da kawayenta duka suka tare gidan , sai bayan an daura aure zasu koma gidan su.
"Amarya ananan cikin fargaba da tsinkewar zuciya ko" AA ta fada da dariyar shakiyyanci.
ita kuwa ko a jikinta dan kamar ma ba ita bace Amaryar domin babu wani alamar fargaba a tare da ita, sai harkokin gabanta take, hakan yasa duk wanda ya shigo sai ya fita da mamakinta , dan iyayinta take zubawa da kadifirinta son ranta .
karfe daya dai -dai ,dubannin Al-Ummar dake gurin suka shaida daurin auren Khadija Abba Tanimu da Angonta Abdurrahman Ma'aoruf, akan sadaki naira dubu dari , zo kuga baki gurin Ango da Amarya domin kwata-kwata bakinsu ya kasa rufuwa, bayan an gama komai, Angwaye suka nufo cikin gida domin gaishe da iyaye da kuma yi pics din biki.
bayan sun gama gagaisawa ne, suka nufi gidan mai lalle wato Mamashu🤣 (Alherin Allh ya kaimi ki har cikin garin kaduna kuma a gwamna road my dear Aunty mamashu).
suna shiga naga Miemie ta daka wani uban tsalle bata dira ko inaba sai gaban Abdul rungumaishi tayi