Free chapter Β· Read without an account
11&12
πΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*MR ARROGANT*
_The story about young police man_
πΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*STORY AND WRITTEN*
_BY_
*REAL ESHAA~*
*WATTAD*
_Realeshaa_
*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* πποΈ
( Ζ³anci don cigaban al'umma, Ζ΄an ci ya Ιara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)π*
***
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 11&12*ποΈ
_____________________πAlh jabir haifeffen garin jammaina ne acikin jamhoniyar Chad yataso cikin so dakuma 'kaunar iyayensa kasancewar shi ka'daine 'da awajen mahaifiyarsa Hajiya Rabi dakuma mahaifinsa Alh yusuf"Sun bawa jabir duk wani gata dakuma tarbiya da yakasance iyayen 'kwarai na baiwa 'ya'ya yensu toshi yasamu daga nasa mahaifan.Yana girmama nagaba dashi sannan yasan darajan dattawan unguwar domin yanda yake girmama mahaifinsa hakayake girmamasu shiyasa yake shan yabo awajen jama'ar su,koda acikin unguwane ko kuma Makaranta jabir bashida abokin fa'da haka zalika bashida aboki,shika 'dai yake rayuwarsa cike da nutsuwa dakuma tarbiyan dayasamu daga iyayensa"yayi saukan alkur'ani mai girma tun kafin ya kammala secondary school din sa bayan ya kammala secondary sane Alh yusuf yatattara iyalansa domin sukoma maiduguri baki 'daya kasancewar kasuwancin baya tafiyan masa yanda yake bu'kata Uwa uba kuma basu da family acikin garin jammaina domin shi ka'dai yarage acikin danginsu duk sun'kare sede abokanan arziki wa'anda akayi zaman mutunci dasu wannane dalilin da yasanya shi tattara inasa inasa domin barin 'kasar sa tahaihuwa wato jammaina yadawo Nigeria 'kasa mai kamala da mutunta ba'ki musamman ma jahar Borno.
Bayan sun dawo Maiduguri ne Alh Yusuf yakira abokinsa Alh ayuba wanda suke zumunci duk dakasancewar su ba yare 'daya sukeba domin Alh yusuf shuwane shi kuwa Alh ayuba bare bareni.shi yamasa hanya yasamu yasai gida sannan yaci gaba da kasuwanci wato har'kan tulare kama daga humra tularen wuta kayan hadin kolacca tularen 'kamshi nafesawa babu abinda baya sayarwa Wanda yashafi 'kamshi.Cikin Ikon Allah shagon nasa ya bun'kasa fiye da yanda yake acikin 'kasarsu wato Jammaina"yayinda yasanya jabir yayi jamb cikin ikon Allah yasamu makin da ake bukata ya jona university,kara tunsa yake cikin nutsuwa da sanin abinda yakawosa batare da 'kale'kalen duniya ko kuma bin 'yan mata ba kamar yanda wasu samarin zamin keyi"Acikin hakane Allah ya ha'da jininsa da na Kabeer Wanda yake saida magani acikin 'dan basket jabir yayaba da tarbiyan Kabeer dakuma nutsuwarsa hakanne yasanya sa yarda da abokan takansu Kabeer ya 'dan fisa ashekaru ma anma haka suke abokan takansu inda har jabir yakai Kabeer wajen mahaifinsa,sosai shakuwa me 'karfi yashi ga tsakanin jabir dakuma Kabeer Wanda hakan ba'karamin da'di yayiwa iyayen jabir ba kasancewar sa bameson tarun abokanai ba hasalima bashida ko 'daya se yanzu da Allah ya ha'da sa da Kabeer sun 'daukakesa inda Alh Yusuf yasanya Kabeer acikin 'daya daga amintattun yaran shagonsa Koda Alh Yusuf ya'ajiye Kabeer yatamba yesa ina mahaifan sa seya sanya kuka yace sun da'de da mutuwa 'yan uwansu kuma sunki ri'kesa wannan dalilin dayasa yake gantali"Ba'karamin tausaya masa Alh Yusuf yayiba dan haka ya'dauki 'damaran temakonsa"haka suka ci gaba da rayuwarsu cike da kulawa sannan Allah Na da'da sanya musu albarka acikin kasuwancinsu.
"Ranace mafi muni awajen jabir dakuma masoyansa domin gobara ce tatashi ansara daga inda tatashi,anyi anyi akashe wutan anma abin yaci tura seda wutar tacinye baki 'daya gidan dakuma rayukan iyayensa gashi babu wutar nepa bare ace daga nan ne haka suka gama jimamin abin tare da al'ajabi.Ha'ki'ka mutuwar ba'karamin jigatashi tayiba dan seda yayi sati beci komai ba iyakacinsa ruwane kadai yakashe komai na duniya ya masa zafi kasancewar bashida kowa face iyayensa kuma basu dawasu dangi Iya su ka'dai suke rayuwarsu cikin rufin asirin Allah." Kabeer shi yaci gaba da kulawa da shagunan mahaifan jabir yake kuma ne mamasa temako akan Allah yaso yadawo normal kaman da domin mutuwar tasanya shi komawa kamar wani mara lfy" sosai Alh ayuba yake kulawa da jabir shima yana basa temako dede gwargwado.
Cikin ikon Allah datemakon dayake samu yadawo Dede, yakoma normal life dinsa dayakeyi"tsakaninsu da Kabeer yawuce abokantaka sundawo aminan juna kasancewar shima Kabeer din Maraya ne sannan bashida wani 'karfi iyayensa basu barmasa komaiba,Komai na bukatansa jabir ya 'dauke komai nasu kala 'dayane kama daga suturansu,takalma,agogo,huluna,dade kayan rayuwa duk wani yarda dakuma amana jabir ya dan'kasa ahannun Kabeer domin babu sirrin jabir Wanda Kabeer besan dashiba Sun kuma 'dauki Alh ayuba tamkar mahaifi domin duk abinda yashige musu duhu basu saniba shi suke tambaya.
Bayan kammala karatun jabir ne yamaida hankalinsa sosai kan sa'na'ar da mahaifinsa yabar masa wato seda kayan 'kamshi.Sosai Allah yasanya masa albarka acikin sana'an dayake inda ya bun'kasa yakuma shara akan sana'an dayakeyi gari gari ake zuwa saran kayan 'kamshi inda Har ya kafa rashen sa a jahar bauchi,kano,yobe, da kuma yola harma da 'kasar sa tahaihuwa wato Jammaina.Cikin 'kan'kanin lokaci yashara fiye da tunanin me karatu acikin Nigeria ba inda be kafa reshensaba harma da 'kasashen 'ketare.
Yana temakawa gajiyayyu dakuma marayu sosai ake alfahari dashi acikin Maiduguri dama yankinta." Alh ayuba yakira jabir akan yazo ga 'yar sa zebesa saboda ya yaba da nutsuwarsa dakuma 'dabi'unsa dakuma zaman amanan dasukayi da mahaifinsa" bamuso jabir ya amince kasancewar yasan Ruqayyah yarinyace nitsatsiya dakuma sanin yakamata tanada 'dabi'un da duk wani namiji zeyi burin mallakarta amatsayin matar aurensa saboda tanada halayya nagari."
Cike da farin ciki yaje yasamu amininsa wato Kabeer yasanar masa yanda sukayi da alh ayuba ya tayasa murna sosai da addu'ar Allah yasanya alkhairi aciki"Sati biyu akasanya bikin,cikin sati biyun aka shirya komai inda ya 'kera gida nagani na fa'da acikin jiddari ba 'karamin 'daukan hankalin jama'a gidan yayi ba dan kaf unguwar babu gidan dayakai wannan ha'duwa komai shi yasanya acikin gidan domin yace rukayya tamkar 'kanwarsa take dan haka baya bu'katan komai da 'kyar Alh ayuba ya yarda anma yace shizeyi mata kayan kitchen ba musu jabir ya amince dan bayason jayayya tsakaminsu kuma hakan ba'da bi'ansa bane mayarwa Babba magana."Yaso Kabeer yanemo mata suyi aure tare anma ya'ki firrr yace be shirya aure cikin lokaci ka'dan ba, badan jabir yasoba ya ha'kura batare da sunyi aure da aminin'nasaba Kamar yanda yayi niyya abaya"dan haka suka kama shirye-shirye gadan-gadan.
Rana bata 'karya sede uwar 'diya taji kunya a yaune dubban jama'a suka shaida 'daurin auren jabir Yusuf dakuma amaryansa Rukayya Ayuba auren daya halacci 'dubban jama'a na nesa dana kusa manyan 'yan kasuwa dakuma 'yan siyasa angama taro lafiya.Alh ayuba shida kansa yasa Rukayya a mota yanufi jiddari da ita domin yace bayason bidi'a shi zekai 'yarsa da kansa"Misalin 'karfe tara ya kaita gidan nasiyya yayi mata sosai Wanda duk uba nagari zeyiwa 'ya'yansa banda kuka babu abinda take,Waya Alh ayuba yacire acikin aljihunsa yakira jabir bayan sungaisane yace yana nemansa yazo gidansa yasa mesa"Ba'adau lokaciba jabir suka 'karaso shida Kabeer "Bayan sun sake gaisawane Alh ayuba yaha'da su baki 'daya yayi musu nasiyya meratsa jiki,jikin jabir yayi sanyi kuma ya'dauki 'damaran sau'ke hakkinta da yardan Allah, sallama Alh ayuba yayi musu sannan yamike yabar Rukayya dakewar su tana zubar hawaye" shima Kabeer nasiyya yayi musu dede gwar-gwardo sannan ya'ajiye musu kazan amarci yafice Har waje jabir yarakasa sannan ya kulle gidan yadawo ciki.
"A inda yabarta anan yadawo yasa meta tana kuka hadda shesh'sheka cikin taushin lafazi yafara rarrashinta sannan yace tatashi taje tayi alwala tazo suyi sallah sugode wa allah ba musu tami'ke yanuna mata bayin tashiga ta 'dauro alwala sannan tafito bayan tafitone,shima yashiga ya 'daura alwala" sallah yajasu raka'a biyu bayan sun idar ne ya jiyo ya dafa goshinta yafara addu''o'in da manzan Allah (S.A.W) yakoyar ga duk wasu ma'aurata dasuyi adaren su na farko domin slamun zaman lafiya dakuma Neman tsari da she'dan"tambayoyi yai mata akan addini duk abinda ya tambayeta tana bashi amsa Dede da tambayarsa wani ma har yawuce"Beyi mamakin hakanba kasancewar yasan daga gidan da tafito akwai ingantacciyar tarbiya.Mi'kewa yayi yacire babban rigarsa sannan yashiga kitchen 'din ya 'dakko plate ya juye musu gasassun kaji"zama yayi akusa da ita yace bismillah muryanta na rawa tace a'a na'koshi idanunsa ya 'dago ya kalleta gaba'daya atsorece take murmushi yayi yace banson gardama 'kanwata matso kici,batasake cewa komaiba tasanya hannu ka'dan taci tace ya isheta be matsa mataba ya 'kyaleta" shi kuwa sede yaci ya'koshi sannan yakwashe kayan ya mayar inda ya 'debosu.
Bayi tashiga tawanke bakinta sannan tadawo cikin 'dakin tazauna a inda suka yi sallah"kallonta yayi yace kije ki kwanta kinji mi'kewa tayi jiki asanyaye taje ta kwanta atakure kallonta yayi yai murmushi ganin yanda ta takura yagane atsorace take dan haka be tankataba saboda yanaso tarage tsoro aranta tasake dashi.Kur'ani ya'dauka yafara muraja'a cikin suratul nisa'i tun tana sauraron dadda'dan muryansa Har bacci ya 'dauketa,sede ya karanta wajen sumini hu'du kafin ya ajiye kur'anin yarage kayan jikinsa yakashe hasken yahaura kan gadon janyota jikinsa yafara wasa da ita farkawa tayi afirgice zata 'kwace yayi saurin janyota ya ha'da bakinsa da nata cikin sau'ki yasamu nasaran rabata da kayan jikinta addu'ar saduwa da iyali yafara yana Neman hanyarsa.
_Ina ganin haka nayi waje da gudu ππ»ββοΈππ»ββοΈππ»ββοΈππ»ββοΈππ»ββοΈdan My Aunty baby tahanani 'dauko irin wannan rahotanni tace Na manyane_
*ESHAA CE*π€π»