Free chapter Β· Read without an account

Part 10

by Salis M Reza Β· UWATA CE SILA

πŸ™†β€β™€οΈ *UWATA CE SILA* πŸ™†β€β™€οΈ


     *(True lef storry)* 

          *By* 

     *(SALIS M REZA)*









β˜€οΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* β˜€οΈ






 *UWATA CE SILA*

       *PAGE* πŸ‘‰1️⃣0️⃣


...............Mom kuwa jin kaman wayar tanayi ne yasa ta d'ago domin dubawa kafin idon ta ya kai gaban wayar saiga kira ya shigo, kallon sunan mai kiran tayi sannan ta kalli Ameera wacce har lokacin kan ta na sunkuye amma jin ringtone d'in wayar tane yasa ta d'ago ta kalli Mom d'in saitaga itama Mom d'in ita take kallo, sai ta mayar da kallonta izuwa kan wayar, Sunan Jibrin ne yake yawo a kan wayar.


Kafin Mom tayi mgn Ameera ta ce "Mom Jibrin ne class ment d'inane ya kirani ne domin yaga tin da muka gama exam ban kirashi ba. Mom ta ce "To daga yau Kar ya sake kiranki in zumunci ne angode in kuma gaisawa ne a tsaya a iya school bana son wannan zancen banzan. Saida Mom ta mata fad'a sosai sannan tace mata babu ruwanta da yin abokai maza a school domin kuwa ba shine ya kaita...


In kuwa har ta sake ta jita da namiji Wai aboki to sai ta sab'a mata. Itakuma Ameera godewa Allah takeyi da yasa Mom bataga film d'in nanba sannan ta na godewa Jibrin da yakira a wannan lokacin amma jin irin fad'an da Mom d'in takeyine yasa ran Ameera b'aci ta ce "Wai Mom ba nace miki babu komai ba ne amma kuma sai gara mai-maitawa kikeyi. 


Mom ta ce "Ameera ke yarinya ce bakida wayo kuma baki da hankali karatu shine abun da ya kamata ace kina maidakai amma kuma ke bawannan ne a gaban kiba, inada buri da yawa a kanki domin ganinn na gina rayuwarki amma ke ko a jikin ki "Shin Mom mai yasa kikeson dole sai nayi karatu? ta ci gaba da cewa "Saboda kud'i ko Mom? Mom ta kalleta da kyu sannan tace "Ameera wannan 'kasar tamu in bakada kud'i to kaida kare duk d'aya kuke, kin ga kuwa mai zaisa bazan so kud'i ba?


Ameera ta kalli Mom d'in sai ta sake cewa "Dama sabo da kud'i kenan kikeso nayi karatu? To ai Mom kud'i basai nayi karatu bama zan samo miki Mom namiki Al'kawarin wallhi zan tara miki kud'in da bazaki iya gama cinyesuba har kibar duniya.


Mom tayi dariya sannan ta ce "Ameera kenan shi ilimi ko ba dan kud'i ba ana amfanar sa domin zaman wannan duniyar tamu, sabo da haka bana son nasake jin kince zaki samo min kud'i koda bakiyi karatu ba.


Ameera ta ce "To Mom ni bana son karatun nan wallhi wanda nayima ya isheni nifa Allah Mom kullum in naje school gajiya nakeyi wannan zaman class d'in duk ya ishe ne ni kawai kibarni na zauna a gida tindade na d'an yi karatun kuma sun isheni zaman wannan duniyar d'in.


Cikin jin haushin abun da Ameeran tacene Mon ta ce"Ameera Mai yasa kikeda taurin Kaine yanzu? Yan zu ban isa na ce miki kiyi abu kuma kiyi ba shin wai menene ya mayar da ke hk? 


Ameera ta ce "Nifa Mom kece baki fahimtata kawai ni karatunnan ne na gaji da shi kawai ki barni har sai na huta tukunna Ameera tana maganar ne tana kallon wayarda Jibrin yaketa kira tin d'azu. 'Dakagawa tayi had'i da kara wayar a kunnenta sannan tafara magana a gaban Mom d'in.


Cikin tsaninn b'acin rai Mom ta fizge wayar daga hannun Ameera ta bugata da 'kasa sannan ta d'au keta da mari harsau biyu jikake tass tass sannan ta cigaba da cewa...


Daga yau Zan sanar miki tindade bakida hankali... Wannan gidan da kike gani da kuma wannan motocin da kikegani a gidannan duk dalilin karatun bokon da uban ki yayi ne har ya mallakesu, Nima da kikegani duk wannan fariyar da nakeyi duk ta'kamata karatun ne, saboda haka Ameera Kar kiyi karatun daga yau wannan wayar na hanaki amfani da ita sannan kuma na barki har tsawon she kara d'ayan da kikeso Allah ya Baki sa'a, Mom tana kaiwa nan da maganar ta, ta fita daga d'akin ranta a mugun'bace.


Hawayene yake zubowa da fuskar Ameera cikin rashin kwarin gyiwa ta kalli wayar da mom din ta buga da 'kasa sannan taje ta d'auki wayar ta kunnan taga ko mutuwama batiba sai dai ta d'an far-farshe. Cikin ran Ameera kuwa maganar da mom tayi ce take mata yawo a kai, Ni dai yarinyace amma na fahim ci Mom gori ta kemin sannan tana nufin in babu karatun boko babu samun kud'i kenan?!!.


Tin daga ranar tsakanin Mom da Ameera Babu wanda yake shuga sabgar wani, haka Ameera ta kira Nusee ta sanar mata da cewa zata je su had'u da Alhaji lawan. Alhaji laawan wani dan uguwar su Nusee ne tin ba yauba yake bibiyar ta a kan duk abin da takeso zai mata In har ta yarda da shi,


Nusee kuwa dama ita tin bayauba ta sanar wa Ameera cewa... Kiyarda da shi wallhi yanada kud'i Zaki samu kud'i sosai. Amma Ameera sai ta ce ai ita tindade ga Wanda fara lalatamin rayuwa to duk wata damuwata to shine, ganin duk abin da sukeso Uncle yana basune yasa suka bar maganar Alhaji lawan. Yanzu kuwa gashi mom ta mata gori harda cewa ta barni tagani ko zan iya Samar wa da kaina mafita.


Nusee da Meera cikin d'an'kan-'kanin lokaci suka shahara a harka bin maza, tin iyayen su basa ganewa har sukazo suka fahim ta. 'Ban garan Rakiya kuwa duk abin da Nusee takeyi ta sani Amma ganin itama ana bata toshiyar baki ne yasa tayi shuru, yanzu ba 'karamin shiri sukeyi da Nusee ba domin kuwa yanzu Nusee ce tazama uwar ita kuma 'yar, amma fa duk da haka ba ya hana wata rana in 'yan rikicin sukazo ayi dambeba. Daddy kuwa tin yana dukan ta harya fara mata na siha.


Dayaga abun zai fi 'karfinsa ne yasa yace ta koma gurin maman ta, aikuwa aranar da taje mijin ta ya ce bazata zauna masa a gida ba do min kuwa shi bashi da k'arfi, haka Daddy ya cigaba da lallashin Nusee d'in amma ina tariga taji dad'in maza.


'Ban garan Meera kuwa Jibrin ne ya koyamata Shan duk wani maganin hana d'aukar ciki da kuma nuna mata wasu hanyoyin. Meera da Nusee sunkoma school amma basa yin komai domin kuwa Al'kawarin da mlm yamusu na cewa in sunyi exam susa a ransu kawai sun ci Koda kuwa basa zuwa school d'in, kuma hakane ya ci gaba da kasan cewa shi kuwa mlm tin daga ranar da yayi amfani da Ameera basu sake yarda da shiba.


Kuma suka masa barazana da cewa in har bai musu satam amsaba to sunada vedio d'in da yayi da Ameera zasu Kai gurin shugaban makaran ta, jin haka yasa mlm ya dinga basu haguri a kan wallhi zai dinga basu first and second ( Na d'aya da na biyu). Kullum sune suke cin nad'aya da na biyu.


'Ban garan Mom kuwa abun ya na bata mamaki sosai ganin yanzu Ameera duk exam in batazo ta d'aya ba zatazo ta biyu, tanan 'ban garan hankalin ta ya kwanta to amma kuma taga yanzu bata sakar mata kud'i amma kuma tana iya yin komai wani lokacima har kawo mata kud'in takeyi sai tace Daddyn Nusee be ya bata.


Tin mom bata ga newa har tazo ta fahim ci a she Amera bin maza takeyi. Ranar ma wanine yazo har gida ya sanar da ita cewa yaga Ameera a hotel itada wani mutum, tofa tin da Ameera ta dawo fa ranar a kayi ta 'kare domin kuwa tin daga ranar Ameera ta ce "Mom kud'i nima nake nema Amma bada karatun Boko ba, kuma zan taramiki su har sufi naki ma...


Nannan fa Mom ta fara zazzagin Ameera ta na cewa ita tace mata tabi maza ne, Amma Ameera ta ce ai Mom kece kuwa Kik sakani a wannan rayuwar domin kuwa kece sila. Kece sila kece sila wannan kalmar itace kallamar da mom ta keji daga gurin Ameera a duk lokacin da tazo zata mata fad'a. kullom idan Uncle Bala yazo shima Ameera ta soma shinfid'a masa rashin kunya sannan ta ce masa, ita nai man kud'i takeyi Kuma da izinin Mom takeyin komai sannan Kuma Mom din itace sila.


Uncle Bala yazo har gida ya tambayi 'kanwar tasa amma ta fara kuka a kan wallhi bata san komai ba. 


Ana cikin wannan halin ne Anty Zainab ta dawo domin kuwa dama karatun shekara BIYU ta yi Kuma ta kammala, dama ta zo hutu sau d'ay Kuma taga halaiyar Ameera ta koma sai a hankali, Amma batasan cewa tana bin maza ba. 


Nannan fa a kafara wasan, domin kuwa Anty Zainab bata ragawa Ameera ganin irin rashin kunyar da takeyiwa Uncle Bala da kuma Mom, Anty Zainab tayi-tayi akan Ameera ta sanar da ita abun da Mom din ta mata amma ta ce Babu ruwanta, jin hakanne yasa itama Anty Zainab ta fara cin uban Ameera d'in Amma fa itama Ameera ba ragamata takeyi ba domin kuwa in tamata zata rama dukda kuwa ta girmeta nesa ba kusa ba.


'Ban garan Sulaiman kuwa wato (S M) Tare ya gansu itada Nusee lokacin sundawo daga school ne haka ya bisu a baya har yaga gidan da suka shiga. Abinda bai saniba kuwa suma sunsan dashi domin kuwa tun lokacin da ya kafamusu ido suka ankara da shi amma sai suka nuna kaman basu San da shiba. 


Tin S M bai san Meera tana bin mazaba har ya samu labari, Amma a kan yaji ya tsaneta sai yaji ya 'kara sonta fiyeda na baya, ahaka ya je ya tin kareta da maganar soyayya Kuma harda Al'kawarin aure in har zata dai na wannan rayuwar. Amma Meera tayi dariya sannan tace masa ita ba wannan ne a gaban ta ba in har ya shirya domin jin dad'i da ita to mutu'kara yanada kud'i.


Nannan fa S M ya ce "Shifa auran ta zai yi da gaske amma Ameera ta ce Kar ya sake mata ma ganar aure, shikuma ya dage domin kuwa kullum santa 'karuwa ya keyi a zuciyarsa, Haka dai S M kullum yana bibiyar Meera yace meye da muwarta ta ce masa mom d'in ta take son taga ta cika mata buri, haka take sanar wa da S M cewa komai kaganin takeyi UWARTA CE SILA.


Tin abin yana bashi mmk har ya dai na Kuma kullum sai ya kirata itakuwa sai ta zazzageshi a kan ya fita daga rayuwarta Amma Kuma yakasa. 


'Ban garan Nusee da Meera kuwa har yanzu basu daina neman gidan Uncle ba, inda Nusee ta dage da neman Uncle din feye da Ameera. Kullum haka Meera zata fita daga gida zuwa gurin wanda suka shirya a wannan ranar ko gidan sa kokuma hotel. Duk lokacin da tadawo Kuma bata baiwa Mom komai a she taramata ta keyi.πŸ˜‚


Haka wani daga ciki kwaratan nata ya mallak mata mota sabuwa fara sool. Inda itama Nusee aka siya mata itama nata kwarton ne ya siya mata.


Mom ta daina zuwa aiki tin bayan shekara d'aya da ta huce saboda halin da Ameeran ta shi 



*(NI KUWA NACE AI MOM AI KIN GAMA YA RIGA DA YA KAMA, KWARAMA KIKOMA AI KIN KI YA FI)* 


Meera and Nusee sun huce duk abin da kuke tsammani, kudai ku biyo ni domin ko wa yanzu a ka fara.


 Watarana Mom na zaune a palor Ameera ta fito da wata jaka ta zauna tana murmishii sannan ta fara fitowa da kud'i daga cikin jakar ta, kud'ad'ene masu tarin yawa Wanda har da kud'in wasu 'kashashen, haka ta zubasu a kan tebur d'in dake tsakiyar palorn sannan ta ce "Mom ga sunan kaman yanda kikace ba a neman kud'i Saida BOKO to gashi ni na nema kuma na samu.


Mom ta fashe da kuka sannan ta kalli kud'in sannan ta kalli Ameera sai ta 'kara fashewa da kuka ta kasa maga, Ameera ta ce..."Shin mom ba kince kud'i sune maganin zaman wannan duniyar tamu ba? To amma kuma gasu ma ke hargida suke biyoki amma kuma kike kuka?.



TOM YANZU DAI MUN GAMA TINA BAYA.  MUHA'DU A PAGE 11 DOMINNJIN SUWAYE ALHAJI MUDI? DAKUMA A BOKIN SA.....? SHIN SU NUSEE ZASU KAMA UNCLE? SHIN WANI MATAKI MOM ZATA D'AUKA A KAN UNCLE❓❓❓...πŸ“




Pls comment and shre. Hakanne zai sa nacigaba da sauriiiiiiiiii




To be continue....


My FAN'SπŸ™

My friendπŸ₯°

One house🀝

Love all ❀️

S REZA✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.