Free chapter · Read without an account

E2

by Diamond deejarty · SHU'UMA

*🧚🏾‍♀️SHU'UMA🧚🏾‍♀️*


_Ƴar mutan zazzau Naanarh M Shaaban✍🏾_


*SADAUKARWA GA YAAYANARH ABIN ƘAUNATA💖💕*



*✨ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION✨*



**________________

E2


"Nazeer ina so na tabbatar maka daga yanzu har zuwa lokacin da daidaita maka hankali idan ka ƙara ɗaga hannunka da niyyar dukana to wallahi sai na cire maka hannunka" Nazeer a ƙufule yace "ni zaki cirewa hannu? ni kuma kika mara?" Khadija tace "na mareka ɗin, idan kuma ka na tunanin ba zan iya cire maka hannun ba, ka gwada duka yanzu zaka ga aiki da cikawa" jinjina kai yayi, tare da cewa "lallai Khadija yau zan koya miki hankali, ki jirani ki ga abinda ni zan iya yi" ya faɗi haka tare da juyawa ya shiga ɗakin da yake karatu, Khadija kuwa ganin ya shiga ɗakin bata san me zai iya yi mata ba, dan ta fuskanci bashi da imani, yasa ta nufi ɗakinta da gudu ta saka key, ta barshi a jikin ƙofar, dan idan ta zare key ɗin zai iya saka nashi key ɗin ya buɗe, amman idan ta bar key ɗin jikin ƙofar ko ya saka nasa ba zai taɓa barinsa ya buɗe ba, har sai ta zare nata, akan gado ta zauna ta zabga tagumi, cikin kuka ta fara magana "ina zaman zamana a ƙauye, aka zo aka haɗani da wannan mahaukacin mara tarbiyya, Inna me yasa zakiyi min haka? idan wani laifin nayi miki ya kamata ki hukuntani ko dukana ne zaki iya yi, amman meyasa zaki hukuntani da auren Nazeer, mutumin da bashi da halin kirki, duk wani aiki wanda ya saɓawa addini yasanshi, kuma....." bugun da taji ana yi wa ƙofar ɗakinta ne yasa tayi shuru da maganar da take, ta tsayar da kukanta ta share hawayenta,


"Wane mahaukacin ne?"


Nazeer cikin zafin rai yace "ubanki ne mahaukaci, ki buɗe min ƙofar nan idan ba haka ba, idan na shigo ba za ki ji da daɗi ba, dan sai na karkaryaki" Khadija tace "to shikenan ai daman haka nake so, ka shigo ka karyani idan ka isa sunanka NAZEER ADAM KAMSHI" Nazeer jin abinda Khadija ta faɗa yasa zuciyarsa ta shiga zafi, Nazeer mutum ne mai matuƙar zuciya da saurin fushi, baya son raini sam, ita kuma Khadija tunda ta fahimci baya son raini ta samu abinda take cusa masa baƙin ciki, daga chan ɓangaren kuwa Khausar ta ji shuru-shuru Nazeer bai dawo ba, tunda ce mata yayi yana zuwa yanzu zai dawo, tashi tayi ta fito falo, anan ta hango Nazeer ɗin sai dukan ƙofa yake yi daga ganin yanayin yadda yake dukan ta fuskanci yana cikin matsanancin fushi, cikin kwarkwasa da yanga ta ƙarasa inda yake cikin yauƙi ta fara magana, tana ƙoƙarin kai hannunta kan kafaɗarsa.


"Baby" 


Bai ma san tana yi ba, bare har ya kulata, hannunta ta dora akan kafaɗarsa, juyowa yayi cikin fushi ya daka mata tsawa har sai da ta ji ƴaƴan hanjinta sun kaɗa ta ja da baya, ta ji tsoro sosai, dan tunda suke bai bata taɓa ganin fushinsa ba, kuma yanzu da ta ga yana fushi tayi zaton yauƙinta zai sa ya sauko, fuskarsa ta kalla ganin yadda tayi ja sosai yasa ta ƙara tsorata, jikinsa sai rawa yake yi, juyawa tayi da gudu ta fita daga falon ta nufi hanyar bakin fate ko mayafi babu bare takalmi, tana ihu tana kiran mai gadi ya buɗe mata gate, ganin yadda take a firgice yasa mai gadi yayi saurin buɗe mata gate ɗin ta fita.


A ɓangaren Nazeer kuwa akan kujera ya zube yana sauke numfashi da karfi da karfi, abinda Khadija tayi masa yau yayi matuƙar ƙona masa rai, wannan dalilin ne yasa ya ƙuduri aniya a zuciyarsa cewar sai ya ɗauki fansar abinda tayi masa yau sai ya haɗa mata tarkon da sai ta yi danasanin haihuwarta da iyayenta sukayi.


****  ****  ****


"Usaina! ke Usaina kina ina ne?" Asabe ta shigo ɗakin tana kwaɗawa Usaina kira fuskar nan babu alamar murmushi tamkar bata taɓa murmushi ba, chan ta hango Usaina a ƙuryar ɗaki a kwance tana ta faman juyi, Ilham tana zaune kusa da ita tana kuka, Ilham ta juya ta kalli Asabe wacce ta nufo inda suke a fusace, miƙewa tayi da sauri tana cewa "Mama ki taimakawa Mommyna cicinta ke ciwo tun yanzu" Ilham ɗin tayi magana cikin gwaranci, wani irin uban mari Asabe ta ɗauketa dashi Ilham ta faɗi ƙasa wanwar har kanta sai da ya gwaru da ƙasa, "dan uwanki ni zaki cewa na taimakawa wannan shegiyar uwar ta ki, kin ga alamar tausayi a tattare da ni, to ba ciwon ciki ba, ko da jikinta ne gaba ɗaya ba lafiya ana ɗagata ana kwantar da ita ba zan taɓa tausaya mata ba, domin tun da na tashi na tsani na ga ana taimako, bare ita da ta aure min miji" tana kai wa nan ta komar da kallonta kan Usaina tana cewa "ke kuma tsohuwar munafika, kin wani kwanta kina burgimar munafirci ki tashi ki je ki wanke min kaya kuma kiyi mana wanke-wanke" Usaina bata iya cewa komai ba, ta fara yunƙurin tashi zaune, Asabe cike da mugunta ta fincikota, ta dinga janta a ƙasa har sai da suka fita tsakar gida sannan ta saka ƙafa ta turata wanjen uban kayan da ta fito dashi nata da na yaranta, tace "kuma wallahi ki tabbatar kin wanke ya wanku sosai dan idan ma kika yi amaja sai kin sake, kuma bamu da ruwa a gidan ki je ki ɗibo a fanfo ki cika mana ko ina na gidan, sai kuma ki ɗibo ruwan da zakiyi wanki dashi" Usaina ta juyo tana kallonta cikin rawar murya tace "A gaskiya ba zan iya ba, baki ga halin da nake ciki ba ne, ban da lafiya cikina yana ci......." Dukan da ta ji an rufeta dashi ne yasa bata iya ƙarasa maganar da take son faɗa ba, Habu ne wanda shigowarsa kenan gidan ya ji abinda Usaina take faɗa, kanta ya kama ya dinga gwarawa da bokitin ƙarfe, abinka da farar fata nan take goshinta ya fashe ya fara zubar da jini kamar fanfo, Ilham ce ta ƙaraso wajen tana ƙoƙarin cire hannun Habu daga kan Mummynta tana kuka tana cewa "kai ka sakin min Mummyna" ganin yaƙi saki sai gara mata kai yake, yasa ta daddage ta gantsara masa ciwo a hannu, Habu cike da azaba ya saki wuyan Usaina yana yarfa hannu, fuskarsa a murtuke yana kallon Ilham wacce ta faɗa jikin Usaina tana kuka, Asabe kuwa cike da zuga tace "Kutumar uba, lallai Habu ka auro karfa,gashi nan suna ƙoƙarin su illata ka a banza, kalli yadda hannunka ya kumbura wannan sai kace mayya" Habu cikin fushi ya miƙe ya shige ɗakinsa, ko second 3 bai yi da shiga ba ya fito hannunsa riƙe da wata bulala murtukekiya, irin ta dukan jakuna, yana zuwa ya shiga zabga musu ba ji ba gani, Usaina ganin yana ƙoƙarin ya kashesu ita da Ilham yasa tayi ƙarfin halin riƙe bulalar, Ilham kuwa da ta sha duka dan har ta fara fita daga hayyacinta ta kwanta a ƙasa tana jan numfashi tana kuka, Usaina kuwa miƙewa tayi tsaye duk da irin yadda jikinta yake yi mata rawa amman a haka ta dake ta tsaya tana kallon Habu ido cikin ido "Habu abinda ka ke yi mana ya isheka kuma, ni ba jakarka ba ce kuma ni ba ƴar aikinka ba ce, wallahi Habu ina faɗa maka idan har ka cigaba da dukana ni da yarinyata to za'a kwashe ƴan kallo domin za'ayi duk wacce za'ayi dan daman ni ba sonka nake ba, dan na rabu da kai babu abinda zan ji a zuciyata" Habu yayi murmushin mugunta tare da sakin mata bulalar yana cewa "Lallai ƴar talakawa har kin isa ki kalli cikin idona ki dinga faɗa min maganar banza" Usaina tace "an faɗa maka ɗin" Girgiza kai ya shiga yi idanuwansa suka kai kan ruwan dattin da yake cike cikin babban bokiti sannan ya dawo da kallonta kan Usaina kanta ya riƙe ya daddage ya dannasa a cikin wannan bokitin ruwan dattin, Usaina ta shiga ƙoƙarin ƙwatar kanta amman ta kasa kwacewa daga riƙon da Habu yayi mata dan kuwa ya riƙe kan sosai, gaba ɗaya karfinta ya ƙare, shi kuwa Habu babu imani a zuciyarsa ko kaɗan Asabe kuwa bata yi yunƙurin hanashi ba sai ma zugashi da tai tayi akan ya danna mata kan sosai domin ya koya mata hankali, Jikin Usaina ya saki gaba ɗaya ta daina motsi, Ilham kuwa bata san inda kanta yake ba, nishi kawai take yi.


"Assalamu alaikum" Hassana tayi sallama gidan, idanuwanta ta zazzaro ganin Habu yana ƙoƙarin kashe mata ƴar uwa, ashe daman shiyasa tana zaune a gida ta ji hankalinta gaba ɗaya ya kasa kwanciya, ta ji tana son ganin halin da ƴar uwarta take ciki, ashe abinda ke faruwa da ita kenan, da gudu ta ƙaraso inda Habu yake ta ɗauki wani bokiti ta maka masa a goshi a gigice ya ɗago yana kallon Hassana, ita kuwa huci kawai take tana yi masa kallon azzalumi ɗago Usaina tayi daga cikin ruwan ta kwantar da ita, sannan ta dawo da kallonsa kan Habu tana cewa "Kashe min ƴar uwa za ka yi, to wallahi ka saka wannan a ranka idan har Usaina ta mutu wallahi na rantsi da girman Allah sai na kasheka har lahira domin ba zan taɓa barinka a raye ba, daga kai har matarka ba zan barku ba, kuma ka jira ka ga abinda zai biyo baya sai na kai ka ƙara sai an bi wa ƴar uwata haƙƙinta ba ɗan gidan Alhaji Sule mai siminti ba, ko ɗan gidan Alhaji Sule mai barewa ne sai na tabbatar an ɗauka a gidan yari"✍🏾



Anya kuwa Usaina bata mutu ba?


Shin burin Hassana yana cika kuwa ana ɗaure Habu?


Ya zata kasance tsakanin Khadija da Nazeer? anya kuwa Nazeer zai yi nasarar ɗanawa Nana Khadija tarko kuwa?


Duka waɗannan tambayoyin zaku iya samun amsoshinsu a next page💃🏼.


#Comment

#Share

#Free book

#Book 1



*DIJARTY ƳAR MUTAN ZAZZAU💜*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol