Free chapter · Read without an account
chapter 10
by Zainab Yerima · MURADIN RAI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*_
_this page is for you my *khadious❤️* I love you so much💞_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
10📚
Tashi sukayi suka tafi bayan ya harun yagama cika mata ciki da kalaman soyayya, tun tanajin bugun zuciya harta farajin nishadi… koda suka fito gida yakaita direct don tasan zeezee zata iya gane halin da take ciki.
Suna zaune acikin mota shida farida hoton ya shigo mishi.. nuna mata yayi yace kinsan waye wannan? Yana nuna na mijin… ƙanƙance ido tayi tana mishi kallon tuhuma, yayan zeezee ne, meye haɗinka da mardiyya? ɗagowa yayi tareda ware hannu yace mata nothing… kawai anturo min ne, kanta ta kawar tana wani huci zuciyar ta na tafasa, hannu yasa ya kama haɓar ta ya juyo da fuskanta, matso da fuskan shi yayi daf da nata har suna shakan numfashin juna yace, look baby waƴanda suka turomin sun ɗauka muna tare ne, amma kema kinsan babu abunda zanyi da ita, cikin wani irin yanayi yake maganan tareda yawo da hannu shi a wuyanta, turarenta yana kara birgita mishi kwakwalwa. A hankali yakama leɓenta yana tsotsa kamar wanda yasamu minti take ya mantar da ita wannan maganar…
Bayan tagama duka shirye shiryen ta na bacci ta kwanta amma sam bacci yaki zuwa mata, kalaman ya harun ne suke ta yawo a kunne ta, murmushi tayi tareda juya baya sannan tace dagaske waini ya harun yakeso?.. kirjinta ta dafa sannan tace tayaya zan fara soyayya da ya harun… idon ta ta runtse tace gaskiya inajin kunyan shi… bana tunanin zan iya, to me zance mishi kenan? Ya harun kayi haƙuri bazan iya soyayya dakai ba… no bazan iya faɗa ba sai yafi zama abun kunya, tunda shi ya cire duka kunyan shi yagayamin abunda ke ranshi idan nayi haka zansa ya tsani kanshi….
Karan shigowar message taji, tana buɗewa taga sako kamar haka:
_nakasa bacci my mardeey, soyayyar ki kara fisgana yakeyi, banajin zan iya wani rayuwa babu ke… please kiyi tunanin wajen yanke hukunci akaina…. Sai naji daga gareki_
Ajiyan zuciya ta sauƙe sannan takashe wutan ɗakin.
Washegari haka kawai taji tanajin kunyan zuwa gidan su zeezee.. don haka bata fita ba, shi kuwa tun safe yakesa idon ganin ta amma shuru har ya kasa hakuri ya tambayi zeezee. Message ya mata yace
_yau ba zaki shigo bane? to ni Zanzo yanzu inason ganin ki.._
_No kabari zanzo nan minti talatin_
_Ok ina jiran ki, I miss you_
Murmushi kawai tayi tagama abunda takeyi.. abaya tasa grey color as usual babu wani kwalliya a fuskar ta banda powder data shafa sai man baki… saidai kuma hakan yafi fitar mata da asalin kyawunta.
Tun safe farida take shirye shiryen dawowan ya Abbas… mama kam binta da kallo kawai takeyi aranta tace kodai yaran nan soyayya sukeyi ban sani ba? Allah yasa dai ba ita kaɗai take haukan ta ba.
Sosai ta tsaya wajen sa me girkin su ta haɗa mishi abinci kala daban daban da drinks kala kala.
Tunda ta shiga gidan zeezee tagane sam taƙi sakewa da kowa, bayan azahar yaya harun yagama shirin shi na tafiya amma sam bayason ya tafi baisan matsayin shi agun mardiyya ba don haka duk jikin shi yayi sanyi..
Kiran ta yayi a waya yace tazo site ɗinshi kuma ita kaɗai, sam tadage wai ita kunya takeji, daƙyar ya shawo kanta taje.
Tunda tashigo ya kafeta da ido duk yazamo wani abun tausayi… a hankali yace mata mardiyya zan koma kd, bakice min komai ba..
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da en yatsunta, yanzu ita meyakeson tace mishi, to yaya zatayi ne? katse mata tunanin yayi da cewa idan har kinga bakyajina aranki please karki ɓoyemin… I’ll maintain my position, I will forever be ur brother.saidai kuma bazan taɓa daina sonki ba kuma bazan sare ba…
Ita da zeezee suka rakoshi har waje saida sukaga ɓacewan shi suna kokarin komawa ciki sai ga motan ya Abbas tsayawa sukayi shima parking yayi ya fito dukansu da fara’a ɗauke a fuskan su daga shi har su, zeezee ne tafara cewa oyoyo ya Abbas mu muka fara ganin ka… cikin farin ciki yace nima naji daɗi da ku nafara gani ina shigowa, mardiyya ce tace sannu da dawowa ya Abbas… cikin nutsuwa ya kalleta yace yauwa, da fatan na sameku lafiya? Lafiya kalau suka ansa… sannan yace naga kamar zaku shiga gidane kar in riƙe ku… umh muyiwa ya harun ne rakiya zamu koma gida, a ranshi yace thank God da bamu haɗu ba… haka kawai yaji aranshi bayason ko ganin ya harun ɗin nan...
alright bari in karisa gida… kahuta gajiya haka sukayi sallama.
Yana shiga da farida yafara cin karo a falo ta tsantsara kwalliya kamar me zuwa gidan biki ta gyara ko ina ta cika gidan da kamshi daga ita har falon komai yayi kyau, duk kiyayyar ka da ita dole ka yabawa gayen ta.
Da sallama ya shiga falon kamshin turaren wutan da ya daki hancin shi shiyasa shi lumshe ido buɗe idon shi da zaiyi suka sauka akanta wannan shine lokaci na farko dayaji zuciyar shi ta buga akan farida, don haka da sauri ya kauda kanshi akanta, kafun ya ankara har ta taso ta iso wajen shi, kawai jin hannu ta yayi acikin nashi, ta wani matso daf dashi… sannu da dawowa ya Abbas, nayi farin cikin sake ganinka, dan kwana biyu nan jinsu nayi kamar sati biyu… cikin wani irin salo na yanga da shagwaɓa take maganan tareda narkewa … damke idon shi yayi sosai don turaren ta bakadan yake birkita mishi lissafi ba…
Zame hannu shi yayi acikin nata a takaice yace mata thanks sannan yasa kai zai wuce ɗakin shi, cikin hanzari tasake riko hannu shi tareda cewa ya Abbas all this are for you falon da ita kanta da dinning take nuna mishi, tun ɗazu nake jiran zuwan ka, nasan yanzu kagaji amma inka huta please kazo kaci abinci, kai kawai ya gyaɗa mata sannan yawuce… yana shiga ɗakinshi ya tura kofan ya jingunu a jiki yana sauke ajiyar zuciya a fili yace wannan wane irin bala’I ne yarinya kamar aljana, wayan shi ya ciro ya ƙira nabil, yana ɗauka yace mishi abokina yah? ka iso ne? eh nadawo dan Allah kazo mu kwana please… dariya nabil ya fashe dashi don yanzu ya gano yawanci Abbas na neman shi idan yanason ya gudu a hannu farida ne… zanzo don nasan amaryar mu zatayi ma tarɓa na musamman, tsaki Abbas yayi ya kashe wayan.
mamace ta Ƙira farida a waya, ɗakin ta tawuce, tana zuwa taganta rai a ɓace sai sintiri takeyi, lafiya mama gani?.. cikin ɓacin rai tace farida meye kike tunanin kinayi? Ashe bakida hankali har haka? Duk abunda kikeyi ina kallon ki… karki yadda kizamo sakarai acikin mata, tayaya zakiyita cusa kai wa na miji, bakisan kina zubar da darajar ki bako? Kinada kyawun da za’a so ki, amma tsabar rashin nutsuwar ki da kamun kai bazaki taɓa barin na miji yaji sonki ba saidai ma ki koya mishi tsanan ki…
to yanzu mama meye nayi, don kawai nayiwa ya Abbas sannu da zuwa… rufemin baki nace shashashar banza… juyawa tayi tana tafiya tana gunguni… oh ina cikin miki magana zakisa kai ki wuce kibarni ko? Lallai farida kin girma.
baifi minti talatin ba saiga nabil... Lokacin yafito a wanka yana goge kanshi… zama nabil yayi tareda cewa duka acikin shirin dawowan mu ne naga an wani gyara falo kamar na amarya… daina goge kan yayi ya zauna akan kujera guda ɗaya dake ɗakin, yace seriously nabil bana ganin zan iya jure ɗabi’un farida… abunta kara tsanani yakeyi kaga dai ba wani shiga hidiman ta nakeyi ba amma yau farida har ta samu ƙarfin gwiwan riƙe hannu na… wani irin fito nabil yayi sannan yace kaidai mutumi na kawai kabada kai bori ya hau, karka haukata yar mutane, Allah yarinyan nan tanason ka dayawa tunda har bata iya controlling feelings ɗinta, dondai ta tsaneni ne da nazamo mata chief advicer dana koya mata yadda zata riƙeka ba tareda kasani ba, hararan shi Abbas yayi, shi kuma yakashe mishi ido ɗaya, nabil ne yaci gaba da cewa matsalar ta ɗaya rashin kamun kai I swear farida indai haɗuwa ce ta haɗu…
tsaki Abbas yayi tareda tashi ya ɗauki rigan shi yana cewa kaima na lura kafara samun matsala, to bari kaji ingayama farida ko tazamo kamar hurul ayn ce wajen haɗuwa bazan so ta ba.
Fitowa sukayi tare dinning table tana ganin nabil taji ranta ya lalace, ya ɓata mata show, taso suci abinci daga ita sai shi tacigaba da nuna mishi irin son da take mishi… aranta tace duk da haka bazan fasa ba, suna zama ta kariso tana cewa bari inyi serving ɗinku, karki damu zamuyi da kanmu Abbas ya bata ansa… shikam nabil har sake baki yayi saboda baima taɓa tunanin haɗuwan ta yakai haka ba, zungurin shi Abbas yayi da ya juyo yace mishi, zata raina ka kasa kasa...
Ita kuma sosai ranta ya taɓu jin yadda Abbas ya gwale ta don haka ɗaki tawuce tafara sintiri tana saƙawa da warewa.
Bayan isha ya ƙira mardiyya, bayan sun gaisa yace idan bakya wani abu zanzo mu gaisa… bana komai ya Abbas, aima naso inzo inyima sannu da zuwa… to meya hanaki zuwa? Shuru tayi… yace is alright innazo zamuyi maganan.
Koda yaje yasamu itama ta haɗa mishi snacks… sosai yau sukayi taɗi har ya tambaye ta meyasa bata zuwa gurin farida saboda ya lura kamar basa shiri… bata ɓoye mishi komai ba tabashi labari tun yarintar su har zuwa yanzu…. Yasha mamaki dahar farida zata daina kula mutun akan saurayi…
cikin nutsuwa yacewa mardiyya amma dai kinsan gaba bakyau ko? Kai ta ɗaga mishi halamun eh sannan tace aini ban daina kulata bs don har yanzu ina mata magana itace bata ansawa… haka dai sukayita hira cikin fahimtar juna, da zai tafi tayi packaging samosa da springrolls masu yawa tabashi, yaki karba amma tace mishi shi tayiwa idan har bai karba ba batasan yaya zatayi dashi ba, yaji daɗin jin haka sosai cikin farin ciki ya karɓa…
Tunda ya koma yasa snacks ɗin a gaba, banda murmushi babu abunda yakeyi.. nabil ya mishi magana yakai sau uku bayajin shi… ganin yayi nisa a tunani ya ɗauke abun gaban shi… da sauri yace lafiya… leƙa cikin snacks ɗin yakeyi sosai, me kake nema haka aciki inji Abbas, ina dubawa ne ko mardiyya ta haɗa da hoton ta aciki ne…
girgiza kai Abbas yayi sannan ya mike yana cewa kaidai kullum labarin ɗaya soyayya, duk macen dakagani dani babu wani labari saina soyayya…
Katseshi nabil yayi dacewa, Abbas shifa so baya ɓuya basai anfurta shi ba yake bayyana, bari inbaka misali meyasa yau duka abunda farida tayi bakaji daɗin shi ba saina mardiyya…
Ware hannu shi yayi tareda cewa look nabil farida fa kanwata ce…. Zan iya kiran ta ma ince tamin duk abunda nakeso, kallon tuhuma nabil ya mishi tareda harɗe hannu shi a kirji yace umhum… mardiyya kuma waye ɗinka ce, ɗan daburcewa yayi don ya lura nabil na ƙoƙarin sa mishi magana a baki… a hankali yace itama kanwata ce and also a friend, a hankali ya faɗa… murmushi nabil yayi tareda buga kafaɗan Abbas yace abokina karka ruɗi kanka ita zuciya da kake gani ba’a hanata abunda takeso… with time kai da kanka zaka gayamin komai…
Kokarin cire rigar shi yakeyi sannan yace koma dai meye ne kafi kowa sanin da banbanci tsakanin farida da mardiyya, bana musu kallo iri daya a idona saboda komai nasu ya banbanta.
Bayan ta fito daga wanka tasa kayan baccinta wani hand cream take shafawa a hannu ta taji halamun shigowan text tana dubawa taga WhatsApp chat ne daga ya harun,
_Salam my mardeey na isa lafiya, dafata kina lafiya? Naso inkira ki sai kuma nayi tunanin kar in takura miki don naga dare yayi.._
Goshin ta dafa tareda cewa oh Allah… bad me, I even forget to ask him ka isa lafiya.
Take ta rubuta mishi..
_i’m sorry ya harun naso kiranka sai abubuwa suka shigemin gaba, mashaa Allah tunda ka isa lafiya._
_Lafiya kalau…. Mardiyya banason yakasance na ta kura miki, amma zuciya ta ta matsu dajin matsayi na agunki, banajin yau ko bacci zan iya… dan Allah idan kin amince dani kituromin wannan smiley 🥰, idan kuma No ne kituromin wannan 😔.
*ZEETY DELIGHT*💖