Free chapter · Read without an account

DUK TSANANI 1

by Khadija · DUK TSANANI

[5/10, 3:31 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

    [Yana tare da Sauk'i]


 By Mmn Amatullah


Paid book 200

Free page

    Phone number ***



*Sadau karwa* Nasadaukar da wannan shafin ga duk kan masoya na a duk in da kuke inasonku irin over dinnan Allah ya bar zuminci,Ameen..





 Chapter {1}


  Kuka take kamar ranta zefita, duban ta Salma tayi cikin sanyi murya tace " *Yayah Nasreen* kiyi hak'uri ki bar wannan kukan Haka kada kuma wata matsala tazo ta sameki bayan wacce mike ciki,kitina fa cewa kullum kece kike bamu hak'uri akan ahalin rayuwar da muke ciki,kitina *yayah Nasreen* kullum kina fad'a mana cewa *DUK TSANANI* yana tare d sauki."


"In kina wannan kuka kina kara karyan mana da zuciyah,sannan kinsan indai kina cikin wannan hali Mama baza ta tab'a dena tinani ba kuma kinsan halin da take ci,mune kadai farin cikin ta mune muke kawomata jin dad'in a rayuwar ta ."



  "Kuma kinsan yawan tinani zai kaiga jikinta y tashi,Dan Allah, Yaya Nasreen ki k'arfafa zuciyarki duk d nasan abun d wahalah Amman ki daure ko Dan samun farin cikin Mama d walwalar ta"....


•••••••

"Tabbas nasan abin da ciwo kumah abun da kamar wuya mu manceshi nan kusah, Amman duk da Haka yazama dole mudanne ko Dan lafiyar Mahaifiyarmu"..


 Ta karashe maganar Tana sake du ban Yayar Tata..


••••••

Tabbas kamar yan d Salma t fad'a abin d ciwo had'e da takaici gami da tozarta amman, yazama dole su Dan gana subarwa, Allah danshi zaiyi musu maganin wannan matsala d suke ciki,..

  

 Duk wannan maganar tanayi ne a cikin zuciyarta,Kafin ta dubi k'anwar tata..


•••••

Rinannun idanunta ta d'ago ta dubi k'anwar tata, cikin kuka ta ce, "Salma waishin nika d'ai ce,"ya da irin haka taketa faruwa dani? shin Salma wannan wacce irin masiface? Haka take bibiyar mu da wanne zamuji da wannan masifar ko d habai cin mutanan gidannan,ko d n "yan unguwar nan?,shin Salma wai,meyasa haka bata faruwa a kan kowa,sai ni? Meyasa! Salma Meyasa!! Meyasa!!!," ta k'arasa maganar tana kara fashewa d kuka mai cin rai,...


••••••

Duk yan da Salma takai ga danne zuciyarta Dan kar tayi kuka arasa mai rarrashin wani sai, sai da hakan ta gagara ta fashe da kuka tare da rungume yayar tata,suka cigabah da rera kukansu, abin ganin ban tausayi..


•••••••

Dakyar Salma tasamu t tsai da nata kukan,tare d cewa, "Haba Yaya Nasreen kidena fad'ar haka,manah duk abin d yake faruwa da mu Allah ya na sane da mu kuma shi zai kawo mana karshenta"..


 "Wannan lamarin addu'a kad'ai yake d bukata,plz sister kishare hawayanki,muje daki wajen Mama,itamah tana chan tana kuka,kuma kin san in da muwa tayi mata yawa akwai matsala''..


••••••••

Da sauri,Nasreen ta dago rinannun idaninta wa in da suka rine sabi d kuka t kalli Salma tare d cewa, "kina nufin Mama tin dazu tana d'aki tana kuka? "Kwarai kuwa,kuma ganin murmushi a kan fuskarki kinsan shikad'ai ne zaisa Mama taji sanyi a zuciyar ta"..


*****

 Tabbas tasan hana shi ne kad'ai zai ragewa Mamansu yawan damuwar d ke ranta,Dan ta tabbatar suka dai ne,suke bata farinci,awannan rayuwar da suke, ciki,.


•••••••••

Da sauri ta goge hawayanta tare d kama hannun Salma suka nufi dakin Mamansu,da Sallamah sukashiga tana zau ne,a gefen gado,tana sharar kwallah,da sauri duk subiyun suka karasah,in da take,...


••••••••

Hannu Nasreen tasa tana gogewa Mamansu hawayen d ke zuba tare d guntin Murmushi wan da yafi kuka ciwo,kafin tace "Haba Mama Dan Allah ki daina kuka,haka kisani cewa duk wani Abu d yasamu bawa to to daga Allah ne,kumah babu wan d ya Isa ya gujewa kaddararsah,mama mudauka cewa wannan itace,tamu k'addarar rayuwar, Mama kisani cewa DUK TSANANI,yana tare da sauk'i,kuma Allah be manta da muba yana sane da mu,shi ya Dora mana kumah shi ne ze yayaye manah"


  "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalinki,kicire damuwa daga ranki tamkar wani Abu maka mancin Haka betabah faruwa ba,kinsan farin cikinki shi ne namu,Dan Allah Mama kiyi mana murmushi ko maji sanyi a zuciyoyin mu",t karasa maganar ta na murmushi wan da be kai zuciba....


•••••••

Duban su mama tayi tare da cewa "Haba Nasreen kinsan, wannan abun abune me Kamar wuya mumanta da shi,shin ko kinmanta anyi abinnan baso d'aya ba ba sau biyu ba har sau uku,me kike tinanin,mutane zasu dingaa kallonmu da shi?..


•••••••

"Nasani Mama Amman kamar yan da nafad'a mu dauka,tawa kaddarar kenan,kumah Allah yana sane da mu shizai kawo mana karshen wannan lamari d yake t faruwa d ni, Amman Dan Allah kid'anyi murmushi kinji Mamarmu",murmushi tayi har tanajin kasko 30/% nadamuwar t yasauka,.....


Yawwa mama harkinsah munji dad'i


My fans kuna ganin wanne abune HK y faru d Nasreen,haka,har sau 3,? 


Plz Banason hrt ko tnx comment kawai nakeso,Dan shikadai ne zai bani kwarin guiwar yimuku typing😉



     Plz share fisabilillahi😘



👉🏻 *Mmn Amatullah CE*

[5/10, 3:45 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

     [Yana tare da sauk'i]


        

   By Mmn Amatullah     


   Paid book

     Phone number ***.


Chapter {2}


  Duk kansu murmushi sukayi wan da yafi kuka ciwo,..

Suna cikin wannan halin suka jiyo muryar Mahaifinsu a parlour yana kwad'awa Mama kira,"Habibah! Habibah!! Habibah!!!"



Cikin hanzari duk kansu suka nufo parlour, tsaye suka samesa yana ta huci kamar wani zaki,..


Mama ce tai k'arfin halin tambayarsah,murya adakushe,baki narawa ta ce,"Al..ha..ji lafiya kuwa?


  A hasale ya dubeta tare d cewa,"Auke har tambayata lafiya ki ke?Nunata ya yi da yatsa tare da cewa Habibah Wallahi kikiyayeni nagaji da wannan iskancin da kukeyimin acikin gida,kuna nemah,Ku mai dani karamin mutin,agari anamin kallon banza..


To Wallahi barikiji na fad'a miki,anyi nafarko anyi n karshe,daga yau ba za kusake sawa na Tara mutaneba,sannan ango yazo yace ya fasa,to Wallahi bazeyuwuba,kinji n fad'a miki.."


 "Ko dan kinga anyi na Fako anyi na biyu duk ban d'auki wani matakiba,na zuba muku ido shiyasa yanzuma,kuka sake,kwatawa,sabi da ke baki da mutinci ko?


"Sabi da nasan duk wannan kulle_kullen kekike kullah sa sabi da bak'in halinki"


 Tin da yafara fad'a babu wan da ya dago acikinsu,balle ya tanka,har sai da yazo dai-dai wannan gabar,da yake cewa,Mama ce take sanadin duk da akefasa auren sabi da bak'in Halinta,..


  Dagowa tayi ta dubesa,rai ab'a ce,tafara da cewa,"Yan zu Alhaji kai da bakinka kake fad'ar wannan maganar a kaina kamar bakasan halina ba,kada kamantafa tin auren saurayi da budurwa,babu wani hali nawa da baka sani bah,Haka nima sannan in ka manta bari na tinamaka,kazo gidanmu Neman aure nane sabi da tarbiyan gidan mu"


"Sannan da kake maganar ina da sahannu akan fasa auren "yata da akeyi,har sau uku,aranar daurin aure bayan muntara jama'a

  Katab'a ganin uwar da tayiwa "yarta,haka ko da a labari ne?,Ai burin kowacce uwa be wuce ta ga ta kau da yaranta daga gabanta,bawai ta sakasu agaba tana kalloba.."


"Sannan Abu na karshe ni banazargin wani ko wata,akan duk abin da kefaruwa,a cikin rayuwar Nasreen ba mun daukesa a matsayin kaddarar rayuwar ta ce,haka kuma da sannu Allah zaiyimana maganinta"



A wulak'ance ya sake dubanta bayan yaji tayi shiru ya ce "Oho duk kekika San wannan dan ni be dameniba,sannan kekuma na dawo gareki, yafad'a Yana nuna Nasreen da yatsa,yace "Nabaki nan da Dan kankanin lokaci kifitomin da mijin aure tin da kun hada baki kuda uwarku kunkori wa " yan chan,idankumah ba haka ba to Wallahi kowa na samu zan aura miki,Dan ba za ki cigaba da zaunamin agida babu aureba,kece babba Amman,duk k'annanki sunyi aure,sai ke kina zau ne,agida,to ya isheni HK kinji n fad'a miki" yana kai wa nanan ya fice Daga parlour'n yana huci..


•••••••••

Durkushewa tayi a wajen tasakin wani d'an marayan kuka,wannan wacce irin,k'addara ce?me datsewa mutin farinci,wannan wacce irin rayuwa ce? mikeyi mecike da wahala Ya Allah, Kai ne Allah kakawomana d'auki a cin rayuwar mu, Ya Allah kakawo mana karshen wannan matsalolin" Ta karasa maganar tana kara fashewa da kuka me cin rai...


•••••••••

Cikin Mama da Salma babu wan da ya yi yunk'urin hanata Dan kukan da zatayi shi ne ze rage mata wani radad'in d ke cikin zuciyarta,......


•••••••

Sai da tayi me isarta tayi shiru,matsowa tayi kusa da Mama ta kamo hannuwanta tana cewa, "Mama Wallahi na gaji da wannan rayuwar da muke ciki ayanzu na gwammaci mutuwata da wannan rayuwar" da sauri Mama ta rufe mata baki had'e da cewa, "Kul kar na sake jin irin wannan maganar a bakinki, Duk tsanani yana tare d sauk'i addu'a'u saiful mumini,ita zamurik'e miyitayi Babu dare Babu rana har Allah ya kawomana karshen wannan, damuwar da mike ciki,......tashi maza jeki ki dauro alwalah kije ki kaiwa Allah kukanki" mikewa tayi ta nufi d'akinsu, Salma ta rufa mata baya, mama t bisu da kallo cike da tausayawa,......


••••••••••

  Da yake har yan zu gidan akwai ragowar mutanen d sukazo biki,basu gama tafiya ba,,suna zau ne dg d'aki,sunajin anata habai ce habai ce,....


••••••••••

Muryar Hari suka jiwo wato daya data cikin kishiyoyin Mama kenan tana cewa,"To aiku bakusan wani Abu ba kunsan cewa gidannan masu farar kafa sunyi yawa,saifa mun tashi tsaye munnemawa "yayan mu magani,tin kafin suma ahanasu aure,tin da kunsan Babu abin d ba zata iyaba,ta hana " yayantama balle nawasu"


 Balle mu d akaga "yayan mu sunyi aure sunachan gidajen mazajensu,kunga ai dole mutashi tsaye kar susako mana yara a gaba",..."yan wajen suka amsa,da maganarki haka take,ya kamata mu tashi tsaye tinkafin sumamaye mu...


•••••••

Hari ta kara da cewa "ku dai kuga mutin kawai,yadinga simi_simi,kamar na Allah nan kuwa zuciyar bak'a ce," tini "yan wajen suka dauka da shewa,Tare d cewa kumafa haka ne " yar uwa,zancenki babu kuskure ko gyara,dariya suka karakwashewa d itah,...


•••••••••

Duk abin d suke fad'a kaf akunnan su, Salma ce ta mike a fusa ce zata fita Mama,ta dakatar da ita...



Plz share fisabilillah



Ummu Amsad

[5/10, 4:03 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

      [Yana tare da sauk'i]


 BY Mmn Amatullah


Paid book 200

  Phone number ***


Chapter {3}




   Mama ta dakatar da ita tare da cewa "Salma,da kata ban aikekiba karkisake kije ki tanka musu kibarsu da halinsu"


Tsayawa tayi chak rai, ab'a ce,tace ''Haba, Mama kina jin fa abin da suke fad'a, Wallahi ki kyaleni naje na koyawa mata hankali,ai Dan sunga,kina kyalesu ne shiyasa suke mana wannan cinkashin"


 Amman Wallahi nikibani damah dai-dai nake da kowacce shegi....Mata"


Tin da tafara magana Mama take kallonta cike da mamaki,ko da yake dama tasan halin Salma ba Dan tana hanataba,da kullum sai anyi fad'a da itah acikin gidan,dan bata da hak'uri,bakamar Nasreen ba...



  "To duk naji marar hakuri,ni ban aike kiba,ba dai magana bace ta fatar baki,kumah bata fitowa,mutin ajiki,sannan kinsan duk abin da suke fada ba haka bane,to sai me kuma ki kyalesu suyitayi mana"


•••••••••

"Amma meye amfanin ki biye musu kuyita chachar baki,Sam ba shi da amfani,sannan kinsan bazan laminci HK ba.....


•••••••••

Salma dai ba Haka tasoba amma babu yan da ta iya dole,ta hak'ura ko Dan ta bi,umarnin Mamansu,ammah taso Mama tabarta taje ta gasa musu magana,wacce zasu jima suna tinanin ta,ammah babu komai idan kere nayawo zabo na yawo watarana dole za'a had'u....


•••••••••

Komawatayi ta zauna suka cigabah da fuskantar abin da ke gabansu,.........wannan kenan


____________________________

*Asalin su Nasreen*


Maihaifinsu haifaffan kano ne mahaifiyarsu,haifaffiyar katsina ce,....


Alhj,Ayubah Aliyu shine chikken sunanan sa,shi Dan kasuwa ne,merifin asiri, dai-dai gwargwado,..


Sun hadu da Habibah wato mahaifiyar su Nasreen,a kano tazobiki tin daga wannan lokacin daya kyalla ido ya ganta ya lik'emata,duk da bata basa fuska ba a wannan lokacin hakan baisa ya hak'uraba har sai da yagano gidansu,.....


Betsaya wasa ko b'ata lokaci ba,ya gabatar d Kansa ga mahaifanta,cikin ikon Allah suka yaba da nagartassah,suka basa dama don su dai-dai ta Kansu,babu wani b'ata lokaci ya shawo kan Habibah har ta aminta da shi,.....

••••••••

Ba'a wani b'ata lokaci,ba akasha biki in d Amarya ta tare a gidanta dake cikin garin kano,a unguwar sheka,....

Sosai suke nunawa junansu k'auna,musamman bangaran yakub,....


•••••••••••

Cikin ikon Allah sai d suka shekara 3,da aure sannan,Allah ya azurtasu d samun karuwa,kafin wannan lokacin babu irin tsan kwamar da batasha bah gurin dangin miji cewa wai bata haihuba juya ce ya karo aure,shi dai kwata_kwata Yakub baya tan ka musu,...


•••••••

*(Wai mutane sai su dinga mancewa,da cewa haihuwa ta Allah CE,shiyake ba da itah a duk lokacin da yaso kuma,ga wan da yaso,bawai mutinne kebawa kansa ba,Allah y ganar da mu, ameen)*


•••••••••

Sunyi farin ciki sosai da kyautar "yamace d Allah y basu," ya kyakkyawa son kowa k'in wan da yarasa ga farin jinin muta ne,ranar suna ta zagayo yarin y taci sunanta Nasreen,sosai sukayi shagali,.....


••••••••

Tin da Nasreen ta taso tatashi cikin soyayyar uwa d uba dan babu irin gatan d mahaifin ta baya bata,sosai suka shaku da shi da itah,.....

••••••••

Wasa_wasa har sai Nasreen ta shekara 3 amma babu alamar wani ciki,nanfa akafara tsegunguni,wani lokacima,har tar ta ake da maganar,cewa,har yanzu ta kasah kara haihuwa,kuma ta kanainaye miji ta hanasa ya k'ara aure,,,dayake Habibah ba mai son tashin hankali ba ce,shiyasa bata, tab'a tanka musu ba,da,haka suka k'ara samun damar yimata duk abin da suka ga dama......


•••••••

Sosai abin yake damunta,Dan babu dama sabga ta had'ata da dangin mijinta,ko suzo gidanta sun dingayimata habaici kenan,har ta kai yanzu batason shiga,cikinsu,suna ganin hakan kuma sai suna komacewa ai munafinci ne,.......


•••••••••

Sosai take cikin matsin rayuwa ta b'angaran dangin mijinta,,,,ammah ban garan mijinta suna zaune lfy cikin so d k'aunar junah,......


•••••••

Ganin irin takurar da take fama da itah bata raguwa kullum sai kara karuwa take,,,,hakan yasa ta fara rokon Yakub da yakara aure,ranar da tafara zomasa da maganar sai da sukayi fad'a sosai,Dan gani yake kamar ta dai na san sa ne,........


••••••••••

Kullum tana naci tana kumah nusar d shi akan matasalar da take fuskanta akan HK,har ya amince,amma ba dan yasoba sai Dan farin cikinta,......


  Babu b'ata lokaci ya nemo wata budurwa mai suna, Harira,sabi da tak'ai tawa,suke kiranta da Hari Babu b'ata lokaci Amarya ta tare,,,.......

Bayan Amarya Tatare da wata 2,ta fuskanci irin kulawar da Yakub yake bawa Habibah da "yar,tah........

•••••••••

Kishi sosai take nunawa a fili,ganin ko ita da take Amarya baya dokinta da nuna mata kulawa kamar yan da yake basu,..tin DG wannan ranar,taci alwashin,ko t halin ya ya,sai ta kwace soyayyar da yake musu tare da kulawar nan ta dawo gareta,......


••••••••••

Tin DG wannan ranar ta shiga fafitikar Neman yan da zata,b'ullowa lamarin,tini ta nufi gidan kawarta larai,t zaiyya ne mata komai,hadda Karin karyah,,.gami da sharar,k'wallah,.....


•••••••

"Haba kawata ai ki kwantar da hankalinki,zankaiki,in da za'a ashare,miki hawayanki,in fada miki sha yanzu magani,yanzu" cike da zumud'i Hari tace ,"Allah kawata? "Wallahi kuwa" ",kai,shiyasa nake sonki" "To k'awata in ban mikibah wazanyiwa,ai zaman amanar kenan".


   "Yanzu k'awata yau she kikeso muje,ai k'awata da zafi_zafi ake dukan k'arfe,ai yau ya kamata muje ba sai gobe ba,ke Dan bakiji bakincikin da nakejiba inna,ga yana bawa wannan matar tashi kulawa,ita d wannan " yar tata mekama da Aljanu,jinake kamar na shakesu duka su mutu kowa ya hutah,".


••••••••••

  "Keni bakisan wani abu ba,kinga,wannan shegiyar "Yar tata nekama da Aljanu Wallahi nafi tsanar ta fiye da uwarta,kwata_kwata banaso na bud'e ido na ganta," ",ke da Allah ana babbakar giwa wayake jiyo k'aurin zomo",cewar,larai,ana ta uwa wayake ta "yarta, Hmmm,"Baza ki ganeba kawata"


•••••••••

Kinga bari na d'auko gyalena mutafi yammah nayi kar muyi dare a hanyah,,,,


Tafiyah sukayi sosai bayan sunsauka DG motah,kafin sukarasah wani zaure,wan da yake ciki biyu,zaure na farko matane birjik,akan layi duk,sunaso sushigah,sugah boka megani harhanji,sumah,layi sukabi,.......


*****

Sunjimah kafin layin yazo Kansu,shigasukayi,tare da cewa ahuwan kadai boka megani har hanji,meke tafe daku?,gafarta boka,dama kawata na kawo,tanaso kayimata maganin matsalarta,,,,


*(Wa'iya zubillah,Allah ka shiryar da mu shiriyah ma Dai-dai ciya)..





Ina godiya ga dukkan masoyana



Share fisabilillah



Ummu Amsad

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol