Free chapter · Read without an account

DUK TSANANI 5

by Khadija · DUK TSANANI

[5/12, 12:02 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

      [Yana tare da sauk'i]


By MMN AMATULLAH


 Paid book200 


   Free page


Phone Number ***.




Chapter 13}

     



   Ko da tashiga gida har an fara kiran sallar isha,,Dan haka ko da tashigo babu kowa,,A parlour,, kai tsaye d'akinsu ta wuce,,,,salma tatarar tana sallah,ita mq sallar,ta tayar ganin tana da alwalah...


••••••••

Yana fitowa kai tsaye masallaci ya nufa,bayan sun idar ne ya wuce gida da sallama ya shigo,,baba ne ya amsa masa,,tare da cewa "Aa Nasuru har kadawo? "Eh Wallahi Baba ai dama ba wani da d'ewa,,zanyiba" "To,to madallah","Baba ina Inna? , "Tana ciki INA tinanin bata idar da sallah ba ne,,dan nima yanbzu na shigo",zama ya yi sosai kusa da Baba sukafara firarsu irin ta tsakanin uba da d'a,,


•••••••••

"A'a Yaya Nasreen harkin dawo ne? Salma ta tambayeta,"Eh Wallahi na dawo" "to ya kukayi da shi da fatan dai kun dai-dai ta? Sallama ta fad'a tana, murmushi harara,, Nasreen ta wurga mata tare da cewa,, "Au daga zuwansa yau sai mu dai-dai ta" "Aa to Yaya Nasreen mezai hana haka tafaru" "to baki chan kaba,,Dan kuwa bamu wani dai-dai taba" "To shikenan,,na ji baku dai-dai ta ba to amman ai kya fad'a min ko da sunansa ne" "kinganki da tambaya" cewar Nasreen dariya Salma tayi tare da cewa "kai Antyna" ta k'arasa maganar Tana karyar da Kai alamar rok'o "To sunansa, *Nasrenllah* " "WOW,, Gaskiya Daga jin sunansa ma kun da ce,ko ke bakiji sunanba Yan da suka had'u,,*Nasreen,, Nasrenllah* Wallahi ya yi mugun had'uwa, Amman Yaya daga jin,yan da sunansa ya had'u,,shima, haka ya had'u ko? "Ke ni kin isheni da yawan tambayoyi,kinfa,san shi"

"Da gaske Autyna" Salma ta fad'a cike da zumud'i ,"Au da k'arya na ke yimiki" "Aa ni na Isa na ce haka,ai ban kai nan ba"...


  Ta sake bu d'e baki da nufin sake magana,,,mama ta shigo d'akin,du ban Nasreen tayi tare da cewa "Aa Nasreen yau she ki ka dawo? "AI Mama na Dad'e da da wowa lokacin kina sallah" "OK,bak'on naki har ya tafi ne? "Eh mama ya tafi" ,nan dai ta kwashe duk yan da sukayi da Nasrenllah ta fad'awa mama,ta karasa da cewa na dai cemasa ya bani kwana 2 zanyi shawara," Mama ta ce "Amma daga gani shi mutin ne na gari,,Dan a zamaninnan da samari suke karya gurin "yan mata,, Amma shi ya gwammaci ya fad'a miki gaskiyah ko kisosah ko akasin haka,,gaskiya daga jin haka natabbatar a kwai nagarta,a tare da shi,sannan,, ai ba irinsu ake hanawa aureba,,,tin da ai yana da Sana'a,,,,ai ace yau gaka baka da sana'a kuma kana Nema su ne abin gudu amma,, bame Sana'a ba, ko ya take yafi Mai zaman ban za Dan me nema Yana tare Da sa'a Dan hk ina baki shawara,,amatsayina na mahaifiyarki,,,kinutsu ki yan kewa kanki shawara mai kyau,,,in za ki soshi to ki soshi Dan Allah,,kar ki kalli sana'arsa ko abin da yake samu,,,dominkuwa,,shi arziki,da rashi duk na Allah,ne..

  Ammah dai kitsaya kiyi tinani sosai,,,akai,duk da dai nasan yarana,,bamasuson abin duniya ba ne,,,,,sannan karkiji inata wa" yannan magan ganin kice zaki so shi dole Aa,,kitsaya kiyi tinani inkinga be da ce da keba,,babu dole,,Dan kece,,za ki zau na da shi bawaniba,Allah ya temaka,ya kuma zab'a mafi Alkairi" duk suka amsa da ameen,..


•••••••••••

  Mama nagoda da wa"yannan shawarwarin naki,,,muna matukar alfahari da ke,amatsayin mahaifiyarmu" murmushi mama tayi tare da cewa "kamar yan da nima,nake,, Alfahari da samun ku a matsayin yarana".gaba dayansu sukayi dariya,tashi mama,,tayi tare da cewa nibari naje n kwanta,sai da safe,,,to mama Allah ya tashemu lafiya"....



•••••••••••

Sunyi shirin bacci tsaf,sun kwanta,,,salma ce ta dubi Nasreen,, tare da cewa,,,"Yaya Nasreen,ni kaina shawarar da zan baki,kawai ki amince da wanna'n tayin inaji ajikina,cewa,,shi alkairi ne,a cikin rayuwar ki,kuma a gaskiya,,daga ganin shi,kaga nitsatsen mutun,uwa,uba gashi da kyau da kwarjini" Hmmm nisawa Nasreen tayi tare da cewa "Eh, nikaina Salma, inajin haka atare dani,sai dai mubarwa,,Allah zab'i Allah ya zab'a mana mafi Alkairi" "To amin Yaya" "to ni dai sai dai na ce miki sai da safe,,,,to Allah,, ya kaimu,,ameen"....


•••••••

Rufe ido tayi da niyar bacci amma sai dai me,,hoton fiskar Nasrenllah take hangowa,,ya yin da yake,sakar Mata lallausan murmushin sa da sauri ta bud'e,,ido,,tare da tambayar zuciyarta,,to me hakan yake nufi,Addu'o'i tayi ta shefe jikinta,,,sai dai me daga ta rufe ido fuskarsah,,take gani,,yana yimata,,wani kayataccen murmushi,,,,ga sautin tattausan muryansa,da yahana,don don kunnanta kata,,,,kwata_kwata,ta kasa bacci,,sai dai juye_juye da take ta yi,Sam tinaninsa ya hata sukuni,gamin bacci ya kasa d'au kanta ne yasa ta sauko alwalah ta d'auro,,,tazo ta tada sallah tana kaiwa Allah kukanta,,akan ya zab'a mata,,mafi Alkairi,,,ta jima sosai kafin taje ta kwanta,,,cikin ikon Allah bacci y d'au keta.....



•••••••••••

Cikin wa"yannan kwana biyun da tabasa tatabbar da cewa,,zuciyarta,,,tagam aminta,,da shi,sabi da kulluma,cikin tinaninsa,take,,da son sake ganin kyakkyawar fuskarsa,,sabi da tin ranar d ya tafi bata sake ganinsaba,Dan ko wajen sana'arsa bezoba,,,yau ne ranar da kwana biyu tacika,yau jinta take zuciyarta Fe's gawani nishad'i d takeji yana ratsata Salma ce ta dubeta tare da cewa. "Aa yau wai ya ya naganki sai wani farin ciki,,kikeyi,,dagani,,zuciyarki ta kamu da so, salma t fad'a tana dariya,, "Hmmm kyaji da shi "yar sa ido kawai" "AI Yaya babu wani sa ido sai gaskiya kallifa,yan da kika wani rangad'a makeup,, wan da ba zan iya Tina,,Rabon da kiyi irinsa ba,musamman ma a irin Wannan lokacin da yakasan ce dare" "Wai ke Dan Allah ba kinki baya gajiya dasurutu ne,,ni dai ki rabu dani haka,,,shikenan mutum ba zai yi kwalliya ba sai da wani dalili'' ,DUK wanna abin da sukeyi mama na gefe tana yi musu dariya...


••••••••••

Shiryawa yake cike da far in ciki,,,,,Dan gani ya yi kwana biyunnan kamar anshekara,,yagama shiryawa,,tsaf cikin kananun kaya,masu saukin kudi dai-dai na talaka, amman duk da haka bak'aramin kyau yayi ba,,


•••••••••

  Tin d'azu take tafaman du ba A gogo,,ga shi har anfara kiran sallar isha,,,amma be iso ba,,,jitayi zuciyarta tana harbawa da sauri,, da sauri,,,tare da tinanin ''Allah ys lafiya tashi tayi ta tayar da sallah..


••••••••••

Zuwan Sa k'ofar gidan ya yi dai-dai da Tayar da sallah a masallacin da ke kusa da gidan Dan haka ya wuce,,masallaci,,,ko da yafito beci wata wahalaba,,,wani yaro ya tura yace ayi masa sallama da ita ace injishi,,yaron kuwa,da aka aika ba kowa bane face Isah,Dan gidan Hari,....



•••••••••••

Ba'awani dau lokaci ba,, Husna ta kawo kujeru tare da yimasa iso,,gaisawa sukayi cike da girmamawa,,,,kafin ta koma ciki,ta kawomasa,Ruwa da lemo,,da kuma cake,," Aa sannu k'anwata,,,wanna hid'ima haka duk nikad'ai? dariya tayi tare da cewa "AI babu komai Yaya" "to nagode in kin shiga kice INA gai da mama'',"to zata ji"....



  Da sallma tq k'araso,,,amsawa ya yi idonsa akanta,kwata _kwata ya kasa d'auke idonsa,a kanta,zamatayi tare da gaishesa,,"lafiya k'alau my life da fatan na sameki lpia k'alau,? Alhmdllh,,ita,basa amsa a tak'ai ce,,sannan ta ce,, "Bismillah,,kasha Ruwa" "Ina ai my heart bana jin zan iyacin komai,,,batare da naji,kin amince da soyayyata ba sannan zan samu nutsuwar cin wani Abu,,ina sau raronki my heart kin amince,,kinasona,ko Aa? kan ta a sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,,tace eh na amince" ta fad'a cikin wata siririyar murya ,wani sanyi yaji ya mamaye masa zuciya....



 Cike dq farin ciki ya ce,,"Agaskiya ba zan iya kwatanta tamiki yawan farin cikin da nake ciki ba,,,ngd sosai,da Wannan dama da kika bani,, amman dai ya kamata,,my heart atemakawa zuciyata,kicemin kina sona ko da so d'aya ne,,plz" ya k'arasa maganar kamar ya na shirin yin kuka,,,yan da ya yi maganar ne yaso bata dariya,,,jin tayi shiru ne yasa ya k'ara cewa plz my life ko da so d'aya ne".....


 Bai tab'a tsammanin zatayi magana ba can ya tsinkayi muryarta,da cewa, *I LOVE YOU* 






Ummu Amsad.

[5/12, 12:21 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

      [Yana tare da sauk'i]


BY Mmn AMATULLAH


   Paid book 200

     Free Page

    

 phone number ***.




Chapter 14


    Hannu tasa ta rufe fuskarta,,tana Dan murmushi,,Zara_zaran yatsun hannunta yabi da kallo wa "yan da sukasha Jan lalle,yana murmushi,tare da cewa "Amma fa my life na gode sosai,a yau ba zan iya musaltamiki iya yawan farin cikin da kika sani ba,dan tin da nake,ban tab'a tsintar kaina a makamancin farin ciki irin wan da nashiga a yau ba,dan haka dole na godewa,Allah sannan na gode miki,Ina godiya sosai,sannan inayi mana fatan Alkairi..


••••••••••

Tin da ya fara magana ,ba tace komai ba haka kuma,,bata cire hannunta daga saman fuskartaba,,murmushi ya k'ara saki tare da cewa,,, "Haba my heart,,, kuma rowar ganin fuskar akeyimin,,,,plz ni dai a temaka,,,a fud'emin wannan kyakkyawar fuskar, na gani,,ko so kike,,natafi inata mafarkin ganinta,kai ta girgiza,,alamar Aa, "To in dai,,da gaske bakyaso to kibud'emin ita,na gani,ko naji sanyi a zuciyata"...


•••••••••

A han Kali ta zare hannunta daga saman fuskarta," yawwa ko kefa my life" kan ta sunkuye tana cigaba da wasa da yatsun hannunta,,, cikin muryarta,,me sanyi,wacce ta ratsashi sosai, tace,"Bismillah kasha Ruwa" cup ta d'auka ta zuba masa Ruwa tare da mika masa karb'a ya yi tare da cewa "nagode",sha ya yi,,tare da fad'in "Alhmdllh"....


•••••••••

"Am dama akwai wata magana da nakeso na fad'a maka,,d'an be kamata ace na rufekaba ban fad'a makaba sabi da a bin da yashafi rayuwa tane" ,tana fad'ar Haka ya fahimci akan me takeso tayi magana dan haka ya dakatar da ita ta hanyar cewa,, "My life,,ba sai kin ce,,komaiba,,,sabi da nasan abin da ki ke k'ok'arin fad'a" da mamaki take kallonsa,,gira ya d'aga mata,Alamar eh,sannan yace " Nasan ko Mai akan rayuwarki tin Kafin nazo Nan,har maganar aurenki da k'addara tasa ake fasawa, da fatan nayi dai_dai? kai ta gir giza alamar eh,, sannan ta kara da cewa,,, "Tabbas haka ne kuma banyi mamakiba dan kasani,,sabi da zan cen duniya baya tab'a b'uya"....


••••••••••

"Haka ne my life sannan inaso na shai da miki da cewa ita rayuwa Haka take kowa da irin k'addararsa a rayuwa,,sannan inaso kisa a zuciyarki,dama chan Allah ya k'addara su duka ba mijinki a ciki,,,dama Allah ya k'adarto wata k'ilah ke ranmbo nace,shiyasa duk hakan take faruwa,kuma insha, Allah,da ni za'ayi,,,don inaji ajikina ke tawace," ya k'ara sa maganar yana kashe mata,,ido d'aya,, had'e da murmushi itama,murmushin tasakar masa,tare,da cewa, "INA godiya da irin wannan,, soyayya da kanunamin'', "AI Nike da godiya,sabi da ni kikayiwa,Alfarma,da har kika soni,bani da komai"....



"Aa kaga mubar wannan maganar banaso ka sake cewa,,haka,sabi da shi so guda d'aya ne sannan kuma babu ruwansa da wannan,,, ni dan Allah nake sonka, bawai dan wani Abu'n duniya ba,dan haka kadena irin wannan maganar," murmushi ya yi tare da cewa, "to na bari my life", nan dai sukaci gaba da firarsu,,mai cike da so da k'auna,kafin suyi sallama ya tafi.....


••••••••••••

Haka sukaci gaba d gudanar da soyayyarsu gwanin ban sha'awa


Ko da baba hari tasamu lbr'n,,wan da yake zuwa,gurin Nasreen,,ba k'aramin farin ciki tayiba,,har da taka rawa,,,

Tare da cewa "To nidama ta wasa ce,ai baki Isa kinje gidan hutuba,nafiso kije gidan da za ki, wahala,,,in da wannan kyawun fuskar taki zai disashe" ta k'arasa maganar tana,,kalkyakewa,,da dariyar muguta, tana,"waike me farin jiniko," Hafsat dake zaune ,,tazo gida,,,da "yarta d'aya,tace "wallahi Baba nikaina INA jin haushin kyawunnan NATA,,,innaganta,,jinake,,,kamar,,na watsa mata,acid kowama ya huta,,ga shegen farinji", Hari ta amshe da cewa "To " yata,ai yan zu kinga in da farin jini ya kaita,da ma irin wannan gidan nafiso ta samu,kinga ko rabinki bata,,kamaba" Hafsat ta amsa da "wane ita ai wallahi sai tataho,,rakefa,,yake siyarwa,baba yama za'ayi ki had'ashi da Mannir" "ai nima ba had'asu nayiba,misali nayi miki" "Ah to ni Baba ko misalin ma ba naso'' "to shikenan,, nadaina,,nandai" Nan suka ci gaba da tattaunawa,,suna dariya..



•••••••••••••

Ko da yajewa,,Baba da Inna da maganar Nasreen ba k'aramin farin,, ciki sukayi,ba,nan baba ya yi masa Alkawarin zaije ya nema masa auren ta da yar dar Allah,, haka kuwa akayi sunje,,shi da wasu abokansa kuma anbashi ita,sannan Baban NASREEN ya basu dama duk lokaci'n da suka shirya suzo asaka ranar,,,aure,,,,,sosai sunji dad'in tarban da akayi musu,,,da farinciki suka dawo,,,,baba ya shedawa,,,Nasrenllah abin da baban Nasreen yace,,sosai ya yi murna...


•••••••••

Rike take da waya suna magana da,Nasrenllah,cike da farinciki yace "yau my life ina cikin tsananin farinci" "farin ciki namefa? Nasreen ta tambaya,"Abba ya bani ke mana,,sannan yace duk lokacin da nashirya na fito,kin San wani Abu My life?, "Aa sai ka fad'a","kin San da ina da kud'i babu abin da zaisa na barki,kisake wata,,,batare da kina,,kusa da niba,,a matsayin mata,sai dai kash banajin nan da shekara,zan,,iya had'amiki irin lefen da akeyi yan zu,,kinga wannan,, idan na tinasa Wallahi hankalina ba k'aramin tashi yakeyiba" "Haba yayana,,,wai sau nawa kakeso,,,na fad'amaka,,cewa,nifa kai nakeso bawai,,kayan lefeba da duk sauran abin da ba Addini ne yazomana da shiba,ni sadaki kadai nake da buk'ata,,Daga gareka,,dan haka kadena damun kanka da tinani,kaji yayanah"..



  Gaskiya My life da duk mata,,suna da irin tinanin ki da ba'asamu tarin "yan matan da basu da aureba,inasake godewa Allah,,,a karo na ba iya ka da yabani ke,dan INA da yak'inin cewa,nafi kowan ne namiji samun abokiyar rayuwa,ta gari" ",Aa yayanah kadafa ka fasamin kai wannan irin yabo haka ai yayimin yawa,, "Ina ai sai dai kad'an dan duk abin da na fad'a kin wuce,,nan" "to shikenan naji kuma n gode"...


  Yan zu dai ni anawa ganin nan da wata,4 haka sai asha biki kinga lokacin,,,na dan tattara ko? "Ah haba yayana ina ma kace nan da shekara ko Rabin shekara, amman wata hud'u ai ya yi wuri" ta fad'a a shagwabe,,wan da yin hakan ya yi sanadiyar tashi'n tsigar jikinsa,,har sai da ya limshe ido tare da kamo lebensa na k'asa ya ciza da d'an karfi,,sannan yace "Haba My life kema kin san yan da na kagara,,naga kin zama mallakina shekara 1 ko wata 6 sunyimin yawa,ko sokikeyi na shiga cikin wani hali? ",kashiga cikin wani hali kuma?,akan me zakashiga cikin wani,hali'" tajero masa tambayar a Jere, "Au bakisan cikin, halin da zan shigaba? "eh" tace dariya ya yi tare da cewa, "to shikenan ki Bini ba shi wata rana zan fad'a miki" "ni_ni gaskiya ban yar da ba wayo zakayimin,,ni dai kawai ka fad'amin" t sake fad'a a shagwabe,kamar zatayi kuka.....


••••••••••

Ita batasan,,hakan da tayi ba,,ya haddasa masa shiga cikin wani yanayi marar misaltuwa,da kyar ya dan nemo nutsuwarsa,,ya ce,,kiyi hak'uri My life nayi Alkawari zan fad'amiki,idan lokaci ya yi,kinji my life D'ina kin hak'ura,,kai ta d'aga kamar yana ganinta,,sannan tace eh, "Yawwa ai nasanki da fahimta,sosai".....



   Duk abin da yake yi k'arfin hali ne,,dan shika dai ya san irin halin da yake ciki,,itakuwa,,bata saniba,,,sai kara,,,tsin dumashi takeyi cikin wani yanayi,,,da kyar yaga sunyi,sallama.....


Free pages saura k'ir's👌🏻 ya k'are ga Mai niyar biyan NASA kud'in Dan Jin Yan da zata Kaya ze iya tun tub'ata ta Wannan lambar ***.






Ummu Amsad

[5/12, 12:26 PM] Mmn Amatullah Ce😍: DUK TSANANI

     [Yana tare da sauk'i]


BY Mmn AMATULLAH


  Paid book

    Free page


Phone number ***.



Chapter 15



   Kwanciyar ta tagyara,tana tinanin soyayya'r ta da Nasrenllah,takanyi mamaki,yan da sukashak'u da juna cikin d'an k'ank'anin lokaci,takanyi mamakin Yan da takejin sonsa,yana ratsa duk kan wani lungu da sak'o na jikinta,har wani lokaci takanji,kamar bazata iya rayuwaba in babu shi, tin da take samarinta,bata tab'a,jin son wani kamar yan d takeji akansaba...


Hmmm,nisawa tayi,tare da gyara kwanciyarta,tare da cewa,"ko da yake,Nasrenllah na da ban ne Kuma gwani ne wajan iya soyayya shiyasa ya sace,zuciyata cikin k'ank'anin lokaci" murmushi tayi,,wan da ya kara fito d ainihin kyawunta,sannan tace,inasonka da yawa,my Nasrenllah, ta fad'a cike da shauk'i,,dare da lumshe,idanunta....



  Salma da tun d'azu take tsaye a kanta tana kallon ikon Allah tace "Aa yaya Nasreen,,wai lafiya naga sai wani murmushi ki ke,,tin d'azu inata magana amma ba amsa", Salma ta k'arasa maganar Tana murmushi tare da tab'a Nasreen ,firgigit ta dawo,Daga duniyar tinanin da take ciki tace "Aa Salma yau she,,ki ka shigo? "wai yaya Nasreen kina nufin duk maganar da nakeyi bakijiniba? "ke kinga bana son sa idon da kikasaba" "Ah Haba yaya Nasreen ni shigowa nayi kawai na sameki kina ta faman murmushi ke kadai,kuma nasan wannan aikin yaya Nasrenllah ne" ta k'arasa maganar tana dariya NASREEN tace "you see,,ai ninasan sa idon ne ya motsa,to in ma shine sai akayi ya ya? "Aa yaya Nasreen nibance komai ba",,zamatayi kusa da ita tare da cewa "Kinga yaya Nasreen dama,nazo ne muyi wata,magana...



•••••••••••

  Tin da Nasrenllah ya fara Neman auren Nasreen ya dai na kawo rake layinsu,iya kacinsa,,yaje wasu,, unguwannin,,wani lokaci kuma ya siyar a bakin layinsu,,wai a cewarsa,,yana jin kunyar baban su Nasreen ne,,kada sudinga had'uwa,kullum,,kuma cikin ikon Allah yan zu samunsa yafi na da,,ganin Haka yasa ya cewa,baban sa,,yaje yashedawa,,,baban Nasreen,a iya saka bikin yan zu,Baban shi yace "kanaganin kashirya? "eh,baba" "to ai shikenan,kamar wata nawa kakeso a baka,,kagama shiriko? "ito baba ni dai banaso ya wuce,watanni uku" ya k'arasa maganar,yana sosa k'eya,"wata uku fa kace Nasuru kana tinanin kashirya?,"insha Allah baba,dayakema kaga yan zu inasamu" "to ai shikenan Allah ya nuna mana",ya amsa da Ameen,,,Haka kuwa akayi baban Nasrenllah sunje sun sami baban Nasreen,sun tsayar da ranar,biki,,watanni uku,,masu zuwa,,farinci baya musal tuwa,a zuciyar Nasrenllah,, kwata-kwata ya kasa b'oye farin,, cikin da yake,ci....



••••••••••••

Babu ko sallamah Haka yashigo parlour'n,dan sukam ko da ya yi ba suji  ba lokacin da ya yi taba,,idan ma yayi to aciki,,ya yita,,sudai kawai sunji maganar mutin,,, yana kiran habiba Amsawa tayi da na'am Alhj kadawo sannu da da wowa,ko takan sannunta,bebiba,ya fara fad'ar abin da ya kawosa,cikin fad'a ya fara magana "nazo ne,,nayi muku gargad'i,akaro na k'arshe,yau nasake sawa,Nasreen, ranar,aure akaro na hudu,Kuma na k'arshe Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! in dai aka sake fasawa,to sai dai tanemi wani uban amma ba dai niba danna gaji da bin da kukeyimin a gida ke da yaranki na gaji,,dan haka in kunga da ma Ku kiyaye" ,yana kaiwa nan ya fice,fuuuuuu Daga d'akin,... 


  Idan da sabo sun saba,,tin da ba yau aka faraba,,amma duk da Haks sai da suka zub da hawayen bak'in ciki,,tare da addu'ar Allah ya dafamusu,,adukkan lamurransu.....



Bayan wasu kwanaki



Zau ne suke gaba d'ayansu A parlour'n suna firar,yan da biki,zai kasan ce,,mama ce tace,,,

"DUK da inaji ajikina wannan,, ita ce iyakar kaddararki,,Nasreen,, amma, duk da Haka ba zanyi gayya ba,iya "yan uwana sun Isa,,sai makota,wan da ya shigo Allah yasa Alkairi,amma babu wan da zan gayyata,ba dan komai ba sai dan gudun bakin mutane" "To ai mama kaina ai babu abin da zanyi,Haka ba zanyi wata gayyaba Daga an d'aura aure ai zan ce,,,ya kare,,duk da ina da kud'in da zan iyayin wani Abu ko da bayawa amma bazanyi ba,,kawai a kirawo malam,tayi w'azi ranar yini ya wadatar" cewar, Salma da ke zau ne tana jinsu batayi maganaba,sai yan zu,tace "AI Wallahi yaya Nasreen naci burin da bikinki, amman ina,,Haka Allah ya kaddaro'',"to ya zamuyi Salma,Haka Allah ya shirya,yan zu duk wani tsari sai mu mai da shi kan bikinki,tin da dai kinga Nasrenllah,,, ba shi da karfi,,kuma ni bana so na nunamasa gazawarsa,sai dai kawai muyi fatan ganin ranar lafiya" to ameen......



••••••••••••••

Tin biki yarage,,saura,,wata 1 mama ta fara gyara diyarta,,taciki ta waje,irin gyaran da ba'ayimata irinsaba aduk,wan can lokutan da suka wuce ,dan wannan lokacin Mama tana jinta ne,,,cike da farin ciki,,shi yasa ta zage take,,gyara " 'yarta,,dan ko waje ba'a barin ta fita iyakacinta,parlour' tin Nasrenllah yana nacin ganinta har ya hak'ura,,sai dai suyi magana ta waya,,,yau ma kamar kullum,suna manne, ta waya,,dan ko ita bak'aramin kewan ganinsa takeba,,...


••••••••••

"Haba my life yan zu kina nufin ba zan sake ganinkiba har sai ranar da aka kawoki gidana? dariya tayi tare da cewa,,"eh'',,,"Au dariya ma nabaki ko?,ko da yake ai naga nika dai,nake kewar ganinki,,Allah sarki shikenan tin da ke ba kya kewata" ya k'arasa maganar kamar me shirin yin kuka,"Wallahi yayana ba Haka bane nikaina,,idanuwana suna buk'atar ganinka,to amma babu yan da na iya tin da umarnin mama ne,kana ganifa,,ko gurin aiki bana zuwa,,sai da na d'auki,Hutu","to wai wannan wanne irin gyaran jikine?ke yan zu duk kyawun da ki ke da shi har sai kinyi wani Abu kuma,ni ko Haka aka kawomin matata inason kayata'' ,Dariya tayi tare da cewa "Amman,, ai kasan ance,ko kana da kyau ka k'ara da wanka,ko?, Hmmm "to ni dai yan zu ai babu abin da zance tin da umarnin mmne"


  Yawwa my life asatinnan,nakeso a kawo miki kayan lefe sai dai babu yawa",,"Haba yayana,yan zu sai da ka wahalar da kanka,nacefa,na yafe,"Aa kinga my life, kima dena wannan maganar, ko ya yake ai ya kamata,,kema nayi miki kamar yan da akeyiwa kowacce Amarya,,dan Haka kar kice komai" ",to shikenan,yayana ngd sosai Allah ya k'ara bud'i,,ya amsa da ameen,...


••••••••••

Kamar yan da ya fad'a Haka CE ta kasan ce,a cikin satin "yan uwansa mata mutin biyu suka kawo,,akwati 1 na lefe,tirmi uku na atamfa,sai lace d'aya sai shadda 1 sai mayafi 1 Takalmi 3 sai shijani 2 sai sarka 2 abin hannu sai tirare uku,hoda 2 da sauran tarkacen makeup komai d'aya,,,farin ciki gurin baba bari baya musaltuwa,bayan masu kawowa sun tafi,Haka ta dinga aikawa gida_gida tana cewa suzo suga lefe,duk abin da take babu wan da ya tanka mata acikinsu,sabi da mama ta hana,Nan fa 'yan gulma suka fara tururuwar zuwa gani...



•••••••••••

Nasrenllah tini yasa an gyara d'akin da ya ke ciki an danyi mas kwas kwarima,anyi fenti,,Haka gidansu,shima anyi Masa farar k'asa,tini gida ya koma,,kana ganinsa kasan amarya za'a kawo,,Nasrenllah ya kasa zau ne ya kasa tsaye,sai faman kai wa da komowa yake.....



••••••••••••••

Biki yarage,saura kwana7


Saura page d'aya Free pages su k'are game buk'atar Jin k'arshen labarin da Kuma k Yan da zata kaya ya tun tubeni ta wannan lambar ***. Dan Jin Yan da tsarin biyan yake.




Ummu Amsad

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol