Free chapter · Read without an account
chapter 19
by Zainab Yerima · MURADIN RAI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*
_wanna page ɗin naku ne *MATAN AREWA GROUP* kuyi yadda kukeso dashi sai kunso ma in turawa mutane🥳🥳_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
19📚
Ihu farida tasa tayi gefen maman ta tana kukan munafurci…. Rungumeta mama tayi tana cewa bai dai miki komai bako? a shagwabe tace mama wannan shine karo na uku, yana ritsani bansan meye yakeson mun ba, mama inajin tsoro dan Allah ki shiga tsakani na dashi, bayanta take bubbugawa a hankali tana harar shi…
kallon su kawai yakeyi yana mamakin karfin hali da munafurci irin na farida.
Ganin bashida niyyan magana yasa mama cewa ai dama nasani bazaka iya magana a lokacin da dubun ka yacika ba, kaban kunya Abbas dama ina ganin ka sallah sallah ashe zuciyar ka bakyau? Yanzu zan kira mummyn ka in shaida mata halin da ake ciki...
Bazan miki ranshi kunya ba mama saboda naɗaukeki tamkar mahaifiya ta, kuma bazan hanaki faɗan komai ba, saboda wannan kaɗan ne daga cikin abunda farida tamin don haka bata ban mamaki ba, zata iyayin abunda yafi haka ma….
Ya isa haka Abbas bazaka sani agaba kayita faɗan muna nan kalamai akan ƴata ba, tsabar rashin kunya ma a gabana kana kokarin rungumar ta dakarfi har kuma zaka samu karfin gwiwan faɗan abu a gabana.
what! Yace tareda zare ido bai taɓa sanin sharrin mata da ake faɗa ba sai yau, juyawa yayi cikin hanzari ya nufi ɗakin shi, don ya lura idan ya tsaya sharrin su ba karewa zaiyi ba.
Mummy ta kira tana ɗauka, kawai mama tahau banka bali'I wai ita Abbas ya cuceta yazo yana kokarin lalata mata yarinya acikin gidan uban ta.
kayataccen murmushi mummy tayi sannan tace, ohh bayan abunda ta Ƙulla musu yanzu kuma tanan ta ɓullo? Hajara(asalin sunan mama kenan) bari kiji Abbas ɗina ba lalataccen yaro bane irin ƴarki, na bashi ingantaccen tarbiya kuma nasan abunda gudan jinina zai iya aikatawa…. Kin cuci Hanif da tahaɗa zuria dake kin aifa mana yara mararsa tarbiyya, kinfi kowa sanin tun muna ƴan mata ban goyi bayan aurenki da yayana ba saboda sanin halin ki, kawai mun nuna miki so ne saboda mu tayashi son abunda yakeso…
Ya isa haka kursum! Cikin tsawa mama tayi maganan, karki yadda kice zakimin wani tone tone, yarane na riga da na haifesu Wanda bayason ganin su ya zo yakashe su…
Kinga ai irin rashin hankalin naki da rashin tarbiyya, ni ko kaɗan farida batada laifi a idona tausayi ma take bani na rashin dacen mahaifiya datayi, kuma ina miki kashedi da ki gargaɗi ƴarki dake kanki da kudaina bibiyan yaro na da sharri, in kuma ba haka ba...
Tareta tayi da cewa inkuma ba haka ba sai meye, nace sai meye kursum? Bari kiji niɗin nan da kike gani, nan gani na bari wallahi munfi karfin ku da duka zuri’ar ku… haka sukayita fafatawa har kuɗin wayan mama yakare ita kuma mummy tace bazata kirata ba saboda batada lokacin ta, amma hankalin ta ya tashi sosai tanata tunanin halin da Abbas yake ciki, tasan yana cikin damuwa bana wasa ba.
Zama yayi a bakin gado ya riƙe kanshi da yake sarawa kamar zai fashe, wayan nabil ya ƙira yana ɗauka yace dan Allah kazo dawuri banida lokaci, ya kashe baifi minti goma ba nabil ya iso, ya tsorita saboda bai taɓa ganin Abbas a irin wannan halin ba, tambayan shi yayi akan abunda yake faruwa, tashi Abbas yayi yace mishi yanzu banida lokacin baka labari, katayani tattara kayana mukai ɗakinka zanyi tafiya idan nadawo zangayama komai, ba musu yafara tayashi suka tattare kayan tas suka kai mota.
Farida tana leƙen su ta window ganin suna zuba kaya a mota yasata cewa nashiga uku badai tafiya zaiyi ba? waima mena aikata ne? ya Abbas zai ɓacewa ganina, take hawaye yafara fita a idonta…. Karfa abunda nayi yajawo ya tsaneni har abada? bazan iya rayuwa babu shi ba, shine sanyin idaniya ta wayyo Allah na… zubewa tayi a wajen tafara rera kuka kamar wacce akayiwa mutuwa.
Suna fitowa saida ya tsaya ya kalli gidan su mardiyya, agogon hannu shi ya duba yace yakamata muyi sauri saboda karsu tafi, tambayan shi nabil yayi yace su waye? Mardiyya yace mishi a takaice tareda murza kan motan shi yasa gudu…
suna ajiye kayan mummyn shi yakira, yace mummy ki gafarceni nabar gidan uncle Hanif bada izinin ki ba, kuma Dan Allah karki cemin in koma bazan iya zama dasu ba…
Abbas karka damu nasan komai, dama ko baka bar gidan ba ni zan ƙiraka ince kabari, zan turoma kuɗi domin kasamu comfortable wajen da zaka zauna… duk ni nasaka a cikin wannan halin saboda tun farko ka nunamin bakaso amma na tursasa ma saboda inason ku koyi zumunci, ka kuma yadda duk don kamin biyayya…
Kidaina faɗan haka mummy, wannan rubutaccen abune da Allah ya rubuta zai faru dani, bake kika jawomin ba, kuma ai dama dolena in miki biyayya…
Allah ya muku albarka, nidai yanzu dan Allah Abbas kayi kokarin tsare mutuncin ka, karka bani kunya, karkasa wataran inyi dana sanin bin bayanka danakeyi..
Huh! Inshaa Allah bazan taɓa baki kunya ba, bazan canja hali a bayan idon ki ba…. Haka suka gama wayan sunata baiwa juna karfin gwiwa.
Nabil zan tafi Dan Allah inason katayani neman wajen zama mekyau kafun indawo…. Kafaɗan shi nabil yadafa sannan yace gaskiya bazan iya barin ka ka tafi kai kaɗai a irin wannan yanayin ba, zan bika duk inda zakaje.
Karka damu nabil zan iya kula da kaina kuma banason saka acikin rikici na.
a’ah ko kaɗan bazaiyu in zauna ba kayi hakuri dole tare zamu tafi…
Saboda yadda yaga yadage yasa suka tafi tare, suna shigowa layin anguwan su motar dazata kai mardiyya na fitowa don haka ba ɓata lokaci ya rufa musu baya suka kama hanyan bauchi.
Zeezee saida tayi kuka iya isarta sannan tafara neman wayan mardiyya saidai switch off takeji saboda Abban ta ya kwace wayan, don haka a gigice ta nufi gidansu mardiyya saidai sunyi saɓani don motan su nawucewa tana shiga, antyn mardiyya ce tagaya mata abunda yake faruwa, sosai zeezee tayi kuka kamar da ita abun yafaru… dakyar antyn, ta rarrasheta saida tayi shuru sannan tace to zainab abunda yadameni shine haryanzu bansan yaya akayi har sukaje hotel tare ba, ko kinada wani masaniya akan abunda yafaru?girgiza kai zeezee tayi tace bansan komai ba, nima na matsu inji asalin kan labarin saboda kaina yakasa ɗauka, kuma bazan taɓa yadda mardiyya zata aikata hakan ba.
Saidai dukda bata nan bazan zauna ba saina nemo asalin kan lamarin… bazan bari sunanta ya ɓaci inaji ina gani ba..,
hannu ta antyn mardiyya ta kama tace ina nan tareda ke zeezee, nima inason komai ya bayyana kodon Abban ta yagane ba haka kawai na yadda da ita ba, nasan ta ne kamar sanin danayiwa yaran dana haifa aciki na.
Basu suka isa kafin madaki ba sai karfe shadayan dare...
*ZEETY DELIGHT*💖