Free chapter · Read without an account
chapter 27
by Zainab Yerima · MURADIN RAI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*
_this page is for you my sweetheart ❤️ *maryamah nah*❣️, i can't love you less, u ar one in million i love you fissabilillah🥰❤️_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
27📚
Hmm… zeezee kin kasa gane me nakeson gayamiki, I don’t want to rush into any relationship… yanzu kiga irin na ya harun nayi tunanin shine mutun na karshe a duniya dazai cire hope akaina, sai kuma yazamo mutun na farko dayafara samun tantama akaina, duk da banga laifin shi amma nasamu disappointment a wajen…
hannun ta zeezee takama tace mardiyya bake kaɗai ba harni ya harun yaban mamaki kuma yaƙara nunamin halin mutanen duniya…
To yanzu da kikeson inkarbi Abbas bamusan shima me zaifaru gaba ba… dasauri zeezee ta tareta da cewa subhanallah karkice haka mana, kuma ai babu wanda yasan gaba sai Allah, amma ni jikina yanabani Abbas shine other half ɗinki, amma tunda kince yanzu baki shirya ba bazan takura ba, saidai inason inbaki shawara da karki wulakanta shi wataran kizo kina da kinsani…
Dariya mardiyya tayi wanda ya nuna tsantsar kyanta, don sosai zeezee tabata dariya, wai kartayi data sani…
Zeezee dana sanin mezanyi?
Ba’akai wannan state ɗin bama kinyita zazzabi wanda daƙyar muka samo kanki balle yanzu daya furta… kedai kawai kinason raina min hankali ne… to kisani wannan karon ko leko ki bazan yi ba, tunda keda kanki kikeson daɓama kanki wuka..
Haba zeezee nah, ai nasan bazaki iya ba… koda zan rasa kowa nasan banda ke…
Suna shiga ɗaki nabil yace Abbas gaskiya farida tanaban tausayi tabiyewa zuciya gashi yajawo mata dana sani, daɗin abun ɗaya dai daga kaganta zakaga nadama a tattare da ita…
Hmm… Abbas yace tareda kallon shi sannan yace, kaifa yanzu ka yadda da tuban ta ko…
eh mana, gashi kana gani ko akan fuskarta…
Lallai kam, aini Allah ɗaya farida zata gayamin in yadda, ta tsorita kuma tayi kalan tausayi amma ba lallai bane tayi nadama, may be waƴancan ma tayisu ne saboda batayi tunanin asirin ta zai tonu haka ba…
Huh… please Abbas karka riƙeta a zuciya kaga ƴar uwarka ce na sosai.
Allah yasa in iya amma gaskiya abunda tamin ko a mafarki ban taba tunanin wani ma zaimin ba balle ita, nasan with time zuciya ta zata sake, kuma idan mardiyya ta yafe mata nima zan iya mantawa, saidai gaskiya bazan kara sata ajiki ba, kowa yaje yayi rayuwar shi…
Policemen aka tura gidan su Hasib, amma ba a sameshi ba, kuma dama a order da aka basu shine idan basu sameshi ba su taho da ɗaya daga cikin iyayen shi, suka tambayi baban shi shima baya gari, don haka suka tattara maman shi, ba yan gidan su kaɗai ba, hatta yan anguwan su saida suka shiga damuwa, don sosai matar tabasu tausayi duk jikin ta sai ɓari yakeyi kannenshi mata sai kuka sukeyi… ita kuma haka Allah ya jarrabeta da yara masu jawo mata fitina, kuma duk baban sune yake lalatasu da kuɗi gashi kullum akazo neman su ba samun su duka harda baban kowane masifa kanta yake faɗawa…
Yangidan suka roƙi polisawan akan suyi hakuri sukaita a motan gida amma fir sukaƙi haka suka sa ta a motan su me budadden bayan nan….
Take yaran Hasib suka sanar dashi ai an tafi da maman shi kuma ance idan bai fito ba haka za’a riketa a maimakon shi (ɗan kuka kenan me jawa uwar shi jifa)…
Daga farko yace karya sukeyi idan sukaga bashida niyan zuwa zasu saketa… amma sai yakasa samun kwanciyar hankali, yakulla wancan ya ware, karfa suyiwa maman shi wani abu? Idan takwana a wajen fa? Dole zata sha wahala ga sauro ba wajen kwanciya me kyau… mikewa yayi yazauna… gashi tanada hawan jini, karfa maman shi ta mutu dalilin shi… dasauri yatashi yatsaya yafara safa da marwa, gaskiya idan wani abu yasameta bazai yafewa kanshi ba…
Key motanshi ya figa yafice… abokin shi nata kiran shi amma ko sauraron shi baiyi ba, bai tsaya ko ina ba sai police station… yana zuwa aka kamashi aka rufe sannan aka cire maman shi… ko ta kanshi batayi ba yaranta suka ɗauke ta sai gida dama tunda sukazo basu tafi ba…
Wayanta ta ɗauko babu wacce tafaɗo mata sai wata kawarta hajiya ladi… kiran ta tayi tana ɗauka tace hmm… hajiya hajara kenan, idan anji ki dai damuwa tazo, zaman lafiya bayasa ki tuna mutane…
Ohh shedan da kikamin kenan?
dariya tayi tace ai ba shaida bane abunda kikeyi ne, yanzu gayamin meke tafiya hajiyar kissa…
Hmm… kedai kibari wannan karon kam kissa na yakasa yin amfani, hanif ya birkice yadda bazan iya shawo kanshi da wani dabarata ba… inaga wannan karon kam dole ki kaini inda za’a temaka min.
Tohh, abu baiyi daɗi ba, aitun da can ina gayamiki kissa bazai rike miki miji ba, balle yanzu da shekaru suka fara jaa duk abunda kike tunanin zakija hankalin shi dashi, yanzu ba burgeshi zasuyi ba, dole sai ankamo miki shi an sa miki a tafin hannu..
Yanzu kam ai dole in yadda, saboda idan auren nan ya mutu za’amin dariya a duniya saboda kowa yasan dama can ni nafison hanif, balle irin su khursum zasu zuba ruwa a ƙasa su shaa kuma bazan taɓa barin hakan yafaru ba..
Shikenan idan kin shirya saikizo katsina.
a’ah zuwa yanzu bazaiyu ba kije kiyi bayani idan da akwai abunda ake buƙata sai in turo..
To badamuwa hakan ma ba matsala, ai idan muna nan bazakiji kunya ba…
toh nagode kawata Allah ya barmin ke, Amin.
Yanzu kam fargaban kiranta yake amma bashida wani option dole haka zai ƙirata, dialing ɗin number ta yafara ɗauka tayi tareda sallama tunda ya ansa sai shima yayi shuru…
Hello tasake cewa… cikin I’ina yace mardiyya please inason ganin ki…
Murmushi tayi aranta sannan tace, wani abu yafaru ne kakeson ganina?
Eh… abu yafaru dayawa mardiyya zanso kibani lokacin ki please, inason muyi magana…
shuru tayi sannan tace, shikenan kaje ka tambayi Abba izinin ganina…
Ido ya zaro yace haba mardiyya Dan Allah karki min haka, kinsan bazan iya tambayan Abba ba..
Ni kuma bazan iya ganin ka bai sani ba.
Kiyi hakuri dan Allah, nasan ni me laifi ne amma Dan Allah yakamata muyi magana ido da ido..
Gaskiya ya harun bansan me kakeson ingayama ba…
Ganin yakasa fahimta ta yasa kawai ta kashe wayan ta…
Tunani yafarayi yanzu ta yaya zaisamu ganin mardiyya… shifa gaskiya bayajin zai iya rabuwa da mardiyya don shi yanzu ji yake kamar inya rasata zai mutu..
Dabara ce ta faɗo mishi… yace bari yasa zeezee aiki bazai barta tasamu daman zuwa gidan su mardiyya ba hakan zaisa mardiyya biyota…
Shigowa cikin falo yayi, yaganta tana danna waya… dan tsayawa yayi.. ganin shi a tsaye yasata daina abun takeyi ɗagowa tayi tana kallon shi sannan tace kana neman wani abu ne?
Am.. dama wani abu nakeson kimun idan kina free…
Ok, ai bana komai..
Yauwa side ɗinane yayi datti ko zaki gyaramin…
amma fa dazun me aiki tagyarama..
No lokacin ina abune nace mata ta tafi..
Tashi tareda cewa ok muje..
Dagangan ya birkita ko ina don karta gama dawuri… hakan kuwa akayi don ta ɗauki lokaci duk da haka ranshi baiyi daɗi ba ganin tagama still ba’a ƙira magrib ba..
Tana ƙoƙarin fita yace harkin gama dawuri haka?
Kallon mamaki ta mishi tace yaya duka lokacin da ɗauka ina abu ɗaya dawuri ne?
Kanshi ya sosa yace kuma fa hakane… am idan baki gaji ba dan Allah indomie nakeso…
bari inje gidan su mardiyya idan nadawo sai indafama…
Da sauri yace a’ah bazan iya jira ba kiyi hakuri kidafamin kafun ki fita…
mamaki takeyi, kamar ba ya harun ɗin dayake lallaɓa ta ba idan tayi aiki kaɗan yace taje ta huta tagaji amma sai aiki yaketa zabga mata..
Agogo take ta dubawa har tafarajin bacci tana jiran dawowan zeezee, ganin yamma yayi sosai yasa tashi zaune domin ta kori baccin saboda tasan baccin yamma bakyau…
daga baya ma tace bari dai tabi zeezee, dama tunda tadawo bata shiga ba…
Har ta ɗauki mayafi da wayan ta saiga kiran Abbas…
Zama tayi tareda sa wayan a kunne ta, sallama yayi tareda cewa Amincin Allah a gareki tauraruwar mata…
Murmushi tayi, a yayin da wani sanyi ya ratsa zuciyar ta sannan ta ansa mishi tareda cewa Amincin Allah a gareka ja… saita tsaya…
Murmushi yayi wanda sukasa dimple dinshi suka lotsa ba tareda hakwaran shi sun bayyana ba, fararen idon shi yaɗaga ya kalli samma sannan yace ina sauraron ki gimbiya ta ki karasa…
Bakinta ta rufe sannan tace nifa bance komai ba…
To bari inkarisa miki tunda kinajin kunyata…
Dariya kawai takeyi batareda tayi magana ba.
Da yanayin muryanta yayi maganan yace Amincin Allah a gareka jarumi nah…
Idonta ta rufe kamar wacce yake ganin ta…
Amma fa ni ba iliya dan mai karfi ba acemin jarumi… sunan soyayya me daɗi nakeso…
Wannan karon kam bayan rufe ido harda kwanciya tayi ta ɓoye fuskanta…
Saida ta nutsu sannan tace ya Abbas!
Na’am yace mata…
cikin muryar sakalci tace nifa ji nake ban shiryawa soyayya ba, tsoro yakeban don kamar bana dace acikin shi…
Hmmm.. nikuma yanzu ne ma nakejin zanyi, kuma na shirya mata kamar yadda mayaƙa ke shirya fita yaƙi…
Mardiyya, bazan ta sarewa ba akanki, bazan taɓa jada baya ba, bazan jure ganin ki da mutanen da basusan darajar ki ba, bazan kara sadaukar da soyayya ta akan wayanda zasu tozarki ba… bance lallai ki karɓi soyayya ta yanzu ba, saidai inason kisani ni Abbas inason ki fiye da son danake yiwa kaina…ke kaɗai ce MURADIN RAI NAH!...
Mamakin shi takeyi yadda yake zagewa wajen nuna mata soyayya, ajiyan zuciya ta sauƙe sannan tace, inason inje gidan su zeezee yanzu idan na dawo zamuyi magana…
har yace saikin dawo saikuma yace… nifa banason kina haɗuwa da harun ɗin nan…
Murmushi tayi tace, ka kwantar da hankalin ka ba wajen shi zanje ba…
Huh… shikenan nidai ki kulamin da kanki…
murmushi kawai tayi..
Tana shiga daidai lokacin lokacin zeezee tana fito mishi da indomie…
Kiciɓus sukayi a falo, murmushi sukayiwa juna sannan zeezee tace lahh yanzu fa nake shirin zuwa sai gaki…
Ji yayi zuciyar shi ta buga, kasa juyowa yayi yakalle su..
Ai danaji ki shuru ne nace bari inzo kuma dama tunda nadawo banzo muka gaisa da maa…
Maa ce ta fito tana cewa a ah yau mardiyya ce a gidan mu, inata cewa fa zan shiga in dubaki, banje har kika zo..
Cewa tayi bakomai maa tareda tsugunawa tana gaisheta ansawa tayi…
zeezee kuma karisawa tayi ta ajiye mishi indomie, ya gagara ko ɗago kanshi saima gumin dayaji yana tsatsafo mishi… cikin baiwa kanshi karfin gwiwa yacewa zuciyar shi, kaifa ka haɗa plan ɗin yadda zatazo idan kuma kabari ta tafi baka mata magana ba zakayi dana sani…
Ganin yadda yakasa ɗago kanshi bayan sun gaisa maa tace haruna ɗago kanshi yayi tace ga mardiyya tazo… tana faɗan haka tasa kai tawuce ɗakinta, daga zeezee har mardiyya binta sukayi da kallon mamaki…
Cikin yanayin kore kunya yace mardiyya sannu da zuwa yauwa kawai tace tareda kau da kanta, ganin taɗan takura yasa zeezee cewa zo mu shiga ciki ko…
Har sun fara tafiya yace zainab meyasa bazaku zauna anan ba? Idan don nine sai in baku waje ai..
Kanta ta girgiza tace a ah kaci abinci ka zamu shiga ciki…
Idan dai badon ni bane zaku shiga ciki ba kuzo ku zauna anan…
Kallon juna sukayi, murmushi mardiyya tayi tace karki damu magrib ma yayi bari inje gida kawai sai kin shigo..
Idan dai don nayi magana ne zaki tafi gida, idan kin tafi zeezee bazata sake zuwa gidan ku ba…
A razane dukan su suka kalleshi, shiko ɓata rai yayi yafara cin indomie shi…
Kallon juna sukayi sannan zeezee cikin rashin fahimta tace kamar ya? Yaya…
Kara tamke fuskar shi yayi yace mata kamar yadda kikaji…
Da sauri mardiyya ta juya ta fita.. zeezee ce ta bita tana mardiyya amma sam bata tsaya ba saima saurin data kara, harda ɗan gudu..
Ganin bazata tsaya ba yasa zeezee komawa ciki ranta a ɓace… tsayawa tayi kamar zata mishi magana saikuma tafasa tawuce ɗakinta ta bugo kofan, saboda yadda ranta yaɓaci tasan idan zatayi magana bazaiji me daɗi ba don haka tafiyan tane mafi alkhairi..
bin kofar yayi da kallo, aranshi yafara cewa wai meya aikatane? Shida yakeson suyi magana kuma ya wargaza komai… hannu shi yasa ya shafi kanshi tareda fesar da iska me ɗumi… bayason lamarin yafi karfin shi, amma dai idan abun yafi karfin shi yanaga dole yaje yacire kunya ya baiwa Abba hakuri..
Tana shiga ciki kan gado tafaɗa ta fashe da kuka… meye ya harun yake nufi da ita? That means he never feel sorry for her…
To meyasa zatayi kuka don ya mata haka, tashi tayi tafara goge idon ta…, sallaman goggo taji da sauri ta tattaro nutsuwarta ta gyara zama..
karisa shigowa tayi tana cewa ke kuma kullum kina ɗaki kamar mummunan amarya bazaki fita waje kisha iska ba..
Murmushi tayi tace ai na saba da zaman ɗaki goggo…
hakane don tun kina karama haka kike…
Ni ina labarin mijin mu ne?
shuru tayi bata gane ba sannan tace wa goggo waye kenan ?
ja’ira shidai cingam ɗin naki Abbas, sam nadaina ganin shi…
Murmushi tayi tace goggo yana gidan su, dama yawanci sai in zai koyamin abu yake zuwa…
Ohh to inkunyi waya kice mishi nakusa sakinshi fa tunda dai bazai iya riƙeni ba, dariya mardiyya tayi tace zangaya mishi.. haka sukayita taɓa hira goggo tana ta janta da wasa amma dayake ita bata iya wasan kaka meyawa ba, yawanci dariya kawai take mata.
Wannan karon sosai Abba yake shan mamakin shirin tsakanin mardiyya da goggo, sai yanzu yaga ashe kaitan da yayi can ma yayi amfani tunda gashi sun fahimci juna.
Bayan tagama isha tana naɗe abun sallah Abbas ya kirata, zama tayi a bakin gado, tareda naɗe dadduman a hannu ta.
Tana ɗauka yace my angel ashe kina kusa? Murmushi tayi tana jinjina yadda Abbas yake bata sunaye kala kala… sannan tace ina kusa yanzu na iddar da sallah… ajiyan zuciya yayi Sannan yace I’m missing you princess, inason zuwa inganki amma banason mutane suga wani abu..
Ajiyan zuciya tayi… a zuciyar ta tace nima inason ganinka amma bazan iya gayama ba… a zahiri kuma cewa tayi bakomai,
Yace a ah nikam da komai…
Dariya tayi tace dazun ma goggo take tambayar ka, tace ma ince ma takusa sakin ka..
Ahh… kice mata dan Allah tayi hakuri, inta sakeni ai zan mutu…
Haka takawar da zancen sukaci gaba da taɗinsu…
Washegari lokacin zuwa kotu yayi kuma an samu ankamo hasib, don haka ana tsammanin a ranan komai zai ƙare..
Tunda aka shigo da hasib yake hararan farida da mardiyya… aranshi yake cewa bazaku taɓa samun nasara akaina ba, saboda nagama tsara komai, kuma ana gamawa duk sai kun gane kuren ku dani…
Ba ɓata lokaci aka gabatar da tuhuman da ake musu, take farida ta karɓi laifin ta cikin nadama, koda aka iso kan hasib musawa yayi…
Sau biyu alkali na tambayar shi, yana cewa shi baisan maganan ba bashi da hannu aciki… take alkali yasa aka kawo shedu, call ɗinsu da faisal aka fara kawowa, ya girgiza don baiyi tunanin zai sake samu ba, na biyu kuma original video nan aka kawo sannan lauje yazo yayi bayani akan su suka mishi aikin.. yanzu ma haka ya baiwa sauran abokan aikin kuɗi duk sunbar garin shine kaɗai bai karɓa ba…
Mamakin ganin lauje yakeyi don ya ɗauka yatafi, ba a gaya mishi yana nan ba aida yasa an ɓoyeshi..
Sheda na uku kuma farida ce don tace tabbas tare sukayi, karshema duk shi ya daurata akan abubuwan da tayi…
Take alkali ya yanke musu hukunci… farida anyake mata hukuncin wata huɗu a prison amma da sassaucin kuɗin beli saboda bata baiwa shariah wahala ba, ta yadda da laifin ta, da kuma kuɗi naira million uku na ɓatawa mardiyya da Abbas suna.
Shikuma hasib anyanke mishi hukuncin shekara shida a prison tareda horo me tsanani kuma ba beli sannan da kuɗi shima naira million uku na ɓatawa mardiyya da Abbas suna.
Take yafara ihu yana cewa wallahi sharri ne bazaiyu ba.. haka ƴan sanda suka fita dashi yanata hayaniya…
Farida ma kuka takeyi sosai, amma har cikin ranta tana farin ciki, koba komai tahuta….
Maman ta ne taje ta rungumeta tana kuka… baban ta kam zuwa yayi tsaya, ɗago jajayen idonta tayi tace hanif tunda anbamu daman beli yakamata muyi wani abu..
Girgiza kai yayi yace babu abunda zamuyi wata huɗu ai bayawa kamar yaune zata gama shi…
Saketa tayi tazo gaban baban tace lallai hanif bakada mutunci da tausayi, saikace ba ƴarka ba sakace ƴar riko… to wallahi koda komai nawa zai ƙare bazan bari ƴata tayi zaman prison ba..
Kafaɗan farida ya rike yace haushin hukuncin kikeji ko farin ciki?
Goge hawayen ta tayi tace ina farin ciki baba, wani nauyi yasauƙa akaina… nasan Allah yana sona shiyasa komai ya baiyana tun a duniya, goge mata hawaye yayi yace Allah ya miki albarka, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce kinji… tace toh baba na, yasa kanshi yawuce.
Binshi da harara mama tayi tace shikenan tunda ni zaki bulawa kasa a ido, amma duk da haka bazan barki cikin wannan halin ba.. hannun maman ta riƙe tace dan Allah mama na kiyi hakuri… kibi duk abunda baba yace kinga ranshi a ɓace yake…
Da Allah rufemin baki ke me kika sani, yaushe aka haifeki da har zaki gayamin abunda zanyi….
*ZEETY DELIGHT*💖