Free chapter · Read without an account
chapter 29
by Zainab Yerima · MURADIN RAI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*
_i'm back🥰🤗❤️_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
29📚
Ajiyan, zuciya mummy tasauƙe sannan tace gaskiya kayi tunani akan abunda yadace wanda koni ban tuna hakan ba, amma fa saidai hanzari ba gudu ba, bana tunanin farida zata samu soyayya a gidan Abbas, saboda nasan Abbas akan abunda ranshi bayaso sannan nasan yadda yake ɗaukan abunda yakeso da daraja…
zai nuna banbanci a tsakanin su sosai kuma nasan bazai iya ɓoyewa ba, kaga anan a kokarin muyiwa farida gata zamu sata cikin kunci…
saidai kuma yanzu yakamata muji tabakin shi tukunna …
Hakane, zamuji tabakin shi, amma kinsan ai lokuta da dama kiyayya takan iya zamowa soyayya… kafun mu mishi magana sai munji tabakin hanif, eh ba laifi hakan ma yayi Allah yasa mudace ta ansa da Amin.
Harun duk yadda yake tunanin abun ba haka bane… don yanzu yanaji yana gani mardiyya tadaina ɗaukan wayan shi, amma duk da haka bai sare ba, kara baiwa kan shi ƙarfin gwiwa yakeyi…
Harta gama shirin kwanciya saiga wayan Abbas… yadda yaji muryanta yasashi tambaya ko tafara bacci ne, tace mishi a ah yanzu dai take shirinyi…
Ajiyan zuciya ya sauƙe sannan yace rabin rainah yau na miki laifi...
Da mamaki tace laifin meye kamin?..
Yace, yakamata muyi magana dake kafun inyiwa su daddy magana tunda har yanzu bansan makomar soyayya ta ba a gunki, amma ganin zasu tafi yasa nagaya musu abunda yake raina, shikuma daddy yanzu haka har yayiwa Abba magana…
Ji tayi kamar anbuga mata guduma akai, meye Abbas yake nufi? Ita datace mishi bata shirya ba shine zai turo iyayenshi….
Jintayi shuru yace nasan na miki laifi bazakiji daɗi ba, amma banyi haka don na ɓata miki rai ko na takuraki ba, nayi shine saboda banason inyi wasa da dama ta…
Kiyi hakuri kiyafemin kinji…
Hawaye ne kawai sukafara zubowa a idon ta wanda ita kanta batasan na meye ba, tasan taji haushi da farko, amma maganan da yayi yanzu ya sanyaya mata zuciya saidai kuma gaskiya zuciyar tana mata wani iri….
Ganin batada niyan yin magana yasashi cewa it’s ok, na fahimci halin da kike ciki, ki kwanta kinji… saidai inason kimin alfarma ɗaya… dan Allah karkicewa Abba bakya sona, hakan zai iya sawa in rasaki, rasaki kuma zai iya sani cikin wani hali mardiyya inasonki fiye da yadda nakeson kaina, kuma navmiki alkawarin kulada ke fiye da yadda zan kula da kaina, duk rintsi bazan barki ba koda kuwa ke kika nemi hakan, ke kaɗaice macen da zuciya ta ta aminta da ita, kuma nakejin zan iya rayuwa da ita….
Haka kawai taji kukanta ya tsananta takasa riƙeshi, kawai ji yayi ta fashe da kuka sosai…
Kafun ya tambaye ta meye ne tuni ta kashe wayan…
Tsayawa yayi yana kallon wayan, har haka yaɓatawa mardiyya rai, anya kuwa rantane yaɓaci… toh kukan me takeyi?
Huh… shidai yasan mardiyya nason shi kawai dai watakila abubuwa ne suka mata yawa a zuciyar ta, bazai takurata zai bata lokaci sosai har sai zuciyar ta tasake…
Kuka takeyi amma zuciyar ta cike da farin ciki ke , ashe Allah zai nuna mata ranan da Abbas zai buɗe mata sirrin zuciyar shi irin haka, ashe dama Abbas yana jinta a zuciyar shi kamar yadda itama takejinshi a kowane bugawan zuciyar ta….
Allah yasa daga kan Abbas tagama shan bakin ciki a soyayya, tashi tayi taje tayo alwala tahau sallah…
Washegari bayan su mummy sungama shiri kafun su Abbas su fito suka nemi Alhaji hanif domin shaida mishi abubuwan da suka tattauna da dare.
murmushi kawai yakeyi yana kallon kasa, saida yaɗauki kamar mintu biyu sannan ya ɗago kanshi tareda cewa, khursum babu abunda zan iya ce muku a irin soyayyar da kuke nunamin na tabbata banda naka babu me maka haka Allah ya saka muku alkhairi, saidai kumin afuwa karkuga kamar komeye kukason temakamin ina juya baya, amma bana tunanin Abbas zai iya auren farida idan kukayi haka zaku shiga hakkin shi, nasan farida tanason Abbas kuma so me tsanani, itama zanso ta auri wanda yafisonta ba Wanda tafi so ba kodon gudun kar tarihi ya maimaita kanshi (shi da maman ta).
Kubar Abbas ya auri matar dayakeso, kubar mardiyya ma tasake a gidan aurenta da wanda takeso ita kuma farida Allah ya bata wanda zai sota.
Amma yaya da kabari mungwada taya musu ko Allah zaisa a dace..
Khursum ko Abbas, mardiyya da farida sun yadda sun fahimci juna, ina me tabbatar miki hajara bazata barsu suyi kwanciyar hankali ba, nasan ta sarai zatayi ruwa tayi tsaki domin ganin takawar da mardiyya ko kuma sun samu hankalin Abbas sukaɗai…
Shikenan tunda kace haka na tabbata kafimu sanin kan gidan ka kuma zakafimu hango abunda zai faru, alfarma na karshe zanso idan farida ta fito ka kawo mana ita su zauna da bilkisu, watakila zama da mace me daidai shekarunta zaifi bata kwanciyar hankali kuma inason inbata kulawa sosai, bazanso tana fitowa hajara ta kuma ɗaurata akan wani hanyan ba.
Shikenan indai wannan ne ba damuwa jibi zanje inyi belin ta daganan zamu wuce abuja…
Yana gama breakfast bai tsaya ko ina ba sai prison… koda akace mata anzo wajenta ta ɗauka baban ta ne, amma ga mamakin ta saita ga faisal.. zama sukayi kowa shuru, ita yanzu kunyan shi takeji ba kaɗan ba, tun lokacin da iklima tace Mata ai shiya bata jini kuma tagaya mishi komai…
Tunanin ta ya katse mata da cewa farida ki gafarceni… sai kuma yayi shuru.
Tasan gafarar meyake nema don haka tace mishi, bakayi komai ba faisal, godiya ma yakamata inma badon kun temaka wajen bada sheda ba na tabbabta Hasib bazai karɓi laifin shi ba, kuma ni hakan da kukayi gata kukamin koba komai nasauƙe hakkin tsakani na da mutane saura nida ubangiji na, hawaye tafara gogewa Wanda yahanata karisa maganan...
Farida! Sunan ta aka kira dukan su suka ɗago don ganin waye ne, baban ta ne da mummy da daddy.. dasauri ta tashi ta rungume mummy, saikuma tasake ɓarkewa da kuka, shafa bayan ta mummy takeyi tanacewa ki kwantar da hankalin ki komai ya kusa wucewa, jibi yaya zaizo yayi belin ki kuma direct Abuja zai wuce dake, ɗagowa tayi da sauri takalli mummy, kafaɗan ta ta rike tace kodai bakyaso ne, kigayamin duk yadda kikeso haka za’ayi..
girgiza kai tayi tareda cewa mummy inaso, ina bukatar canjin environment… zanfijin daɗin kasancewa dake…
Murmushi mummy tayi tace nidai inason kicire kowane damuwa aranki.
Baban ta ne yace, wannan saurayin dana gani fa meyakeyi… sunkuyar da kanta tayi tace yana cikin waƴanda suka bada sheda, yazo yaban hakuri ne yanaganin kamar bai kyautamin…
murmushi baba yayi yace ai baiyi komai ba hakan da yayi shine daidai, kodai kema kinaganin bai kyauta miki bane…
girgiza kai tayi tace ko kaɗan baba ni ai temako na yayi…
Muryan mama sukaji daga baya tana cewa amma hanif bakada imani meyasa zaka rufe belin farida kace idan bakai ba kar abawa kowa, nifa ban taɓa ganin uba irinka ba, Wanda yakeyiwa yar cikin shi mugunta ba sai kai…
da sauri taje ta riƙe hannu mama tana kuka tace dan Allah mama kibari haka ki watsar da makaman yaƙin ki… kiyiwa baba biyayya..
ɗaga hannu tayi zata wanketa da mari, baba ya riƙe hannun.. kallon shi tayi shima kallon ta yakeyi…
Da kakkaurar murya yace hajara ya isheki haka, karki kuskura ki taɓa ta, na lura kekam bakida rabo a hankali, bazaki taɓayin hankali ba, ƴar cikin ki ma tafiki tunani… saboda taɗauki darasi acikin abunda yafaru, amma kekam halamu ya nuna haka zaki tabbata dakikanci, tun kafun aurenmu nake tsammanta miki hankali amma yanzu kam nacire rai..
Fizge hannu ta tayi tace ya isheka haka… nace isheka hanif kadaina jifana da mugayen kalamai…
Matsowa yayi daf da ita yace, nasan abunda kike nema bazai wuce saki ba…
take zuciyar ta ta buga duumm.. sai yayi murmushi yace wallahi bazan sake ba amma kisani zanyi aure nanda sati biyu domin nemawa yarana uwa tagari…
Take taji abunda yafaɗa yafi maganar sakin tashin hankali… cikin gigicewa takai hannu zata cakwame rigar shi… mummy tasa hannu ta tare ta, tace kiyi hakuri nan bawajen faɗa bane….
Fincikewa tayi tareda cewa da Allah cajan munafukar banza munafukar wofi… ainasan duk abunda ake haɗawa kece kan gaba kuma wallahi khursum saina nuna miki matsayina…
A fasuce baba yayo kanta, mummy ta riƙeshi tareda cewa dan Allah ya isa haka yaya mu tafi kar mu makara..
Haka suka tafi suka barta a wajen sai surutai takeyi, karshe dai gandiroban wajen ne yazo yace ta tafi.. haka aka korata amma bakinta baiyi shuru ba..
Suna fitowa faisal ya taresu, yacewa baba dan Allah yanason suyi magana don haka su daddy sukayi gaba suka barshi..
ɗan rage tsayinshi yayi yace dama baba akan maganan farida ne, gyara tsayuwan shi yayi yace inajinka..
Sosa kanshi yayi yace dan Allah baba kayi hakuri ayi belin ta, wallahi zaman ta anan yanasani ganin kamar nayi babban kuskure..
Murmushi baba yayi yace karka damu da nace jibi zanzo nacireta amma yanzu saboda maganan dakayi gobe zancireta…
Wani irin daɗi faisal yaji har ranshi Wanda harya kasa ɓoyeshi.. yace nagode sosai ba Allah ya kara girma, baba yace nima nagode da nuna kulawarka garemu...
Su Abbas kuma suna gida suna breakfast don yacewa su mummy suyi gaba tunda zasubi prison zai kawo bilkisu airport ɗin, dama nabil ne ya roƙeshi don yanason suyi bankwana da bilkisu ai kuwa sun samu yadda sukeso… don saida Abbas yayi dagaske suka fito nan ma har sun kusa makara… bilkisu haka kawai taji kamar bazata iya tafiya tabar nabil ba …don haka ma koda sukazo shiga mota ganin yanayin fuskarta yasa nabil tambayan ta meyafaru aikuwa nan take hawaye sukafara bin fuskar ta..
ganin haka yasa Abbas shiga mota…
Duk bakin nabil shima jiyayi jikin shi yayi sanyi… inama dayana da halin rarrashin ta yadda yakamata..
Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan yace please baby kidaina wannan kukan nima kina karyamin zuciya…. Kiganni ba musu ta ɗago idonta tana kallon shi, yace ki kwantar da hankalin ki inshaa baza a ɗauki lokaci ba zamuzo da Abbas kinji… girgiza kai tayi, sannan yace nima kinsan bazan jure rashin ki… bantaɓa tunanin aure ba sai a haɗuwa na dake cikin kwana biyun nan.. inasonki bilkisu, inasonki son da bakina bazai iya faɗa ba…
Murmushi tayi tareda sa hannu ta rufe fuskar ta… yauwa haka nakeson ganin ki cikin farin ciki, karki bari mummy taga damuwa a fuskan ki kinji tawan…
horn Abbas ya musu.. nabil yace muje kafun yafara mita.. shiga motan sukayi, ita kaɗai abaya su kuma a gaba.. harar shi Abbas yayi yace zaku kara neman alfarma, dariya nabil yayi yace we are sorry ya babba… oh habaici ma zakamin?
Bakinshi ya rike yace wane ni inyi sirki na habaici… taɓe baki Abbas yayi yace su Abbas sirki manya… kwashewa sukayi da dariya…
Suna isa daidai lokacin su mummy ma suka isa… ba a jima ba jirgin su ya tashi…
Abba yaje gaida goggo bayan sun gaisa ne yake shaida mata yadda sukayi dasu akan maganan mardiyya da Abbas take farin ciki ya lulluɓe goggo hannuta tasa ta rangaɗa guɗa… baki Abba ya buɗe yace amma goggo na hanaki irin wannan ɗabi’un…
to ai nadaina sabir yanzu ma kamawa tayi dakaci sa’a ma ban tashi nataka rawa ba… kai Allah nagodema yau naji labarin dayafimun kowane labari daɗi, bazan ma tafi ba sai bayan bikinsu.
murmushi Abba yayi yace ba’afa sa rana ba, yanzu ma muka fara maganan…
Aikaga dalilin dazaisa ma in tsaya, saboda karku tsaya janjanin lokaci asa shi kusa kusa…
Shifa Abba sam yarasa gane meye yasa goggo farin ciki gameda maganan auren nan..
Kamar tasan abunda yake faɗa aranshi tace… nifa sabir bawani abu bane yasani farin ciki illa banasonb mardiyya tarasa Abbas,saboda inya wuceta na tabbata bazata samu masoyi irin shi ba, kuma hakan zai iya taɓa rayuwar shi saboda ba karamin so yakemata…
Shidai mamakinta kawai yakeyi, wai har goggo ce me bada labarin soyayya haka…
Zeezee tashigo tasamu mardiyya na bacci…
kafanta taja tace kitashi kigayamin yaushe kika koyi bacci irin wannan lokacin…
Ɗan juyawa tayi tana cikin yanayin bacci tace dan Allah kibarni inkara kaɗan… toh shikenan bari intafi gida..
Dasauri mardiyya ta tashi tanacewa karki tafi mana
Ohh daa gadinki zanyi kina bacci ko…
Mikewa tayi tanacewa yanzu kam ai natashi, toilet tawuce sannan ta fito… kallon zeezee tayi tace bari inkawo mana breakfast..
Oh keɗin har yanz baki karya ba… eh wallahi jiya banyi bacci dawuri bane, kedai akwai labari bari inzo inbaki…
Ba tafi minti biyar ba tazo da tire a hannun ta ɗauke da kayan kari…
Zama tayi tareda zubawa zeezee chips da egg source ta miko mata tana cewa zeezee dai bakisani ba… karɓa tayi tace saikin faɗa..
Hmm… jiya anyiwa Abbas tambaya.
dagaske anan gidan?
Eh… take zeezee taɗaga hannu ta sama tana cewa Alhamdulillah… gaskiya naji daɗin wannan maganan…
Girgiza kai mardiyya tayi tace nidai tawani waje naji daɗi tawani waje kuma banji daɗi ba…
Meya hanaki jin daɗi?
Gaskiya ni inajin tsoro… banson wani abu yaje yadawo…
Kamar wane abu kenan?
Kiga dai abubuwa sukayita faruwa da masu zuwa tambayan aure na… kuma ko wanne daga farko bazaka ga komai ba sai daga baya…
Mardiyya kenan, ni anawa tunanin duk sun shiga hurumin da banasu bane, yanzu kuma me waje ne yazo… banason kiyi gigin koran shi, saboda bakida masoyi kamar Abbas…
Hmmm… nima hakan nake tunani, amma fa karki manta yaya harun ma da haka nayi tunani,kuma kinga yadda abun yakasance…
Tabbas zeezee tana tausayin yayan ta, amma hakan bazaisa taki gaskiya ba, dole ya hakura saboda mardiyya ba rabon shi bace…
Haka sukayita taɗawa daga bisani zeezee tace zataje gida…
A falo ta tadda ya harun… zama tayi kallon ta yayi yace yaya mardiyya ta take?
Murmushi zeezee tayi sannan tace yaya, lokaci yayi dazaka cire mardiyya aranka…
Da sauri yace mata saboda meyasa?
Saboda anbada ita…
Mikewa yayi yace awaye?
Tace Abbas…
Wallahi bazaiyu ba, wannan ai rashin adalci ne…
Baki zeezee ta buɗe tana kallon shi..
Dama ni tun farko jikina yabani yaron nan son mardiyya yakeyi amma kikacemin ba haka ba, watakila ma shi ya haɗa abunda yafaru don ya koreni…
Gaskiya ya harun bazaka taɓacin jarrabawa a soyayya ba, saboda baka tsaida zuciyar ka waje ɗaya kuma kanada zarge zarge.. ko yanzu ma kasake faɗuwa a soyayyar mardiyya…
Ya isheni, dama nasan ke ko yaushe a bayan kawarki kike… yanzu zanje insamu Abba ayita takare, fuu yawuce..
Binshi da kallo zeezee tayi, ta bayanta taji maa nacewa kedai shasha ce… maimakon kibi bayan ɗan uwanki amma ke kike ƙara mishi damuwa… na tabbata zaki aikata zuga ta ma taƙishi yadda naga kina zaƙewan nan…
Wallahi maa… da sauri maa takatse mata maganan dacewa da Allah rufemin baki… zaki cikamin kunne don kinfi kowa iya tsara maganan ko… to inason ki sani idan bazaki goyi bayan shi ba kifita acikin maganan nan….
Wayan ta ne yafara ringing, maa kuma tawuce ɗakinta..
Ɗauka tayi tareda cewa wata sabon gani, da halamu dai kayi mafarki nane…
Jigina yayi jikin motan sannan yace ai abunda nayi yafi karfin mafarki, nazo ɗaukan amarya tane, dariya tayi tace saikace amaryan ƴar baby..
Kina ganin kamar wasane ko, kifito ina haraban gidan ku, kashewa yayi batareda yajira jin mezata ce ba, kallon wayan tayi tace me mujaheed yake nufi dagaske ne yana cikin gidan mu?
Gyalenta ta yafa tafita domin tabbatarwa kanta… aikuwa hango shi tayi ajikin mota… harta kariso mamaki bai bar fuskarta ba.
Murmushi yayi yace kina mamaki ne?
Aikasan dole inyi mamaki, saboda kwanakin nan ko waya bamayi balle kacemin zakazo…
Na shirya miki surprise ne, kedai yanzu bar wannan maganan munada abun tattaunawa dayawa…
Tace toh shikenan zo mu karisa, gaba tayi yana biye da ita, falon dasuke kai baki tawuce dashi..
saida yazauna sannan tace bari inkawo ma ruwa
yace badamuwa…
Ɗakin maa tafara zuwa ta sanar da ita zuwan mujaheed sannan tawuce kitchen fruits ta yanka mishi tareda drinks takawo mishi ..
Ɗan kaɗan ya taɓa sannan yace, zeezee nazo da abubuwa masu tarin yawa, gyara zamanta tayi tace inajinka..
Huh! Nasan kina tunanin ko na manta dake ne, wallahi ko kaɗan ba haka bane kullum kina raina, zeezee babane yadage akan dole yanzu sainayi aure, ko inkawo mata ko kuma yanema min, shine nazo muyi magana, shiyasa ma ban kiraki a waya ba nataso…
Murmushi tayi tace gaskiya mujaheed bazan iya auren ka ba! Jin maganar yayi kamar daga sama, a zubure ya ɗago ya kalleta yace saboda meye zeezee…
Saboda munjima da daina soyayya, yanzu ma bawai don soyayya da mukayi bane yasa kayi tunanin aurena ba, sai don kar ama auren dole, ko kuma may b duka ƴanmatan na abuja sun gudu… irin nice last option ɗinka… gaskiya hakan bazai yu ba, nima ina bukatar inyi auren soyayya kamar yadda ko wace mace takeyi…
Bai taɓa tunanin samun irin wannan matsalar daga gareta ba don haka take yafara gumi… hankalin shi ya haɗa waje ɗaya sannan yace wallahi zeezee ba haka bane, Allah inason ki kuma ban taɓa tsara rayuwata da kowa ba saike, kuma banajin akwai macen data kwantamin kamar ki… dan Allah ki yadda dani wallahi maganan nan danake gayamiki gaskiya ne…
Nifa mujaheed a soyayyar dakake cewa kanamin ban taɓa ganin shi akasa ba…
kuma ni bazan taking risk in auri wanda bayasona ba, saboda haka ni kaga tafiyata..
Yana kiranta amma ko kaɗan bata tsaya ba…
Hannu shi yasa ya tura hulan shi tareda cewa innalillahy wa inna ilayhir raji’un…wayar shi taciro ya kira abokin shi…
Yana ɗauka yace ango dafatan kasamu amarya lafiya?
Wane ango ne Zainab tana kokarin juyamin ba… cewa ma take batasan inason ta.
Mujaheed kullum abunda nake gayama kenan mata suna bukatar kulawa amma sai kullum kacemin kai zeezeen ka babu ruwanta, karka manta kowace rai tanason me kyautata mata, watakila kana nan wani yaje yasace zuciyar ta.
Nifa duk ba wannan ba yanzu kagayamin meye mafita?
Mafita ɗayane shine kazauna a kano ka tabbatarwa da zeezee kalan sonda kake mata, karka dawo abuja har sai ta gamsu dakai…
Toh shikenan zanyi kokarin yin haka ɗin..
Yanafita gida yawuce direct saida yayi wanka sannan ya zauna ya tsara mata message wanda yake kunshe da tarin soyayyan shi da kuma faranta zuciya…
Koda takaranta, ta yasar da makaman yaƙinta amma tasawa ranta saita koya mishi yadd zaisan darajar ta yakuma koyi nuna mata so.
Yana fita bai tsaya ko ina ba sai gidan su mardiyya, me gadi ne yaje ya cewa Abba yayi baƙo ya tambaye shi waye ne?
Yace haruna ne yayan zainab na nan makobta gidan kanurai nan…
Mamaki yake toh meye haruna yazoyi?
Sannan yacewa megadin kace mishi ya shigo..
ce mishi yayi wai ka kariso inji Alhaji…
Da sallama ya harun ya shiga falon yana ƙoƙarin zama a kasa Abba yace mishi ga kujera ka tashi ka zauna…. Cikin yanayin kunya yace a ‘ah Abba nan ma yamin…
Bayan sun gaisa saikuma yayi shuru don baisan ta ina zai fara ba..
Abba ne yace ina jinka haruna meke tafe dakai?
Kame kame yafara sannan yace am dama Abba akan maganan mardiyya ne… nasan nayi kuskure, amma dan Allah amin afuwa inason mukoma kan maganan…
Murmushi Abba yayi sannan yace ai haruna yanzu kam kaddara ta riga fata, dama Allah yayi ba matar ka bace shiyasa hakan yakasance amma ni bakamin komai ba ban kuma ga laifin ka ba saidai kawai a yanzu haka na riga da nabada mardiyya kuma aikaga bazan warware ba, ko naka ma bani na warware ba kai ka janye da kanka, gaskiya yanzu babu abunda zan iya cema saidai ince kayi hakuri.
Gumi ne yafara keto mishi, ganin bashida niyyan tashi yasa Abba cewa dawani matsala ne?
ɗago kanshi da zaiyi sai hawaye, cikin muryar kuka yafara cewa dan Allah Abba ka temake ni wallahi inason mardiyya sharrin shaiɗan ne, Allah nayima alkawarin hakan bazai sake faruwa ba.
Gyara zama Abba yayi sannan yace, haruna banfa hanaka mardiyya ba, abu ɗaya nakeson kagane shine wani baya auren matar wani idan Allah ya kaddara mardiyya matarka ce babu wanda ta isa hana auren ku dole kai zaka aure ta, idan kuma Allah yasa ba matarka bace duk son da kake mata dole zaka hakura , rashin dangana ga abunda zuciya takeso yana jawo dan Adam ya butulcewa ubangijin shi… yanzu abunda nakeso dakai katuromin babanku muyi magana..
Haka yatashi ya tafi jiki ba ƙwari.
Da yamma mama tasake kaiwa farida ziyara, farida tanajin tausayin mamanta yadda sam bata gayawa kanta gaskiya kuma bata ganeshi… hannu ta mama ta rike tace karki damu manga na jibi kamar yaune yana belin ki zan ɗaukeki muje katsina gidan kawata..
Mama nifa hankali na a kwance yake kece nakeson ki kwantar da hankalin ki dan Allah duk abunda yayi farko zaiyi karshe..
Naji karki damu, hankali na zai kwanta ne idan naga kinsamu rayuwar data dace dake… haka sukayita taɗawa farida tana nusar da uwarta akan abubuwan dasuka dace…
Bayan su mummy sun isa takira baban farida tana tambayan shi akan maganan auren dataji yace zaiyi dagaske ne?
Yace mata dagaske ne anbani Mata yar limamin masallacin mu, nace sutayani neman mata me tarbiyya babbar mata ko budurwa, shine yacemin akwai wata ƴarshi tagama NCE kuma ta haddace alqur’ani me girma idan inaso inje ingan ta mu tattaunawa idan mun sasanta sai in mishi magana, ba laifi naje mun sasanta duk da yarinya karama ce amma tanada hankali da kamala da dattaku… bazata wuce sa’ar su farida, amma ni mashaa Allah hakan tamin..
Toh Alhamdulillah nima nayi farin cikin jin wannan labarin dama inata tsoron kar gidan ka ya mutu… Allah ya tabbatar da alkhairi yace Amin.
Zeezee kasa zama tayi don haka tana idar da sallan la’asar tawuce gidan su mardiyya… tana shiga mardiyya ma daidai lokacin take sallama, zama tayi tareda yin tagumi, bayan mardiyya tagama addu’a ne taƙare mata kallo tabbas zeezee tana cikin damuwa don ita mutun ce me fara’a da yawar magana, duk abunda zaisa kaga tayi shuru kuma har annuri yaɗauke a fuskar ta ba karamin abu bane…
Bayan ta tattara abun sallah gefen ta taje ta zauna, sannan tace lafiya zeezee naganki cikin tashin hankali haka?
Huh ajiyan zuciya ta sauƙe sannan tace lafiyan daikam da sauƙi..
Gayamin meyafaru please ?
Mardiyya mujaheed ne…
Murmushi mardiyya tayi aranta tace bakince ke soyayya bazai saki damuwa ba, bari dai mugani..
Kallon ta zeezee tayi tace meye kike smiling tun kafun kiji meyake faruwa…
No babu komai fa, gayamin dai yanzu abunda yafaru…
Mardiyya haka kawai ba waya ba zuwa dubani babu duk wani caring na soyayya ace wai haka kawai rana tsaka yacemin wai zai turo iyayenshi…
Da sauri mardiyya tace ke kuma sai kikace mishi meye?
Ce mishi nayi bazan aure shi ba…
Meyasa zaki gaya mishi haka gaskiya baki kyauta ba..
Kamar ya? So kawai kikeyi ince mishi ya turo?
Amma ai yadda kuke soyayya tsarinki ne, kece bakyason damuwa, ni inaga shiyasa shima yasaba da yadda kikeso kuma kowa yasan mujaheed nasonki..
Adaa kenan mardiyya, yanzu fa ana iyayin sati biyu bai kirani ba, kuma dai keda kanki ma kin faɗa damuwa ne banaso amma dole zanso kulawa tunda nima mutun ce…
nidai inaga a yanzu ne zai gane darajar soyayya ta idan har ya dage, amma idan najishi shuru nasan basona yakeyi ba…
Umhm… hakan ma ba laifi… I trust you nasan kinayin komai ne da tunani amma dan Allah karkiyi pushing ɗinshi dayawa kinsan mujaheed yanada abunda ko wace mace zata so shi...
Hakane… nan sukaci gaba da tattaunawa.
Zeezee bata daɗe ba suna gama magana tafita… ga mamakin ta tana zuwa gida mujaheed tasamu yana jiran ta… nan suka fara kwasan drama amma ko kaɗan bai barta tashiga gida ba, dole saida ta tsaya sukayi magana nan ya ɗauki tsaraban daya kawo mata yabata, yace dama tun ɗazu ma dashi yazo don kawai ta tafi basuyi sallama ba shiyasa bai bataba, sannan yace mata yanzu kam ai komai yawuce ingayawa daddy na…
Tsuke fuska tayi tace gaskiya saitayi tunani, yace bakomai zai jirata tagama tunanin… amma tasani wannan karon a soyayyar shi ba ɗaga kafa..
Abbas ji yayi bazai jure rashin ganin mardiyya ba.. don haka ko Kiranta baiyi ba yakama hanyan gidan… yana shigowa ya kalli ya harun a harabar gidan…
kallon kallon sukafarayiwa juna.. daga karshe yawuce ciki yabarshi a wajen, cije baki harun yayi yace gaskiya nayi sake yanzu har yaron nan yafini samun daman shiga ciki… amma dai duk haka bazan sare ba..
Kiran ta yayi yace yana falo… ba dɓata lokaci ta fito, don ba ƙarya itama tayi kewan shi…
Tunda ta fito yakasa ɗauke idon shi akanta, ita kuma hakan baƙaramin takura ta yayi ba…
Don haka ko idonta takasa ɗagawa..
A hankali yace please karkimin rowan ganin kyakkyawar fuskarki mana… kinsan fa nayi ƙoƙari.. ai kuwa kamar zugata yayi hannun ta duka biyu tasa ta rufe idon…
Ko ki buɗe ko inzo in buɗe… da sauri ta buɗe tana zare ido amma sarai tasan zai aikata.. don haka tahau kame tafara tura baki tana cewa to ai kaine saikayita kallon mutun… kasa take maganan, yace me kikace, babu tace tana ɗan satan kallon shi ta gefe..
Murmushi yayi wanda yabayyana dimple ɗinshi sannan yace in tambayeki mana..
Jin ya anbaci tambaya yasa taɗauki duka hankalin ta tabashi, yace meyasa kikejin kunya ta dayawa nifa mijinki ne..
Murmushi tayi tana kallon kasa tace nifa haka nake..
Yace shikenan nikuma saina cire miki..
Megadi ne yayi sallama yacewa mardiyya tayi bako… kallon juna sukayi da Abbas sai lokacin ma ya tuno da ya wuceshi a waje, take annurin fuskarshi ya ɓace…
Kallon megadin tayi tace wayene?
Yace haruna ne…
A razane ta kalli Abbas shiko kauda kai yayi kamar bayajinsu..
Tace kace bana nan…
Da sauri Abbas yace kace mishi tana zuwa…
Kallon Abbas kawai takeyi…
Saida megadin yatafi tace mishi nifa bazan je ba..
Meyasa?
Banida abun faɗa mishi…
Hmm… nima bawai inason kiganshi bane, kawai na baki chance ne kuyi maganan karshe kice mishi an bada ke, banason inkara ganin ku tare..
Kallon Abbas kawai takeyi yadda yayi maganan in a serious tune..
Kije kidawo kinji…
zatayi magana yace shshshh Dan Allah karkice komai kijeki please…
Ba musu ta tashi taje…
Yayi farin ciki da mamakin ganin ta, kawai yatura ne amma baiyi tunanin zata fito ba…
Ɓata rai tayi sosai… amma shi ko kaɗan hakan bai dameshi ba…
Ba walwala tace mishi gani… cikin farin ciki yace nagode da kika bani daman ganinki..
Hannu taɗaga mishi tace a gurguje nakeson kafaɗamin dalilin nema na domin ana jirana…
Mamaki yakeyi wai mardiyyan datake bashi girmane yau take mishi magana ba ɗa’a?
Dan Allah mardiyya kiyafemin kinsan inasonki, kawai mutane ne suka shiga tsakanin mu, yaron nan dayake koya miki karatu na tabbata da hannu shi aciki sai yanzu nake ganowa ashe tarko aka ɗanamin..
Kayi hakuri ya harun mu rabu cikin mutunci kuma ina ganin girmanka, kadaina jifan Abbas da munanan kalamai saboda yanzu ma albarka cinshi kaci, shiya samma lokaci kuma yace inzo wajenka..
U see baga irinta ba, wallahi munafurci ne mardiyya ki yadda dani inasonki… kuma banajin zan iya rabuwa da ke duk rintsi…
Rabuwa dani kam aikayi shi angama tun ba yau ba, nikam zan shiga kuma dan Allah karka sake zuwa wajena…
Tana kaiwa nan tajuya cikin yanata kiranta amma taki juyowa, haka ya juya cikin tashin hankali….
Tana dawo wa ana kiran sallah don haka Abbas tashi yayi yace toh zanje massalaci kuma kinsan yanzu nabar anguwan nan inaga kawai sai gobe…
Kallon shi kawai takeyi tana son tagano ko ranshi yaɓaci… amma sam batagane yanayin shi..
Saida tarakashi bakin kofa.. ta kira sunan shi cikin sanyin murya tace… ya Abbas! Juyowa yayi, a hankali tace I’m sorry nasan ranka yaɓaci…
Murmushi yayi yace mezai ɓatamin rai bayan nasan inada ke… kawai dai kishin mata ta nakeyi.
Bazan so yacigaba da zuwa wajenki ba..
Inshaa Allah bazai sake zuwa ba..
Ana idar sallahn magrib ya harun wajen baban su yawuce… zuwa yayi ya sheda mushi yadda sukayi da Abba sannan yagaya mishi akan yace yaje suyi magana..
Take baban ya haɗa rai, yace lallai haruna bakada kunya… toh bari kaji zanje amma zance mishi yafita a harakar ka ya aurar da yar shi, tun wuri kaje ka nemi wata, donma kaci sa’a Alhaji sabir yanada hakuri dawani ne ai korar kare zaima..
Dan Allah baba karkamin haka wallahi inason mardiyya bazan iya rabuwa da ita ba…
Rabuwa da ita fa yazamoma dole, saboda anbada ita.
Baba idan kaje nasan Abba nagani mutuncin ka komai zai iya canjawa..
Haruna na lura kafara samun matsala a kwakwalwar ka, ni ba marar lissafi irinka bane, kaga tafiyata ma banason damuwa…
Washegari tun sassafe baba yaje yayi belin farida daga nan direct Abuja suka wuce…
Abba yana fitowa zaije aiki yacikaro da harun a waje yana jiranshi… gaisawa sukayi kawai yafara cewa dan Allah Abba akan maganan mardiyya ne ka temakamin..
Shifa Abba gaskiya lamarin haruna yafara bashi tsoro, wannan wane irin abu ne? amma dai yasan ta inda zaishawo kan abun…
Toh haruna kaga yanzu office zanje, ai nace kagayawa babanku ko…
Abba yace ko yazo saidai ya zuga ka…
Naji kabari idan nadawo ni zanje insame shi…
Koda mardiyya ta baiwa zeezee labarin abunda yafaru jiya…
Shuru zeezee tayi don ita yanzu lamarin ya harun ma kunya da haushi yake bata shi wane irin mutan ne da bazai karɓi kaddarar shi ba…
Daddy ya kira Abbas yake shaida mishi appointments ɗinsu yafito shida nabil don haka next week suzo verification, sannan dole zai tsaya da service ɗin nan yazo ya rike aikin shi tunda watannin da suka rage mishi ma kaɗan nan…
Nabil dayaji labarin nan ya rasa inda zaisa kanshi don farin ciki, don haka take yawuce gida ya sanarwa maman shi… itama tayi farin ciki ba kaɗan ba, sai yanzu take ganin amfanin jajircewan nabil akan karatu gashi Allah yanata bude mishi kofofi…
Nasiha ta mishi akan duk rintsi karya manta alherin Abbas da iyayen shi, karya yaci amana zumunci ya rikesu tamkar yan’uwan shi…
Abba dakanshi yaje yasamu baban su zeezee, yamishi bayani halin da suke ciki da harun, buɗan bakin baba cewa yayi kafita a harakan shi ka aurar da ƴarka, ni shawaran dazan baka ma shine kajawa bikin yarinyan nan yadawo kusa kusa inaga idan yaga an aurar da ita dole zai hakura…
Abba yace hakane bari zan kira iyayen Abbas ɗin muyi magana..
Yakira daddy ya shaida musu halin da ake ciki kuma yace idan bazai takurasu ba yanason amaida bikin nan da sati biyu…
Ba jayayya daddy ya Amince.. suna gama waya yakira Abbas ya shaida mishi halin da ake ciki… Abbas kam ma yarasa me zaice tsabar farin ciki he can’t believe it wai nan da sati biyu mardiyya tazamo matar shi, ikon Allah kenan meyin yadda yaso a lokacin da yaso…
Haka Abba ya kira mardiyya dasu goggo da anty yasanar musu abunda yafaru da dalilin dayasa aka matso da bikin…
Kowa yayi murna banda mardiyya, don jitayi kamar an ɗaura mata wani nauyi… nanda sati biyu shikenan tazamo matar aure? She can’t believe it…
Take akafara tattaunawa akan hidiman bikin tako ina…
Abbas ma cikin farin ciki ya kira mardiyya amma ga mamakin shi sai yaji tasa mishi kuka…
Ji yayi duk jikin shi yayi sanyi… a hankali yace me yakefaruwa mardiyya bakyason auren ne? idan bakyaso sai inyi magana afasa… da sauri tace a’ah ni ba auren bane so, yayi kusane ta ina nasan zan fara ya Abbas..
Huh… indai wannan ki kwantar da hankalin ki bazan barki ke kaɗai komai tare zamuyi kinji, kuma zan kasance dake har karshen rayuwata… da haka yayita kwantar mata da hankali..
Kiran zeezee tayi nan tazo suka fara tattauna yadda zasu fara abubuwan…
Washegari tun safe faisal yaje gidan su farida don a yadda sukayi da yakamata tadawo gida… yaci sa’a daidai lokacin baba zai fita don haka suka gaisa yake ce mishi yazo duba farida ne, baba yace mishi ai tana abuja… number dazai sameta ya tambaya, number mummy baba yabashi sannan sukayi sallama.
Mama dayake yanzu kowa rayuwar shi yakeyi a gidan babu ruwan ta da neman baba balle yasan shiganta da fitan ta…
Don haka sassafe ta tafi prison amma ga mamakin ta akacemata ai tun jiya akayi belinta… take zuciyar ta tahau tafasa to ina hanif yakaita? Meyake nufi?
Amma tayiwa kanta alkawarin bazata kulashi ba sai tadawo daga katsina don haka daga wajen direct katsina ta wuce..
Ta isa bayan azahar tana ɗan hutawa kaɗan suka wuce wajen boka… take yafara musu duba akan matar da hanif zai aura… shima saida ya firgice yahau muzurai suka tambayeshi ko lafiya? Yace musu aifa ba lafiya ba don yarinyan da za’a aura tana tsaye da kafanta bata wasa da addini kullum tana cikin kariyar addu’o’i…
Zama hajiya ladi tagyara tace toh malam babu abunda za a iyayi..
Yace abu ɗaya zan iya yi shine bayan tashigo gidan sai musan yadda zamuyi mu koreta…
Saboda babu abunda zaikamata daga nesa saidole tazo ansamu yadda za’a ciyar da ita dakuma sauran abubuwan…
Haka dai suka bar wajen boka babu wata kwakkwaran madafa…
Ya harun kuma yanzu bashida wajen zama sai kofar gidan su mardiyya abun har ya fara sashi zama kamar wani zautacce..
Faisal yakira mummy ta haɗashi da farida… bakaramin girman faisal farida take gani ba, saboda bayan abunda yafaru nan babu wanda yakasance da ita sai shi…
Abbas kam yanzu baya baiwa mardiyya iska, duk inda take yana nan, kamar yadda yayi alkawari… baya barin ta taji wani damuwa ko kaɗan…
Mujaheed ma yasamu ya lallaɓa zeezee ta yadda amma tace tabari sai bayan bikin mardiyya kafun iyayen shi suzo saboda yanzu batada zama..
Anty kuwa tadage wajen gyara ƴarta don tun randa aka matso da bikin sukafara gyaran jiki da duk wani gyaran daya kamata ayiwa amarya.. don haka kullum kyanta kara fitowa yakeyi, babu yadda anty batayi ba wajen ɓoyewa Abbas mardiyya ba amma sunki bata haɗin kai saboda yanzu sun dawo kamar cingum…
A satin bikin su sukaje verification… basai na kwatan muku yadda nabil da bilkisu sukafaɗa cikin farin cikin ganin juna ba, ansha soyayya na kwana biyu kafun suka gama suka dawo…
A wannan satin baban hasib yadawo take ya kira commissioner of police ya rufeshi da faɗa akan meye zai bari har a yankewa ɗanshi irin wannan hukuncin… hakuri commissioner yayita bashi yace wallahi abun yafi karfinshi ne saboda human right sun shiga..
Toh yanzu dai kasan yadda za’ayi yafito zanturama abubuwan bukata a account ɗinka…
Shikenan Alhaji amma fa saidai idan yafito yabar garin sai bayan kamar shekaru biyu yadawo…
Bakada damuwa akan wannan kasarma zaibari…
Cikin dare akazo akacireshi… murmushi ta gefen baki shi yayi yace aidama nasani idan daddy na nan bazanyi zama prison ba kuma duk sunci bashi wallahi….
Yaune ranar walima gobe kuma za’a ɗaura aure… sam sunce bazasuyi bidi’a ba…
A yaukam nima dakaina dakyar nagane mardiyya saboda shekin da takeyi, ta zamo tamkar balarabiyya duk inda tawuce saitabar tsaraban kamshi… abundai ba’a magana..
Yaukam fir anty taƙi tace sam Abbas bazai ganta ba yabari gobe idan ankai mishi ita sai ya ganta…
dole haka ya hakura amma kusan kwana sukayi suna waya… yan uwan mamanta ma sunzo daga bauchi gida yacika sosai.
Washegari ƙarfe biyu aka ɗaura aure…. Abbas jiyake duka ranakun shi na duniya babu ranan dayakai wannan… bakinshi sam baya rufuwa sai karɓan gaisuwa sukeyi shida nabil sun sha fararen kaya… karkuso kuga yadda yake haska waje farin mutun cikin fararen shiga abun sai mashaa Allah…
Tun bayan magrib akafara kimtsa amarya… ana sallan isha’I akazo ɗaukan amarya za a kaita gidan shi na nasarawa gobe sai su wuce abuja…
Ƴan kususu ne sukazo don haka akafara ƙoƙarin fito da ita bayan angama mata duka nasihun da iyaye keyi…
Da kawayen amarya sunkin bada ita, sunce sai ankai mutane amma masu ɗaukan amarya sam sukace su amarya zasu fara ɗauka…
Koda aka kaita bakin motan da suka tanadar domin ɗaukan ta, nan ma sukace ango yace ita kaɗai za’a ɗauka a wannan motan… abun haryaso yajawo tashin hankali saboda yan uwan mamanta sunce dole ko mutun ɗaya yabita… amma ganin yadda suka dage ɗin akabaiwa yanuwan ta haƙuri..
Haka tashiga motan tana kuka kamar ranta zai fita…
Zeezee ma ranta yaɓaci don haka ba shiri takira Abbas tafara ce mishi gaskiya bai kyauta ba…
Saida tagama maganan yace shifa yan kususun shi yanzu suke zuwa kuma hardashi za’azo donshi yakeson yaɗauki matarshi dakanshi..
Take zeezee taji ta kiɗime tace toh ƴan kususun da sukazo suka tafi da amarya fa suwaye?
Take yaji ya gigice yace bangane ba, me kike fadane haka..
Nima bangane meyake shirin faruwa ba, Abbas dan Allah kazo bansan mezanfara faɗaba…
Gani nan yanzu nan..
Ko bayani bai iya yiwa mutane ba yace maza dukan su suzo su tafi, tsabar tashin hankali baiwa nabil key ɗin yayi don yanajin bazai iya tuki ba…
Zuwan sune ya tabbatar da cewa ba gidan su Abbas bane suka ɗauki amarya ba..
(toh fa gaskiya zeety saitasha tea kamar na sati biyu sannan muje neman amarya)
*ZEETY DELIGHT*💖