Free chapter · Read without an account

chapter 31

by Zainab Yerima · MURADIN RAI

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 




*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋 





_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*





_ku kara hakuri dani🥰🤗_ 




By: *ZEETY*💞 





*wattpad @Zeety-AZ* 

karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻 





31📚




Lokacin ya harun ya ankara da abunda yake shirin faruwa… take yahau sambatu yana cewa wallahi bazaiyu ba mardiyya mata tace babu me hanani aurenta… zeezee ya kalla tareda nunata da yatsa yace ke kuma zaki gamu dani dake za’a haɗa baki a munafurceni ko, sannan ya juyo kan Abbas kai kuma wallahi inkayi yunƙurin shiga tsakani na da mardiyya zan iya hallaka ka, wallahi nine zan auri mardiyya..



Subhanallah malamin yace sannan yace ku fahimtar dani abunda yake faruwa, zeezee ce ta matso gaban ya harun hawaye na zuba a idonta tana girgiza kai tace wannan ba yaya na bane, ba haka ya harun ɗina yakeba, ya harun ɗina mutun ne me nutsuwa da cikar kamala sannan da sanin yakamata... hannu shi ta riƙe tace dan Allah yaya na kadawo hayyacinka kasan me kakeyi wallahi na tabbata akwai abunda yasamu kwakwalwar ka…



Daidai lokacin police suka shigo tareda Abba, Abba ma ya girgiza da ganin harun, tattara su akayi duka amma dukda haka bai daina sambatu ba… zeezee gwiwan ta tasa akasa tana kuka kamar ranta zai fita, wai shin ma meta aikatane da hannun ta aka kama yayanta, in maa taji tashiga uku…


Mardiyya ce ta dafa kafaɗan ta, sannan itama ta tsuguna a wajen, tace zeezee nima jikina naban ya harun yasamu matsala wannan ba yaya harun ɗinmu bane hawaye ne yafara bin fuskarta tace amma ki kwantar da hankalin ki inshaa baza a mishi komai ba…


Abbas ne yakaraso kansu yace kuyi hakuri ku tashi mu tafi…


Abbas buɗewa mardiyya kofar baya yayi, nabil da zeezee suka zauna a gaba shikuma ya shiga gefen mardiyya, tada motar nabil yayi a yayin da Abbas ya rike hannu mardiyya gam… kallon shi tayi sannan ta kalli nabil da zeezee... murmushi yamata saboda yagane meye take nufi, matsowa yayi daf da ita sannan yasa hannu shi yazagaye kafaɗan ta dashi yazamanto dukanta tana cikin kirjin shi.. ajiyar zuciya tasamu kanta da saukewa a hankali ta kwantar da kanta ajikin shi tareda lumshe idonta shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya matseta gam… wani iska me daɗi taji yana shigarta wanda bata taɓajin irin shi ba, take nutsuwa ya sauƙo mata sai yanzu takejin kanta a killace batajin wani sauran fargaba a zuciyar ta…


Ba suma san an iso ba muryar nabil suka tsinto yana ce musu, mudai mun iso gida amma kuɗin bansan ko zamu barku acikin mota ba.. dasauri mardiyya ta janye jikin ta tafara kokarin buɗe kofa , hannu shi yasa akan nata ya rike, juyowa tayi tana kallon shi shiɗin ma ita yake kallo… a hankali ya zura hannu shi a cikinta tareda cusa kanshi acikin wuyanta acikin kunneta yace inason in karajin ki ajikina ko zankara samun nutsuwa…. Lumshe idon ta tayi tsabar yadda ya kashe mata jiki ko lebenta takasa buɗewa balle tayi magana… 


a hankali yace mardiyya dan Allah ki kasance dani har abada kar barni duk rintsi… hawaye ne suka fara bin fuskarta a zuciyar ta tace ta ina zanfara barinka na tabbata kaine jigon numfashi na… shunshuna kamshin wuyanta yakeyi yace tell me please bazaki taɓa barina ba… juyowa tayi, tayi hugging ɗin shi, sosai shima sosai ya kankameta… cikin muryar datake shaking tace ni yakamata innemi wannan alfarmar, saboda rayuwa ta idan babu kai aciki zato zamo tamkar nikaɗai ce a duniya ta…. Dan Allah Abbas ka kasance dani har abada, kara matseta yayi ajikin shi yace inshaa Allah surooraty!



Zeezee kam tana fita gidan su tawuce nabil kuma dayaga Abbas bashida niyyan fitowa don haka sai yabi bayan zeezee…


Yana shiga yasamu har labari ya iso gidan su don haka zeezee tana shigowa maa tahau kanta da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba sallaman nabil ne yasa tayi shuru…


zeezee ce tace mishi ya kariso, zama yayi sannan yagaida maa sama sama ta ansa don ranta a ɓace yake sosai, baban su ne yashigo… shima kana ganin shi zakaga bacin rai karara… zama yayi zeezee da nabil suka gashe shi…



Kallon maa yayi yace kinga irin abunda nake gayamiki kullum nason zuciya da son kai abunda yajawowa harun, yakasa ɗaukar kaddara tsabar sonkai gashi yanzu abun ya taɓa mishi kwakwalwa…



Cikin faɗa maa tace duk abunda yasa meshi da hannu zainab aciki saboda ta fifita kawarta fiye da ɗan uwanta…



Cikin tsawa baban yace nifa rashin hankalin ki yafara isata ban taɓa ganin inda ake girma anacin kasa ba sai a kanki… ai zainab rahma ce a gidan nan don tafimun dukan ku kuma bazan daina godewa Allah da yabani ƴa irinta ba… da badon itaba ba’asan meye harun zai aikata ba, kinga temaka mishi tayi data tsamoshi daga halaka…


Jikin maa sanyi yayi saboda itama kanta tasan sonkai ne yasa take biyewa harun, to amma ya zatayi kowa yajuya mishi baya dole ita ta fuskance shi….


A hankali tace yanzu ina haruna yake? Ajiyan zuciya baba yayi sannan yace da aka kirani a station ɗin naje nasamu anata rikici dashi sai sambatu yakeyi ko nima yakasa nutsuwa ya kaleni balle muyi magana…


wannan dalilin yasa akace ana tunanin yasamu taɓin hankali ne don haka a wuce dashi asibiti…. Mun wuce asibiti take aka haɗamun da likitan kula da kwakwalwa yamishi gwaje gwaje dayagama allura ya mishi wanda atake bacci yaɗaukeshi… shine yayi mana bayani akan lovestruck ne yakamashi wato ciwon taɓin kwakwalwar da mutane ke samu a sakamakon soyayya, kuma bakaramin hatsari bane dashi saboda yakan iya sa mutun aikata komai koda kuwa kisa ne…. 

Zare ido maa tayi tadafe kirjin ta sannan tace yanzu kana nufin shikenan haruna ya haukace….


girgiza kai yayi yace bai haukace ba saboda zaiyi mu’amala lafiya da kowa, akan wacce yakesone ciwon zaina tashi…..


Yanzu ma likita yace abunda yasa ya birkice sosai saboda yaga ana ƙoƙarin rabashi da mardiyya ne…


Fashewa da kuka maa tayi tace ayyeh haruna am meyasa kazabi irin wannan soyayyan meyasa yarona….kuka takeyi kaf wajen babu wanda yayi yunkurin hanata harsaida tayi sosai sannan baba yayi ajiyan zuciya yace ya isa haka wannan kukan bashi yakamata ki mishi ba addu’a yakamata kimishi kowane bawa baya tsallake kaddarar shi, abu nagaba kuma banason inji kina jifan zainab da mumuna nan kalamai, idan baki godewa Allah da ni’imar azurta ki da ƴa kamarta ba, bai kamata ki butulce mishi ba… 


Share hawayen ta tayi tace hakane ko ni kaina nasan na haifi yarinyan da ta fini zurfin tunanin kuma kullum ina godewa Allah daya bani ita, akan maganan haruna ne nake ganin laifin ta wannan ma kuma nasan son zuciya tane amma lokuta da dama nima zuciya ta nagaya min tafimu gaskiya …


samun mutun irin zainab a zamanin nan shiyafi komai wuya…


Nabil ya karɓa da cewa gaskiya ne mama kunyi dace da ƴa mai hankali da zurfin tunani ga kuma tsoron Allah don akan gaskiya zata iya ɓatawa da kowa, me gaskiya kuma ko waye ne zata iya tsaya mishi… muma kanmu kwaɗayin halaye irin nata mukeyi da kuma yaba mata a ko wane fani...


baba ne yace kinji ko meyafi wannan daɗi ace har mutane waje suna gane kyawawan halayen abunda ka haifa, hakane Alhaji ba abunda zamuce sai Alhamdulillah… 

Yaushe ne zaka kaini asibitin inganshi? Umh sai anjima domin yanzu haka bacci yakeyi shiyasa likitan ya sallame mu…. Toh shikenan bari yanzu inje in mishi girki….



Bayan sungama guntun romance ɗinsu da koke koke… dasauri mardiyya tazare jikin ta tana cewa ya kamata mu shiga a kofar gida fa muke….


Suna fitowa daidai lokacin nabil yana fitowa daga gidan su zeezee, ganin lokacin suke fitowa a mota yasashi kama baki, hararan shi Abbas yayi yace meye? 

Kunshe dariyar shi nabil yayi yace babu, amma kuzo maza mushiga ciki in sanarwa Abba da yabaka matarka tun yanzu ku tafi kafun ayi abun kunya, kamar dagaske yakama sauri, tsayawa mardiyya tayi tareda yin narainarai da idanu tace dan Allah nabil karkamin haka juyowa yayi ya kwashe da dariya sannan yace ai baki isa ba kusan awanki guda acikin mota kin makale, inbaso kike akai ɗakin ki ba ai da tuni kin shiga gida…


hawaye ne sukafara bin fuskarta tana cewa wallahi nabil ba haka bane dan Allah ka tsaya… 

Hannu ta Abbas yakama yace da Allah rabu dashi inyafasa… hannun shi yasa yana share mata hawaye yace ji zakiyi asaran hawayenki a banza, indai nabil zaki biyewa wataran saiya sa miki hawan jini..


Juyawa yayi yacewa nabil kai kuma kaci bashi inadai matata kasa kuka, saina zana wannan figigiyar budurwar taka… 

Da sauri yazo gaban mardiyya tareda kama kunne shi yana cewa affuwan matar yaya wallahi na manta ne… kiyafewa in law ki kinji harda karya wuya irin abun tausayin nan ita dariya ma ita yabata….


Suna shiga ciki suka samu su Abba a falo… goggo na ganin su tace ku kuwa ina kuka tsaya tuntuni munajira muga shigowan ku….abba ne yace ai danaga motan su nasan sun shiga gidan su zainab ne, Abbas takalla dawuri ido yakashe mata dasauri ta sunkuyar dakanta aranta tana cewa nashiga uku kaddai Abba yaganmu…


Maganar shi ne yadawo da ita…. Yace toh mudai babu abunda zamu ce saidai muce Alhamdulillah, acikin kwanakin da bai wuce wata daya da wani abu ba munga jarrabawa iri iri babu abunda zamuce saidai mu godewa Allah… mardiyya Allah yasa iya karshen wahalan ki kenan duka wajen suka ansa da Amin… kafun ku shigo munyi magana akan tafiyan mardiyya gidan ta, danace kawai ku wuce da ita, amma su goggo sunce akwai gajiya a tattare da ita a bari sai jumma’a, nidai nace ajiraku saboda yanzu sai abunda Abbas yace don shi yakeda iko akanta idan yace zai tafi da matarshi babu wani matsala yanzu sai ku wuce… gyara zama Abbas yayi sannan yace babu wani abu Abba abari sai jumma’an kawai nima nasan tagaji tana bukatar hutu…


Toh mashaa Allah ba wani abu Allah yayi muku albarka..


Goggo ce tazo gefen mardiyya tace sannu kawata, rayuwar ki tana kunshe da jarrabawa kala kala… fatana Allah yabaki ikon cinye kowane jarrabawan duniya… 

Kai kuma angon mu kaga dai mardiyya marainiya ce kuma kaga irin yada rayuwa take fama da ita, dan Allah Abbas ko bama duniyan nan ka riketa amana batada wani gata yanzu sai kai… kuka ne yahana goggo karisawa… a hankali tace Allah yayi muku albarka sannan ta tashi tawuce ɗakin ta tana share hawaye… jikin kowa sanyi yayi, mardiyya kam kamar an buɗe mata sabon shafin kuka, anty ma kasa magana tayi….



Da yamma duka gidan suka shirya domin dubo harun…suna shiga ɗakin da yake daidai lokacin yake tashi daga bacci…maa ce tafara shigowa da sauri ya mike yana cewa maa kinga inda suka kawoni wai don na ɗauki mata ta, kema shaidace mardiyya batada masoyin daya kaini, kuma nasan itama tana sona, dan Allah maa ki fitar dani anan inje insamu mardiyya ta karsu kaita gidan yaron nan, batason shi ki yadda dani maa Allah gaskiya nake gaya miki… kuka maa tafashe dashi don dagajin maganar kasan ba lafiya ba, zeezee ce ta turo kofan tareda sallama, shanye maganan dayakeyi yayi yace maa zainab batada hankali kuma bata sona, kina ganinta tana abu kamar mutumiyar kirki wallahi da ita aka haɗa baki aka kamani, nidai bazan sake kulata ba amma maa ki lallaɓeta ita kaɗai ce zata iya samomin mardiyya … zeezee ma kuka ne yaci karfin ta, bata taɓa tunanin matsalar tashi takai haka ba… ta tausaya mishi wannan wane irin soyayya ce haka….


Dakyar maa ta lallaɓeshi yadaina surutu… tareda mishi alkawarin zata kaishi wajen mardiyya sannan ya hakura.


Bayan sun gama duba shi maa tayi magana da baban su akan su nemi transfer akaishi maiduguri saboda ciwon shi bata tunanin asibiti zai magance sai dole sai an haɗa da rokon Allah, ba musu baban su yaje yayi magana da likitan take aka fara musu processing akan gobe kawai su kama hanya….



Maman farida tana can katsina boka yagama shirya mata komai, tana shirin dawowa don saura kwana biyu auren Alhaji hanif da khadija, tsabar kiɗima bata gane komai damuwar ta kawai taganta a kano taga idon hanif ko kunya babu wai aure zaiyi tana raye, sai yayi tagani…



Baban hasib yayi niyyan tada rikici dayaji an samu mardiyya kuma ba hannu hasib aciki, commissioner of police ne yace mishi rikici banashi bane, don ɗanshi tsohon me laifi ne, yin hakan zai iya tono wasu rufaffun ɓarnan shi, yanzu kamata yayi yasa ɗanshi yayi nesa da Nigeria kuma inda hali yakaishi wajen horo wato rehabilitation, shuru yayi sannan yace hakane kayi gaskiya, nasan inada kaso mai tsoka wajen lalacewar hasib, yakamata in zamo sanadin shiryuwar shi kodon gujewa abunda zai faru gaba… kuma idan har hankali yazo mishi zai tsaneni gwara hankalin yazo mishi da hannu aciki… yauwa haka nakeson ka fahimta tun ba yau ba mashaa Allah tunda kagane gaskiya da kanka… 



Kamar kullum faisal ya kira farida a waya suna jajanta abunda yafaru, a hankali yakira sunan ta … ansawa tayi tareda bashi duka nutsuwar ta don dagajin yadda ya kira tasan akwai magana… cewa yayi yaushe zaki dawo ne? shuru tayi sannan tace bana tunanin zandawo…. Rufe idon shi yayi ya buɗe sannan yace meyasa? Ajiyan zuciya ta sauƙe sannan tace faisal da wane idon zan fara ganin mutane, na aikata abun kunya me tsanani kuma zamana a kano zai iya hanani samun miji…


Murmushi yayi sannan yace nidai ban karɓi dalilan ki, ido ta buɗe cikin mamaki tace meyasa?


Yauwa kinga nafarko idan akan abunda yafaru ne, yariga dayafaru kuma yawuce kuma mutane da kike gani mantuwa ne dasu more especially ma idan mutun yacanja daga mummuna zuwa mekyau…


na biyu kin riga dakin samu miji saidai in ke kika ƙishi…


Shuru tayi sannan tace kaine kamin mijin?sosai ma kuwa… murmushi tayi tace gaskiya bazan karɓeshi ba saboda nasan baisani ba kuma bazan cuce shi ba…


Yafi kowa sanin ki kuma a hakan ya yadda dake kuma yakeson ki… karki damu zuciyar ki da tunani bawani bane sai faisal..


Zaro manyan idanun ta tayi tareda sa hannu a baki… kamar yana kallon ta, ji tayi duk jikin ta yayi sanyi… a hankali yace kiyi hakuri idan na miki shishshigi, idan ban miki ba karki damu kigayamin amma dan Allah karkice zaki daina kulani… wasu hawaye ne taji suna zuwa mata… ta ina tasan zata fara? Faisal dayasan ta tareda munanan ayukan ta, bazan iya ba gaskiya…


Farida kiyi magana please… karkiji nauyin gayamin abunda ke zuciyar ki karki barni a duhu please….


Cikin muryar kuka tace please faisal karkayi haka, dan Allah kabari muyi zumunci kawai… da sauri yace meyasa?...


I didn’t deserve you… baka cancanta da mace irina ba, u know how bad I was…


Shshshh banason jin wannan maganan… a hakan nace inasonki saidai in kuma keɗin ce bakya so na, hawayen idon ta ta goge sannan tace faisal idan nace bakamin ba nayi karya saidai kawai banason in cuceka ne…


Kidaina tunanin wani abu, karkisawa ranki wai inason temaka miki ne… ko kaɗan ba haka bane zuciya ta ce ta aminta dake, so nake in rayu dake acikin rayuwa ta… dan Allah karkiyi kokarin tureni, ki bani daman shigowa cikin rayuwar ki…. 


Kuka ne yaci karfin ta har shiɗewa takeyi…


rintse idon shi yayi saboda har ranshi yakejin kukanta…. A hankali yace it’s ok, kidaina wannan kukan haka karkisawa kanki ciwo, zan baki time kiyi tunani kinji, kashe wayan yayi tareda tsayawa yana kallon wayan itama wayan ta take kallo hawayen idonta basu daina korar juna ba…..



Mardiyya ita kaɗai a ɗaki tana tariyo abubuwan dasuka faru… ji take kamar a mafarki… a hankali tayi murmushi sannan tace wai yanzu shikenan nazamo matar aure… ya harun ta tuno wani ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kira zeezee bayan sun gaisa ne tace mata ya labarin ya harun? Nan zeezee ta kwashe duk abunda yafaru tagaya mata…. Sosai mardiyya ta girgiza dajin irin ciwon da yake damun shi kuma wai a dalilin ta, innalillahy wa inna ilayhir raji’un dama har haka yakeson ta? Wannan wane irin bala’I ne… 

Zeezee to yanzu wane mataki aka dauka…


murmushi zeezee sannan inshaa Allah zai warke gobe zamu wuce maiduguri dashi za’aje a mishi rokon Allah acan…. 

Allah yasa a dace inji mardiyya zeezee ta ansa da Amin…


Bayan sun gama ta ajiye wayan tana tunanin duniya saiga wayan Abbas… ɗauka tayi tareda yin sallama lumshe idon shi yayi muryar ta tana ratsa kunnuwa zuwa sassan jikin shi…ansawa yayi tareda cewa babe… murmushi tayi Wanda yaji sautin shi a kunnen shi… cikin wani irin yanayi yace I need my wife… inason inji ɗumin mata ta, inason ina ganinta akusa dani banason idona su ɗaukewa ganin ta…. 

A hankali ta rufe idon ta ta buɗe tanajin soyayyar shi yana ratsa dukkan jikin ta… 


Anya kuwa zan iya hakuri zuwa Friday? Banason kiyi nesa dani banason ko kuda ya taɓaki…. Murmushi bai ɗauke a fuskar ta tace karka damu indai wannan ne, ina gida ba abunda ba abunda zai sameni… kema ai kinsan ba wannan bane kawai…. Bakinta ta rufe tana noke dariya saboda tagane meyake nufi… a haka sukaci gaba da waya yanata bayyana mata kalan soyayyar da yake mata….


Washegari tun sassafe su maa suka tashi zuwa maiduguri amma dakyar ya yadda aka ɗaukeshi saida aka ce mishi wajen mardiyya ma za’a kaishe kafun ya yadda …. Ganin haka yasa likitan yimishi alluran bacci saboda karya ya musu rikici…


Kafun baba ya fita faisal yazo yasameshi… ya shaida mishi auren farida yakeson nema…. Yaji daɗi sosai kuma yace kar yadamu ya turo iyayenshi kawai…


Take baba hanif ya kira mummy ya shaida mata… itama farin ciki ta shiga, don haka ba ɓata lokaci ta sanarwa daddy sannan tace mishi kasan meye nakeso yace a’ah, inason bilkisu tacewa nabil ma ya turo iyayenshi kullum basuda aiki sai waya duk ina lura da abubuwan dasuke faruwa kawai ban mata magana bane… murmushi daddy yayi yace Alhamdulillah gaskiya yau kinci kyauta me tsoka , saboda kin kawomin labarai masu daɗi wayanda suka sani farin ciki… naji daɗi danaji nabil shiyake neman bilkisu ba shakka Allah ya azurtamu da sirki ɗan Amana, Hakane nima abun yamin daɗi yanzu zanje in sanar dasu….


Kiransu tayi labarin na farida tafara faɗa musu take taga farida ta firgice…. Hannu ta mummy takama tace meyafaru? Ko bakyason shi ne, idan bai miki kigayamin babu me miki dole… girgiza kai tafarayi cikin kuka tace ba haka bane mummy, shi idan bai kini ba ainima banida dalilin kinshi mummy inason shi don faisal yamin halacci shikaɗai yasoni a lokacin da duniya takini….


Murmushi mummy tayi tace mashaa Allah, bilkisu takalla tace kema daddy yace kicewa nabil ya turo iyayenshi ido ta zare tareda buɗe baki harararta mummy tayi tace ohh da kin ɗauka bamusan me kuke ciki bane, idon ta rufe tareda rungume mummy, dariya mummy tayi tace yaran zamani kenan…. 



(kuyita addu'a insamu in muku typing kafun in gudu🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️)




*ZEETY DELIGHT*💖


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol