Free chapter 路 Read without an account

11/12

by Rabiatu bashir 路 SILAR FYA茒E

*馃崁SILAR FYA茒E馃崁*

      Free Book 




     NA馃拫

UMMU MAHER(MISS GREEN馃挌)


Wattpad user name

  Rabiatu333


Arewabooks

rabiattu0444







   11馃煢12



. . . .haka muka yi ta kukanmu babu mai rarrashin mu tun daga ranar babu wanda ya 茦ara kukani,Salimat da khadija ko kallon inda na ke ba sayi,Afra ce kawai ke kulani don dama hutun sallah suka zo.






 *Bayan wata uku 3*




  Rannan ina 茩wance naji wani mugun ciwo baya ya kamani ga ciwon mara me tsanani ni ka蓷ai a cikin 蓷aki ina ta kiran sunan Allah gwanin ban tausayi abin sai wanda ya gani,na ha蓷a wata uwar zufa sannu a hankali gumi ya ringa tsattsafomin 蓷an cikina ya koma 茩asa baki 蓷aya yana ta motsi kamar zai fito.

 Afrah ta shigo kawomin abincin safe taga halin da nake ciki,da sauri ta je ta kirawo su Khadija sai da suka zo bu蓷e bakin Salimat ta ce"wallahi da ina da dama da sai na kashe Wannan cikin harda uwar ma,don sun jawo mana raini da cin fuska da zagi a gari,ta juya ta kalli Khadija ta ce to ni dai na tafi wajen Asil birthday 蓷inshi idan kinga dama ki zauna wajen wannan akuyar idan kin ga dama ki taimake ta".

 tana fa蓷ar hakan ta saka kanta gaba ta yi tafiyarta.



Khadija ma tafiyarta ta yi tana surutai,Afrah ta kalleni cikin tausayi ta ce"Anty jikin da sau茩i yanzu ko in aika akira abba a majalisa".



 Da sauri na girgiza mata hannu alamar kada ta kirasa,ni dai kawai kiran sunan Allah na ke asannu ,a sannu kan 蓷a ya fara fitowa na 茩wanta a kan gado ba bu蓷e 茩afafuna Afra ta ri茩e hannuna tana zubar da hawaye,kanta a sunkuye don ba ta son ganin tsiraicina,a haka na dinga fa蓷in sunan Allah har 蓷a ya fito kyakkyawan yaro fari 茩al kamar 蓷an larabawa.

Da gudu Afrah ta fita tana ha蓷a hanya ta shiga gidan Mmn Nusaiba don ta fa蓷a mata,ta kalli Afrah she茩e茩e ta ce oh yau Allah ya yi an haifi shege ni da ina da iko da sai na kashe shegen banza".

 Tana fa蓷in hakan ta yi shigewarta 蓷aki tana ta surutai.


 Har ta fito daga gidan ta hango mmn junior kishiyar Maman Nusaiba,ta ce"a ah lfy Afrah me ya farunne?".kunsan maganar gwarawa.



Nan Afrah ta fa蓷a mata a ta茩aice,da sauri Mmn junior ta fa蓷a gidan tun kafin Afrah ta 茩arasa fa蓷a mata.


Tana shiga 蓷akin ta jiyo nishin Rabiatu da sauri ta 茩arasa ciro mata 拼ar budurw 茦ya茩茩yawar gaske,wani gauran numfashi Rabiatu ta saki tana kiran sunan Allah.


 Yaran mmn junior ta fara gyarawa tsaf,sai dai babu kayan saka musu da sauri ta tafi gida ta 蓷ebo kayan da ta fara tarawa saboda haihuwar da za tayi watan gobe, kala biyar ta 蓷ebo masu kyau ta sakawa yaran sukayi 茩yau gwanin sha'awa.



 Sannan ta gyara Rabiatu tsaf ta gasata da ruwan zafi sannan ta ri茩o ta kamar 茩aramar yarinya,ta saka Afrah ta dafa min ruwan tea da harda madarar 拼an boarding su Afrah.



wani kuka ne yazo min tuna maraici,idan banda maraici me zaisa har mace ta haihuwa a rasa me gyarata,duk da cikin shege ne amman da mahaifiyarta tana nan duk 茦in da ta ke yiwa yaran za ta kulasu.


 Asannan na tuno da AUNTY Rabiatu 茩anwar mahaifiyata wacce ta ke a merica da mijinta,wacce har yanzu bata san yayarta ta rasu ba,saboda sanin irin halin da zata shiga.

***     ***     ***



wani mummunan fa蓷uwar gaba yaji a take ya zauna yana fa蓷in sunan Allah messenger 蓷insa ya shigo kawo mai sa茩o,da hannu ya nuna mai ya ajje ya tafi,messenger 蓷in ya kalli ogan nasa amman babu damar magana saboda halin da ya tsinci kansa alokaci 蓷aya,ya shiga kiran sunan Allah har dai abin ya tsagaita masa,amman ranar babu damar aiki don haka ya nufi gida,don har yanzu zuciyarsa zafi ta ke masa.





 ***  ***   ****



"Aliyu abinda ka ke ka yi gaggawar zuwa gida ina son yin magana da kai".


"oky hjy gani nan zuwa".


Hajiya Barakat ta zauna a 蓷aki tana jiran zuwan Aliyu,Fatima tace"Hajiya kada ki fa蓷awa Bro wannan maganar ransa zai 蓳aci wallahi".cikin yaren yaroba ta fa蓷i hakan.


Hajiya Barakat ta daka mata harara ta cigaba da danna wayarta.






*Miss green ce*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.