Free chapter · Read without an account
1-2
*ZURU...!*
_*Warmth of love and compassion*_ 😢❤️
Fri, May 27.
*FATIMA SUNUSI RABIU*
_UMMU AFFAN_🤏
*Godiya ta tabbata ga sarki Allah me kowa me komi. Dubun tsira da aminci ya ƙara tabbata ga Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bisa har zuwa ranar sakamako.*
DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN ƘAI.
*FREE PAGE 1-2*
Ina zaune takure a jikin ƙofar parlournmu. A ƙalla na kai wajen awa ɗaya ko ma fiye da hakan, hawaye ne wasu ke bin wasu a kan kumatuna, ya yin da wani sabon kuka ya ƙwace min.
Wannan rayuwar ta isheni baƙinciki yayi yawa a gare ni. Wacce irin mummunar rayuwa nakeyi a cikin gidanmu? Ace mutum da uwarsa da ubansa amma yake cikin mawuyacin hali, anya Umma ita ce ta haifeni? Nasha yiwa kaina wannan tambayar. Domin ko makaho ya shafa yas an da walakin goro amiya, ma'ana dai duk wanda ya kalli yanayin zamana a gidan zai iya fahimtar ba itace ta haife ni ba.
Zuciyata tayi rauni yaushe ne za a sanar dani sirrin dake bibiyar rayuwata?
Wata tsawa da na ni ita ce ta dawo dani daga duniyar tunanina, Aunty Rahma ce na ga ni tsaye a kaina sai wani jijjiga take. Kallona tayi a wulaƙance kafin ta ce "Makira munafuka mai halin mayu maitar ce taki ta motso?" Duk da na sa ba jinn irin wannan kalaman, amma a kullum najisu sai naji ba daɗi a raina.
Na ce "Kiyi haƙuri Aunty Rahma ba wani dalili yasa ni zama anan ba" Ɓata fuska tayi tare da fusgoni ta haɗa da garu (Bango) ta fara kima.
Cewa take, ''Uban me ki ka zauna yi anan munafuka? Salon baƙi suzo su ce cutarki ake? Muryar Umma muka ji wacce tafito daga Parlour ta ce,
"Ai munafincinta ya wuce da haka Rahma, so take ubanku yadawo ya ce na mata wani mugun abin" Itama taja wo ni "Yar kaza-kazan ubancen ayi mace sai shegen fi'ili kamar ƴar gidan wani hamshaƙin? Sai anyi mata abu tazo tana Allah Annabi kamar wata ta ƙwarai?"
Kuka nake ina bata haƙuri "Don Allah Umma kiyi haƙuri bazan sake ba"
Tsaki taja "Mtsuuww!" Ta sake ni. A gurin na zube. Ta kalleni, "Wallahi kika shugo min parlour sai na karya ki shegiya kawai"
Ta kama hannun Rahma sukayi ciki. Rahma har da sa ƙafa tasake tureni. Sosai nake kuka ina tausayawa kaina da rayuwata, nayi ƙasa da kaina ina matse ƙwalla kafin wasu zafafan hawaye su wanke mini fuska daidai shugowar Abba.
Da sauri ya ƙaraso sai ji nayi yana share hawayena. Na miƙe cike da murna da niyyar ɓoye damuwata. Amma na makaro kallo ɗaya Abba yai min yasan ina cikin damuwa, daman daga shi sai yah Al-ameen su ke gane halin da nake ciki sai ko ƙawata kuma aminiyata Zainab.
Kallona yayi ya ce "Naanah me ki ke yi anan har yanzu? Baki ganin dare ya fara? Kuma ba na hanaki zama waje idan dare ya yi ba? Ko ba komai ma wannan sanyin da ake sai ya shiga jikinki mura bata da daɗi Mamana."
Ɗan murmushin yaƙe nayi, tare da kamo hannunsa nace "Abba kai fa nake jira ka dawo, nasan zaka Sayomin tsarabata shiyasa ko abinci banciba sai kadawo" Shima murmushin yayi ya ce "Naanah manya! Ke sai an Kawo miki tsaraba sannan Zakici abinci ko?"
Turo baki gaba nayi cike da shagwaɓa nace "Abba ba kai ne ka koya min ba? Kumatuna ya ja yana dariya yana san gani na cikin farinciki, kama min hannu ya yi muka shiga ciki.
Su Umma suna Parlourn muna shugowa ta bi mu da harara tare da taɓe baki. Zaunawa mukayi ina liƙe jikin Abba kaina a ƙasa ko ɗagowa na ka sa dan ban san mu haɗa ido dasu. Soyayyar doya da Ƙwai Abba ya miƙo min cike da murna na amsa don rabona da abinci tun safe, buɗewa nayi nahauci. Abba da kallo ya bini ya ce ‘’Naanah kin ci abinci kuwa?" Ɗago kaina nayi aikuwa muka haɗa ido da Umma kallon da ta min yasa da sauri na gyaɗa kaina kamar wata ƙadangaruwa "E! Abba naci" Na faɗa tare da ɗaukar doyar nayi ɗakina. Jikina ya bani kallona suke har na shige ciki.
ABBA POV.
Mai do idanuwansa ya yi gurin Umma bayan shigewar Naanah ciki ya ce "Karimatu na dawo babu sannu balle in samu matsayin ko ruwane a bani nasha" Wani mugun kallo ta watsa masa kafin cikin rashin ɗa'a ta ce,
"Sai yanzu ka ganni tun da ta tashi ko?" Girgiza kai ya yi ya ce "Kiji tsoran Allah Karimatu. Naanah fa ƴarki ce me ya sa ki kee nuna mata banbanci da sauran yaranki? Baki tunanin jefa rayuwarta cikin wani hali da garari?" "Mtsuuww!" Taja wani mugun tsaki mai ƙarfi ta ce, "A Inda ba ƴa kenan, ni ka dena haɗani da waccen shegiyar yarinyar" Karimatu!!" Abba ya kira sunanta cikin tsawa. Da sauri tayi shuru tana wani yi masa kallon tara saura kwata.
Miƙewa ya yi ya kalli Rahma ya ce "Ina Sakina?" Kame-kame ta fara don har yanzu Sakinar bata dawo gida ba. Girgiza kai ya yi tare da faɗin Allah ya shiryaku" Ya wuce cikin ɗakinsa.
Da sanɗa Sakina ta shugo gidan domin ta daɗe da dawowa ganin Abba a falon yasa bata shugoba, sai da taji ya shiga ciki. Umma ta ce "Me ne ne na wani sanɗa?" Ta ce"Uhmm Umma Abba mana, kin san halin tsohon nan yanzu ya cikawa mutane kunne da wani wa'azinsa me kama da faɗa"
Guri ta samu ta zauna Umma ta ce "Me aka samo mana? Yau Allah ya sa akwai kuɗi masu auki kin san zan kai kuɗin adashi da nake tarawa idan bikinku yazo(A'uxubillah wai ke uwa ce ke faɗin hakan, Allah ka shiryamu ka shirya mana zuria)
Sakina ta turo baki gaba "Wallahi ke Umman nan kin cika san banza, ni da dhan wuya ke da ƙwace kuɗi. Kin san ma me nayi na same su?" Umma ta ce, "Dan kaza-kazanki ban son ji, idan ban barki kin fitan ba zaki samesu? Sai in haɗaki da tsohon naku in ce gaki kin dawo, daman yanzu ya gama tambayarki" Sakina ta ce "Ke Umman nan kin cika kwafsi, daga wasa nifa wasa nake miki" Nan ta buɗe zaka ta kwaso kuɗi taba Umma. Nan haƙora suka washe ta ce "Da kyau 'yar albarka, kin ga da bikinki zaki kwashi kaya, ban da su Naanah da ba abin da aka iya sai zaman gida da zuwa makaranta hali sak irin na tsoho" Gabaɗaya suka sa dariya har da tafawa.
NAANAH POV.
Girgiza kai nayi daga cikin ɗakina, nayi juyi a kan yamutsattsiyar katifata hawaye na tsiyaya. Sai yaushe Umma zata ga ne gaskiya ta kula da tarbiyyar yaranta? Allah ka shiryasu. na faɗa tare da goge hawayena nayi addu'ar barci. Nan take kuwa barcin ya kwasheni.
Washe gari da wuri na tashi kamar kullum, alwala na ɗauro na gabatar da sallar salatul fijur, sannan nayi sallar asubah, na daɗe ina addu'o'i sannan na shafa.
Kasancewar ranar asabar ce babu boko, sai na koma na kwanta. Juyi kawai nake ina tunanin irin rayuwar gidanmu, ban kai ga yin barcin ba naji ana kwala min kira. Ta shi nayi ina tafiya cikin sanyina, duƙawa nayi sai tin Imma wacce ita ce tayi kirana.
Nace, "Umma gani!" Cikin masifa ta ce "Wallahi duk munafurcin ki sai dai ki tsaya iyakar uban naku da Yayanku amma ni bazaki min shi na bari ba"
Aunty Sakina ta ce "Shegen ido kamar na mujiya tana abu sai ka ɗauka ta ƙwarai ce. Simimi kasau da ita sai kace mutiniyar arziki"
Ni dai ban ce musu komai ba, sai ƙasa da nayi da fuskata hawaye na zu ba. Aunty Rahma ta ce "Duk kukan ki na banza ne, domin yau ba zaki je wannan makarantar ba aiki zakiyi" Umma ta amshe maganar da cewa "Abu dole, ai ko bakiso baki kuma ƙaunar gyatumin ki sai kinyi tun da ba zakije ki wani kwantaba sai anyi kici."
Ban ce musu komai ba, na nufi kitchen ɗin, ni kaina ina son yin aikin girki don naƙara ƙwarewa. Sai dai Abba ne ya hana ta sa ni ganin sa ga manyan ƴan mata nan gabanta ba ta saka su ba sai ni.
Sauri-sauri nayi aikin don ƙarfe takwas da rabi muke zuwa Islamiyya, kuma malaminmu ya yi gargaɗi akan duk wanda bai zo ba bulala goma, dan hadda ya bada, kuma zai iya. Malam Sani ba shi da Sauƙi akan karatu. Ni kuwa a duniya idan akwai abin da na tsana to bulala ce.
Ku san takwas saura na gama girkin, na jera komai a ƙara min dinning table ɗin mu, sannan nazo na gyara kitchen ɗin na wuce ɗakina.
Toilet na faɗa, wanka nayi sannan nazo na shirya cikin uniform ɗina purple colour na saka safa na ɗauki niƙaf ɗina a hannu. Parlour na dawo har sun gama breakfast ɗin su, gurin kaca-kaca
Tsintsiya na ɗauko na tattara gurin sannan na karya. Na ɗau ki na wankewa na wanke sannan na fito na ɗ'aura niƙaf ɗina, har lokacin Abba bai fito ba, daman idan ya dawo masallaci yana daɗewa kan ya fito, ɗakinsa na shiga yana zaune kan prayer mat yana lazumi, ganina yasa ya yi addu'a. Duƙawa nayi kusa da shi na gaishe sa, amsawa ya yi cikin sakin fuska da nuna kulawa.
Ya ce, "Naanah har an shirya kenan?" na ce "E! Abba zan wuce sai na dawo" Sha fa kaina yayi ya ce "Allah ya yi miki Albarka ya kareki a duk in da ki ka shiga" Cikin farin ciki na amsa da "Amin Abbana" Gabaɗaya mukayi dariya sannan na sake masa sallama na wuce.
Kasancewar makarantar ta mu ba wani nisa gareta ba, a nan ƙasan layinmu ne da ƙafa ta na ƙarasa. Ina zuwa kuwa Malamin da zai amshi haddar na gani cikin ajinmu, na shiga cikin ajin da sallama a bakina.
Ya kalleni sama da ƙasa sannan ya ce, "Naanah Firdausi Isma'il zo nan" Dawowa nayi na tsugunna daga ƙasan sa na ce "Gani Malam"
Ina ganin agwogwon gidanku bai tafiya dai dai ko?" Ya tambaye ni, ƙasa nayi da kaina ci ke da ruɗani, ni kaina nasan na makara domin tara dai dai na fito daga gida.
A hankali na ce, "Dan Allah Malam kayi hakuri wani aiki nayi" Ya ce "Wanda ya saki aikin bai san lokacin makaranta ne ba?" Yana gayar hakan yana zaro bulalarsa, cikin sauri na miƙe a razane nayi cikin ajin, kallona ya yi yana zare min ido, sannan ya ce "Ke Naanah na lura daman duk cikin ajin nan kin fi kowa raina ni ko?"
"Dan Allah don sonka da Annabi muhammad S A W kayi hakuri bazan sake makara ba" Na faɗa idona rau-rau kamar zan saki kuka.
Ajiye bulalar ya yi yana kallona sosai kafin ya ce"Shi kenan na rabu da ke, amma idan ba ki iya haddar dana baku jiya ba kin san sauran"
"Na yarda" Na amsa sannan na tsugunna na fara yi mishi karatuna cikin natsuwa da ba ko wanne harafi haƙƙinsa, bayan na gama a ka yi kabbara, sannan naje na zauna inda na saba zama, wato kusa da aminiyata Zainab Ibrahim.......
_Sabon salo, kuma sabon kafce daga alƙalamin Ummu Affan. CIKIN WAYE RETURN NE Salonsa da banne sai kun biyoni cikin tafiyar zaku gane inda na dosa._
*ALLAH KA ƘARAWA IYAYENMU LAFIYA🙏 WAƊANDA SUKA RASU ALLAH YAJI ƘANSU.😭*