ZURU...!Free

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

ZURU...!

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1-2

*ZURU...!*  _*Warmth of love and compassion*_ 😢❤️Fri, May 27.*FATIMA SUNUSI RABIU*  _UMMU AFFAN_🤏*Godiya ta tabbata ga sarki Allah me kowa me komi. Dubun tsira da aminci ya ƙara tabbata ga Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bisa har zuwa ranar sakamako.*DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN ƘAI.*FREE PAGE 1-2*Ina zaune takure a jikin ƙofar parlournmu. A ƙalla na kai wajen awa ɗaya ko ma fiye da hakan, hawaye ne wasu ke bin wasu a kan kumatuna, ya yin da wani sabon kuka ya ƙwace min.Wannan rayuwar ta isheni baƙinciki yayi yawa a gare ni. Wacce irin mummunar rayuwa nakeyi a cikin gidanmu? Ace mutum da uwarsa da ubansa amma yake cikin mawuyacin hali, anya Umma ita ce ta haifeni? Nasha yiwa kaina wannan tambayar. Domin ko makaho ya shafa yas an da walakin goro amiya, ma'ana dai duk wanda ya kalli yanayin zamana a gidan zai iya fahimtar ba itace ta haife ni ba.Zuciyata tayi rauni yaushe ne za a sanar dani sirrin dake bibiyar rayuwata?Wata tsawa da na ni ita ce ta dawo dani daga duniyar tunanina, Aunty Rahma ce na ga ni tsaye a kaina sai wani jijjiga take. Kallona tayi a wulaƙance kafin ta ce "Makira munafuka mai halin mayu maitar ce taki ta motso?" Duk da na sa ba jinn irin wannan kalaman, amma a kullum najisu sai naji ba daɗi a raina.Na ce "Kiyi haƙuri Aunty Rahma ba wani dalili yasa ni zama anan ba" Ɓata fuska tayi tare da fusgoni ta haɗa da garu (Bango) ta fara kima.Cewa take, ''Uban me ki ka zauna yi anan munafuka? Salon baƙi suzo su ce cutarki ake? Muryar Umma muka ji wacce tafito daga Parlour ta ce,"Ai munafincinta ya wuce da haka Rahma, so take ubanku yadawo ya ce na mata wani mugun abin" Itama taja wo ni "Yar kaza-kazan ubancen ayi mace sai shegen fi'ili kamar ƴar gidan wani hamshaƙin? Sai anyi mata abu tazo tana Allah Annabi kamar wata ta ƙwarai?"Kuka nake ina bata haƙuri "Don Allah Umma kiyi haƙuri bazan sake ba"Tsaki taja "Mtsuuww!" Ta sake ni. A gurin na zube. Ta kalleni, "Wallahi kika shugo min parlour sai na karya ki shegiya kawai"Ta kama hannun Rahma sukayi ciki. Rahma har da sa ƙafa tasake tureni. Sosai nake kuka ina tausayawa kaina da rayuwata, nayi ƙasa da kaina ina matse ƙwalla kafin wasu zafafan hawaye su wanke mini fuska daidai shugowar Abba.Da sauri ya ƙaraso sai ji nayi yana share hawayena. Na miƙe cike da murna da niyyar ɓoye damuwata. Amma na makaro kallo ɗaya Abba yai min yasan ina cikin damuwa, daman daga shi sai yah Al-ameen su ke gane halin da nake ciki sai ko ƙawata kuma aminiyata Zainab.Kallona yayi ya ce "Naanah me ki ke yi anan har yanzu? Baki ganin dare ya fara? Kuma ba na hanaki zama waje idan dare ya yi ba? Ko ba komai ma wannan sanyin da ake sai ya shiga jikinki mura bata da daɗi Mamana."Ɗan murmushin yaƙe nayi, tare da kamo hannunsa n...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters3
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play