Free chapter · Read without an account
Chapter 8 Chapter 8
ZAMANINMU!!!
(Hattara yanmata)
Written story
By
AUTAR AREWA
Bismallahi Rahamanir Rahim.
🅿️8
📝Bayan kwana biyu,Farrah abin duniya duk ya dameta saboda ita dai harga Allah rabata da wayan da yayi ji take kaman ya cire wani bargo na jikin ta.
Wani tinani ya fado a ranta,tsam ta mike da ga kwanciyar da tayi bisa doguwar kujerar falon ta,takalma ta saka ta dauko hijaf dinta ta nufi hanyar gate.sosai take sauri domin kuwa bata san Momy ta ganta,wurin Baba Auwal mai gadin gate din ta nufa,zaune yake bisa farar kujerar roba Yana sauraron labaran gidan radio,Yana hango ta ya tashi da saurinsa.
"A Hajiya da kanki kika fito,ko kina bukatar wani abu ne"?.
Karasawa tayi tana gaishe shi "Ina yini Baba Auwal"?Lafiya lau Hajiya"
"Am dan Allah Baba so nake yi ka aroman yar karamar wayarka,tawa ta kiyi ne ga shi ina so inyi Kira".
Da saurin shi ya amsa da "To to ba damuwa Hajiya"Dakin shi ya koma ya dauko mata.
"Ga shi bata karasa yin chajin ba,Amma nasan ya isheki har ki gama abinda zakiyi,akwai sauran kati a ciki dan jiya Yusuf ya turoman".
Amsa tayi tana godiya "Yanzu zan dawoma da ita insha Allah".
Bayan gidan ta nufa inda yake da wata yar rumfa kaman ta zana,da fashion na roba masu kyau kalan orange,ciki ta shiga tare da zama Kan daya da ga cikin kujerun, Nomber Hasan ta sanya ta danna call sai da ta kusan cinkewa kamin ya daga,Ba tare da ta bari yayi magana ba ta ce "ka Kira ni ce Farrah" ta katse Kiran dan bata so ta cinyema dan tsohonnan katin shi.
Dan danan ya biyo nomber da ta Kira shi.
Tana dagawa cikin nutusuwar ta furta "Assalamu alaikum sweetyna".
Sosai ya sauke ajiyar zuciya dan kuwa har tana jiyo Jan numdashin da yake.
"Sweety Ina kika shige Ina ta Kiran phone dinki bata shiga, why meya yake faruwa ne"?
"Wallahi matsala aka samu,kasan bazan kashe wayata ba har tsawon kwana hudu,ni kaina duk na damu Ina so inji muryan ka amma ba hali yanzuma wayan Baba Auwal ce na amso duk dan na kiraka".
"Cikin jin haushi ya ce "waye ya anshe wayar taki"?
Shiru ta danyi kafin ta ce "sweety ba fa anshewa aka yi ba,ta lalace ne amma da Dady ya dawo da ga tafiyan da yayi zai siyaman sabuwa".Dan ita har ga Allah a zuciyar ta ta ji ba zata iya fadamai zalimu ne ya anshe mata waya ba,saboda duk da tana San Hasan bata jin dadin yadda yake kushe mata dan uwa,dan ko ba komai Yaya Yasir jininta ne bata da yadda zata yi da shi. (Kai Farrah kodai-kodai kina........🤣🤣ehmmm bari dai inyi shiru kar Jabir ya ji ni 🤭.)
"Ok ai nayi tinanin wannan yayan naki ne ya anshe ta". Amma kina ji na?
"Eh ina jinka sweety na"
"Gobe zan zo in kawo maki sabuwa sai ki dora layin ki,dan kinsan ban jin dadi idan ban ji muryar ji ba".
Hmmm murmushi tayi sosai dan tasan halin rigimar shi."kasan ya za'ayi"?
"A a saikin fada"
"Ka bari basai kar Kawoman waya ba,saboda zan fuskanci matsala idan aka ganni da wata,idan har ba su suka saiman ba,Amma Insha Allah zan rinka aron wannan muna waya kamin su bani wata ka ji ko sweetyna,karka damu ni nasan ba mai rabamu insah Allah"ta karasa fada tana turo karamin bakinta kaman tana gaban shi.
Ajiyar zuciya yayi yana dunkule hannunshi kaman zai naushi wani abu.
"Ba matsala sweetyna na yarda da ke , saboda nasan kina so na".
Daga nan suka ci gaba da firar su irin ta masoya,har sai da ta kwantar mai da hankali kamin suka yi sallama.
Sai yanzu taga dadewar da suka yi suna wayar kusan awa biyu suka shafe.Baba Auwal ta mayar wa da wayar shi ta nufi cikin gidan,Allah ya taimake ta ba Wanda ya ganta momy tana site dinta Nusaiba ko tana makaranta.
***************
Duk cikin week dinnan haka al'amura suka yi ta tafiya.inda a bangaran Farrah duk basu yi mata dadi,sai dai godiyar Allah.
Suna zaune a Falo ita da Momy a yammacin ranar juma'a hira suke yi sosai,inda Momy take Kara yimata nasiha akan al'amuran zamani tare da bata shawarwari a gameda 'al'amuran samarin wannan zamanin.Nasihar tana shigarta sosai dan sai yanzu take gane illar da Yaya Yasir yayi kokarin yimata a shekarun baya,Wanda har zuwa wannan lokacin ba Wanda ya sa ni,Daga ita sai shi,sai Kuma Allah.
Sosai ta lula duniyar tunani,inda kunnuwan ta suka daina jin Nasihar da Momy take yimata.
Momy lura tayi kamar hankalin ta baya wurin,ta dan girgiza ta da hannu.
"Farrah tunanin me kike yi haka kinyi shiru"?
Firgigit tayi alamar bata cikin nutsuwa.
"Ah ehm Momy ina jinki"ta na Yan kame -kame alamar rashin askiya.
Momy tsayawa tayi tana kallanta ba tare da ta ce komai ba,har tatsawon wasu mintina.l
"Farrah akwai abinda yake damunki,amma tunda bakya san ki sanar da ni ba komai,Amma ki sa ni ni dai a matsayin diya kike a wajena,kuma Ina iya bakin kokari na dan ganin na nusar dake daga hatsarin dake cikin wannan zamanin".
"Ba komai momy,Ina jin dadin zama da ke,dan ko Aunty bata yiman irin nasihar da kike yiman,nagode Allah ya saka da alkhairi.kuma insha Allah idan Ina da matsala zan sanar maki,duk da yanzu akwai abinda yake damuna amma na barwa zuciya ta"ta karasa fada tana mai rungume Momy ta kwantar da kanta bisa kafadar ta.
"Ba komai Farrah ki ci gaba da addu'a komai zai daidai ta insha Allah".
Sunyi shiru na dan tsawon wani lokaci,sai Farrah da take ta sauke ajiyar zuciya.
Sai daga bisani ta kalli Momy tana ce wa"Dan Allah idan ya zo yau ki amsoman key din mota ta,saboda wannan Monday din hutun mu yake karewa".
"Tau karki damu insha Allah zan amso maki".
"Tau Allah yarda,bari na je na kwanta Ina jin gajiya"ta na mikewa tsaye.
"Kada kiyi bacci yanzu,kinga yammaci ne ba'a son baccin yammaci".
Ta amsa da "To" tana shigewa bedroom dinta.
* * ** *** ** ****
Cikin ikon Allah Yasir a wannan ranar ya shigo katsin,sai karfe 8:00 daidai Baba mai gadi ya budema shi gate ya danno hancin motar sa.yana mai cike da farin ciki,Yana fitowa site din Momy ya nufa.Fitowar ta kenan daga kitching hannunta rike da cup tana juya coppe da spoorn ,Tana kallan shi ta wutsiyar idanun ta ta yi fiska da sauri ta shige bedroom dinta ta sanya key da sauri dan tasan ba wuya ya biyota.Tana sauke ajiyar zuciya ta ce"Dan kwawa duk weekend sai ya zo,duk kudin salaryn shi anan suke karewa dan rashi aikin yi irin na shi.
Haushi ya ji ya kama shi,juyawa yayi cike da jarumta ya koma part din shi.Wayar Momy ya Kira tana daga wa bayan sun gaisa ya ce"Momy yunwa nake ji,Dan Allah kiba Beby abinci ta Kawoman"
"Tau gatanan,Kuma ka bata key din motar ta da ka amsa".
"Tau Momy zan bata"
Dakin Farrah ta nufa,tana murda kofan ta ji shi a rufe.kwnoking ta yi.
"Farrah ta ce "waye"
"Ni ce bude kofar Farrah meye kika rufe kofa"?
A hankali ta bude duk da ta ji muryar Momy,Amma a tsorace take.
Tana budewa Momy ta ce"ki zo yanzu za ki kaima yayan ki abincin sa Yana part din shi,daga nan zai baki key din ki".
Ita dai sororo ta yi,saboda yadda ta ji kirjin ta ya amsa.ta rasa abinyi ta ce "Momy ganinan zuwa".
Momy juyawa tayi ta koma kiching din dan shirya abincin a babbabn faranti.ita kuwa farrah tunani take yi ta je ko Kuma ta ki zuwa,har ga Allah tana so ta amso key dinta Kuma Bata iya yiwa Momy gardama.
To readers ku bata shawara, shinya zata yi? Ta je ko kuwa. 🤣🤣😜😜
Pls following, vote, comment and share 👏.
BY
AUTAR AREWA.