Free chapter · Read without an account
Chapter 14 Chapter 14
ZAMANINMU!!!
(Hattara yanmata).
Pls ku dannamana subscribe a tasharmu ta Autah Novel Tv,A You Tube channel.
🅿️14
📝Yasir tunda ya fito daga toilet Kan bed dinshi ya kwanta da towel daure a kugun shi.ba bacci yakeyi ba eyes balls dinshi a rufe suke,sosai ya lula duniyar tunani a wani bangaran na zuciyar Shi Yana Addu'ar Allah yasa Beby ta zama mallakin shi.Yana cikin wannan tinanin ya ji Kiran sallar la'asar,Mikewa yayi ya dauro Arwalla tare da shiryawa sky blue na shadda ya saka dinkin yayi mai kyau saboda riga karama ce daidai guywar shi hannun mai link n,kanshi ba hula sau mai santsi da ya taje ta kwanta luf gwanin sha'awa.cikin azama ya wuce masallaci danya sauke farali.
-----------------------
Dady Bishir Yana isowa GRA derect gidan Dan uwan shi ya nufa,mai gadi ya bude mai ya shiga bayan sun gaisa cikin girmamawa,ya nufi hanyar da zata sada shi da falon gidan.A daidai kofar kofar sukayi kicibis,Abbah shida Jabir sun fito zasu je masallaci."A a Dan uwa Kaine tafe da yammacin nan,yanzu muke maganar da Jabir cewar "da mun fito daga sallah zai kaini gidan naka"Ashe kana tafe".cewar Abbah Yana kallan dan uwan nashi cikin so da kaunar juna.
"Wallahi kasa daurewa nayi kawai sai na fito,Amma mu je masallacin mu dawo sai mu tattana".
A haka suka wuce cikin nutsuwa da San junan su Jabir kuwa Yana gefen su.
**************
Farrah baiwar Allah ta dade a cikin toilet tana sharbar kuka,saida ta gaji saboda yanda ta ji kanta Yana saramata da karfi,kamin ta nufi jikin sink fara wanke fuskarta tayi kafin ta gyara jikin ta dan tana fashin sallah.sai a sannan ta tina ko abinci bata ci ba sakamakon kugin da ta ji cikin ta nayi alamar Yana bukatar abinci.Doguwar riga kadai ta zira ta dora dan siririn mayafin saman kanta.
A hankali ta nufi kiching din,cikin sanda dan kar kowa ya ganta tayi sa'a kuwa dan har ta shige ba Wanda ya ganta.Dambun shinkafa ne ta gani da miyar kabeji,Dan kadan ta sanya cikin plate ta dora nama akai bata tsaya daukar lemu ba dan tana da shi a fridge dinta.Cikin sanda ta samu ta shige dakinta,key ta murza a jikin kofar ta fara cin abincin ta cikin nutsuwa kamar wadda bata da damuwar komai a ranta.dan ita har ga Allah damuwa bata hanata ba cikinta hakkin sa.(kamar ni kike Farrah idan ma baka ci ba,to fa damuwar duniya dai kullun karuwa take yi😂😜).
Momy ko bayan tafiyar mai gidan nata,sosai ta lula duniyar tinani Dan ita a nata bangaran tafison a hada Jabir da Farrah, saboda tafi sabawa da shi Kuma zata fi samun kulawa da nasuwa sabanin Yasir da Basu Shan inuwa daya.Da wannan tinanin ta mike dan Kara gyara dakin mai gidan nata.
Pls follow, vote, comment, and share 👏
BY
AUTAR AREWA .