Free chapter · Read without an account
Chapter 23 Chapter 23
ZAMANINMU!!!!!
(Hattara ƴan'mata)
Page 23
Bismallahi Rahamir Rahim.
🅿️23
✍️Farrah tana kammala cin abincin ta mayar da plate din kitching ta dawo bisa gadonta tana jiran karasowar freind din ta.
Bilkisu a tare suka fito da saurayinta daga cikin dakin hotel din suka nufi motar shi suna firarsu da dariya.
Suna karasawa bakin gate din Barhim ta gaisa da masu gadin gidan saboda daman sun santa dan suna yawan shigowa da Farrah.ba tare da bata lokaci ba suka budemasu gate suka kutsa hancin motarsu cikin estate din sun danyi tafiya sosai kafin ta kawo su kofar gidan Basu shiga ba anan bakin gate din gidan daga waje ya tsaya.Saida suka Kara holewar su da tsotsar bakin juna kafin suka rabu ta kwankwasa kofar gate din.Baba Auwal lekowa ya fara yi Yana ganin ita ce ya hade Fuska gaisuwar ta ma a ciki ya amsa saboda shi harga Allah bai yarda da tarbiyar yarinyar ba dan daga ganinta suffar munafikai gareta .
Cikin jin haushi ya ce "yarinya lafiya dai ko ?Yana tsareta da ido.
"Ehmm daman na zo wurin Farrah ne,Ai tasan da zuwana ma"ta karashi fadi tana Kara yin kasa da kanta.dan ta fara jin haushin wannan tsohon da alama Yana iya kawomata cikas a plane dinta.
Maganar shi ta ji Yana cewa "Tau ba matsala shiga .
Cikin sanyi ta nufi hanyar da zata sadata da babban falon gidan.
Duk abinda sukeyi Farrah tana hangensu ta window din falon,Duk da akwai tazara Amma kana iya hangowa.tana ganin ya barta ta shigo tayi saurin fitowa daga falon da gudu ta tari kawar tata tana Kara jin farincikin ganinta.Dan tunda sukayi hutu sau uku kadai ta fita( daya ta je GRA ita da Momyn su sai na biyu da aka kaita salun a fita ta ukku ne tace zata je gidan su kawarta ta shi ne ta nufi hotel dan ta hadu da suarayin ta aka samu akasi Yasir ya kirata ta dawo gida ba tare da sun hadu ba).
Sosai itama ta kadandameta tana murnar ganinta hannunta ta ja suka wuce bedroom dinta ta saka ki a jikin kofar dan karma ayi rashin sa'a wani ya shigo ya ji abinda suke fada.
Fridge ta nufa drinks da swan water masu sanyi ta kawomata bisa dan karamin table din wurin ta aje tana zama kusa da ita .
Kallanta tayi tana cewa "kawata kinga yadda kika Kara kyau kinyi wani fresh da ke kaman amarya? Tana Kara taba fuskarta.
"Hmmm kedai ki zaunan nan kullum kina gida kamar bokanya,Baki da lokacin da zaki fita kidan shakata ke Bari ki ji ai ni yanzu nafi amarya saboda yanda nake shanawa ko amarya bata samun haka,ga kudi suna shigoman tako Ina bani da matsala ko nawa nake da bukata mutanena zasu cikamin jakata da cash kinga ko me zai dame ni"tana Kara girgiza jikin ta.
Hmmm a hankali Farrah ta sauke ajiyar zuciya tana Kara duban kawarta ta ta ce"hmm ke mazaki gane ba wallahi kinsan yanzinma wata matsalar ce tasa nace kizo muji yadda za'ayi danni gaskiya na ga ji. Wannan zalimun Kara matsaman yake yi ga Umman su harta fara tsana ta Ina dalili Kuma ko ni wallahi ba cewa nayi Ina San danta ba".Ta karasa fada fuskar ta cike da damuwa.
Bilkisu Kara matsowa tayi ta dafa kafadarta tana kallan idanunta dan so takeyi shawarar da zata bata tayi tasiri a zuciyar ta da gangar jikinta.
Cikin salo irin na gogaggun Yan bariki ta ce "Ai kawata naga kamar har yanzu Baki gama yarda da ni ba,saboda duk shawarar da nake baki bakya amfani da ita shiyasa ko abubuwa suke Kara tabarbare maki ko,idan kinyi dubi dani kinga yanzu bani da wata damuwa harkokin gabana kawai nake yi,Kuma shi aure da kike magana idan lokaci yayi duk zamiyi,Amma yanzu abinda nake so da ke ki kwantar da hankalin ki sannan duk shawarar dana baki idan har kin bita to bake ba sauran damuwa kina jina ko?ta karashe karshen maganar tana kashe murya.
Ita ko Farrah kamar kurma haka ta koma sai Kai ta gyadamata alamar tana jinta.
"Da farko ko aure suka ce zasu yimaki ki nuna kefa ba yanzu ba sai kin kammala karatun ki kin fahimta?
"Eh na fahimta am........
Da sauri ta katseta da cewa "Amma me ?ke matsalata da ke kenan gardama idan Kuma baki shirya amsar shawarata ba shikenan kinga tafiyata"ta dauki Jakarta tana nufar bakin kofar dakin.
Da sauri Farrah ta tarota tana "Haba kawata kar muyi haka dake mana dawo dan Allah a wanan karon nayi maki alkawari zan dauki shawarar ki kin ji"tana Kara rike jakarta.
Sosai ta tsuramata idanun dan ta gaskata abinda ta ji ta fada .Dan haka ta Kara kashe murya irin ta tausayi ta ce "A a Farrah kawai ki bari tunda har yanzu baki daukeni matsayin yar uwa ba ba komai ke kadai matsalar zata dama danni hankali na a kwance yake".
"Sorry my Friend "cewar Farrah tana janta zuwa bakin gadon.
Bayan sun zauna Bilkisu ta kalli Farrah ta ce yanzu kin shirya amsar shawata ko.
Da sauri ta gyada mata Kai alamar ta amimce.
"To idan na fara magana bana San gardama cewar Bilkisu".
"Karki damu kawata ai nasan ba zaki bani shawara banza ba" cewar Farrah da murmushi saman fuskarta.
Hakan yasa Bilkisu yin wani murmushi da ita kadai tasan ma"ma'anar shi.ta ce gaba da cewa "Da farko dai sai kin tsefare ma'ana sai kin daina tsoran kowa kin cire duk wani tsoro ko shakku da kike ji a cikin zuciyar ki,Kuma meye a ciki ke Bari ki ji in fadamaki da kin saba kin zama yar hannu da kanki zaki rinka nema.kuma meye a ciki dan munje gidan miji fanko ba abinda zai faru,Kuma yanzu zamanin nan da mutun yasha maganin mata shikenan miji bazai taba ganewa ba (ka ji wani batan basira da yammatan wannan zamanin ke yi).
Ta ci gaba da cewa "sannan batun yadda zaki rinka fita wanan karki damu ni nasan yadda zan bullowa lamarin,yanzu ai kince ya amshe wayar ki ko?
"Eh wlh tunda ya amshe bai mayar min ba har yanzu" cewar Farrah tana kwal kwal da ido kamar zata yi kuka.
"To karki wani damu komai zakiyi kiyi kokari a barki ki je school ranar Monday Nima insha Allah zan je to duk sauran bayani zamu karasa tattaunawa kin ji" tana kallan Idanun Farrah da itama ita kadai take kallo.
Cikin sanyi ta gyadamata Kai dan ita harga Allah har yanzu zuciyarta nayimata wasi wasi akan wannan shawarar Amma bata so tayi musu Dan kar kawarta ta tayi fushi da ita.
Cikin sanyinta ta ce "To ba matsala kawata insha Allah zanyima Momy magana ta ansoman key din mota na sai na je mu hadu ko?
"Yauwa ko kefa" cewar Bilkisu a zuciyar ta tana murna hakarta ta kusa cimma ruwa,Dan ita a kullun da wannan burin take kwana tasan ta Kara samun hanyar da zata rinka samun makudan kudade dan duk Alhaji da ta hada shi da Farrah to tasan ba makawa sai yayimata kyauta mai tsoka,Daman tana jin haushin yadda ta fita kyan sura da kyakkyawar fuska.
Ji tayi Farrah ta dafa kafadar ta "kawata me kike tinani"?
"Eh ahm ba komai kawata"tayi saurin wayancewa dan karta fahimci akwai wani abu.
Daga haka suka ci gaba da tattaunawa tana Kara bata shawarwarin banza.ita ko tana Kara dauka.
Lemun ta zuba mata a cup "kawata zaki tafi ko ruwa baki sha ba"
"No karki damu kawata kinsan tun jiya Ina tare da my shuger dan haka bana bukatar komai" ta karasa fada tana Kara kashe idonta daya.
Cikin mamaki Farrah ta ce "Kuma yanzu nan idan kika je gida baza'ayi maki fada ba?
"Hmmmm Farrah kenan ke har yanzu kina abu kamar baki San yadda duniyar take ba,Ai ko su Yan gidanmu ban barsu hakanan ba saida na tabbatar na rufe masu baki kafin na fara wannan harkar "
"Kamar ya"cewar Farrah tana Kara mamaki a zuciyar ta.
"Hmmm kinga mubar wannan maganar sai mun hadu a school duk zan yimaki bayani kin ji"ta fada tana murmushin mugunta.
"To ba damuwa kawata Allah ya kaimu" cewar Farrah.
Mikewa Bilkisu tayi ta dauki Jakarta tare da wayarta suka fito sakamakon Kiran da saurayinta yayi mata cewar Yana jiranta a kofar gidan.
Har bakin gate Farrah ta rakota suna ta labari kafin suka rabu ta koma cikin gida ita Kuma Bilkisu ta shige mota suka fita da Barhim.
By
AUTAR AREWA.
✍️✍️✍️✍️✍️✍️