Free chapter · Read without an account
episod 4
by wasila omar · IDON DUNIYA
wasila omar (mr's f.h)
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
***
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
" Sai ki fito ai gwana kiyi min wanki, kin san banda kaya amma baza ki zo ki wanke min ba saboda kin fara samun guri koh?" ,Hanne da ta banko labulen ta ƙarasa maganar tana hararar Jasra da ke zaune ta rungume Aryan a kirjinta,"kiyi hakuri Aunty yanzu zan fito in fara Aryan ne ke kuka","zaki fake dama da wannan shegen ɗan ne ki na zama a ɗaki to ai ba hutu ki ka zo ba dan ba a banza zaki zauna mana a gida ba, ki fito malama kafin na sa a ɗau mataki", tana gama faɗa ta juya ta koma dakinsu, bin ƙofar Jasra tayi da kallo tana share hawayen da suke sintiri a kan kuncinta, haka ta goya Aryan ta fito tsakar gidan ta fara wankin da bata san ranar gamawa ba.
" Wai ni kam Kausar haka zaki zubawa wannan yaron ido yana bulayi a garin nan yana aikin banza da bazai tab'a samu ba?",“ hmmm ke dai bari ƙawata na rasa ya zanyi da yaron nan","haba dai Kausar ya kin rasa yanda zaki yi da shi ai miƙa sunansa kawai zaki yi a sa ya manta da ita kawai ya auri Farida kin ga zamu samu sauƙin abubuwa ma ko?", “kwarai kuwa ƙawata kin kawo shawara ai kuwa anjima in an zauna meeting zan bada sunansa dan ubansa ko ya shiga hankalinsa" ,haka su ka ci gaba da maganganun da bana ganewa wa ,
nace fans ko wane meeting za a zauna akan Farhan oho
************ Sai dab da magariba ta gama wankin da take yi da ƙyar take mik'e bayanta saboda yanda take jinsa ,haka ta koma ɗaki ta ɗauki guntun kunun ɗazu ta d'urawa Aryan sannan ta je tayo alwala ta.rama sallolin da aka biyo ta domin bata da damar da zata yi sallah in dai an sata wani aikin.
Kamar kullum yana tashi daga office ya wuce cikin gari yana ta zagaye da hotonta a hannu duk inda yaga taron mutane sai ya tsaya ya nuna musu hoton amma yau ma ba labari kamar kullum, haka ya nufi gida rai ɓace ba kowa a falon dan haka ya haura sama kawai ya baje a gado BE bi ta kan kiraye-kirayen sallar da ake ba ya kwanta abin sa, bashi ya farka ba sai wajen sha ɗayan dare ya farka a firgice, take ya ji kansa ya masa nauyi kamar yana jin ya manta da wani abu , zunbur ya mik'e ya nufi toilet yana tangad'i kamar mashayin giya. - - - - - -
"Ni walllahi inna na gaji da zaman yarinyar can a gidan nan, faɗar Hanne da ta ke zaune tana cin tsire aleda" ,"to Hanne ya ki ke so ayi kin san dai muna morar yarinyar nan koh?", “ni wallahi kawai ki sallame ta kullum sai a dinga min gori wai mun ajiye mace da d'an shege a gida ni na gaji," ta ƙarasa maganar a shagwaɓe "to ni yanzu kawai ki kore ta ni na gaji da ganin ta" ,"to shikenan Hanneta amma ki bari kin ga yanzu dare yayi kin ji" ,"to ke inna a yanzu ne zamuyi a sirren ce ba wanda ya san mun kore ta kawai ki ta so mu je " ta faɗa tana mik'ewa ba musu kuwa innar ta bi bayanta suka nufi ɗakin da take ciki
Ai nima ina ganin haka jikina ya fara rawa danjin za a kori Jasra har ban san alƙalamina ya faɗi ba .
mr's f.h📝📝📝