Free chapter · Read without an account

2

by Mamuh gummy · KAUNARMU

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDINE KA NEMI WAINNAN NUMBERS DIN KA BIYA KA KARANTA CIKIN AMINCI_*


***

OR

***


*2*


cigaba da cin abincin fifi tayi tana sauraran hirar su batace uffan ba da dan sauri take dan tuttura abincin tana lura da time,tana aje fork jakarta ta soma jawowa a gurguje ta mike tsaye tace dady pls can i go now?waaro idanun sa waje yay,a shagwabe tace pls,se ya rankwafo kai yana kallon ta kamar me tunanin wani abu can yace emmm not until u give ne a hug,da yar dariyar ta ta taho ta rungume sa sosai yana me sakar mata murmushi cikin tsananin nuna kulawar sa yace akula ok?tace ok bye..dad i love u..bai amsa ba wani irin kallon kauna me fallasa tsananin so yake biyota da shi.. taku dayan biyu tayi sai ta juyo kamar wanda aka tsakure ta tace,"hamee?dago kai hamida tayi ta bita da sassanyar murmushi me ciwon datake jin shi har can kasar zuciar ta.."tace natafi schl..bye..Gyada kai Hameeda tayi Bata ce uffan ba ta mayar mata da murmushi 

Me dan fadi..


tun kan ta maida kallon ta kan dinninh table taga dady shima yana shirin mikewa da alaman zai bar wajen cike da mamaki tace"dady har ka koshi?yace yes dear dama na zauna ne sabida mufida ta samu ta ci abinci,u go ahead ni zanje daki..


murmushin karfin hali ta kwakwalo tace ok Nan ya wuce ya haura sama tayi jugum tana bin bayan sa da kallo


In akwai abunda yake mata ciwo bai

Wuce wannan yanayin datake shiga ciki,nobody have her time,rabon dady yay zama na musamman akan dining table domin ta ita kadai bazata iya tunawa..."oh Allah its always about fifi nikam ko oho..wani lumshe idanun tayi hade da sauke nannauyan ajiyan zuciya can ta mike tayi wicewar ta daki..


Classic bentley stance code shiya sauke ta a kofar makarantar su batare da ta maida hanklin ta kan kowa ba ta haura fifth floor inda ake gabatar da practical din sun


Ta riga da tayi lattin mintuna talatin amma dake ta saba da halin ta na creating drama so tana bude kofar ajin tayi lumui cikin sanda tace hey guys,"anan kusan duka ajin suka juyo suka kalle ta,ganib hakan ya sata ta boye fuskanta ta tana toshe bakin ta ridicoliusly.


Kawarta maheeda ce ta watsa mata harara tana mata alaman shushhhh da hannu..kwabe fuska tayi a shashance tana duban lecturer da sauran daliban da duk suka tsura mata ido tace sorry tazo ta wuce sadaf sadaf ta nemi waje ta tsaya,sauke ajiyan zucia lab co-odinator yayi yace "and that was mufida mande, now lets get back to business. ,jin haka wani dariya ne ya kufce mata inda hanklin kowa ya sake dawo kan ta tun kan malamin sun yy magana ta mike tsaye ta rike kunnen ta kamar marainiya tana cewa sorry sir..rasa abun cewa yyi yana girgiza kai ya rasa ta meyasa fifi taki sa seriousness arayuwan ta 


" ya bita da hararar jan kunne yace sit down,tana xama kuwa ta fashe da dariya duk ajin suma suka dauka da dariyar.


Wani hakurin ta sake bayarwa wannan karon da kyar dai aka agama practical din nan tare da ita cikin lumana...


Khadijat mufida nuhu mande,itace dalibar data fi kowa kokari a set dinsu duk dama bata dauki duniyar nan abakin komai ba,rayuwar ta kawai takeyi bata taba tsaurara tsanani akan dukkan lamarin ta ba.


Duk abunda xai bata nishadi da jin dadin rayuwa bata wasa da shi,great sense of humourn ta wajen iya mu'amala da mutane ya sa kusan kowani dalibi a makarntar ya san da zaman ta.


"Fifi mande" shine nick name din da kowa yake kiranta da shi tun suna shekarar su na farko,sosai sunan ya zaga ko ina in baka san ta dan wani abu ba dole zaka san ta dan wani abun dan duk inda shakatawa dajin dadin rayuwa yake to ita ne akan gaba


Aguje take biyo maheeda abaya dake tafiyar ta cikin masifa tana kukkuni


Mahee..maheeda pls now,juyowa maheeda tayi a masife Tace da Allah malama dakata min

Sau nawa na kira wayar ki?


Tace sau takwas..


Wani angry face maheeda ta sa tace and?...

matsowa kusa da ita tayi ta kama cheeks din ta tana mata murmushi tace and dady ne ya jawo komai wallahy...kinsan wani abu mahee?


Maheeda dake mugun son jin gulma tace what?..yatsinawa fifi tayi cikin iya zolaya tace nothing..in kina son ji ki biyo ni cike da takun ta na rigima ta wice gaba maheeda taja tsuka ta shiga biyo bayan ta..


Hadadden student cofee stall ta nufa nan take tayi odering kofuna biyu na shayin dayafi kowanne jin kayan hadi da dadi da tsada..


suna sha suna yar hirar su ahaka basa yin minti 10 batare da wani ko wata ta katse su da gaisuwa ba


dake mufida kusan favourite din kowa ne a makarantar so duk inda ta xauna sekaga mutane suna son mata magana in one way or the other,wani ajiyayyan numfashi ta saki tace wa maheeda gurl friend saura kwana nawa mugama karatun nan ma?Mahee ta yatsina idanun ta ta zuki shayin ta da alaman rashin kulawa,can tace 1 month i ques,wai meye ne zaki fada min kinsan na matsu inji kike ja min rai?..,dariya fifi tayi tace calm down dama nasan matsalar ki ai sarauniyar son jin gulma ..mahee tace whateva nan mufida ta matso kusa kamar me neman mata yar tsegumi tace ke maheeda ki shirya wannan karon ina so muyi abun da babu wanda ya taba yi a ranar graduation dinsa


Maheeda Tace kamar yay fa?


Tace i mean party ina son in hada babban get togher da ni da dukan abokai na amma kafin nan ina son muje yawon

Shakatawa ina son sauran ragowar college time dina ya zamto wanda bazan taba mancewa da shi arayuwata ba


..Maheee ta ce ehem?karatun fa?tace ohhh mance da wannan zamuyi catch up,.mahee dagaske nake miki 

I want to go wild maheeda tace ure alwys wild,tayi kwafa ta maida bayan ta kan kujeran cikin dauke numfashi tace wannan karon ina nufin"wildest"..


Mahee tace hmmm to me kike shirya mana ne haka? shiru tayi sanda ta karashe shanye shayin ta tas sannan tace alot. Starting from today?..maheeda ta dan dube ta tace and hamida?


Tace oho wallhy bansan ko zata amince ba amma zan tabo ta inji,tace i hope she did nan suka gama yar hirarrakin su suka watse kowa ta nufi gida


Kafin satin ya kare ita da kawarta maheeda da meena yar gidan dr fatima yonas datake daukar ta kamar yar uwan ta da duk sauran gang na friends din ta suka taru suka harhada

Nau'i nau'i na shirye shiryen yadda zasu more rayuwar su a cikin wayannan kwanaki.


Ameed dake shi doctor ne so bai ciika samun lokacin kansa ba amma da shike yana matukar kaunar fifi hakan ya kukkusa ya mata alkwarin samun kulawar sa a dukkan wayannan kwanakin


Fifi tana sane da cewa zasu bar germany zuwa nigeria maybe na har abada amma se ta barshi aranta batare da ta nuna ma kawayen ta ba


bayan tawainiyar ta hameeda da dad dinsu dr fatima ce da yayan ta Ameed da meena suke da masaniya akan tafiyar sun ahakan ma tanajin dan babu yadda ta iya ne,aranta ji take kamar in ta rabu da germany hala tayi tafiyar karshe kenan na har abada waya sani ko ma a nigeria zata mutu.


Tun daga lokacin takanyi abune ta inda kowa zaiji matukar nishadin wanda tasan hala bazasu taba mancewa da hakan aransu ba..


A karo na farko suka shirya fita su biyar yan mata maheeda meena harda hameeda da wasu kyafaffun yan mata guda biyu wato yesmin da arsala dukan su kowa tanajan sport car kaloli mabanbanta


Awani katafaren resort suka sauka ita da kawayen shakawatan nata All girls out so basu gayyaci wani namiji ba


ita yesmin yar gidan wani turkish tycoon ce arsala kuma brazillian ce gaba daya baya


Daga yanayin dressing dinsu zakasan suna matukar ji da wani abu waishi kyau kyaun jiki da asalin wayewa na iya kwalliya da daukar wanka uwa uba dukiya da wadata


Dukan su sanye suke da crazy jeans da brigt colour tops 

Da manyan manyan sun glasses hannun su dauke da jakunan rataya na bvlgari wayayoin su masu tsadan gaske


saidai iya kokari sunyi wajen lullube kawunan su da muflers wasu da kananan veils wasu da hoodie ta inda da kaci karo da su dole zaka san cewa sudin musulmai ne


Kowaccen su ta sha kwalliyar ta na kece raini amma banda hameeda dake sanye da Egyptian jallabiya da pure red veil tayi roling kamar wacce ta fito masallaci


Tun suna gida da ta fito cikin nata haddenen shirin irin nasu fifi daddy ne ya umarceta data je ta sauya dresing dan dole.


Batayi musu ba tabi umarnin san amna Se ta ga mufida ta fito a kile amma bai ce mata uffan akan nata shigar ba and of course ta san bazai wuce dan yana gudun bata mata ranta ba ne


Hameeda ita ta fito odd a cikin su tayi daban sekace dukkan wajen ta girme su,shiru shiru zaka ganta kamar wacce bata da nacewa amma azahirin gaskiya zuciyarta ya fara hura wata wutar da takejin hala nan gaba bazata iya sassaita shi ba


wani irin surutayya suke yi a tsakanin su wanda ya nuna tsananin shakuwa jin dadi da hadin kai

Amma zuciyar hameeda cike yake da sake sake ganin dukan hankalin kowa akan mufida yake,ita kam ma har mancewa da zamanta awajen akeyi,a duk sanda akayi abun dariya ita murmushin karfin hali takeyi


Abu daya yake damun hameeda acan kasan ranta amma bata son bayyana ma kowa dan bata san tana ina zata fara ba.


Shin su dady basa kaunar nata farincikin ne ko ita ba yar su bace rayayya kamar yar uwanta fifi?

Cikin Wannan tunanin ta tsunduma sosai har aka kammala outing din kowacce ta shiga motar ta bata san anayi ba.


Tuki takeyi ita kadai tamkar wacce gangan jikin ta ne kawai ke motsi hankalin ta ya nitsa ne wajen tuno da asalin ciwon dake cin zuciyarta a kullum yana mata zugi.

#mamuh


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.