Free chapter · Read without an account

4

by Mamuh gummy · KAUNARMU

KNM


***


Please SUBSCRIBE


*4*

cikin dauriya hamida ta taso ta taho har bakin kofar domin duba wanda yake wajen,tana budewa a tsaye taci karo da wani mutum Irin Mai bada sako gida gidan nan hannun sa dauke da manyan manyan akwatunan kyauta tare da mai gadi da security sun rakoshi


Kai tsaye Dagowa yay ya dubi hamida cikin harshen turanci yace mata good morning maam House no22 nuhu mande residence?


Ta gyada kai tace yes?


...nan ya mika mata biro ya umarce ta data sanya hannu a yar takardan su na register wanda yake nuni da isowar sako zuwaga maishi tana rantabawa ta mika masa tace thank you,security ne suka juya tare da shi


tsaye tayi tana me kare ma hadaddun akwatunan kyautar da aka killace su gwanin sha'awa agaban ta kallo


Saidai Tunanin abubuwan da suka wakana jiya da shekaran jiya dik su suka bijiro mata a zuciyarta inda take nazarin cewa kusan dukanin kyaututtukar data samu daga wajen su daddy da familyn dr fatima yonas bai wuce yan kayan sawa takalmi da katin gaisuwa irin na greeting card din nan ba


babu wani abu kwakkwara acikin kyaututtukan daya ya burge ta bare ma yaje mata har zuci


Amma Sanin yanayin yadda abubuwa suke a tsakanin ta da yar uwanta yasa a cikin yan kwanakin sai ta tsame kanta tayi gefe duk takurawar da fifi tayi mata akan su bude nata kyautattukar a tare haka taki fir


Aranta ba wani abu mai wuya bane iya cin karo da abubuwan da take so a cikin kyautattukar da fifi ta samu wanda ita ba'a bata ba kuma tasan hakan zai iya jefa ta cikin wani mummunan hali


Ayanzu Tana so ne hankalin ta ya dan dawo jikin ta kafin su isa nigeria tunda bawai sanin ya kasar dazasujen yake ba


A Labari kawai sukeji,bare ita da sau dayama daddyn sun ya taba gaya mata tarihin su waye ammy da yayan ta guda biyun da zasuje su tarar


Cikin wannan halin sake saken taji an dafo kafadun ta inda ta waigo cikin sauri da nitsuwa suna mai hade idanuwan su da yar uwarta tata cikin yanayin jefo tambaya a tsaye fifi take da alaman ta biyo bayan tane tace


Hamida Waye ne?

Tun kafin hamidar ta amsa idanun ta suka sauka akan tarin boxes dake gaban ta awajen


"cike da mamaki ta durkusa gabansu tace waw nawaye?waya kawo miki.. masha Allah..


Nan Hamida tai saurin cewa Bafa mani aka kawo ba


Mai bada sakone yazo shima bai gaya min komai ba sai dai in mun bude hala xamu gani


Nan fifi ta taimaka suka tarkato dukan su suka dauko box daya daya a hannun su suka shigo har gaban mahaifin su da shi saidai baice uffan ba har suka shiga budewa


Atare suka kai hannun kan wani dan madaidaicin katin da aka manno sakon tare da shi wanda sunsan dole anan ne zasu ga sunan wanda yayi sakon da wanda aka aiko ma 


hamida ce tayi nasaran fara dora hannu ta akai dan haka ita ta dauki katin cikin warware makullin sa ta bude shi tsaf ta shiga karancewa


Sako ne me cike da nuna tsantsar so gata da kuma kauna wanda yayi mummunan fallasa girman irin kewar ta da za'ayi...


tsaban kalaman da aka rubuto sun tsaru cikin nitsatsiyar harshe mafi sanyayawa a cikin sassanyar yanayi hamida ta tsince kanta nan take ta shiga maimata kalaman ma zuciarta wanda yayi musabbin janyowa idanun ta cikowa da ruwan hawaye


Danne duk wani abun da takeji tayi ta karance har karshe,ina ma ace ko sau daya zata same irin wannan damar arayuwan ta 


Waye zai so ta ya fifita itama ya turo mata wayannan kalmoni masu ma'ana wanda zai sa zuciyarta tayi saurin amincewa da cewa ita ma mutum ce wanda ta cancanci nuna kulawa da kauna


Duk yadda dadin kalaman suka karbu suka kuma sanyaya zuciyar ta suka ratsa ta hakan bai sauya mata jin komai ba dan kuwa babu sunan ta a jiki sunan yar uwan ta mufida ne Kenan sakonnin na mufida ne saidai bata ga sunan wanda ya aiko ba


Jiki a sanyaye ta mika mata batare da ta nuna yanayin data tsinci kanta na kishi da jin haushi akan fuskan ta ba.


Nan fifi ta amshe sakon tana kan tambayarta nawaye?wani shiru ne kawai ya ratsa wajen har fifin ta kammala karantawa dakanta ta dago idanuwan ta da zimman yin nazarin wanda zai iya aiko mata kyautar


charaf sai idanun ta suka sauka akan wani abu,shima a killace yake shikadai ana shi gidan a gurguje fifi ta dauko shi ta budeShi


Wani abun wuyar danyen dutsen safaya(saphiere)ne kalar sa ya shiga ja sosai yana faman sheki kamar asalin duwatsun diamond


Design din bana engine ko bugun kamfani ba bane asalin hannun kwarancewa ne ya tsara zaman zanen aka dedeta siffar duwatsun ta inda zaiyi matukar kyau wanda ko kallo daya bazai ishesa ba


Wannnan shine abun wuyar data gani a wani jaridar london times tace tana matukar sha'awar sa kuma tasan wa dady kawai ta nuna sukayi hirar kenan shi ya mata wannan sakon?tunda in ba shi ba babu wanda ta taba gaya ma wannan zancen


Daga yanayin yadda yay tsaye yana kokrin saka fuskn tausayi ta fahimci cewa tabbas shi din ne da wani irin gudu ta taho ta fada jikin sa ta saki wani irin kukan murna da tsananin kaunar sa


Tace. "Dukkan wayannan nawa ne? Nagode dady na Suna tayi dai hamida batace musu uffan ba


Wani shiru tayi agefe tana kallon su cikin tuno da Allah me kyautar kunci,..


Agaban ta mahaifin su ya tallafo fuskn fifin yana gaya mata maganganu masu dadin ji,yana me tabbatr mata cewa zai iya sallame dukan arzikin sa da komi nashi a duniya domin jin dadin ta da samun kwanciyar hankalin ta,kayan data sa ajikin ta kalar ja ne dan haka ta warware abun wuyar kamar zata kwama sai ta kuma ta fasa ta dawo tana kallon yar uwanta hamida dake kwakwulo murmushi da kyar


Da faffadan nurmushi fifi ta karaso wajen ta tana me damka mata abun wuyar tace hamida sakamin"ba musu hamida ta karbe,fifi tana ta surutun ta cikin bata labarin abunda ya wakana alokacin da sukayi hirar da daddy.


"Wani irin kishi da damuwa shi yake cin zuciar hamida amma ahakan ta daure ta shiga dannewa da tattausan lafazi tana amsata cikin sautin murmushin ta me fallasa tsananin kuna da ciwo


Warware abun wuyar tayi ta zago da shi a wuyar fifi tana malkaya mata last hook din abun wuyar,yadda ya xauna a wuyar fifin yay matukar kyau ya dada sawa takeji har can cikin ranta dama ace itace ta mallake sa..


Dauke kai tayi cikin sauke maganganun zuci a cikin dukkan tarin kyautattukan nan yanzu babu nata ko daya aciki?


Ta gama fahimtar cewa Bawai ana mata hakan dan ba'a son ta bane mancewa da ita akeyi agabanin farincikin yar uwan ta


Yaya zataji aranta me takeji duk babu wanda ya taba yin la'akari da hakan.


Zama sukayi dukan su suna cin abinci suna hirar ban kwana still wani shiru hamida tayi tana tura abincin bakin ta kadan kadan sakamakon rashin dadin sa datakeji abakin ta


Bayan sun gama sun fito zasu wuce nan ma su dr fatima yonas da yayan ta duka biyun suka tada nasu wasar inda gaba daya suka fi bada muhimmanci da kulawar su akan mufida,har hawaye sukayi ma juna alkwarin zasu na kirar ta sunyi shi yafi abun a kirga 


10am na safiya suka isa aiport babban jirgin zirga zirga na kasan shiya kawo su nigeria aqashe garin ranan asabar karfe 2 na rana..


Kusan dukkan mutanen familyn sune suka zo tarban su,yayar baban su ammy khalid harma da kakar su hajja...


To Hamidar ce ta soma isowa garesu domin ta bar mufida acan baya tana famar tattara nata kayan.


Kallo daya ta musu ta gane su inda ta taho,nan suka tarbe ta da murna da fara'a ayayin da dukkan hankalin ta ita kuma ya koma kan kyakyawar hadadden namijin dake tare da su wanda take kyaun tsammanin cewa shine KHALID MAKARFI wato yaron ammy na biyu 


zuciyarta ne ya shiga tsananin bugu ayayin da suka kalle juna suna masu sakar ma juna murmushi me sanyi


Su ammy da hajja kuwa sai tambayar ina fifi take?da alaman ita kawai suka fi so su gani so tsaban nuna zakuwar su da rawan jikin su ko hamidar ma bata iya samun damar nitsuwa ta amsa su dakyau ba


Haka kawai hamida taji khalid ya mugun dauke mata hankalin ta domin kuwa babu marabar sa da irin namijin data ke muradi a zuciar ta wanda takejin duk duniya da shi kawai zata ita rayuwar ta


Daga yanayin yadda suke satar kallon juna hajja tayi murmushi sbd Shi khalid dama yafi yayansa SAHEEB MAKARFI sakewa dason mu'amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane yafisu fara'a da tausayi Dan komai na uwarsa ammy ya dauko


Sama sama suka gaisa da shi sai ya dan kawo Hannun sa zai karbe Troleyn hannun ta yana mikowa kamar daga sama yaji an wani tunkude sa a mugun razane ya dago kansa ya juyo inda yayi gamo da wata kyakyawar surar data dauke mai numfashi atake ta kuma tafiyar da shi sumewar tsaye yayi yana me tsura mata brown eyes dinsa cikin yanayin da ba sai ka tambaya ba

Hakika yasan yau yaci karo da muradin zuciyar sa 

#Mamuh


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.