Free chapter · Read without an account
Chapter 5
Bayan shekaru biyu.
A yau aka yaye su Hashim daga makaranta sakandare, sun yi taro makaranta ta tara iyayen ɗalibai dan taya su murnar kammalawa.
Baban Hashim da Baba Abubakar ne suka samu zuwa don ganin taron ƴaƴan sun Ado da Hashim, wanda sune suka gama, sai Zaina kaɗai da za'a bari sauran, sun riga da sun gama tuni.
Kasancewar abin nasu ya zo da hutun ƙarshen shekara, hakan yasa aka haɗa da taron canja aji inda ɗalibai daga ajujuwa da dama sun fito sunyi gabatarwa.
Ciki har da Zaina da take aji huɗu za ta tafi biyar, ita ce a gaba sai masu bi mata, haka ta yi nata suma suka yi.
Abin ya ƙayatar da iyayenta ganin ƴarsun cikin mutane tana yaren da tsakanin yayansu maza suke ji. Hashim yafi kowa jin farin ciki ganinta tayi fes abunta, don tun daren jiya har karfe sha ɗayan dare suna tare, shi ya wanke musu uniform ya musu guga kafin ya tafi gida.
Taro aka yi lafiya aka watse, Hashim ya fita da kyauta biyu na ɗalibi da yafi kowa zuwa makaranta baya fashi, sai kuma mai ƙoƙari. Zaina ta samu kyautar tsafta da ƙoƙari ita ma.
Haka aka gama taron aka watse suka tafi. Gidan su Zaina suka wuce, iyayensu mazan suka wuce wajen aikin su.
Abubuwan da aka bawa Zaina ta buɗe, ɗaya ciki yadin uniform ne da kuɗin ɗinki ɗaya kuma takardu da sweets, ɗiban sweet din dukka tayi ta ba Hashim.
"Ya Hash ga sweet nan, tunda takardu ba amfani za ka yi dasu ba da na ba ka."
Ɗaya ya ɗauka ya bar mata sauran.
"Ki riƙe min a gurinki wannna ya ishe ni, amma fa idan kina so ki sha."
Murmushi tayi ta kwasa ta kaiwa Inna tace. "Inna ke ma ki dauƙa."
Girgiza kai Inna ta yi tace.
"A'a ki ajiye a wajenki kawai, Allah sanya albarkar abin da kike karanta."
"Ameen Inna." Zaina ta ce ta wuce cikin ɗaki.
Inna tabi ta da kallo, ba don dole ba ba ta son karatun ƴartan ko don maganganun da yake yawo a cikin dangi, waɗanda ta toshe kunnuwanta daga ji.
Ƙaramar yarinya da bata san me rayuwa ba ake jifa da maganganu iri iri.
...
Cikin hutun da su Zaina suka samu Ado da Hashim suka dinga zirga-zirga da shiga da fice suka samu gurbin karatu a Polytechnic, don samun sauran ƴan uwansu da wasu sun gama suna degree, wasu suna shirin gamawa.
Ado ya samu Business administration Hashim ya samu accounting.
Sun biya kuɗi da komai cikin sati biyun aka fara karatu suka fita, kwata kwata ya daina samun lokaci a cikin satin sai kwana uku, shi ma kuma gurin Baba yake zuwa taya shi zaman shago, karatu suke sosai ba shi da isasshen lokaci.
Idan har ya tafi makarantar to idan zai dawo sai ya saya Zaina abun ci in dai ya gani. Inna ta mishi faɗan ta ce ko ɗan takardu yana saya zai mishi amfani, sai dai yayi murmushi yace. "Inna abuna na Zaina ne, da ma don ita nake nema."
Kullum ya faɗa mata haka sai dai tayi shuru ta rabu da shi, tasan mai raba Hashim da Zaina sai Ƙaddarar Allah.
Haka su Zaina suka cinye hutun su suka koma makaranta, ta shiga aji biyar na Firamare.
Shekarun su Hashim biyu suka kammala karatunsu, suka nemi gurbi cikin University inda Allah ya taimake su suka samu aji bibbiyu kuma abin da suka karanta.
Hashim ya zama ɗan gayu matashin saurayi ɗan shekaru ashirin da huɗu, duk wani tsarin halitta na cikakken saurayi matashi Hashim ya ajiye ga gayu.
Bangaren Zaina hutu suke zasu shiga aji uku na sakandare, alamun ƴan matanci ya fara bayyana a tare da ita wanda ya saka hakan jin mugun kishinta, daga mafarinta ma a cike take ta ko'ina balle gaba.
Daga lokacin Inna ta fara hanata zama ba hijab ko yawan shigewa maza, ba don dan ba ta yarda da ita ba sai don tarbiyya.
Duk ƙoƙarin Inna ta hana Zaina yawan mu'amala da Hashim abun ya gagara, don haɗuwar jininsu daga Allah ne, idan har ta wuni ba ta ganshi ba to ba zata iya kwana ba, sai ta faki idon Inna ta shiga gidansu nemanshi, duk da in ta shiga Mama zaginta take amma da ta gane hakan da zaran ta shigo take shigewa ɗakinsu dake soro duk da shi ma ya hanata, don watarana ta shiga ta sameshi da abokansa biyu suna cin abinci, ta nemi guri kusa dashi ta zauna.
Kallonta yayi ya haɗa rai yace. "Ki je gida zan same ki."
"To ba tun safe ina jiranka kaƙi zuwa ba." Zaina tace tana ɓata fuska.
Harararta ya yi ya ce. "Yanzu dawowata zan same ki idan na gama."
Ƙin tashi ta yi, Hashim ya zare hannunsa cikin abincin ya fita ya wanke. Zaina tabi bayanshi, yana gamawa ya damƙo hannunta ya rankwashi kanta. "Kar ki ƙara shigomin ɗaki bada izini na ba."
Hawaye za ta fara ya ware mata idanuwansa yace."Kar ki yarda su zubo, mai da su maza."
Kukanta ta haɗiye yaja hannunta suka fita, suna fita ta ƙwace hannunta ta kwasa da gudu tayi gidansu, tana shiga ba ta tsaya ko'ina ba sai cikin ɗaki ta fara kuka.
Gidan ya shigo da sallama ya samu Tahiru da Inna, ya gaisheta yace.
"Inna ina Zaina."
"Yanzu ta shigo da gudu tayi ɗaki fuskar nan duk hawaye." Fadin Inna.
Kanshi ya dafe da ma yasan za'a yi haka, ya miƙe yace. "Bari inje anjima zan dawo lallashi."
"Ka rabu da ita, banda sangarci na san ma abun da ka mata bai kai ya kawo ba." Inna ta faɗa mishi.
Fita yayi ya nufi gidansu, ya samu abokansa sun fito zasu tafi ya musu rakiya a bakin hanya, suka samu abun hawa suka mishi sallama ya juya, a hanyar ya tsaya a shago ya saya mata sweet kala-kala cikin leda ya nufo gidansu da shi. Yasan yanzu ko ya shiga gidansu Zaina tana ɗaki.
Bayan magriba da ya dawo ya shiga ɗakinsa ya ɗauki ledar ya fita ya nufi gidansu Zaina, tana jin sallamar shi ta haɗa rai ta ci gaba da cin abincinta, ya shigo ya samu Baba da Inna ya gaishesu.
Ado da Tahiru suka ce mishi Bismillah ga abinci, ya girgiza kai ya zauna wajen Zaina zai saka hannu cikin nata ta ɗauke kwanonta, ƙasa-ƙasa yace. "Har yanzu fushi kike da ni."
Kai ta ɗaga mishi, ya ɗauki ledar gefenshi ya ajiye saman cinyarta yace. "Amin afuwa gimbiya ba zan sake ba."
Ledar ta buɗe taga irin sweet ɗin da take so ne, ta sake fuska tace. "Nagode na haƙura."
Ta ajiye kwanon abincin gaban shi ta ce."Mu ci ko in karo mana."
"Wannan ma ya isa." Yace ya saka hannu ya ci kaɗan ya bar mata don bai jima da cin abinci ba.
Har karfe tara yana gidan suna hira da Ado da Tahiru da Zaina da take gefen Hashim kwance, tana taya su hiran har bacci ya kwashe gurin, Inna ta tasheta kafin shi kuma ya musu sallama ya tafi gidansu.
Tun ranar idan har Hashim bai zo gurin Zaina ba to za ta je gidansu, amma bakin kofar ɗakinsu take tsayawa har sai ya ba ta izinin shiga kafin ta shiga, don kullum yana ƙoƙarin shiga dubata, idan yana da lokaci har bincikar takardunta yake kuma ba laifi yana yaba ƙoƙarinta, amma tafi ƙoƙari wajen lissafi da harkar Islamic.
...
Sauri take ta yi shiri, ta yi kyau har ta gaji da kyau matashiyar budurwa yar shekaru goma sha tara da Allah ya bata kyau da zubin halitta.
Idan ka dubeta yadda kayan jikinta yasha guga da turare da take zubawa ba zaka ce makaranta za taje ba.
Tana gama shirin ta fito ta samu Baba da Yaya Ado, wanda ya zama saurayi sosai har ana maganar aurensa da ƴar jikar Baba Sunusi ƙani ga Baba Lamiɗo.
Tare suka tafi a motar Ado da ya tara kuɗinshi ya saya. A bakin makarantar ya faka motar, suka fito suka nufi cikin makarantar da ake taron yaye ɗalibai ƴan aji shida, wanda Zaina tana ɗaya daga cikinsu.
Suka shiga uka samu guri suka zauna, Zaina ta wuce ciki wajen ɗalibai ƴan uwanta suka fara shirin fitowa don gabatar da taro.
Wata ɗaliba ita ta yi jawabi ta turanci, Zaina ta yi ta larabci da take bashi haƙƙinsa tana furta harufan kamar yadda ya kamata.
Tana cikin yi ta hango wanda take son ganin zuwan shi da har ta cire rai, ta ɗago idanuwanta tana kallon shi, ya zuba mata idanuwansa yana mata murmushi.
Martanin murmushin ta mayar mishi ta ci gaba da yi, tana gamawa aka tafa mata ta koma ta zauna.
A haka aka yi taron aka basu kyautattuka, Zaina ta samu kusan uku kafin a fara ɗaukar hoto. Ta sulale ta samu zuwa wajensu, ta zauna kusa da Hashim tace.
"Har na cire rai da zuwanka."
"Kin san ke ma yanayin aikin namu, da kyar aka barni na zo ganin ƙanwata." Yace yana murmushinsa mai kyau tare da binta da kallo.
Ita ma har lokacin murmushi bai bsr saman kyakkyawar fuskarta ba ta ce. "To ya Kadunan da aiki?"
Ƙasa-ƙasa ya ce mata."Allahamdulillahi sai kewar ƴan gida musamman ke."
Murmushi ta yi, ta miƙe ta ce. "A mana hoto."
Kai ya ɗaga mata, ta ƙira mai hoto ya zo suka gyara har da su Baba aka yi musu, Hashim ya tsayar da Zaina ya ce a musu tare.
Bai ankara ba yaji ta rumgumosa, ya kalleta ita hankalinta naga camera man, shi ma ya daure aka ɗaukesu kafin ya rabata da jikinshi cikin dabara, don jinta ya yi tamkar ba Zainarsa ba ce a jikinsa, wannan wata ce da take neman haddasa masa jin wani yanayia jikinsa.
Bayan gama hotunansu suka kamo hanyar gida, bayan isansu gida Zaina ta wuce ɗaki ta canza kaya ta fito da hijab a wuyanta ƙarami da ya zama mata sabo, don tun da Inna ta takura mata da sawa har ya zama jikinta ta saba zama da shi kona gida.
Kyautattukanta ta buɗe kuɗi ne dubu ashirin da su turare da sweet, ta raba ta bawa Baba kuɗin dubu goma ta bawa Inna biyar ta bawa Yaya Ado turare ɗaya, sauran ukun ta bawa Yaya Hashim, ya ɗauki ɗaya ya ce. "Kyautarki ce fa ki riƙe abinki."
"Ni dai na baka." Zaina ta ce tana ajiye masa saman cinyarshi ta miƙe ta kwashe sweet din ta wuce ɗaki, Hashim ya bita da kallo.
Karfe uku suka dawo gidan bayan fitarsu sallahr azahar, Ado ya saka Zaina zuba musu abinci ta kawo musu, ya buɗe yaga shinkafa da wake ne da man gyada a gefe, ya zuba a plate ya cewa Hashim."Bismillah."
Sun fara ci Hashim ya dubi Zaina dake gefensu zaune, tana danna wayarshi da ya bar mata zai tafi sallah ya ce."Ke fa ba za ki ci ba."
"Na ƙoshi." Tace ta ci gaba da danna wayar.
Ado yace. "Tsiri dai da iyayi."
"Haka za ki zauna." Hashim ya ce yana ajiye spoon ɗinshi.
Kai ta ɗaga mishi, ya miƙe ya isa wajenta ya zauna yana ƙwace wayar ya jefa aljihunsa ya ce.
"Oya me za ki ci, ko ki tashi ki zuba ki ci. Haka zaki zauna da yunwa."
"Ni fa na ƙoshi da shinkafar nan, kifi nake so." Ta ce tana tura bakinta cike da shagwaɓa.
"Tashi muje mu sayo." Yace yana miƙewa, ta tashi ta shiga ciki ta canja hijabi ta fito suka fita Ado ya bisu da kallo.
A ƙafa suka tafi bakin titin suna hira yana ba ta labarin Kaduna da yanayin aikinsa. Kifi ya saya mata da awara da ta gani ta ce tana so kafin su dawo gidan.
Taburma ta shimfiɗa musu bakin bishiya suka zauna, ta kawo musu ruwa ta zauna sannan, ya buɗe ledar ta fara ci tace. "Ka ci mana."
Girgiza kai yayi yace. "Duk naki ne Zayn."
A nutse take ci ya zuba mata ido yana kallonta, yana tuna every movement nasu da ita cike da shauki.
Ta ɗauka ta kai baki da sauri ya ce."Um um kar ki tauna."
Bakinta ta buɗe ta za ta duk wani abu za ta tauna, taga ya saka hannunsa ya ciro duk yawunta ya kai bakinsa ya fara taunawa.
Da mugun mamaki take kallonsa tace. "Me haka ba ka Ƙyama, duk na ɗauka wani abun na ci."
Kallon cikin idanuwanta yake da har yanzu bakin ciki brown ne yace.
"Ƙyamar wa zan ji ke? Tun kina ƙarama idan abu ya shiga bakinki ina iya cirewa in ci balle yanzu da kin girma."
"Ni dai bana so." Tace tana turo baki ta ɗauke idanuwanta a cikin nashi, yayi murmushi kawai yana mamakin Zayn ɗinsa. Ita ko ta ci gaba da cin abinta.
Hannu ya saka ya ɗauka ya kai bakinta, ta waro ido ya ce. "Buɗe bakin mana dalla."
Buɗewa ta yi ya saka mata a hankali yatsunsa suna gogar leɓbenta. Jin haka ta cijeshi, ya cire yana yarfe hannunshi ya kalleta ya ɓata rai.
"Sai na rama." Ya ce ya cafko hannunta ba zato.
Zaina ta yi wiki wiki da ido tace."Wallahi wasa nake maka."
"Ni dai sai na rama." Ya ce ya ɗaura yatsar hannunta saman lips ɗinsa, idanuwanta suka cika da hawaye tace."Kayi haƙuri don Allah."
Bai sake yatsunta ba ya ce. "To ki zaɓa min inda zan rama."
"Ni dai ka yi hakuri don Allah." Ta faɗa kamar za ta yi kuka.
Kissing ɗin yatsunta ya yi a hankali, ya ce. "Zan rama amma ba yanzu ba, kuma lokacin zan zaɓi inda nake so."
Kai ta ɗaga mishi sannan ya sake hannunta, kifin taji ya fita a ranta ta tashi ta kwashe ta kai gurin murhu ta rufe, ta wanke hannunta ta koma bakin baranda ta zauna.
Hashim ya kalleta ya ce. "Duk dai inda kike ina nan, ni kike gudu."
Girgiza masa kai ta yi ta miƙe ganin ya nufo wajenta, ta ɗauki tsintsiya ta fara shara, ya tsaya yace.
"Da dare zan zo muyi hira gobe da safe zan koma."
To kawai ta ce mishi ta ci gaba da aikinta ya fita. Gaba ɗaya ta tsorata da shi yau, tamkar ba yayanta ba.
#vote