Free chapter · Read without an account

16

by Aisha Ahmed Machika · Halin Dana Shiga...

🤳🏻



💘 нalιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@shooly84*



*_Not edited_*




💘 *16* 💘





Kwana biyu ya rage Ibraheem ya zo, da yamma ya kira wayata bayan mun gaisa ya ce anya ko Siyah ba zan miki laifi ba, na ce laifi wane iri Ibraheem?


Game da zuwa na kaduna, gabana ya faɗi kar dai ace ya fasa, banyi magana ba yaci gaba da cewa, yardarki zan nema inkin karɓi uzrina to, in baki yarda ba shikenan sai nayi yanda kike so kina jina? 


Asanyaye na amsa ina jinka, Siyah ina son ganin wasan polo wanda za'a fara cikin satin da zamu shiga anan kaduna shine na ce inba zan sa miki damuwa ba kimin adalci na ɗaga zuwana har zuwa lokacin sai na taho gaba ɗaya koya kika ce?


Nai doguwar ajiyar zuciya kamin na nisa na ce zuwa yaushe kenan?


Nan da kwana bakwai ko ya yi tsayi?


Na juya kai ina faɗin Allah yasa muna da rai, yai saurin amsawa da Amin na gode Asiyah kinyi min adalci sosai dan gaskiya ina jarabar son wasan polo ko ƙanƙani bana son kallonshi ya wuceni.


Nayi ƴar dariya na ce ra'ayinmu ya zo ɗaya kenan, kema kina son polo ko?


Sosai na faɗa cikin dariya, wasan yana matuƙar birgeni ya shiga raina ainun, kina nufin kina zuwa kallon?


Yai maganar ne kamar aruɗe kuma atsorace , na ce a'a ban taɓa zuwa inda akeyi ba kuma bana sha'awar zuwa, sha'awata na kalla a tv in anayi hankalina akwance.


Uhm! Naji saukar numfashin shi kamin yace har hankalina ya kwanta, na tambayeshi game me?


Yace kin gane ko Asiyah abin ne...koda yake ma share kawai, na ƙyalkyale da dariya na ce na ɗagoka fa Ibraheem, shima yai dariyar aiba wani abu bane dan kayi kishin abinda kake so ko? Uhm haka ne aishi kishi halak ne, to ina kishinki da yawa ina sonki da yawa nai murmushi na ce na gamsu da cewarka tuni, abinda kawai nake so da kai kayi ƙoƙarin ganin cikar burinmu, karki damu da wannan Siyah, insha Allah nan da ƙanƙanin lokaci ni dake zamu zamo ƙarƙashin inuwa ɗaya.



Kwana biyu ya rage Ibraheem ya zo kaduna kwatsam Abbanmu ya kwanta ciwo ƙasar England alokacin kwananshi tara da tafiyar, hankali tashe ni da Mami tare da Hashim muka bi jirgi muka iske shi acan.


Mun tarar jikinshi ya yi tsanani hankalinmu ainun ya tashi, wai ciwo ne na lokaci ɗaya ya fito bayi santsin tails da ruwa suka jashi ya faɗi tun daga faɗuwar har zuwa lokacin da muka isa asibitin baisan inda kanshi yake ba.


Likitoci sai ƙoƙari suke akanshi amma kamar ba'a komai ko ɗan yatsa baya motsi ajikinshi, mukan munga tashin hankali bamu da abinyi sai kuka da addu'a domin halin da Abbanmu yake ciki sai Allah kawai.


***


Kwananmu shidda cikin zunlumi da jimamin halin da Abbah yake ciki, mun duƙufa gayawa Allah ya taimakemu ya ɗaga mana kafaɗun Abbanmu.


Aranar da yamma muna tare aɗakin da Abbanmu yake harda Abbas daya biyo bayanmu munsa Abbah agaba muna kallo dukkanmu muna riƙe ɗa carbi kowa da irin addu'ar da yake acikin zuciyarshi.


Kamar almara naga hannun Abbah yana motsawa, da fari nai zaton idona kemin gizo sai ban damu ba, lokaci kaɗan na ƙara gani motsin kamin nai tunanin wani abu naji Mami tace kuna ganin abinda nake gani koko idona kemin gizo?


Na gani Mami hannunshi ya motsa ko? Inji Hashim nima na ce na gani atare mukayi kanshi nina riƙo hannunshi ahankali ina cewa Abbah tashi sannu Abba, kamar yaji abinda na ce sai idonshi ya kama rawa gaba ɗayansu.


Haba nan da nan muka rikice tini Hashim yadanna ƙararrawar kiran likita lokaci kaɗan suka shigo dai dai lokacin da gaba ɗaya jikin Abban ya kama rawa yana wani irin girgiza.


Hankalinmu ya sake tashi gaba ɗayanmu muka rikice irin fisge-fisgen da yake kamar irin na fitar rai, irin yanda akace mala'ika mai zafi yazowa mamaci karɓar rai...


Akayi waje damu gaba ɗaya, inda likitoci da nos-nos aka taru akanshi da kyar suka iya danneshi akai mishi allurar barci lokaci kaɗan barcin ya ɗaukeshi.



Mu duka muka zuba tagumi tare dasa mishi ido acikinmu kowa da abinda yake zantawa azuciyarshi, ni dai abinda nake tambayar kaina wai banda faɗuwar da Abbanmu yayi akwai wani abu daban dake damunshi ne?


Domin irin firge-fisgen da yake yi mai tsoratarwa ne matuƙa.


Lafiya dai ko? Mami ta tambayi Hashim daya dawo daga wajen kiran likita, ni da Abbas muka bishi da kallo inda ya zauna gefen Mamin ya zuba tagumi cikin damuwa mai girma.


Ya soma magana asanyaye meyiwuwa Abbanmu ya sami matsala a kwakwalwa...duk muka fito da idanuwa irin nal razana danjin maganar da baka zata ba.


Ya juya kai yaci gaba da cewa, abinda likitan yace dani kenan saboda faɗuwar da yayi ya bugu ne akai, sai dai basu zaci buguwar zai iya kawo matsala akan ba sai yanzu da sukaga irin abinda yake suke wannan hasashen, amma dai zasuyi hoton kwakwalwar kome kenan ma gani.


Mu duka matse kwalla muke da tunanin wace irin masiface wannan ke neman shigowa cikin rayuwarmu?


Anyi hoton anfito da sakamako dama can mun sadaƙar dan kwanaki biyun da suka biyo bayan farkawar shi abubuwsn daya rinƙayi bamasu daɗin faɗa bane sai dai kawai du'a'i.


Jini ne kwance cikin Brain ɗin tashi, amma ba wani mai yawa bane inda likitocin suka bamu tabbacin zasu iya shawo kan abun cikin ƙanƙanin lokaci, amma sai sun danganashi da asibitin mahaukata na babbam birnin bayan ya gama warwarewa kenan.


___________________


Kwana biyu a asibitin nan jikin Abbah yayi sauƙi baya tare da wata matsala sai ta rashin gane waye wancan da wacece, sai kuma acikin hirarshi wani lokacin zakaji duk shirme ne, abinda yake tayar mana da hankali yadda al'muranshi ke numa kamar ya mance baya wato(memory loose).


Cikin satin da muka samu sallama daga asibiti muka wuce asibitin na mahaukata wanda dama anshirya komai lafiyar jikinshi ake jira.


Cikin satin Mami da dasu Hashim suka koma Najeriya domin sake sabon shiri wajen Mami inda aka barni dashi a gidanmu dake can ƙasar, ni ɗaya ce gidan sai masu aikin dake zuwa suyi gyare-gyare su tafi, kullum safiya ina zuwa wajen Abbah domin ɗebe mashi kewa duk da cewa ya mance ni ɗin wacece amma na kula zuwan nawa yanai mishi daɗi dan yakan tsareni yaitamin fira wadda gaba ɗaya hirar tashi ni kuka take sanyani saboda ba wani abin kirki ɗaya da zaka tsinta cikinta sai shirme.


Cikin sati na uku da zaman Abbah asibiti Hashim da Mami suka dawo dama kullum cikin waya muke.


Mun dawo daga asibiti da yamma Mami take cemin da zamanki haka Asiyah dama makaranta kika koma kiyi Digree ɗinki anan, Hashim yace abinda ya dace kenan Mami, in kuma zata koma gida Najeriya to... Na tura baki gaba ina dire-dire inda ya ƙunshe dariyarshi ya wuce cikin ɗaki, Mami tai murmushi tace kyaleshi gobe ki shirya ya kaiki duk University ɗin da tayi maki kuga abinda hali zaiyi.





Satinsu uku suka sake komawa Najeriya kamin tafiyar sai da Hashim ya kammala min duk wani shirye-shirye na komawa makarantar inda zan ɗora akan course ɗin danai diploma kai (mass com.) shi Hashim ɗin ya koma kan harkokin Abbah inda yake yawo ƙasa-ƙasa yayinda Abbas ke tafiyar da na gida najeriya.


Satin dana fara ɗaukar lectures hankalina ya ƙara kwanciya duk wata damuwa na tattara gefe na aje na rungumi karatuna dan duƙufa da addu'a ɗan nemawa Abbanmu saiƙi.


Cikin satin cikin dare misalin biyu da rabi na agogon Englan na janyo waya na haɗata karon farko tun isowata ƙasar, layin Ibraheem wanda alokacin nan kewarshi da ƙaunarshi sun addabi zuciyata fiye da wata biyu ba muji juna ba.

Sai dai duk lokacin da Abdul yayo waya zai isarmin da saƙon gaisuwar shi, a bakin shi naji labarin zuwan shi kaduna da irin halin daya shiga na damuwa da bai sameni ba.


Ringin uku aka ɗaya wayar muryarshi can nesa-nesa ya amsa da assalamu laikum, wani daɗi ya ratsani har tsakiyar kaina, na rintse ido na amsa sallamar na ɗora da cewa daga gari mai nisa ne...


Asiyata! Ya faɗa da ƙarfi da alama akwance yake ya miƙe da sauri, kece Siyah na, ya sake faɗi nai sansanyar dariya na ce ni ce Ibraheem...uhm naji ajiyar zuciyanshi...shiru ya biyo baya kafin yace ya jikin Abbanmu?


Da sauƙi na bashi amsa, Allah ya ƙara mishi lafiya, amin na amsa na ƙara dana gode...muka sake yin shiru na ɗan lokaci..daga bisani ya nisa yace kin kyautamin kenan Asiyah?


Kin barni cikin damuwa da kewarki, sau ɗaya ki nemeni nasan halin da kike ciki kiji lafiyata bakiyi ba, anya ko Asiyah kin damu dani da wani al'amarina kuwa...amma kasan hankalina ba'a kwance yake ba ko?


Duk da haka sau ɗaya ki nemeni aizan san kin damu dani cikin rayuwarki, amma kin barni lokaci mai tsayi yaba zan shiga damuwa ba.


Kisa aranki nine nai miki irin haka yaya zaki ji?


Allah ka ɗai yasan abinda zaki ɗauka aranki game dani...Ibraheem! Na katse ƙorafin da yake, na'am Asiyah, kayi haƙuri naji na amsa laifina in sha Allahu irin haka ba zai sake faruwa ba...yai ɗan shiru daga bisani ya nisa.


Kin bani wahala da yawa Siyah, kinsani cikin damuwa na shiga ƙunci da tashin hankali *halin dana shiga* akan banzatar da al'amarina da kikkeyi mai girmane dan...na amsa laifina Ibraheem na faɗa ba zan sake ba dan Allah abar maganar haka adaina tada...ya wuce nima to meye labari ne Siyah?


Kai zan tambaya labari Ibraheem, nayi kewarki da yawa dan bakiji yanda nake jiba tamkar nai tsuntsuwa na ganni inda kike, na lanƙwashe murya na ce ko Ibraheem?


Na damu dake da yawa Asiyah ina buƙatarki sosai, karka damu ni taka ce Ibraheem, amma kinsan wani abu? Na juya kai da faɗin a'a, hankalina ya tashi ainun da zamanki garinnan musamman da akace har kin fara karatu sai na karaya na ayyana araina ba ranar dawowarki.


Nayi dariya ka bar masu ni kenan? Kai haba aike tawa Siyah shima yana dariyar, to ka yarda kenan zan dawo? Um to nufina ba yanzu ba ƙilama sai kin ƙarasa karatunki.


Kai haba aiban iyawa ace tsayin shekaru ban leƙo gida ba da yardar Allah muna samun hutu in yayi dai dai da hutun yaranmu anan zan zo Mami ta amsheni ni nazo gida nayi hutuna.


To kinji har hankalina ya kwanta amma dai ina zulumi da tunanin kar daganan ayimin..bai ƙarashe abinda zai ce ba sai dariya, nima ina dariyar na ce ka ganka ko Ibraheem wani lokacin baka da yadda, ba haka bane Asiyah kinsan abinne...kai dai kanada kishi da yawa, amma ba laifi bane dan kayi kishin abinda kake so ko?


Um..um aimu burinmu kenan in ana sonmu arinƙa nuna kulawa akanmu kaga ayi kishinmu ma babbar hanyace da take nuna an damu damu, inko haka ne na damu dake da yawa, ina matsinancin kishinki kishi ko irin mahaukacin nan wanda ba'a ko ason fadar irinshi.


Nayi dariya na ce na gode da kulawarka akaina, nima na gode da bani soyayyarki Siyah, mun shafe lokaci mai tsayi awayar daga bisani mukayi sallama bayan na tabbatar mishi layin dana kirashi dashi nake amfani acan.


Aiko shikenan hanya ta buɗe dan yanda muke mu'amula da juna ta waya kamar ina najeriya ne, so ƙauna da kulawa muna ma junanmu, yanda mukeji da juna ji muke tamkar mu kaɗaine halittun dake rayuwa adoron ƙasa musamman inmuna manne da juna awaya.


***


Al'amarin jikin Abbanmu abun sai dai neman sauƙi daga Allah, ba za'ace baya samun sauƙi ba amma dai abin nashi kamar ba'a magani, addu'a kullum yinta muke ko yaushe cikin roƙon Allah ake har Umra munje ni da Mami da Bashir da Abdul musamman dan Abbah amma abin gashi nan dai ne kawai.


Yau in anga kamar sauƙi ya fara samuwa lokaci kaɗan sai ya sake rikicewa akoma har gara jiya da yau, kai ba ƙaramin wahala muke sha ba a al'amarin jinyar Abbah.


Dai dai lokacin dana sami huyun sati uku alokacin Mami dasu Abbas da Rabi'a suna tare damu dan haka ne Mamin tace nazo najeriya nayi hutuna, gaskiya ban soba dan alokacin jikin Abbanmu yayi tsanani bana son matsawa.kusa dashi dan haka na ce gara nayi hutuna anan hankali na zaifi kwanciya.


Abbas ya dawo dasu Rabi'a nida Mami muna tare da Abbah, washe garin ranar dasu Abbas suka isa gida da yamma Ibraheem ya kirani yake cemin nasarai da ganinki ainun Asiyah da kika ce kin samu hutu har nayi shirin zuwa kaduna amma yau Abdul ke faɗamin su Abbas ne kawai ba tare dake ba.


Na ce wallahi Ibraheem jikin Abban mu yai tsanani ba zan iya barin shi cikin halin da yake ciki ba, ya ce wannan gaskiya ne dan aduk inda majinyaci yake babban abinda yake buƙata kulawar iyali da jinshi kusa dasu wannan kawai gatane musamman ace kana ƙasar da ba taku ba, dan haka ina ƙara baki ƙarfin gwiwa kici gaba da nuna kulawarki ga Abbah, da fatan Allah ya ye mishi wannan lalurar, amin na amsa asanyaye da godiya mun ɗan taɓa hira kaɗan mukai sallama.





Bayan shuɗewar lokaci muna tare da Abbah, sauƙi dai sai godiyar Allah, karatuna yayi nisa dan ina cikin shekara ta biyu kenan.


Har zuwa lokacin ban leƙa najeriya ba, sai dai koda yaushe muna waya da ƴan'uwana suma akoda yaushe suna hanyar dubamu, Mami kuma aduk lokacin da yara suka samu hutun makaranta tana tare damu, Anti Lubah lokaci zuwa lokaci muna waya da ita haka Muhammad wanda akullum roƙon shi dan Allah Asiyah kisani aranki kar nisan dake tsakaninmu yasa ki mance dani, na kanyi dariya kawai na ce Muhammad kenan.


Al'amarina da Ibraheem kuwa tamkar akoda yaushe ƙara iza wutar ƙaunar junanmu ake, lokaci bai taɓa shuɗewa ba tare da muna begen juna ba, rana bata taɓa gushewa ba tare da son junanmu na ninninka ba, kaini fa al'amarin ƙaunarmu abin har ɗauremin kai yake...





Machika novel

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol