Free chapter · Read without an account

Free pge 2

by NANA HAFSATU · MASARAUTA!!!💕

_*MASARAUTA*_

_(A Cinderella story)_

      👑💘


  _FREE PAGE: 2_


_NA:_



®️ _NANA HAFSATU_


©️ _ZAFAFA BIYAR WRITERS_



_wattpad:missxoxo00_

_Arewabooks:mssxoxo_


_BUSINESS:👇🏾_


_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_


_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_


_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_


_KHUMRAHS_

_KULACCAMS_

_TURARUKAN WUTA_

_NA TSUGUNNO_

_NA KAYA_

_NA GIDAH_

_NA GASHI_


_NA WANKA_

_NA WANKI_

_NA MOPPING_


_AIR FRESHENER_

_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_

_WARDROBE BALLS_

_SCENTED PEBBLES_


_ARABIAN OIL PERFUMES_

_HAIR SPRAY AND CREAM_

_DILKE AND HALWA SET_


_KABBASA_

_BURNERS_

_KASKO_

_TONGS_

_COAL IGNITERS_


_SKIN CARE PRODUCTs_

_OUR TURARE SAMPLE SETS_

_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_

_KUJERAR TSUGUNNO_


_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_


_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_


_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_


_instagram:yerwaincense_and_more_*


_WhatsApp: ***_


__


×××Ina baje akan tabarmar gidan su Wasila mun gama cinye awarar da Adamcy ya aiko da ita. Na mike ina gantsare bayana. Saboda yadda hakarkari na ke ciwo tsabar durkushen wanki.


Yarkaccacciyar akuyar gidan su Wasila tayo kai na tamkar zata ciza. Nasa kafata na shureta ina had'e fuska.


"Idan talaka ne kai. Kowa da komai raina ka yake."


Innar su Wasila dake gefe tana tankade tayi daria.


"Ke Kuma da wa yar albarka?"


"Da akuyar nan mana Inna. Kamar mayya zata cinye mun kafa. Banda tsabar reni ta isa tayiwa masu kudi haka?" Na juya na gallawa akuyar harara hade da gatsine baki. 


Inna tayi dariya kawai tana girgiza kai,


"Sabo ne kawai da tayi da ku. Kudi kuma da yardar Allah yar albarka wataran sai kin bawa wasu ma kyauta."


Sosai naji dadin adduar da innar su Wasila ta mun. Na dashare baki na saki murmushi kawai ina mai jujjuya zobena dake karamin yatsana na karshe. 


Na zundumawa Wasila kira dake can kuryar daki tana neman hijabin da zata mun rakiya .


"Ke ni zan tafi. Bar rakiyar."


"Haba kawata"


"A'ah ba za'ai haka ba, Ke Wasila zo ga nawa jikin taga ki dauka ki mata rakiya har gidah." Cewar innar su. 


Da sauri Wasila ta fito ta zura hijabin muka tafi , Bayan nawa innar su sallama.


Muna tafe a hanya muna hira. Ba wani tazara bace sosai tsakanin gidan su da gidan mu . Amma dake hirar bamason ta Kare ba kuma ma so mu rabu, Sai muke tafiyar ahankali. Bokitin kayan wanki na na dauke a hannun Wasila. 


Har kofar gidah tamun rakiya. Muka tsaya a kofar gidan namu muna masu cigaba da hirar mu. Wanda rabin hirar dik zancen wulakancin da Fati kawar mu tayi mana ne. Babar su ta haihu, Fatin tahada pati ta gayyaci kawayen mu yan gayun yankin mu mu kuwa bata gaya mana ba , Su kaci biskit da su lemon kwalba ance har da cincin da kankarar lemon leda ta bakin kasuwa. 


Naja kwafa hade da daga hannu sama na nanawa cinyata duka bayan na kwararo rantsuwa na dire.


"Ai Fati zataci kwal haka kaza na ubanta. Gidan ta tabo. Ko a islamiyya ta nuna ta sanni sena mata dukan kawo wuka, Shegiya da kai runtume-me uwa randa "


Wasila ta kece da dariya. Ta bani hannu muka sake tafawa. 


Daga can lungu na hango baban mu yana tahowa da yar leda a hannun sa. Ai ban bari mun karasa hirar mu da Wasila kawata ba na tafi wajen sa aguje Ina murna.


"Baban mu sannu da zuwa"


"Yauwa yar albarka . Ba dai sai yanzu kuka dawo ba?"


Na sosa kai ina girgiza shi a tare. 


"Na tsaya gidansu Wasila munyi wasa"


"Masha Allah. To Allah yayi albarka. "


Wasila ta karaso wajen mu ta durkusa ta gayar da baban mu. Ya amsa mata fuskar sa dauke da fara'a.


Nan yabar mu tsaye zai shige cikin gidah na figi bokitina dake hannun Wasila nayi cikin gidah da gudu ganin yar bakar ledar dake hannun baban mu. 


Wasila dake tsaye ta girgiza Kai kawai tana daria kafin ta juya ta koma gidan su. 


 ×××GIDAN KWANO×××


 Ina shiga gidah na rafka sallama. Hade da zubewa akan kujerar Inna Harira. Da sauri tayo kai na tana makamun harara.


"Daga min kujerar uwar sarkin yan hankali. Daga tashi na kin dora wadannan kazaman duwaiwan naki akai. Bayan kashedin da nake rafka miki akan karki sake zama akan kujera ta. Tashi ina magana kin zubamun wannan idanuwan naki na mujiya." 


Tunda ta fara magana na zuba idanu kawai ina kallonta, Duk rashin tsafta ta nafi Inna Harira . Domin haka kawai seta jera kwanaki bata wanka bare wanki.


"Kaii, Tashi dan kunzugurin buroaban ki. Ina magana kin zubamun idanu. "


Zumburo baki nayi gaba, Ta yo kai na zata dakeni nayi wajen Babanmu da sauri. Ya sha gabanta yana bata hakuri 


"Aikin kawai. Yo ai dama kai ka bada dama ta rena mu. Tsintacciyar mage dai ba ta mage. Ka dinga fifita yarinyar da ba yar cikin ka ba akan 'yayan ka. "


Maganar Inna Harira ta doke ni kwarai matuka. Nayi hanyar dakin Umma ina mai danne hawayen da ke san kufce mun. 


Umma zaituna dake shiryawa a daki tayi saurin riko ni ta rungumo ni jikinta. Kukan dana keson boyewa ya kufcemun. Duk kuwa da karancin shekaru na, Rashin sanin tushe na sam bayamun dadi. Gorin da akemun nagaji da shi Murya ta na rawa nace,


"Umma, Dan Allah waye mahaifi na ne? Menene tushe na, Taya akai aka same ni Umma? Wacece ni? Umma ki gayamun tushe na, Ko ni din she..."


"Kar ki karasa fada Inteesar, Kar na sake ji. Kema 'ya ce kamar kowa, Haifar ki akayi kamar yadda aka haifi kowa, Kina da tushe da usuli me kyau da yardar Allah. Bar kuka kinji diyar kwarai. Allah ya miki albarka." 


Kuka na na share, Na shiga kada kai na alamar toh. 


"Ga abincin ki can cikin kwanon ki. Maza wanko hannun ki kici kinji."


"Zo nan uwata." Babanmu ya kirawo sunana. Na share hawaye na na fita tsakar gidah wajen sa.


Takardar kifi ya mikomin daya kakkasawa kowa.


"Rike ke dana umman ku."


"To mungode Allah ya saka da alkhairi."


"Aamin"


Daki na koma bayan na wanke hannuna. Umma ta raba mana namu kifin. Na shiga yaga da fatar ina hadawa da abincin inaci. Kwan kifin kuma na dagargajewa mageta shi a takarda da abincin na ajiye mata taci idan tadawo daga yawon ta. Ina kaunar yar mageta, Jinta nake tamkar kanwa ta ta jini. 


××× Ina daga kwance a daki na fara jiyo muryar Babanmu yana bawa su Inna labari kan makarantar maza da zaa gyara ta boko wadda zata zama za'a dauki har yara mata. Masarautar birni ce ta dauki nauyin komai. Ina karasa ji na fita da gudu ina haki.


"Babanmu me kace? Makaranta? Boko? Mata? Kowa kenan ze iyayi?"


Babanmu yayi murmushi hade da kada kansa. 


"Shakka babu uwata. A dan guntun ilimin de da nake da shi. Makarantar ma sunanta yana nuna taci sunan marigayi sarkin birni na baya. Mai taken: SARKI ALIYU (ALKALI) MEMORIAL JUNIOR/SENIOR SECONDARY SCH. KINDAU)"


Ai ban bari ya karasa magana ba. Na figa nayi waje aguje, Ban tsaya ko ina ba se gangaren makarantar maza ta boko. Inda naga anata fashe fashe ana sauke kayayyakin gini. Bansan sanda na barke da hawayen da nake da tabbacin na farin cikin bane. Banda hamdala ba abunda nake maimaita wa cikin zuciya tah...



**ENGLAND**

LEICESTER CITY TOWN OF LEICESTERSHIRE (EAST MIDLANDS)



_

MASARAUTA (LABARIN SOYAYYAH) YANA AREWA BOOKS👇


https://arewabooks.com/book?id=6284e72eef85a63a21dbc5f5


SO DA ZUCIYA


SHIMA YANA AREWA BOOKS👇


https://arewabooks.com/book?id=623f824f9c4af77be0e96e3d


🥰😍

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_


_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_


_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._


_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH 


_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_


_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰


_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍


_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰


_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️


_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍


***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*


_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_

_HUDU: 700_

_UKU: 500_

_BIYU: 400_

_DAYA: 300_


_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_***_*


*KATIN MTN*👇👇 


***


YAN NIJAR 👇


+227 95 16 61 77


Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number

______________________


ZAFAFA BIYAR


VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)


VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.


TWO PAGES DAILY

INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.



*_TEAM ZAFAFABIYAR_*


_MSS XOXO WRITES ❣️_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.