Free chapter · Read without an account

19

by Aisha Ahmed Machika · Halin Dana Shiga...

🤳🏻



💘 нalιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@shooly84*



*_Not edited_*




💘 *19* 💘






Rayuwa agida ta zamo abar birgewa agareni dan ina tafiyar da ita cikin kwanciyar hankali, bani tare da damuwa bani tare da matsala hankalina kwance, na sake na wataya da iyayena da ƴan uwana, ga tallafin so ƙauna da nake samu daga abin sona, duk da cewa bamu tare amma akoyaushe ƙaunar junanmu naƙara zafafa ne azukatanmu.


Naso na fara zuwa aiki tun baifi wata ɗaya da dawowata ba amma Abbah ya hana wai sai agidan mijina ban damu ba da yace hakan musamman da naga har zuwa lokacin bai fara matsamin akan na kawo miji ba..


Amma fa ako yaushe ahirarshi zaice in zan aurar da Asiyah ko yace auran Asiyah za'ayi abu kaza da kaza da dai ire-iren haka, wanda wannan alamace dake nuna cewa kwarai Abbah amatse yake yaga ya aurar dani, dan hakane nake cewa Ibraheem ina tsoranfa kar Abbah ya tasomin lokaci ɗaya da maganar kawo miji, nasan ba zaiji uzrina ba alokacin meyiwuwa ma yace zai bayar dani ga wanda yaga dama..


Ya kance insha Allahu kamin lokacin da hakan zai faru ina tare dake wanda ƙilama kina ƙarƙashin kulawata ne alokacin, na kanji daɗin kalamanshi na ce na damu da kai da yawa Ibraheem, ina ƙauna da burin kasancewa da kai..


Na fiki burin son ganin munkasance tare da juna, babban burina ace yau muna ƙarƙashin inuwa ɗaya muna kulawa da juna tare da...uhm naja numfashi da ƴar dariya..ina sonki da yawa Asiyah ina muraɗin kasancewa tare dake ina burin ace akoda yaushe nine kusa dake, kamar yadda nasan akoda yaushe nine manne cikin zuciyarki.


***


Da daddare ina tare dasu Hashim agidanshi ana gobe sunan ɗiyar da matarshi Saudatu ta haifa(haihuwarsu ta fari kenan) tare da ƴan uwan Saudat ɗin dani dasu Fareeda munata shirye-shiryen gobe suna.


Yaro ya shigo da sallama wai ana neman Asiyah awaje, na dubeshi da mamaki danni bansan kowa a Unguwar ba balle ace har ana nemana, na tambayi yaron me yace sunan shi?


Ya juya kai da faɗin bai faɗa ba, nai dum kamar bana jeba amma ƴan wajen suka matsa akan na fita mana naga ko waye, Fareedah ta ɗora da cewa ƙilama wanda kika shekara da shekaru kina son gani ne, faɗar hakan ya faɗar min da gaba dan nasan hakan na iya faruwa.


Nai saurin miƙewa na sami gyale na rufa jikina nabi bayan yaron...


kallo ɗaya naiwa baƙon nasan cewa wannan ba Ibraheem ɗina bane, nan naji raina ya ɓaci kamar na juya sai naji yana cewa aimin adalci mana malama Asiyah, na tsaya ina kallonshi ya gyara tsayiwarshi gabana ya soma magana anatse.


Duk wanda ya biyoki har inda kike ya sanki kenan ya kuma damu da al'amarinki yana kuma burin ƙulla wani abu mai muhimmanci dake ne, dan haka karki mamakin ganina awajanki abinda kawai nake so dake ki fahimceni muyi magana irinta fahimta, kisan madosana nasan inda kika nufa...ina fatan kin fahimceni?


Na kalleshi kaɗan na ɗauke kai haka kawai naji ban iya mashi wulaƙanci dan haka na ɗage kai da faɗin ina jinka, ya gyara tsayiwa Asiyah banzo gareki da siffar wasa ba magana ɗaya ce takawoni ita ce ƙauna babban burina ayau naga na mallakeki ta hanyar aure, nai mashi wani irin kallo mai ɗauke da alamomi da yawa.


Bai damu da irin kallon da nake mishi ba yaci gaba da magana, kamin nazo gareki sai da na kama bincike da nazari akanki, na gamsu da halayenki na gamsu da ɗabi'unki na yadda da al'amuranki dan hakane tuni na gama yankewa kaina shawara kece abokiyar rayuwata ta din..din..din kece wacce na zaɓa ki zamo matata mai kare daraja da mutuncina mai kula da biyan buƙatuna, na kuma yadda dake ki zamo abokiyar sirrina mai riƙe amanata ki zamo Uwar 'ya'yana mai basu tarbiya ta gari...Asiyah ina da burin kasancewa tare dake cikin lokaci ƙanƙani...amma me kikace game dani?


Uhm! Nayi ƴar dariya bayan sauke numfashi na kuma gyara zaman hannayena aƙirjina idanuwana suna kafe akansa, yana kallona bakice komai ba kinyi dariya ko baki yadda da al'amarina bane?


Na juya kai ina kallonshi, nace da farko ko sunanka ban sani ba, oh! Ya dafe kai Sorry Asiyah hankalina yayi kanki duka sai nakeji tamkar kema kinsanni ne amma sunana *Hussain* ina rayuwa anan cikin kaduna tare da iyayena wanda asalinsu kanawane, kuma ni ɗan kasuwa wanda kasuwancin nawa inayin shi ne tsakanin Nigeria, Dubai da kuma sauran ƙasashen da ba'a rasa ba.


Na taɓa aure shekaru huɗu dasuka wuce Allah yaiwa matar rasuwa wajan haihuwar ɗanmu na fari wanda yaronma Allah yayi bamai rayuwa bane kwana uku bayan hiahuwar tashi ya rasu, ya kalloni to kinji ɗan taƙaitaccen tarihina...na kalleshi da tausayawa nai mishi gaisuwar rashin da ya yi tare da fatan samin madadinsu.


Munyi shiru na ɗan lokaci daga bisani ya katse shirun da cewa, Asiyah me kika ce game dani? Na tada kai na kalleshi ataƙaice na ɗauke kai, (maganar gaskiya bana son mutumin nan, dan tunda na kalleshi kallon farko naji sam-sam bai munba) to amma sai na tsinci kaina da ban iya duban idonshi na ce bana son shi..


Dan haka amsar dana bashi alokacin shi ne Allah ya zaɓa mana abu mafi alkhairi cikin rayuwarmu, yace ban fahimci inda kika dosa ba Asiyah, na ce cikin dukkan al'amurana nafi miƙa zaɓina ga Allah, yai shiru yana kallona daga bisani ya nisa yace na fahimceki kuma nima zan kasance cikin bin tsari irin naki domin ko acikin dukkan al'amura anfiso abar zaɓi ga Allah dan zaɓin nashi shi ne abin so.


Cikin ƴan kwanakin nan Hussain ya zamemin abokin hira a duk inda nake yana biye dani shi buƙatarshi ɗaya gareni na amince da buƙatarshi na amsa zan aureshi, ni kuma wallahi ko ƙanƙani bana jinshi araina kuna nakasa fitows fili na faɗa abinda ke raina domin ni dai kawai ina ganin girmanshi bana iyayi mashi wulaƙanci dan haka duk lokacin daya zo ganina zan fito mu gaisa lokaci kaɗan na kawo uzrin da zaisa ya tafi shiko da yake mai sauƙin kaine baya damuwa zaimin sallama ya wuce abinshi.


Ubangarin Ibraheem alissafin da muke baifi saura wata ɗaya da sari ɗaya ya dawo ba, inda ya tabbatarmin da cewa cikin satin daya dawo zai gabatar da maganar auranmu yace da son samune Asiyha aɗan tsakankanin nan ki zama mallakina koda kuwa za'a ɗaura aure ne kawai daga baya biki ya biyo..


Nayi dariya da dai kayi haƙuri a haɗa gaba ɗaya, danna tabbata dasa ranar da zuwan bikin ba zaifi wata ɗaya ba kacal, kacal ne ma awajenki ko Asiyah? Kacal ne mana Ibraheem in anduba tsayin shekarun da suka wuce.


Kuma fa haka ne amma kinsan wani abu? Na juya kai da faɗin a'a, wallahi Siyah ji nake tamkar na buɗe ido na ganki kusa dani, nayi dariya nace ko Ibraheem, wallahi Siyah na damu dake ban taɓa son abu fiye da son da nake miki ba.


Dan haka dan Allah Asiyah ki ɗaukeni da muhimmanci arayuwarki ki sani na zamo mafi kusanci dake fiye da kowa...wai ko kana shakku akainane? A'a ya faɗa da sauri, yaci gaba da cewa wallahi Asiyah ina sonki da yawa ne, na damu dake na matsu da in ganki kusa dani in atsoron ranar da zan dawo asa bikinmu lokaci mai tsawo.


Karka damu da wannan Ibraheem, nai maka alƙawarin insha Allahu auranmu ƙaramin lokaci za'a sa ka kwantar da hankalinka ni taka ce wadda tafi kowa ƙaunarka.


__________________


A ɓangaren Hussain ya matsamin ainun da son turo magabatan shi gidan mu, inda ni kuma hankalina ya tashi dan ina tsoron yakai kanshi ga Abbanmu babu makawa zai amsa maganarshi balle kuma ace ya turo magabatan shi, dan hakane na shiga rarrashin shi ya bani lokaci kaɗan na gama nazari.


Yau daya zo muna jira yace, Asiyah ki shirya na kaiki ki gaida mahaifiyata, na kalleshi da alamar tsoro banyi magana ba yace koba zaki bane?


Na ce kayi haƙuri zuwa lokacin daya dace, ya haɗe rai nina rasa inda kika dosa game dani na karanceki na fahimci sam hankalinki baya tare ɗani, duk inda na ɓullomiki da buƙatata kinsan hanyar da zaki bi ki shareta, ina so ki faɗamin gaskiyar abinda ke zuciyarki game dani, inbakya ra'ayina ki daina yimin yawo da hankali ki fahimtar dani nasan halin da nake ciki, nai shiru ina kallon ƙasa ba tare da na ce dashi komai ba..


Shirun ya ƙara kular dashi ya buɗe murya ya kira sunana *Asiyah*, na tada kai na kalleshi shima idonshi akaina maye matsayina agunki dan Allah dan darajar Annabi karki rufeni, ki faɗamin abinda zuciyarki game dani, wallahi duk inda kika ajeni bazan ji zafinki ba, burina dai nasan matsayina karki barni inata hauka da son ran da bai damu dani ba.


Ban iya tankashi ba dan azahiri in gaskiya yake son na faɗamishi baya cikin zuciyata kuma wallahi harga Allah ba zan iya duban cikin idonshi ba nace bana sonshi, innai hakan tamkar cin fuskane agareshi, yawan alkhairin shi agareni da irin so da kulawar da yake bani ya wuce na furta bana sonshi, dan haka agareni shirun nan shine mafi a'ala.



Bayan kwana biyu munsake zama da Hussain inda yake cemin na kula dake Asiyah Ibraheem yafi kowa da komai tasiri cikin rayuwarki, na kalleshi da sauri da mamakin ina yasan Ibraheem...karki mamaki dan nasan Ibraheem shi ne zaɓinki, abin sonki wanda kike fata da burin ya zamo abokin rayuwarki na aure..yai shiru yana kallona bakin shi da alama nason firta wani abu harya buɗe bakin sai kuma ya fasa ya sakeyin shiru na ɗan lokaci sannan ya kira sunana atausashe Asiyah, ban iya kallonshi ba, yaci gaba da maganarshi..


Na tabbata Ibraheem daya shiga rayuwarki shiya hana na sami so da kulawa daga gareki, banji haushi ba Asiyah danna san dama da wuya ace mace kamarki bata da tsayayye azuciyarki, amma ina so kisan wani abu duk da nasan Ibraheem shi ne aranki shi ne zaɓinki da burinki ni ba zan iya janyewa daga gareki ba.


Zanci gaba da kasancewa tare dake da jarraba sa'ata inhar kinga na barki Asiyah to tabbata kin shigan wani ne, awannan lokacinne nasan lallai ke ba rabona bace saina haƙura na dangana, amma kina ahaka ba nauyin kowa akanki bazan iya barinki ba, sai inhar kekace na barki sai na kyaleki dan babu yadda na iya.


Ina fatan kin fahimceni ban kuma shiga rayuwarki, ma'ana na takura maki kona haddasa maki wata damuwa ba? Babu komai Hussain kuma na gode da kulawarka gareni, ya yi ƴar dariya karki damu da irin haka daga wajena, amma akwai abu ɗaya danakeso dake na ɗaga ido na kalleshi.


Ki dubi girman Allah ki daina shiga sabgar yaron can Asiyah, nabi hannunshi da kallo inda ya nuna Muhammad dashi wanda ke zaune gefe yana jirana mu gama na same shi.


Na maida kallona gareshi da tambayar saboda me? Yace na tsani tarayyarki dashi, na tsani na ganki dashi ko sunan shi kika kira agabana raina yakan ɓaci...nasani kasha faɗamin ka tsaneshi, amma baka taɓa faɗamin dalilin dayasa kake son na rabuda shi ba, ya juya yana ƙoƙarin buɗe motar shi yana faɗin babu abinda zan iya ce maki game dashi amma ako da yaushe ina faɗa miki kiyi taka tsantsan har yanzu ke yarinya ce Asiyah akwai abubuwa da yawa daya kamata aimiki gyara game dasu, ya gyara zamanshi cikin mota ina kallonshi yaja ya rufe yana kallona..


***





Machika novel

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol