Free chapter · Read without an account
23
🤳🏻
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@shooly84*
*_Not edited_*
💘 *23* 💘
Na fito falo bisa tirsasawar da Mami taimin, wanda harya kaita da nuna min ɓacin ranta ta hanyar yi mani kaca-kaca (faɗa), har da zagi aranar nan dukana ne kawai Mami ba tayi ba...
Ita duk cikin al'amarin bata ganin laifin kowa sai nawa, abinda ta rinƙa cewa wai da gangan na mayar da kaina sakarya har akemin irin haka, ta ɗora da cewa, in banda kina sakarya mara tunani mai zaisa anyi na farko kin gano shiri ne har kuma ki yadda aƙara shirya maki wani irinshi ki hau kai ki zauna.
Yanzu kuma danta bayyana irin wancan ne sai ki zo kisa mutane gaba kinajin haushinmu kamar mun kashe maki Uba..to wallahi ki kiyayeni ki cire wannan maganar aranki ki shiga cikin ƴan'uwanki, inba haka ba zanyi mugun saɓa maki acikin gidan nan.
Faɗan Mami shiya razana ni, dan ban saba jin irin haka daga wajenta ba, dan haka na fito falon duk da cewa ban sake ba amma na zauna acikinsu muna kallo wanda agareni babu abinda nake fahimta sai saƙe-saƙe nake cikin raina.
Abubakar ne ya kirani awaya yana faɗamin na sameshi awaje yana jirana, na miƙe tsam dama zaman falon ya isheni, na iskeshi jingine jikin mota amma bashi ɗaya bane su uku ne sauran ban sansu ba..
Ya kalleni da kyau yace meya sameki haka Asiyah kinga kau yadda kika koma ne? Uhm kawai nace mishi.
Ba dai maganar Saleem ke damunki ba ko?
Kawai sai naji hawaye sun zubo min [To tayama za ai ace ba zan damu da wannan *halin dana shiga ba*], ya matso kusa dani shima ga shiga damuwar yace banga abun tayar da hankali ba anan Asiyah, kamata yayi ki mance da antaɓa makamanciyar magana irin haka, inya so sai kiyi ƙoƙarin kiyaye gaba kar irin haka ta sake faruwa.
Amma ya ake so nayi da zuciyata Abubakar?
Yayi shiru yana kallona, naci gaba da faɗin anraunana min zuciyata Abubakar, ansamin damuwa irin wacce ba zata taɓa barina ba, kayi tunani kaga shekara nawa ina fama da abu ɗaya, kuma aƙarshe duk adawo acemin abun nan ba haka bane, saboda Allah ya akeso nayi da rayuwata ina ake so nasa kaina..
Ancika min zuciyata da son gaibu, ina ake son nakai zuciyata data cika sonshi Abubakar ka duba al'amarina mana..kuka yaci ƙarfina na kifa kai ajikin mota naci gaba da rera kukana, ni nama mance da cewa sam Abubakar bashi ɗaya bane awajen.
Gefen kunnena naji maganarshi hakan yasa na fahimci ya matso kusana sosai, yace ya isa haka mana Asiyah, na tada kai na kalleshi yanayinshi duk damuwa da tausayi sun cika fuskarshi, sai kuma ƴar kunya ta kamani ganin mutane biyu sun samin ido suna kallona da alamar tausayi, n agoge hawayen na gyara tsayuwata ina fuskantar Abubakar dake magana...
Dama Saleem ne ya matsa na kawoshi wajanki yai maki bayani akan abubuwan da suka faru tare da baki haƙuri, yaimin nuni dashi da hannu.
Na kafa mashi ido wanda tashi ɗaya naji duk duniya babu wanda na tsana irin Saleem, dalilin abinda yaimin alhalin bai sanni ba, bai taɓa ganina ba, baisan inda nake ba kawai...
Ya gama dogon bayaninshi wanda dama nasan daga ƙarshe *Abdul ne* ya sashi, amma duk da haka banajin zan iya yafe mashi tunda dashi aka haɗa baki aka cuceni.
___________________
Abdul ko aɗakinshi na tirkeshi, wanda tun randa shirinshi na biyu ya bayyana ya rasa gane kaina da inda na dosa, sai yau dana kai kaina har ɗakinshi...
Abinda na fara tambayarshi, Abdul me kake nufi danine arayuwata? Ya juya kai me kuwa zan nema dake Asiyah in banda alheri...ƙarya kake wallahi Allah arayuwarka baka taɓa nufata da alheri ba sai sharri, ni na rasa abinda na tsara maka a gidan nan dayasa dukkan ƙulle-ƙullenka sai ka tsallake kowa ka jeho shi kaina.
Nifa na kasa fahimtarki Asiyah ni atunani zaki gane cewa duk gidan nan nafi ƙaunarki fiye da kowa, nace abaki ko? Sam ba maganar abaki ba...mubar doguwar magana muyi wadda ta kawoni, nasan dai zuwa yanzu kasan na fahimci meye makomar maganar Ibraheem?
Yai ƙasa da kai jin inda na dosa, nace ka dubi girman Allah da darajar Annabi kar muja magana da nisa abu ɗaya nake so na fahimta awajanka shin Abdul kawai Ibraheem ko babu shi?
Yai shiru na tsayin lokaci daga bisani ya tada kai bai iya kallona ya sanyaya murya yace, gaskiya guda ɗaya ce kuma ita kika roƙeni, to agaskiya Asiyah sai dai kiyi haƙuri kimin afuwa amma kam azahiri babu wani Ibraheem.
Nasa mishi ido cike da matsinaciyar tsanarshi, yayinda zuciyata ke azalzamin da azabar ciwo, muryata cike da damuwa na tambayeshi sam-sam babu shi?
Ya ɗaga kai ba'a taɓa yin wani mai suna haka ba wanda ni nasan yana sonki, kwalla ta ciko mun ido ban bari ta gagaro ba, na dake da muryata nace amma na tambayeka wani Abdul, yace ina jinki, dan Allah ka faɗamin dalilinka na shirya min irin haka kaina daga wannan har wancan daya wuce.
Ya kalleni kaɗan ya ɗauke shiru ya biyo baya, ina jinka Abd...dan Allah kiyi haƙuri ki mance komai, insha Allahu irin haka ba zai sake faruwa ba, amma kai atunanika ka kyauta ko kayi min adalci?
Banyi ko ɗaya ba, ki dai yimin haƙuri, naji na ƙara tsanarshi yadda yake man magana sam babu alamar wata damuwa atare dashi, asanyaye na tashi na nufi ƙofa zan bar mashi ɗakin, Asiyah, na tsaya tare da juyawa yana tsaye dab dani.
Nasan ban kyauta maki ba, shiyasa nake roƙonki yafiya aƙarshe nake roƙonki akan ki daure ki dawo da zuciyarki gareni, wallahi Asiyah Allah kaɗai yasan irin jarababban son da nake maki, ina sonki Asiyah fiye da son da nakewa rayuwata, dan Allah ki taimaka ki maye gurbin da kika rasa dani acikin zuciyata...
Ya bani dariya, ya bani haushi naji na ƙara tsanarshi, naji araina zan iya kasheshi da azababbiyar ƙiyayyarshi, na juya kawai zan fita ya riƙo gyalena ta baya, ya ƙara ɓatamin rai na juya ahargitse na watsa mashi mari da hannayena biyu na ɗora da bala'i na ashar iri-iri, aƙarshe na tabbatar mashi da cewa ya shirya barin gidanmu, dan wallahi na ƙudurci ƙulla mashi sharrin dako da Ubanshi aka haɗa kuɗi aka gina gidan sai ya barshi.
***
Abubuwan da suka biyo baya sun haɗa da kwanciyata asibiti sakamakon ciwon zuciya daya so kamani, bayan an sallameni aka zauna case da Abdul dasu Hashim, kai magana dai har gaban Abbah inda ya buƙaci agaya masu gaskiyar magana akan Ibraheem, ƙarshe dai batu guda ne shi ne ba Ibraheem ba kuma wani ƙwaƙƙwaran dalili daya sashi shirya hakan.
Haka ya ƙara tinzira su Hashim inda sukasha alwashin sai sunyi ƙarar Abdul ga iyayenshi, da ƙyar Mami ta kashe wutar danshi Abbah baice komai ba alama ta yafi kowa jin haushin abinda ya faru.
Kamar wasa dai ya tabbata ba Ibraheem, dan haka na haƙura na dangana, sai dai na rasa yadda zanyi na cire so da ƙuanarshi acikin zuciyata, musamman inna tuno wannan mutumi mai baƙaƙen kaya, sai hankalina yafi kullum tashi danme?
Dan atun farko al'amarin an dangantamin da shi ne Ibraheem, dan haka ni dai shi zuciyata ke muraɗi shi ne nake so da ƙauna, " *The Man In Black* ɗan fari kyakkyawa mai saje gwanin sha'awa da murmushin shi mai kwantar da zuciyar me bege.
Na kammala rubuta labarina wanda Anti Lubah ta bashi suna *Halin Dana Shiga*, da yamma tai sanyi na rungumo littafin aƙirjina zan kaiwa Anti Lubah, jikina ina sanye da Arebian jallabiyya marar nauyi Milk colour mai kwalliyar stones jefi-jefi masu walainiya, na rufe iya kaina da ƙaramin hijab, sai ƙafata dana sanya takalmi silifas na roba shi kuma baƙi ne mai ƙatuwar flower asamanshi, hannuna ɗaya riƙe da littafin sai kuma ɗayan riƙe da wayata *Nokia Asha...*
Business center dake kan layin na nufa dan nayima wayata loɗi, aka bani kati na ɗari biyu na tsaya ina sanyawa, Raheedah ta iskeni wajen itama katin ta siya ta tsaya wajena muna maida magana.
Kamar daga sama muka ji sallama akanmu tare muka juya ga mai sallamar , wanda ganin nashi nan take ya saukar min da wata irin faɗuwar gaba game da matsinancin tsoro da mamaki, (ya kuma tuna min baya), kamar ganina dashi awancan karon, tunda kai hula kenan har zuwa takalmin ƙafarshi baƙaƙe ne hatta glass daya rufe ƙwayar idanuwanshi.
Kamar wancan karon miryar shi atausashe yace dan Allah katin MTN zaku bani, ni kam ido na zuba mashi yayinda Rasheeda ta nuna mashi masu siyar da katin, kai tsaye ya wuce ya amsa har zai wuce sai kuma ya tsaya yana ƙare mana kallo, kana ya saki tsadadden murmushi yace dan Allah sunayenku fa?
Gabana ya sake faɗuwa kamar dai waccan haɗuwar muka kalli juna da Rasheeda muka sake kallonshi, ya saki ƴar dariya wadda sautinta ya saukarmin da wata irin zufa aduk gaɓɓan jikina, yasa hannu ya cire baƙin glass ɗin daya boƴe ƙwayar idanuwanshi wanda suke ƙunshe da tarin abubuwa da yawa.
Ya sake faɗaɗa dariyarshi tare da nunoni da glass ɗin dake hannunshi yace *Talatuwa ko*? Lallai na shaidaki, fuskarki taƙi ɓacemin tsawon waɗannan shekarun kin tsayamin arai na kasa cireki araina na kasa daina tunaninki amma kome yasa haka, na kasa gane dalili...
Ya maida glass ɗin ya rufe idonshi ko dan yaga na ƙurawa idanuwanshi nawa ne oho, ya sake yin dariyar data ƙawata ƴar kyakkyawar fuskarshi, ya soma tafiya yana faɗin sai gani na uku *Talatuwa Asiyah*, na ƙara shiga mamakin ina yasan *Real sunana*?
Harya ɓacewa idanuwana ban farga ba sai da Rasheedah ta taɓoni nai saurin sauke ajiyar zuciya, tunanika jingim acikin zuciyata, mukai sallama da Rasheeda na kama hanyar gidan Anti Lubah cike da ɗoƙin bata sabon labari na sake ganin *The Man In Black* ɗina.
Wannan shi ne ƙarshen *Halin Dana Shiga* akan batun Ibraheem, sai kuma sabon salon dana sake jefa kaina adalilin yaɗuwar *Social Media* ta ɓangaren *Facebook* wanda yafi na Ibraheem muni da takaici tare da ban haushi, aƙarshe na zamo abin tausayi da bani fatar ya ɗore har abada...
Machika novel