Free chapter · Read without an account

8

by Aisha Ahmed Machika · Rumanah (Zabin Iyaye)

*...Rumanah*🕊️

 (Zabin Iyaye)





*Arewabooks@shooly84*



©️ *Aisha Machika*






*Page~8*





Cikin bacci naji ana man sosar ƙadangare, na janye ƙafar tare da buɗe ido, Khalipha na gani zaune yana murmushi, yace wane irin bacci kike har bayan la'asar? Yanzu fa huɗu da rabi, na miƙe zaune ina miƙa da salati, wallahi gajiyar zaman motar haya ne, har ka dawo daga ofis ɗin? Ni ba ofis naje ba, daga Zaria nake shigowata kenan nayi sallah Iyalle tace man kin dawo kina ɗaki, albishir biyu na zo maki dasu, na farko dai jiya naji Saraki na gaya ma Baba Sarki cewa jarabarku ta fito, ku biyu mata kawai kuka haye sauran maza ne, sai ki shirya dan gwamnan garin nan zai haɗa maku walimar jin daɗi da ƙwazon da kuka nuna na jajircewa domin zama mata likitoci.


Na biyu kuma gashi, kwalin waya ya miƙe mani ƙirar Nokia mai open&close, na amsa da murna tawa ce khalipha? Kwarai rai ko tun kina Abuja na sai mana ni da ke, da caji harma da kati na sanya maki da lambobin dukkanmu, daɗi ya kamani nama rasa wace irin godiya zan ma khalipha dan gaskiya ina son waya, abun na birgeni in na ga ƙawaye na ana passion da ita a makaranta, yace na tsareki da surutu bari na barki kiyi sallah anjima ma haɗu, ya miƙe ya bar ɗakin ni kuma na shige toilet.


__________________


Gaggarumar liyafar da mai girma gwamnan jahar Kano ya haɗa mana ta yi taro mai kyau wanda ya haɗa da ministoci da gwamnonin sauran jahohi harda mai martaba sarkin Kano, awa uku aka yi cur ana gabatar sa liyafar, iyayen dukkanmu ɗaliban suna tare da mu, an bamu kyautuka tare da yabon ƙoƙarinmu daga ƙarshe gwamnati tayi alƙawarin ɗaukarmu aiyuka, a ranar ni kaina ban iya cewa ga kalar farin cikin da nike ciki, nayi murna tare da yin godiya ga Allah tunda shiya kawoni wannan matsayi.


Sati biyu tsakani takardar ɗaukata aiki ta iso wajena, asibitin NASARAWA aka kaini, dan haka na ɗauki fannin ƴan'uwana mata, babu wata matsala na soma zuwa aiki, ofis ɗina babba mai cike da tsari da ƙayatuwa dai-dai na likitoci, ganin yawan zirga-zirgar da nike Baba Sarki ya bani gudunmuwar mota wata ƙaramar *kia picanto* khalipha shiya koya man tuƙin cikin sati biyu na soma jan motata da shaidar *L* gaba da bayan motar, shi kuma Yaya Saraki ban sake saka shi a idona ba tun Abuja, wani lokacin dai na kanji muryarshi tare da Iyalle in ya shigo gidan, bana fita balle ya ganni, abun mamaki kuma har yau banji Baba Sarki yana maganar aure na ba ga bikin khalipha nata matsowa.


Masu iya magana sunce girma nasa mutum ya rage yin wasu abubuwan, toh ina jin siyasa Baba Sarki rage wasu aƙidun da ɗabi'un nashi, dan yanzu zai shigo ya ganmu zaune kusa da juna ni da khalipha baya cewa komai, wani lokacin kuma ina danganta cewa idan na farko sun sha wahala na baya sauƙi suke ji, koma dai miye ni aiki na nasa a gaba, dan maganar aure nasan zanyi ne konan da shekara nawa ne.



A bangaren Saraki kam yana cikin wani yanayi da damuwa da rashin makamar dafawa, bayan ya dawo daga makaranta kafin ya ƙarasa gida ya biya wani restuarant yaci abinci dan yasan ko yaje gida ba ganin shi zaiyi ba, yana isa gidan bayan yayi fakin mota ya kira Lado mai masu wanki ya bashi kuɗin da zasu siyo abinci suci, Lado ya amsa ya yi godiya ya wuce, shi kuma ya yi tsaki yana zance a ranshi, ace gida da mace kuma matar gida amma babu abinci sai dai kullum a sawo saboda tsabar wulaƙancin Jamila.


Ya shiga falo ta re da sallama, toh a yau dai an samu Jamila ta amsa mashi sallamar, tana zaune kamar kullum tayi wanka taci uwar kwalliyar data saba, ya kalleta anatse, yarinyar ba dai kyau ba amma shi kam baiga ranar da zai so ta ba, abu mace ba ladabi ba kyautatawa sai shegiyar rashin kunya data aje, shi baiga riba ko alfanun auran nasu ba, ina ma Baba Sarki zai yarda ya yi mata saki har uku ya huta da bacin rai kullum.


Bai tsaya falon ba bayan kallonta da gama tunanin shi ɗakinshi ya nufa, kai tsaye toilet ya faɗa ya watso ruwa koyaji daɗin jikinshi, bayan ya fito kayan shan iska ya sanya ya kunna Ac ya kwanta kafin anjima ya sake fita, amma kuma sai yaji ana buga mashi ƙofa, yai shiru yana tunanin waye, yasan dai Jamila bata shigo mashi ɗaki, tashi ya yi ya buɗe, Jamilar ce tsaye hanunta ɗauke da trayn abinci, fuskarta ɗauke da wani mayaidarin murmushi, kallo ya bita da shi harta wuce ta shige cikin ɗakin.

[6/10, 5:16 PM] Ummu~Yusrah: Ta aje trayn kan stool, bai motsa ba balle ya koma cikin ɗakin, tsabar mamaki ya hanashi komai, me Jamila ke nufi? Ya ce aran shi, ganin ya yi tsaye yana kallonta ya sata cewa lafiya kake kallona haka? Ko na canza maka ne? Rainin hankali kenan yace, sai kuma yaga ta nufoshi, jan hannun shi ta kama yi tana magana, abinci na kawo maka dan nasan kana tare da yunwa, amma kayi wani tsaye kana kallo na kamar kaga wata sabuwar halitta.


Ta kaishi gaban abincin ta zaunar ta soma buɗe kulas ɗin, haɗaɗɗiyar jalop ce ta shinkafa taji veges sai papper soup ɗin kifi da yaji kayan ƙamshi, a gefe kuma haɗin lemon abarba da kwakwa ne da lemon kaɗan, yabi abincin da kallo, rabonda yaga lafiyayyen girki haka tun Rumanah na gidan, ya soma magana a zuciyarshi, waya koya ma Jamila girki? Ko dama ta iya tsabar iskanci da wulaƙanci ne ya hanata yi, ya ɗauke kanshi daga kallon abincin ya haye gado.


Jamila ta bishi da kallo, tasan hakan zai faru, idan ta tuna abubuwan da ta rinƙa yi mashi a baya, data san zata soma son shi data yi haƙuri tun farko tayi mashi biyayya, amma ina a lokacin tana ganin ta wuce da sanin shi ƙari da zugar ƴan 'uwanta, sai yanzu daga baya ta gane duk hassada da baƙin ciki suke mata, ganin ta samu miji mai kyawo da kyan hali ga ƙwarjini, ita kanta yanzu tasan tayi dacen mijin aure mai haƙuri.


Ta kalli abinci da tayi wata biyu tana koya a cikin vedios da litattafan girke-girke masu dama, takaici yasa kwalla ta zo mata, ta kalli Saraki dake kwance ya lumshe ido, kenan ma baya son ganinta a ɗakin, cikin sanyin da jikinta ya yi tace, Saraki ya ya zaka haye gado bacin abinci na kawo maka, ko bai yi maka bane?


Ya buɗe ido ya kalleta da kyau yace, yaushe na samu matsayin ayi man girki a gidan nan? Ban saba ganin shi ba, kuma yanzu dana gani ba zaisa inci ba, tayi shiru tana kallon shi, ya kuma cewa yanzu dai tattara komatsanki ki bar mun ɗaki, surutanki na damun kai na, ba gaddama na ta kwashi trayn ta nufi ƙofa, tana gab da fita ta juyo tace mashi kome zaka yi ka tuna dai ni matarka ce, inka tashi ramawa kayi man da sauƙi, ta fice ya bita da kallo, yaja tsaki yana faɗin da sauranki yarinya.


Da safe tun ƙarfe takwas ya shirya ya fito, yana fitowa falo Jamila ce kwance kan kujera har tayi wanka, ya yi mamakin ganinta a falo dan yasan har ya gama shirinshi ya fita bata fito ba, tana ganin shi ta miƙe har da ina kwananta, ya amsa a ɗaure, tace ga fa kalacinka can na shirya maka, bai ko kalli dinning ɗin ba yace toh kici mana, ai saboda kai nayi su Lado ma na basu nasu, wani murmushi yayi a saman lips ɗin shi bai yarda ya kalleta ba yace, gashi ni kuma ba cin zan yi ba, duk da yaji daɗin ba su Lado abinci da tayi sai bai nuna ba, ya yi ficewar shi bai sake ce mata kanzil ba.


Yana fita ta rushe da kukan dana sani, sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe ta shige ɗakinshi ta sha re mai ta gyara ko ina har toilet ta wanko.


Yana shiga ofis ɗinshi wata ɗaliba tayi mashi sallama, ƴar 300L ce a fannin comouter, yana ganinta ya haɗe rai, yasan halinta tun ba yau ba, ta jima tana bibiyarshi tana nuna mai alamomin so yana shareta, ta gaisheshi tana wani yauƙi da fari da idanuwa, kallonta kawai yake kamar ya miƙe ya shaƙeta yake ji dan haushi, yabi kayan jikinta da kallo, riga da siket ne sun matseta ainun wanda suka fiddo mata da yanayin ƙirar jikinta.


Shi duk a gane-ganenshi bai taba ganin kirar mace irin ta Kareemah ba, ko shi da yake namiji yasan ya fita kyan gani, tsaye take kamar an tsaida sanda, ba hips balle bom-bom ƙirjin wayam kamar na namiji, a fuska dai ba laifi tana da ɗan kyan fuska, amma shi ba irin macen da yake so ba kenan, ƙira mai kyau ai sai Rumanah.


Ta sake kaɗa harshe tana cewa mallam Saraki kwana biyu shi ne nace bari dai inzo mu gaisa, ya ɗanyi yaƙe yace aifa yana da kyau, taci gaba da janshi da fira, shi kuma suk ya ƙosa ta fice dan ganin take-takenta nema take ta faɗo mashi a jiki, ya dai gashi yace kinga Kareema yanzu aiki gareni, kin kuma dameni da surutu, tace ok toh bari in baka waje amma jibi zan zo maka wuni, bai cw mata komai ba ta fice, tana fita khalipha ya shigo suka shiga gaisawa da tambayar lafiyarsu Baba Sarki.


Khalipha yana dariya yace Baba Sarkin ma ya taso ni zuwa wajenka, yace wai laifin me suka yi maka ka daina zuwa gaishe su, dariya Saraki ya yi, ba laifin komai dama gobe nake sa ran zuwa inyi mashi wata muhimmiyar maganar da tafi shekaru shidda ina fama da ita, Khalipha yace toh Allah yasa ta alkhairi ce amin, ni kaina ina zuwa gidanka bana samunka sai wannan matar taka, hmmm kasan me jiya ma sai gata wai tazo gaishe dasu Iyalle, muka dinga mamaki dan bamu taba ganinta gidan ba, kaga ladabin da take ma Iyalle wallahi kamar ba Jamila ba.


Saraki murmushi ya yi kawai ya sako maganar Rumanah, Khalipha Ummu na nan kuwa? Tana nana Yaya danko jiya firarka muka yi har tana cewa zata bugo maka waya taji ko lafiya shiru ba'a ganinka, toh ta kira wayar taka a kulle, Saraki yace mutane suka dameni na kashe, nan dai sukayi ƴan hirarrakinsu na tsakanin wa da ƙani daga bisani suka yi sallama Saraki na jaddama Khalipha yafa gaya ma Baba Sarki goben zai zo.

[6/10, 11:24 PM] Ummu~Yusrah: __________________



Nayi fakin motata a harabar gida, ina mamakin ganin motar Yaya Saraki saboda na daɗe ban sanya shi a idona ba, cikin gidan na ƙaraso na gaida Iyalle na shige ɗakina, ruwa na watsa na kwanta da niyyar bacci sai ga Khalipha ya zo kirana wai Baba Sarki na kira, Saraki da Baba Sarkin ne zaune kawai a falon, nima na zauna ina gaidasu nace gani Baba, yace a'a dama ɗan'uwanki ne keson ganinki, to kai Saraki gata nan sai ka faɗi abinda zaka faɗa, ina jin haka gabana ya faɗi Allah yasa ba maganar yana sona zai yi ba.


Sarakin ya yi gyaran murya ba shakka balle tsoro ya zaiyane ma Baban irin son da yake mani, Baba Sarki da farko shiru yayi, a yayinda ni ke cewa shikenan zama na gidan ya ƙare daga yau, ga zato na zan Baba Sarki tsinka ma Saraki mari ko ya ɗauko bindigar shi amma sai naga bako ɗaya illa magana daya soma yi a hankali.


Baba Sarki yace ka tabbatar kana sonta Saraki? Ƙwarai Baba wajen shekara shidda ma kenan, Baba yace kasan shi auran zumunci wuya gareshi, ana so ma yaya aka ƙare balle banu soyayya, ka tambayi ita Rumanan tana sonka? Ya sunkuyar da kai yace bata sona Baba tasha gaya man hakan, nayi maza nace ko yanzu zan maimata maka, Baba bana mashi son aure, ban taba kallonshi da wannan manufar ba, Baba Sarki ɗan murmushi ya yi yace Rumanah ba'a gaggawa, kai Saraki kaji amma ba zan saurin yanke hukunci ba kaje ka lallasheta harta amince.


Bayan ya sallame na fita jikina na rawa na tashin hankali, ɗakin Iyalle na faɗa na faɗa mata a jiki ina kuka wiwi da faɗin bana so! bana so wlh!! Ummu lafiya ko? Kukan me kike haka?


Na ɗago Iyalle bana son Yaya Saraki da aure, kinji wai sona yake yanzu ya gaya ma Baba, Iyalle kiyi mashi magana nasan zaiji taki, murmushi ta yi tace, kin gwammace ki auri zabin Babanki Rumanah? Nace eh, Ummu gara ki auri wanda baki san halinshi ba? Yanzu ke ba abin jin daɗi bane ɗan'uwa yana sonki da aure, kuyi aurenku hankali kwance, na girgiza kai.


Lafiyar Rumanah lau Iyalle? Khalipha ya ce bayan ya shigo, lafiyar ƙalau wai daga Yayanku Saraki yace yana sonta da aure shi ne ta ke wannan kukan, caf! lallai ma Rumanah inji Khaliphan, wallahi nafi kowa murna yaya Saraki ya aureki, Iyalle sun fa dace da juna, dama ni Baba yace in kawo wacce na ke so, Iyalle tace ita bata ga dacen ba, na sake fashewa da kuka, yanzu Iyalle duk kun goyi bayan Yaya Saraki? 


Gida ɗaya fa muka tashi, to sai me Rumanah, ince da aure tsakaninku? Inji Khalipha, nabar jikin Iyalle ganin sun maidani da maganata wasa,ina shiga ɗaki Khalipha ya biyoni.


Kin fa bani mamaki Rumanah, wallahi na daɗe ina maku fatan auren juna dan kun dace, na juyo rai a bace nace Allah ya isa Khalipha, dama kai kayi mani wannan muguwar fatan, toh bari in gaya maku kowa ya sani, bana son shi kuma ba zan aure shi ba sai dai in gawa ta za'a kai gida, da ranki zaki gudan yaya saraki, kiji daɗi Rumanah yanzu Baba ya sauko daga doka fa ƙa'idojin shi, me kike zaton zai faru inda kamar da yake? Da yanzu zaman gidan ya gagareku, nayi maza nace ya gagari Saraki dai danni ba zan aure shi ba.

To wai dan me baki son shi ne? Haka nan kuma ban ga abinda zai sa na so shi ba, to mudai muna so, kuma sai anyi, maganganun Khalipha sun soma ƙuleni ganin ma zolayata yake son fara yi mashi shiru kawai.


Kai naga ƴa'ƴanku Rumanah, kyau da kyau ya haɗu, nayi banza dashi, baki tausayinshi Ummu, har fa wata rama yakeyi kwanan nan, sai yanzu na fahimci duk ta ƙaunarki ce, kinsan yarda cutar so take? Ban sani ba kuma bana fatan sanin, dan Allah Khalipha ka fita tun kafin in ida haukace maku, ya fice yana dariya, kwanciyar ma ta gagareni sai famar kai gwauro da mari nake a tsakar ɗakin.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol