Free chapter · Read without an account

SIRRIN ZUCIYA 3

by Nusaiba · SIRRIN ZUCIYA

SIRRIN ZUCIYA






Na

Nuceeyluv😘




3.....




Fitowar ta kenan daga gida suka hadu da sumayya zata biyo mata su tafi dan yau zata fara zuwa, fatima tace,


"laa ashe kin iso"


sumayya tace,


"danma na tsaya shanyar kaya ne da tuni nazo"


suna tafiya a kafa fatima tace,


"sumayya ya yanayin gidan yake?"


Sumayya tayi dariya tace,


"keda zakije yanzu zaki ga komai ai"


fati tace,


"ba haka nake nufi ba kinsan wasu masu kudin akwai wulakanci basu dauki talaka a bakin komai ba musamman idan kana aiki kasansu sai su dauka baka da wani gata."


Sumayya tadan numfasa kafin tace,


"kinsan dan adam kowa da irin halinsa, kuma indai xaka nemi halak sai kayi hakuri kinga duka satina biyu kenan da fara aiki a gidan, gidan babbane kowa dame masa aiki toh ni a bangaren wanke2 nake aikina kawai nake nayi gaba bansan kan gidan ba."


Ajiyar zuciya fatima tayi tace,


"ai shikenan Allah ya sadamu da Alkhairin dake cikin gidan sharrin dake ciki Allah yyi mana tsari dashi"


"Ameen"


Sumayya ta fada tana tare musu Napep, Indian quarters suka bukaci me napep ya kaisu yace su hau ba matsala.




••••

Tun kafin su shiga gidan fatima ta fahimci Naira tayi kuka a wajen, daga bakin gate ma checking dinsu aka farayi, sumayya dauko ticket dinta tayi ta nuna musu nan sukace Fatima ta nuna nata, cikin rashin fahimta tace,


"ticket din meye kuma?"


Sumayya tace,


"ya salam na manta ban fada miki ba duk 'yan aikin gidan kowa da ticket dinsa na shiga gidan, tunda ke bakida shi saidai su kira Mummy"


Rai bace fati taso yin mgn wata zuciyar ta danne ta, lura da hakan yasa sumayya ta karasa wajen masu gadi ta sanar musu a kira mummy, ba bata lkci kuwa aka kirata mgnr few seconds ce ta hadasu aka katse wayar,


"Ku shiga"


wanda yyi wayar ya fada musu, jawo hannun fati sumayya tayi sbd taga alama bata da niyyar shiga, saida sukayi nisa da masu gadin fatima ta warce hannun ta tace,


"Wanne irin gidane wannan shigarsa saida ticket sai kace shiga jirgi?"

Tayi mgnr ranta na baci sbd ta tsani wulakanci, Sumayya ta dafa kafadar ta tace,


"fatima komai na duniya dan hakuri ne, kefa kike nema a gunsu kinga kuwa dole kibi procedures dinsu dan cimma burin ki"


Kwafa fati tayi tace,


"sumayya badan karna badawa hajjo kasa a ido ba da tun a gate na juya wlh sai kace dole."


Sumayya ta kama hannun fati tace,


"mu karasa daga ciki munayin late i know mummy tana jiran zuwanki tunda tasan an kirata."


Fati batace komai ba saima binta da take kamar jela tana nazartar yanayin tsarin gidan.



A kiyasce zata iya hango part2 na gidan, saidai kowanne akwai er karamar hanyar da zata sada ka da kowanne part, a haka suka karasa part din mummy knocking sukayi saida sukayi tsayuwar wasu seconds kafin aka basu damar shiga, bakinsu dauke da sallama sumayya ta bude kofar,


Tsaye sukayi suna kallon ikon Allah wata budurwa ce zaune kan kujera ita kadai a parlon na latsa waya ko kadan bata nuna tasan da tsayuwar wasu a wajen ba saima tsiyaya lemo da take a cup tana sha kadan2, Fatima uwar zuciya ta kasa dannewa da karfi tace,


"hey are you deaf??"


Daidai lkcin wata budurwar ta sakko daga bene, ita kuma ta zaunen ta mike cikin masifa sbd ji take ba'a taba wulakanta ba irin yau wai en aikin nan ke mata tsawa? Hannu ta kawo zata wanke fati da mari wacce ta sakko a benin tayi azamar rike hannun ta tace,


"haba Aunty sameera da girman ki?"


Sai a lkcn sameera ta magantu cikin kallon raini da kaskanci ta jefi su fati dashi kafin tace,


"khairat Kinji tsawar da wannan wawiyar er aikin tamin ne? Meyasa zaki rikeni baki barni na gurji bakinta ba?"


Jawota khairat tayi ta xaunar da ita kan kujera tace srry Aunty bakya ganin new commer ce? Ki mata uzuri pls,"


huci sameera tayi tana me jifan fati da mugun kallo, khairat tace,


"haba ta saraki gadanga kusar yaki Ya Abutturab mene abun fushi kuma? Ki share zancen next time ta kwatanta haka ki kwashe ta da mari harma da duka"


dan murmushi sameera tayi sbd wasa wanda takeso da tayi tace,


"Khairat tawa shiyasa nake yinki"


dariya suka saki gaba dayansu suna tafawa, daidai lkcn kuma wata babbar mata ta fara takowa daga saman benin.


A bangaren fati kuwa sai matse hannun ta take a cikin hannun sumayya tana tankwarar zuciyar ta, badan haka ba saita koyawa sameera hankali, suna tsaye a haka mummy ta karaso wajen su.


Zamanta keda wuya, su fati suka durqusa a gabanta, haka kawai fati taji wani irin girma da nauyin matar ya shigeta, ba yabo ba fallasa mummy ta amsa musu, Bayan sun gaisa sumayya tace,


"Mummy wannan itace Fatima wacce Innata ta miki mgnr ta."


Mummy ta kalli fatima na tsawon lkci tana nazartar ta, A yanda ta fahimci fati tayi mata 100% duba da yadda ta ganta tsaf-tsaf, farcen hannu da kafa a yanke jikinta sumul babu yankwane wa tasan lalle tayi dacen me aikin part din 'yan ukun ta, dan sunada tsananin kyankyami daga kallon me aiki ma idan bata musu ba korar ta suke mummy tasha kawo musu mai aiki abun baya tsawo tun dawowar su kasar, daga karshe ma khairat itace keyin komai duk yadda sameera taso cusa kanta zatayi kin amincewa sukai, khairat na fushi da tura baki haka zata gyara musu part ta jera musu food, toh yanzun University zata tafi can BUK kano dama zaman jiran Admission take shiyasa Mummy ta fara bada cikiyar me aiki.



A hankai Mummy ta sauke ajiyar zuciya kafin tace,


"Fatima ina fatan zaki bada hadin kai wajen zaman lpy babu munafurci, bacin Amana and Lastly banda kazanta."


Fatima cikin girmamawa tace,


"Insha Allahu Hajia zanyi iyakar bakin kokari na."


"Masha Allah"


Mummy ta furta tana me ci gaba da fadin,


"Yanzu TRIPLES basa nan sunje wani program Abuja tun shekaran jiya, Amma muna sa ran gobe ko jibi su dawo dan haka zaki fara aikin ki daga yanxu, zan hadaki da khairat ta nuna miki komai na part din da yadda zakiyi, sauran maganar zakuyi da ita."


"Toh hajia"


suka amsa a tare, Mummy ta kalli sumayya tace,

"kije kitchen nasan su gwaggo Rabi sunyi nisa a aiki koh"


"hakane"


sumayya ta fada tana mikewa, Nan Itama Fatima ta hadata da khairat dan zuwa part din 'yan uku.



Sameera na zaune duk tana kallon abinda ke faruwa ta tashi rai a bace tayi hanyar part dinsu itama tana me ayyana abubuwa a ranta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol