Free chapter · Read without an account
Chapter 3.
by Sayyada Tahir · Akwai'kura
Akwai'kura.
Book 1.
*P*5️⃣↘️6️⃣
By princess sayyada tahir mrs faisal zakhari.
Fur Amrah taki bari,dan akwai ranarda Iya tafashe da kuka,sbd Alhaji Usman ne yaturo musu dasako ciki harda na Amrah kan mgnr skl nata wani makaranta takeso kuma maita keson karanta amman Amrah tace aje acemasa bataso inda kudinshi zatai karatu bata bukata kuka IYA tafashe wannan tsinkasu da Amrah tayi gaban dan aike direba shine yasa Iya kuka sosai ummynta Zainabu tadauki muciya tabita da duka Amrah nakuka Zainabu nakuka ganin ummyn nata tana kuka sosai tana dukanta yasa Amrah tasaurara dana kukan dan takaranta gani addini yamana magana da kaukasan murya kan sanya Iyaye kuka musamman Uwa cikin lallashi tabata hkr tareda alkawarin zatayi karatun ummy sboda mijinkinkike dukana shikenan tunkafin.ayi auren ko taturo baki yana buga kafa Sai tausayin Amrah yakama Zainabun tajawota jikinta tana laashinta tareda neman alfaman dan Allah tarage wannan kiyayyan ga Alhaji usman malam Ahmd kwanan sane yakare koda yana kwance gida wannan ranar saiyamutu baxai kara kwanaba, tsakanin da uwa tuni suka sasanta kansu saigashi dukkansu suna dariya ZAinabu tace haba kaman kunbo kaman kayanta wnna kishin na Amrah haline tadauko irin na maaifinta, bayan gama takaban zainabu bada jimawa ba akadaura auranta da alhaji Usman saibayan andaura aurene sukagane ashe Alhaji Uman attjirine nagske kuma maaikaci babba ga hukumar nan ta sirri wato Dss mai matakin DG kuma babban dan kasuwa, Aurensu da ummyn Amrah Zainabu takara samun cigaban rayuwa arxiki yasamu ga kwanciyar hankali itakanta Iya tanacin moriyan Zainabu da mijinta sunzuba mata komai najin dadin rayuwa agidan nata sungyara mata daki uku kowanne dauke da bandaki aciki na Amrah daya na Iya daya sai extra daya saboda baki Ko Amrah inzata cire kiyayyar Alhji Usman ta tabbatr maaifiyan ta tasamu nutsuwa sosai kuma tasu miji mai.kaunarta da gaske zaman lfy sosai suke da hajiya sadiya matarshi hakan yaranshi sunabata girma sosai gidan Zainabu daban yagina mata mai kyau k aturai yahadu dafarkon auren yaso amra takoma gaban su daxama itaada iya amman Iyan tace bazata iya wannan abun kunyanba saidai Amrah takoma itako Amrah kalloma bai ishetaba bare har ta tamka..
Ikon Allah auren Zainabu da wata 11 kacal taaifowa Alhaji usman yy uku reras maza biyu mace daya inda yayi karawa Zainabu namijin yasamasa sunan Ahmad macen daya yama Iya takwara wato Hapsat suna kiranta da Amlah dayan kuma yaci sunan nashi baban wato mahmood.amir da khalifa ake kiransu, cikin shekara biyu Amrah tagama deploma Afederal.poly kaduna gawanta kedawuya tafara HND anan polyn inda yanzu take shekaran karshe Amrah makerin kyau yagama kera mata halitta tabarkalla masha Allah komai hassadanka inkagnta kasan itadin mai kyaune gason gayu ga rigima inkaga suturan datake sanyawa saikace diyar Gomna ummynta da mijinta sunwadata ta dakomai datake bukata sutura da kayan kwalliya baya karewa kafin wannan yakare ankuma mata oder nawasu Alhaji usman komai xaisaya wa yaranshi tare yake oder da Amrah hakan accnt dinta duk wata kudindake bada yaranshi shike turamata hakan yasa takara zama babban yarinya tana fantamawanta inda takeso saidai babu shakuwa ko kadan tsakaninta da rabia da mariya yaranshi domin dasuna kaunarta tunda sukagane irin kiyayyanta ga maaifinsu tuni suka fara takun saka dasu sau million inxasu hadu fada kerabasu hakan yasa Amrah batacika zuwa gidan ummyntaba saboda mariya da rabia nakaunar Zainabu kamar yadda itama take nuna musu kauna wanda suma suke mata lakabi da ummy kusan duk weekeend gidanta sukeyi tare da ummyn da kannansu en uku .
postin nasune yafito natafiya Attacment wato IT abun mamaki sai gashi antura Amrah Dss office dasunan IT ranar da takarbi takardan das karewa tayi kasa tashi daga gaban malamin nata tsaban damuwa domin tasan wannan sharrin Alhaji usman ne inbanda sharri itada karatunta daban meya hadata dawani I T ofishin security ? Rokon malamin nata tashiga yi kan yataimaketa yacnaxa mata musaman data bude takardan ta tabbatr ofishin ubansu Amlah aka kaita kamar yadda take masa inkiya.cikin kasala tabar masa office nashi saboda damuwa tana fita direct mashin yahau tacedashi yakata ofishin nasu Abban Amlah aganinta tanabukatar sanin dalilin daya aka kawota gurinshi kuma abakinshi takeson ji ganinta monday yayi nisa dahar xatajita tafara zuwa kamar yadda tagani ajikin takardan aiko tana zuwa gareshi da rashin kunyanta anan tayi karan bartan karfe dashi inda yabata aikinda yasanyata acikin garari baibata fuskanda har xata iya mayar masa da raddiba yakoreta cikin office nashi hmm!! Tofa ga Amrah ga Babanta dasannun zamuji dalilin dayasa yakaita wannan ofishi.