Free chapter 路 Read without an account

3

by Binta Umar Abbale 路 Sadauki Omar

SADAUKI!!馃徆

  _OMAR馃挮馃憫_

 


Free pege 


3






Jiki a sa'bule Ikilima tayi sallama ta zube gabanta cikin sanyi murya tace"Allah yaja zamanin ki yace." Yana Dan wani uziri yanzu kiyi hakuri......"Saurara min."! Ta katse ta tun kafin ta 'karasa maganar tata mik'ewa tayi zaune tana wani irin huci! Tace"Kamar ni na kirashi yace." Yana da uzuri ko wane uziri yake dashi nasan nawa uzirun yafi nashi tunda yana a matsayin mai bauta ne bashi da uzirin kansa sai uzirin iyayen d'akinsa yau zai gaya mun Wanda yake d'aure masa gindi a cikin masarautar nan." Mik'ewa tayi Ikilima tayi saurin gyara mata rufaffafun takalmanta masu wani irin gashi a jiki tare suka futa ikilima na take mata baya gabanta sai fad'uwa yake! Ganin ta nufi sashen su Omar din......... Omar na gama bawa dokuna abincin su ya futo daga tsakanin su can wata rumfa ya nufa kafin ya karasa yaji alamun taku an shigo gurin da sauri ya juya suka had'a ido kallon kallo suke wa junansu Ikilima taja gefe ta tsaya kanta a kasa.



Tsayuwarsa ya gyara yana watsa mata wani irin kallo kai da ganinsa kasan na kaskanci ne. Wani irin b'acin rai ya sake kamata ita yake wa kallon raini irin haka. A fusace! Ta nufe shi ta d'aga hannu da niyar kwad'a masa mari! Hannun ya rike yana murd'ewa! Ba tayi tsammanin zai dauki matakin haka ba. Cikin dauriya gami da tsananin azabar da take ji ta buga masa tsawa tare da fadin"Sakar min hannuna ma kaskancin bawa Wanda takalmin kafana ma yafi ka daraja a gurina."!! Omar ya murd'e! Hannuna da karfi har sai da ya bada sautin 'kas-'kas! Ta cije baki cikin dauriya don saura kadan hawayen azaba ta kufce mata abunda saboda kar yaga gazawar ta yasa take kokarin dannewa duk da haka dai kana ganin kwayar idonta zaka gane tana kar'bar gashi.!


Hannun ya yarfar yana kallonta a ya mutse yace." Ne man me kike min.!? Aysha ta rasa me zata ce saboda takaici Kuka tasa tana nuna shi da hannunta da yake karkarwa tace"Wallahi sai kayi nadamar murd'e min hannuna da kayi bakin mugu azzalimi sai na kaskantar da kai cikin gidan nan wallahi!


Zagin da take masa bai dame shi ba don haka gyara tsayuwarsa yayi fuska a kirne! Ya sake maimata mata tambayar sa ta farko "Nai man me kike min.''!?


Hannu ta sake d'agawa cikin shammata zata sake kai masa mari a karo na biyu taji ya damk'i hannun da iya karfin sa! 'Kara ta saki! Tana kokarin zubewa a gurin! Saura kadan futsari ya kufce mata. Saurin sakin hannun yayi yana kara daure fuska hade da kafe ta da jajayen idanunsa masu girma."!!! 


" Allah ya isa na."!! Abunda take iya fad'a kenan tana matse hannunta hawaye na silalowa a kumatun ta. Ko alamar tausayin ta babu a tare dashi ya sake gyara tsayuwarsa a karo na uku ya sake maimata mata tambayar sa ta farko " Ne man me kike min. "!?? Aysha yanzu ta fara dawo wa hayyacin ta kwata-kwata sai ta manta Neman ma me take masa ta diriri ce..... Nashi b'angaran so yake kawai yaji Neman me take masa da zata dunga aiko masa 'yan aike..... Ganin tayi shiru yasa ja tsaki ya juya da niyyar barin gurin....." Wawa Bakin azalimi Makaskanci Mara Iyaye kawai sai kayi nadamar zaman ka cikin masarautar mu Dan iska sai ka San ni kayi wa haka ni zaka ta'bawa jiki ko? Sai kayi nadamar abunda ka aikata a gare ni."!!! Kalamanta sunyi masifar bata masa rai har ya tsaya sai kuma wata zuciyar tace"K'yaleta kawai kar ka kulata." Ci gaba da tafiya yayi ya jiyo ta tana fad'in"Shashasha mai siffar Askarawa kawai."! Murmushi kawai yayi ya bude d'akinsa ya shige 



Ta juyo a fusace! Ikilima tayi saurin sunkuyar da kanta Don duk abunda ya faru a kan idonta ya faru..."Allah ya taimake ki."! Ta fada tana sake dankwafar da kanta kasa, Cikin mutuwar jiki tayi gaba ba tare da ta cewa Ikilimar komai ba, da saurin ta rufa mata baya tana mamakin karfin halin Omar da jarumatar sa tunda take bata ta'ba ganin kukan gimbiya Aysha ba sai yau lallai Omar ya cika namijin da za'a jinjina masa.




Jikinta ta zube tana kuka harda shassheka Hajiya Kulu mai dakin kusurwa ta d'ago kanta tana cike da mamakin Wanda ya sanya 'yar gaban goshin ta kuka irin haka tabbas abunda ya faru Babban lamari ne..... Sai da taci kukan ta ta koshi kafin ta fad'a mata abunda ya faru.



'Kwafa kawai Kulu take tace"Wannan ta'kadirin yaro wannan annamimin yaro! Wannan Dan iskan yaro! Ya addabe mu na tsane shi na tsani na bude ido in ganshi cikin masarautar nan har kullum Idan ka zauna da mai martaba bashi da aiki sai na kwarzanta bajintar yaron gami da kwarzanta jarumatar sa wato d'aurin gidin da ya samu gurin mai martaba yasa yake ganin kamar yana ra wata fawa a cikin masarautar nan lallai yau tunda ya sanya ki kuka sai ya raina kansa tabbas zai gane shi din ba kowan kowa bane. Face makaskancin bawa."



Aysha ta sauke ajiyar zuciya tana fadin"Mammah duba ki gani fa yanda ya mummurd'e min hannuna duba ki ga saura kadan ya kwashe min fata."



Tace"Rabu da d'an banza Idan ma maye ne shi to sai dai yaci kansa domin dai ke Kin fi karfin sa shin wai ma me ya kaiki har inda yake."? Aysha ta soma inda inda "Nifa ba zuwa nayi ba aike nayi yazo yaki zuwa shine na futo domin zuwa nan kawai naganshi nake masa magana shine kawai ya kamani ya mummurde min hannu.''



" Yanzu na fahimce ki, Wane irin mataki kike so a dauka a kansa."? Kawai ki aika a kirashi ni nasan matakin da zan dauka a kansa."



"Baiyo."!!!!! Wacce aka kira da wannan suna futo daga wani karamin daki dake cikin palon gabanta ta zube tana fadin" A gafarce ni Uwar d'akina ina kimtsa miki gado ne."!



Tace." Maza je ki kira min Tafida."! Ta mike da sauri ta futa... Mintuna uku sai gasu sun shigo tare Tafida ya zube yana kwasar gaisuwa. Tace"Na amsa maka Tafida maza je ka kira min Makaskancin bawan nan."! Tafida ya gane ko wa take nufi da sauri ya mike ya futa.


"Baiyo kije ki cigaba da aikin ki."!

Da sauri ta mike tana godiya.



Suna tare da Yunusa Sakon Mai dakin kusurwa wato Kulu ya same shi kwata-kwata ya manta abunda ya faru tsakaninsa da Aysha don shi mutum ne Wanda baya barin Abu jikin ransa jin Kuli ce take Neman sa da kanta yasa ya amsa suka jera tare da Tafida har suka isa shashen nasu Tafida yaja ya tsaya kofar shiga daya daga cikin masu tsaron kofar ne yayi masa ido har katafaran palon Uwargin sarki Wato kulu mai dakin kusurwa!! Bai ji wani d'ar! Ba don ganin Ayshar hakimce cikin kujera ba ya dai yi saurin kauda kansa saboda ganin yanayin suturar dake jikinta dama haka take k'ananun kaya matsatstsu take sanyawa a jikinta kafin ta d'ora alkyaba gata ita tubarkallah macece mai zati a cike take ko ina mussaman a kirinta tana da manya manyan nonowa masu fadi da tsine. Ga uban ships dake bata da tsayi sosai yasa suka futo sosai ko cikin alkyabbata take motsi suke Idan babu alkyabba a jikinta ko ke mace kika kalleta sau daya sai kinyi marmarin sake kallonta saboda yanda take da tsarin jiki mai kyau.



Omar ya rankwafa tare da fadin"Barka da yamma Ranki shi Dade sakon ki ya isa gare ni wai kina nema na."



Tace." Wato wai ne ma ko? Omar yayi shiru tace"Kai wawa Wanda bai San hallaci ba ina mai tabbatar maka da cewar karshen ka yazo wato baka sanni ba har yanzu ko!? Omar yayi shiru yana sauraron hayaniyar da take masa ta cigaba da cewa"Nice nan Kulu Mai dakin kusurwa Kulu mai magana da aljanu idan baka San labarina ba to kaje ka tambaya kaji wacece Kulu Uwar gidan mai martaba nasan kafin ka futa wajen gari cikin gidanan za'a fada maka wacece ni."



Omar dai shiru yayi yana sauraran ta tace"Takad'iri kana ganin kana da girma da kwanji na daukar dutse da k'arfe to duk wannan karfin naka da jarumatar taka basa bani tsoro kawai naso zaman ka cikin masarautar nan Idan da ban so ba da tuni na fatattake ka domin ni nan da ka ganni sharrina yafi dubu naci dubu sai ceto."!!!!! Takaici da b'acin rai ya kamashi! Ya lura matar kamar bugaggiya take a nutse yace." Ne man me kike min ko da wani taimako da za'ayi miki." A fusace! Ta mike tsaye tana nuna shi da hannu "Kai baka isa ka taimake ni ba don ubanka! Waye kai me kake takama dashi!? Duk sanda wannan Kalmar ta sake futowa daga bakina sai ka kwana bakwai a daure."! Omar yayi shiru yana jinta a fusace! Tace''Me Aysha tayi maka kake kokarin karya mata hannu."? Gefen da take zaune ya Dan kalla yayi saurin dauke kansa.


Cikin tsawa tace" Ba magana nake da kai ba ka sunkuyar da kai kamar munafiki." 


"Mammah! Kyaleshi."! Tafad'a lokacin da take mik'ewa inda yake tsaye ta nufa kansa dake sunkuye ta dago da hannunta ta ware karfinta ta kwashe shi da mari!!! Ko gezau baiyi ba...... " Baiyo."!!!! Ta kwala mata kira ta futo da sauri tana amsawa tace"Je ki taro min bayin dake sashen nan su kuzo tare." Baiyo ta futa da sauri domin cika Umarnin da aka bata.





3/3/2020


BINTA UMAR ABBALE

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol