Free chapter · Read without an account

episod 10

by wasila omar · IDON DUNIYA

Wasila Omar (mr's f.h)



🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*

***


*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~

     



    ....Turus ta tsaya domin ganin Anty tsaye gaban dorowan d'akin ga kaya a zube a kan gadon nata wanda da alama sababbi ne, cike da mamaki ta ƙarasa cikin ɗakin "Anty sannu da aiki" Anty da sai yanzu ta lura da ita ta juyo "yawwa ɗiya ta ya makarantar" ta faɗa tana ci gaba da shirya kayan cikin sif d'in "makaranta alhamdulillah,shine baki jira na zo ba kike aikin da kanki"ta karashe maganar da shagwab'e fuskar ta,dariya Anty tayi kana tace "haba wa ɗiya ta ai na ga kina makaranta ne kuma kinga kin dawo zaki gaji shiyasa na ɗan taya ki"  

 "to Anty kawo dai na 'karasa tunda kin kusa"

 "A'a ki je kiyi wanka tukun ki ci wani abun kinga yanzu kika cawo, inyaso in ban gama ba sai ki kar'ba" cewar Anty tana cigaba da shirin kayan,ba ta son musu da ita dan haka to kawai tace nufi bayin ɗakin dan ita kanta tana buk'atar taɗan watsa ruwan dan ta gaji sosai


  ......."FAHAD wai meke damun ka ne kwana biyun nan? ka mai da ni kamar sa'ar ka ina magana ka na ji na ba za ka bani amsa ba" hajiya lubna ta faɗa a hasale domin shirun nasa ya kai ta bango,shi kuwa fahad da shigowar sa kenan ta fara sababi ko kallon inda take beyi ba ya nufi hanyar da zata sadashi da ɗakin sa,ai kuwa hakan ya kuma ƙular da hajiya lubna tai saurin shan gaban sa" tass tass" ta sauke masa lafiyayyun mari har guda biyu amma ga mamakin ta ko gezau beyi ba haka ya raba ta gefen ta ya shige ɗaki ya sawa kofar key,ri'ke kanta tayi dan ranta ya ɓaci da shi,

"ya zanyi da wannan yaro ni Lubna ? kar ya zo ya ja IDON DUNIYA ya dawo kai na na shiga uku ni diyar mutum biyu"haka tai ta maganganu da wasu ma bana gane me take nufi ta nufi d'akin ta tana ta saka da warwara,

   A ɓangaren Fahad kuwa yana shiga rage kayan jikin sa ya yi ya nufi bayin ɗakin, ya kusa minti talatin kafin ya fito da tawul 'daure a ƙugun shi da kuma karami a hannun shi yana tsane ruwan jikin shi,zama yai a bakin gadon yana ta tunanika iri iri sai yana jin kamar ya rasa wani babban shashi a rayuwar sa amma ya kasa tuna koda abu d'aya da yake son tunawa,haka besa kaya ba ya zame ya kwanta akan gadon yana ta tunani ka barka tai,

   JASRA na fitowa ta ga har Anty ta gama ta gyara komai kamar ba a gurin aka ajiye wasu kaya ba murmushi tayi ta karasa gaban mudubin ɗakin tana cewa "Allah ya biya ki Anty na ya miki jagora akan abinda kika saka a gaba"haka ta shirya a gurguje dan ta jiyo kiran salla kafin ta ta da sallah dan tayo alwala a bayin,haka ta idar sannan ta tashi ta nufi falon dan gano ARYAN wanda tunda ta tashi ba ta ganshi ba......



MR'S F.H ✍️



share and comment

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol