Free chapter · Read without an account

Two families

by Azizat Hamza · Miss Nigeria


*MISS NIGERIA*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Biyu



Two families

***

A garin Lagos aka haifeta a nan kuma ta girma. Gidansu ya kasance babban gida domin ahalin Adetimeyin Brown na da ƙaurin suna a garin na Lagos.

Omolola ko kuma Lola kamar yadda aka fi kiranta ta saka hannunta a ƙugu tana ganin wannan walaƙanci da mahaifiyarta ta ja musu.

Kakarta wato Ajoke Brown na zaune akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yayinda hannunta ke ɗauke da wine glass tana kurɓan wine lokaci zuwa lokaci. Ko kaɗan bata damu da matar dake tsugunne gabanta ba ko kuma jikarta dake tsaye chan nesa da su.

Lola ta tauna leɓenta na ƙasa, ita bata damu da yin hutu a Lagos ba. Amma mahaifiyarta Bisola ta ɗauki burin duniya akan sai sun je hutu a UK. Gaba ɗaya ahalin na su na da passport na fita ƙasar waje a duk lokacin da suke so amma ita da Lola basu da shi. Wannan fadanci da banbaɗanci da take yi tun ɗazu wai dan ta sama musu passport ɗinne.

Bisola ta sha faɗawa 'yarta Lola cewa babu abinda mahaifinta ya bar mata sai kyau da sunansa amma duk wani dukiya daya tara baturiyar matarsa da ke chan America ta cinye, a cewarta aurensu bai rabu ba kafin mutuwar Oluwafemi Adetimeyin Brown wannan yasa kotu ta damƙa mata komai da Femi ya mallaka.

Ita kuwa Bisola dama ciki tayi ba wai aure suka yi ba. Ta gode ma da Femi ya karɓi cikin kuma har yayiwa 'yar tasa rajista da sunan gidansu, da an barta da biyu babu. Wannan ya sa a kullum take ƙasƙan da kanta dan ta samu wani abu a jikin mahaifiyar Femi, kuma a koyaushe take nausar da Lola akan cewa idan tana so ta tsira da wani abu a gidan dole ta farantawa kakarta Ajoke Brown rai.

"Lola fa 'yar Femi ce, kina tunanin Femi zai ji daɗin wariyar da ake yiwa 'yarsa?"

"Lola za ta samu passport a lokacin da ya dace. Ki kame bakin ki daga faɗin irin waɗannan kalamai"

Bisola tayi shiru sannan ta juya ta kalli kyakyawar 'yarta tace " Lola wan bi"

Lola ta taune leɓenta da ƙarfi kamar zata cire shi.

"Lola" Bisola ta sake kira.

Lola ta matso wajen da suke ta tsaya kusa da mahaifiyarta. Bisola ta sa hannu ta tanƙwarar da ita sai da gwiwowinta suka zube ƙasa. "Maami" Lola ta faɗa da ɗan ƙarfi saboda zafin da ta ji.

"Ki roƙi passport a wajen kakar ki"

Lola ta kalli Maami sannan ta kalli Mommywa (Mamanmu) kamar yadda kowa ke kiran kakartata.

Bata da niyyar roƙo, bata da burin fita ƙasar waje, sannan bata da ƙarfin yiwa Maami musu.

Yemisi Adetimeyin Brown ta sauko daga stairs ta ƙaraso inda suke.

Ta ɗauki wine da Mommywa ke sha ta kwankwaɗa sannan tace " what's happening here?"

"Lola darling why are you kneeling down?"

Lola ta yi shiru ta duƙar da kanta ƙasa

Yemisi ta dubi mahaifiyarta tace "Mommywa laifi Bisola ta miki ne?, miyasa zaki hukunta Lola da laifin mahaifiyarta. Gaskiya bai kamata kina treating jikar ki haka ba"

"Come here darling" ta faɗa tana ɗaga Lola daga inda take durƙushe.

Mommywa bata yi magana ba, hakama Bisola bata ce komai ba. Wannan yasa Yemisi ta ja Lola suka fice daga gidan da niyyar zasu je shopping.

A cikin mota Yemisi ta dinga surutu tana faɗa mata sabon boutique da za su je na wata ƙawarta ce da ta takura akan sai ta patronizing ɗinta.

Ta san Anty Yemisi a wajen siyayyar kaya za ta iya ɓata ko nawa ne, haka nan idan kuna ɗasawa da ita za ta iya kashe ma kuɗi ta siya ma duk abinda kake so.

Anty Yemisi kaɗai ke ɗaukarta tamkar cikakkiyar mutum mai 'yanci a gidan, amma duk sauran ba abun da suke gani a tattare da ita face ita ɗin 'yar mai aikinsu ce.

Tun bata wuce shekara huɗu ba ta fahimci tarihin asalinta da kuma dalilin da ya sa Mommywa ba zata taɓa amincewa da ita a matsayin jikarta ba, ba wai kawai dan ita ɗin an haifeta ba tareda aure bane, tunda cousin ɗinta Jide ma ɗan shege ne kamarta amma yana samun gata da kulawa na musamman a wajen Mommywa. To amma shi ɗin mahaifiyarsa likita ce kuma 'yar babban gida.

Ita kuwa Lola mahaifiyarta Bisola 'yar aiki ce, girki take a mansion ɗin Adetimeyin Brown na kusan shekara takwas kafin kuma alaƙa ɗaya ta shiga tsakaninta da Femi wanda har ciki ya shiga. Femi ya amshi cikin a matsayin na sa shiyasa lokacin da Bisola ta haihu yai wa yarinyar suna da sunan gidan su. A 'yan watannin da yayi kafin mutuwarsa ya ƙaunaci Lola sosai har ma dalilin haka yai tunanin auren Bisola duk da babu soyayya tsakaninsu amma kash mutuwa ta zo ta yanke wannan buri.

Gaskiyar Maami ne da take cewa babu abinda Femi ya bar wa Lola sai kyau da kuma suna amma duk tarin dukiyar gidansu rayuwar da suke ita da mahaifiyarta rayuwar walaƙanci ne da ƙasƙanci, babu wanda yake ɗaukansu a matsayin ahalin gidan.

A da bata san miyasa Maami ta ƙi barin gidan ba bayan mutuwar Femi, amma a hankali ta fahimci cewa kwaɗayi ne da dogon buri ya Maami tafiya.

Babban gidansu ya ƙunshi kakarta Ajoke Brown, Aunt ɗinta Yemisi, Aunt ɗinta Shola wacce ta kaso aurenta ta dawo gida da 'ya'yanta biyu, Aunt ɗinta Elizabeth wacce ita da mijinta ke zaune a gidan da 'yar su ɗaya, sai Jide idan yana ƙasar.

'Ya'yan Ajoke Brown biyar ne, na farkon shine Femi mahaifin Lola kenan, sai mai bi masa Shola sannan Bayo mahaifin Jide, wanda ya mutu tun kafin a haifi Jide sannan Yemisi da Elizabeth.

Mahaifinsu Dr David Adetimeyin Brown ya mutu kusan shekaru ashirin da suka wuce dan haka duk wani dukiyarsa ya dawo ƙarƙashin ikon matarsa Ajoke. Ita ta building empire ɗin Adetimeyin Brown wanda yau 'ya'yansa ke tinƙaho da shi. Ita ce mai faɗa aji a gidan kuma maganarta shine ƙarshe.

Shopping da Yemisi sai ka gundura dan bata gamawa da wuri. Sai da suka kusan awa biyu a boutique ɗin kafin suka fito. 

Lola tace Yemisi ta siya mata ice cream ladan rakiya. Ana gama loda musu kaya a mota suka wuce cold stone.


***


"Zahi... Zahi"

Cikin ƙuryar wani ɗaki ake ƙwala mata kira amma sam bata ji ba hankalinta yayi nisa akan wayarta da take latsawa da sauri sauri. Sai kikit kikit keypad ɗin wayar Tecno T402 da ke hannunta ke bayarwa.

Tunda ta fara facebook da wayartata kusan abinda yafi ɗauke mata hankali kenan idan ka cire jin waƙa da karatun litattafan Hausa na soyayya.

Cikin watanni uku kacal da ta buɗe shafi a facebook ta samu friend request sama da ɗari biyar kuma kowanne accepting kawai take yi ba tareda ta san mutum ko bata san shi ba musamman masu sunan indiyawa ko turawa.

Bata ankara ba ta ji saukar naushi a gadon bayanta "Wayyo Allah!" Ta miƙe da sauri tana sosa bayanta.

"Wanke-wanken ne tun ɗazu kika kasa ƙarasawa. Kin san cewa bayan wannan ma akwai markaɗen kamu da zaki kai"

"Ummani Allah wanke-wanken..."

"Miƙo min wayar"

"Umm..."

"Miƙo min na ce"

Zahira ta miƙa mata wayar idonta yayi raurau yana gab da hawaye. Wai miyasa Ummani bata san cewa ta girma bane. Tana SS3 fah, nawa ma ya rage ta shiga jami'a. Su wani wanke-wanke da kai markaɗe duk ya kamata ace ta dena shi to amma ya zata yi tunda a ɗakinsu ita ce mace babba, sai da Ummani ta haifi 'ya'ya maza uku kafin aka haifi autansu Munnirah wacce ko yayenta ba a yi ba.

Bayan Ummani ta karɓi wayan sai kuma ta samu sukunin ƙarisa wanke-wanken da gaggawa. Tsabar haushi ɗauraya ɗaya ta musu ta kifa a tsohuwar kwandonsu da ta gama cin duniya duk ta yayyage. Lokacin da ta ɗauki kwandon tana sauri za ta kai kitchen sai ga wani kofi da wasu kwanuka sun zubo ƙasa. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya taso mata ta ji kamar ta jefar da kwandon ƙasa sauran kwanukan ma su sha ƙasa kawai. Ta dinga tura baki tana tsaki har ta je ta ajiye kwandon.

Kamar ta kauda kai ta manta da kwanukan da suka faɗi take ji, ta riga ta zubar da duka ruwan wanke-wanken taya za ta fara ɗebo wani ruwan a rijiyansu mai shegen zurfi saboda 'yan tsirarun kwanuka. Ai kuwa bata ɗauraye kwanukan ba ta karkaɗesu ta je ta haɗa su da sauran wankakkun...

"Zahira Isa Maihula" ta ji an kira sunanta dai dai ta fito daga gidan da ta kai markaɗe.

Ta juyo a hankali tana Allah yasa ba 'yar ajinsu bace, ai kuwa caraf ta yi ido huɗu da Shamsiyya Bello.

"Dama ta anguwar nan kike?"

Babu wanda yasan gidansu a cikin 'yan ajinsu sai mutum biyu suma kuma dukkansu jirgi ɗaya ya ɗauko su dan kowa gwani ne wajen ɓoye asalinsa a cikin makaranta.

Irinsu Shamsiyya Bello ko kallon kirki basa samu a wajen Zahira balle har magana ta haɗa su.

"Akwai gidan Kakata a ƙasan layin nan"

Ta faɗa tana wucewa da sauri ba tareda ta jira amsar da Shamsiyyar zata bayar ba. Yadda take tafiya cikin sauri sai markaɗen ya dinga fetsuwa mata a zani dama ya cika bokitin tam.

Tana isa gida ta shiga tatar markaɗen, gobe Ummani zata karɓi girki idan ta ƙi yin tatan ma tayiwa kanta ne.

Bayan ta gama komai ta shirya cikin uniform ɗin islamiyya amma hankalinta duk ya karkata wajen Ummani dake ta jan carbi tun ɗazu da ta yi sallar la'asar ta ƙi ƙarewa. Wayarta take so a bata dan dama kullum a ajin nasu raba hankalinta biyu take ɗaya na kan karatun ɗayan kuma na kan wayarta wanda akasari ke maƙale cikin littafin Akhdari da ake musu.

"Ummani wayata"

Ko kallonta Ummani bata yi ba ta naɗe sallayar da ta yi sallah ta ɗaura shi a hannun kujeran three-sitter dake ɗakin

"Ummani dan Allah"

"Idan baki fice min daga ɗaki ba sai na gaura miki mari. Allah ya ƙi ki na je na samu baki yi tatan kamun nan ba"

Zahira ta fice daga ɗakin tana ƙunƙuni, har zata saka takalmi ta tuna ko jakar islamiyyarta ba ta ɗauka ba. Ta koma cikin ɗakin ta ɗauko ta fito da sauri dan kar Ummani ta dake ta.

Ita kam tana ji ana cewa Fulani na kunyar 'ya'yansu na fari amma Ummani kam bata da wannan kunyar, ko dai Fulanin Jama'are daban su ke ne?. Kamar ba 'yar fari ba haka Ummani ke sake jiki ta lakaɗa mata duka idan ta yi laifi, tun tana yarinya, har yanzu kuwa bata girmi duka ba, dan Ummani akwai saurin hannu.

Yawanci zaka ga 'ya'ya sun fi tsoron iyayensu maza akan mata to amma ita kam Zahira gara ka haɗa ta da Baba akan ka haɗata da Ummani. Ba za ta iya tuna ranan da Baba ya sa hannu ya daketa ko ya zageta ba amma Ummani, Hmmm.

Baba baya cika faɗa ma sai in an kai shi maƙura wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba.

Sana'ar ɗinki da wanke huluna Baban Zahira yake, a lokacin damina kuma yakan taɓa noma, da wannan yake riƙe matansa biyu da kuma 'ya'yansa goma shabiyu, idan ka haɗa da 'ya'yan ƙaninsa guda uku daya ke riƙewa sun kama goma shabiyar...

Da dare bayan Zahirah ta idar da sallan Isha ta je ta ɗebo tuwo ɗan kaɗan ta sa a gaba tana kallonsa yana kallonta. Da ta san miyan kuka aka yi da ba ta ɗebo ba. Ga busashshen kuɓewa ba za ayi ba sai wannan baƙin kukan.

Ko uban me ya hana Yaya Bilya dawowa tun jiya oho. Da yanzu tana da ƙullin tsirenta ko suya da zata haɗa da wannan gayan abincin ta rage asara.

Ƙaninta Salisu ya faɗo ɗakin nasu babu ko sallama yace " Zahi wai kije in ji Yaya Bilya"

"Dan uwarka ni kake cewa Zahi"

"Ba uwata ba sai dai naki"

Ta miƙe za ta bishi Ummani ta daka mata tsawa.

"Ke!"

"Ummani kina gani fa"

"Ungo naki Zahira"

Zahira ta haɗiye sauran maganar.

"Wani irin banzar tarbiyya ne wannan. Dan kin ga kwana biyu ban taɓa lafiyar jikin ki ba ko. Wallahi ki kiyaye ni a gidan nan. Ki kiyaye ni Zahira"

"Kiyi haƙuri ba zan sake ba"

Ko kaɗan Ummani bata karɓan rashin kunya. Shiyasa 'ya'yanta suka banbanta da 'ya'yan Innar su Salisu. Ummani ta riƙe su ne da iron hand dan ta san idan tayi sake irin rayuwar da sauran yaran gidan ke yi na rashin kunya haka nata ma za su yi. Zahira ce kaɗai ke bata ciwon kai amma itama ta san halin mahaifiyarta sarai.

Zahira ta koma ta zauna tana Allah yasa ta kama Salisu gobe a hanyar makaranta.

"Shi kuma wanda kika bari a waje fa"

Dama a matse take dan haka ta ɗauki hijabinta da ke kan kujera ta fice.

A zaure ta samu Baba yana ɗinka hula ya saƙala wani torchlight a kafaɗarsa ya haɗa da wuyansa ya riƙe.

"Baba, Yaya Bilya ne ya zo"

"To kada ki jima"

Mahaifin Yaya Bilya da Baban Zahira 'ya'yan Baffanu su ke, dan haka yadda iyayensu suke cousins ita da Bilyaminu ma cousins ne.

A ƙofar gidansu ta sameshi yana zaune akan tabarmar da Baba ke zama idan yana aiki a ƙofar gida.

Ba ta ji ƙanshin tsire ko suya ba dan haka ranta ya sake tunzura, kar dai yau lami haka ya zo bai riƙo komai ba.

Bayan ta zauna ta masa sannu da dawowa tana rarraba idanu cikin hasken farin wata ko zata ga leda akan tabarmar amma babu komai.

"Yaya ba tsaraba ne" ta faɗa da sigan raha

"Na isa Zahira tah""

Ji fa wai Zahira tah, shi irin sweet sweet names ɗin nan ma da saurayi ke faɗa wa budurwa bai sani ba. Allah Yaya Bilya ɓatawa masu degree suna yake. To dama Animal science har wani course ne.

"Ehm" ta ɗan yi gyaran murya

Daga aljihunsa ya zaro wata leda ya miƙa mata. Ta buɗe sai ta ga roll on ne sai kuma turaren body spray wanda ta tabbata duka biyu ba zasu wuce ɗari shida ba.

"Nagode" ta faɗa ƙasa-ƙasa. Matsalar a bayar da kai a gida da wuri kenan babu competition akan ka balle har ka dinga samun abubuwa dayawa.

Wai miyasa ma ta ce ta amince ne lokacin da Baba ya tambayeta. To da wani ido zata kalli Baba tace bata son Bilya bayan ɗawainiyar da yake da ita tun bata da wayo. Amma duk wannan kyau da Allah ya bata ace da malamin primary za ta ƙare.

"Zahira lafiyan ki?"

"Lafiya"

"Idan akwai matsala ki faɗa min" ya faɗa cike da nuna damuwa. Yaya Bilya is caring ba ƙarya, ko kaɗan baya wasa da lamarinta.

Maganar suya ke ranta amma dai duk kwaɗayinta ba zata iya fitowa fili ta faɗa masa ba.

"Maganar kuɗin jarrabawar WAEC ne dama"

"Ban manta ba ai, ina ce satin nan aka fara biya"

"Eh"

"Idan Allah ya kaimu ƙarshen wata zan san yadda za ayi, idan ba a biyamu da wuri ba akwai raguna da nake son sai da su a salllah sai na siyar da ɗaya daga cikinsu"

"Nagode Yaya"

Shiru ne ya ratsa su. Bilyaminu ba ma'abocin magana bane sosai shiyasa hiran na su dama yawanci baya wuce minti talatin duk da kuwa awa ɗaya Baba ya basu.

"Zahira dama nace ko zaki min list na abubuwan da kike buƙata a kayanki. Anty Asabe za ta fara haɗa miki kayan"

"Kutmelesi, Anty Asabe"

Bata san a fili ta faɗi hakan ba sai da taji yace " akwai matsala ne?"

Ta girgiza kai amma chan cikin ranta tana faɗin yaushe Anty Asabe ta waye da zata haɗa mata lefen aure. Anty Asabe matar wansa ne wai dan ta taɓa zama a Jos shine take ganin tafi kowa wayewa, ɗaukan kanta take kamar wata wacce tayi zaman Wuse, Asokoro ko Garki a Abuja. Ai ƙanwar Anty Asaben ta tona mata asiri kwanaki da ta zo take cewa a Barikin Ladi suke bama cikin garin Jos ba.

"Ba kya so ta haɗa miki kayan ne?"

"Ni Yaya gaskiya, gaskiya kayan nan a barshi fa tukunna"

Duk da babu haske sosai amma yadda ya waro ido waje sai da ta ga ƙyallin farin idanunsa.

Murya na rawa yace " kin kin fasa aure na kenan?"

"Ba haka bane Yaya. Abinda nake nufi shine da dai an dakata da maganar auren nan har sai na fara university, zuwa lokacin da zan shiga aji biyu kaima ka gama duk wani shirin ka. Tunda Baffa ya rasu kusan kaine jigon gidan ku, yanzu haka ba an saka ranan Rashida da Fatima ba wa zai musu kayan ɗaki, ba kai ba. Yaya ba wai bana son ka bane amma mu bi komai a hankali idan aka yi auren ma duk ƙarin nauyi ne a kanka. Ka yi min alƙawarin zaka bari nayi karatu, dan Allah ka bari na fara a gida kafin aurenmu"

Shiru yai na tsawon lokaci. Tana jin yadda ya ja wani dogon numfashi ya sauke ta san tunani yake a kan maganganunta. Tana son Yaya Bilya amma ba so har chan chan ba, kusan soyayyar 'yanuwantaka da kuma kyautatawarsa gareta yafi tasiri a zuciyarta fiye da soyayyar da take mishi a matsayin shi na namiji. Yana da kyau yana da rufin asiri da zuciyar nema, yana da yawan kyautatawa amma kuma baida irin wayewar da take so, bai da irin kuɗin da take buri. Sannan ta sani idan ta aureshi a wannan gaɓa da take cika shekara shabakwai ba ƙaramin tauye mata burinta zai yi ba. Tana buƙatar two years of freedom, ta fita daga gida ta je university ta yi mingling da manyan mutane koba komai za ta ƙaru da wasu abubuwan.

"Ki bani lokaci in yi tunani"

Yanayin yadda yai maganar ya tabbatar mata da cewa akwai ƙanshin nasara. Bilyaminu baya wasa da buƙatunta...



Like

Vote

Follow me on wattpad

@ Azi_zat

And plz plz subscribe to my youtube channel Azi's corner



©Azizat Hamza

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.