Free chapter · Read without an account

Chapter5-6

by Firdausi Rabi'u Abubakar · GIDAN BALARABE

*🪴GIDAN BALARABE🪴* 

      BY

  *🪴MAMAN NABEELA🪴*


 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION* 




🅿️5️⃣↔️6️⃣



 *RIJIYAR ZAKI* 



Yana jawo kular yaga ashi lafiyayin dambun nama ne acikinta wanda yake ta zuba kamshi,ɗaguwa yayi ya kali Ammy wadda itama shi take kalo yace"Ammy yunwa fa naki ji naga kinki sawa akawo min abinci ,zancinyi miki wannan dambun fa"yafada yana me karyar da wuya yana me shagwaɓe fuska kamar wani kara min yaro



Ammy dariya tayi tace son kaidai akwai ka da rigima,banda rigima kawai katahu kazu ka cinye mana abinci to bamuyi da kai ba.kwaɓe fuska yayi kamar zaiyi kuka yace"Ammy bafa sanan"murmushi Ammy tayi tace"ina suka je"cewa yayi "ita Laila ta tafi kasuwancinta Dubai,ita kuma Asiya taji gidan ƙawar ta"



Ammy tace "tu nayarda kasan nibana so kazo kacika cikin ka kaji gida ka kasa cin abincin matan ka baza suji daɗi ba,mace bata jin daɗi tayi girki namiji yaƙi ci.



Balarabe shafa kansa yayi yana me istigifari na ƙaryar da yayiwa mahaifiyar tashi dan yasan indai bahaka yayi ba zata kora shi gidansa ne tace ya tafi yaci na matansa,shikuma baya jin zai iya cin Abincin Asiya a yau yanda ta ɓata masa rai dolene ma ya hukunta ta,




maganar Ammy ce ta dawo dashi daga tunanin da yake,tana ciwa"Son me kake tunanine haka har an kawo maka abincin baka sani ba"shafa sumar kansa yayi wanda da alama dabi'ar sa ce haka yace"Ammy bakumai kawai ina tunanin wani taro da zamuyi ne a Abuja"danshi baya so yadinga fadawa mahaifiyarsa laifin matansa koda yaushi,saboda yasan yanda take matukar sonsa,



Huda ce autarsu ta shigo tana sallama haɗe da ciwa"Ammy barka da gida wallahi Ammy nagaji"tana me zama kusa da mahaifiyar tata tana rungumota tace"Ammy nayi missin dinki susai"Ammy tace"barka da dawo wa auta nima nayi kiwar ki"Balarabe ne yace"ke "daguwa tayi da sauri dan ita kwata-kwata bata kula da shiba shiyasa ma take ta zoba shagwaɓar ta,saurin cewa taye "lah Yaya dama kazo wallahi ban kula da kai ba"ta faɗa tana me sakin murmushi,shima murmushin yayi mata yace "kinshigo kina ta faman zoba shagwaɓa ina zaki ganni"tace"Yaya ina su ayiman"yace "suna school basu dawo ba"tashi Huda tayi ta nufi sama tana cewa"Ammy bana watsa ruwa na sauko,Yaya dan Allah karka tafi yanzo zandawo akwai labari" cewa yayi "tu kiyi sauri in ba haka ba natafi kanki fito"cewa tayi "tu"tace gaba da hawa benanta.



shikuwa kwanon abincin yaja yabuɗi wani lafiyayin tuwon alkama yaga ni da miyar ɗanyar kuɓewa wada tasha naman rago da tantakwashi ga ƙanshin manshano na tashi,tashi yayi ya wanke hanunsa yadawo ya zauna yana bissimila yasa hannu yafara kai loma yaji kamar kunensa zai cire ,shidai a rayuwar sa yana sun tuwon alkama lomshi lumsasun idanonsa yayi wadanda suke kamar na me jin barci yana ƙara kai wata lomar bakinsa. 



*******************



HOTORO




Ganin da Salman yayi ta tsaya a ƙofar gidansu ta ɗaure fuska yasa yayi murmushi a ransa yana aiyana Allah ya nuna masa ranar da Khadija zata soshi yanzu ma badan I'man tayi masa kwatancin gidan ba da sai dai yayi ta wahalar yawo a hanyar makarantar su,tu sai Allah ya taimake shi I'man tayi mai kwatance,tahuwa yayi daga inda ya ajiye motarsa yace "Assalamu alaiki"khadija tace "wa'alaikumussalam"tana me ƙara ɗaure fuska,




"dan Allah inso kibani dama na nuna miki irin son da nake miki bada wasa nazoba auren ki zanyi da gaske Khadija"numfashi ta fesar sannan tace "banaso kaci na yaudare ka saboda ni yanzu gaskiya ba aure zanyi ba karatu nake,shiyasa bana kula kuwa sabuda banaso na haɗa soyayya da karatu,ina me baka hakuri"Khadija tayi maganar tana me juyawa zata shiga gida,da cikin sauri yace "indai dan wannan ne banida matsala zan jiraki dan Allah ki taimaka kibani dama"juyo wa tayi tace "tu zanyi shawara"cike da farincikin amsarta yace"tu dan Allah ko zaki bani phone number ki kinga idan kinyi shawarar sai ki faɗan kota wayar ne" meƙa hannun ta tayi yabata wayar tasa masa dan ita taƙagu ta kuma gida,




cikin tarun farinciki ya ɗauko wayarsa ƙirar samson yabata,karɓa tayi tasa masa number mahaifiyarta tace"gashi"karɓa yayi yace"zankira yanzu sai kiga number ta"tace "tu sai anjima"ta juya ta shiga gida batare da ta tsaya jiran me zai ce ba.




shikuwa Slaman cike da farinciki ya nofi motarsa waɗansu yara ya kira yace su kwashi kayan boot ɗin motarsa su shiga dashi gidan su Khadija manyan leduji ne guda uku yaran suka ɗauka suka nufi gidan dasu,Khadija tana shiga ɗaki tashiga tacire hijabinta tana ɗakin taji goɗar I'man.




Khadija fitowa tayi da sauri dan ta ga me I'man kiyiwa guɗa haka! tana fitowa Ummy ma ta fito daga banɗaki tana faɗin "I'man kanki ɗaya kuwa kin ta ƙarƙare kina zuba guɗa kamar gidan da aka......"maganar tace ta makale ganin manyan leduje zuɓe a tsakar gida,yaran da suka kawo na ƙoƙarin juyawa Ummy tace " 'yan samari wayi yasa kukawo waɗanan kayan!"ɗaya daga cikin so ne yace"wanine da yazo gurin Malama Khadija yace "mu shigo da weeso"Ummy tace "to sannunku Allah yayi muku albarka"da amin suka amsa suka juya suka fita.




Khadija jen an ambace ta yasa tayi saurin ɗaguwa tana kallon yaron da yayi maganar harsuka fita , sannan ta kalli Ummy da itama i'ta take kallo tace"Ummy wallahi baruwana nima yanzu na gansu" 



Ummy cewa tayi "I'man maza leƙa kigani Allah yasa be tafi ba amayar masa da kayansa,banda abunsa daga fara zuwa sai ka jubgo wannan kaya kakawo,tu nidai na fi so duk wanda zaku so ku soshi dan Allah ba dan abin hanunshi ba,shima kuma ya so ku dan Allah ba dan wani abu ba"I'man ce ta dawo tace" Ummy ya tafi banga kowa ba"Ummy tace"to I'man ɗauki kayan ki duba inba abun lalacewa ki kaisu ɗakin yayanku ki ajiyi duk randa ya dawo amayar masa da kayan shi",zuwa tayi ta buɗe ledar farko kayan kwaliya ne leda ta biyu kayan zaƙe ne dangin alawa,biscuit,chigom,chocolat

leda ta uku kuma turaruka ne kala-kala,I'man tace"Ummy ba abinda zai lalace"Ummy tace tu ɗauki ki kai ɗakin yayanku ki ajiye,ga mukoli chan saman taga"ɗauka I'man tayi takai ɗakin, ta dawo ta share gurin da sukayi wankin dan Khadija da Saudat sun ƙarasa har sun shanya.


Da dadare suna zaune suna cin abinci wayar Ummy tafara kuka alamun kira ke shiguwa Saudat da take kusa da wayar ce ta ɗauko ta meƙawa Ummy,Ummy karɓa tayi tana danna gurin amsa kira ta kara akunne,


daga ɓangaren Kubra jin an ɗaga yasa tace"Barka da dare babbar yaya" 



cikin farin cikin jin ƙanwar tata tace"barkanki dai Kubra ya su mamena da Adnan" "lafiya lau "Kubra ta amsa tace gaba da cewa "Anty dama cewa nayi su Khadija zasu zo goben!" "eh zasu zo"Ummy ta faɗa,"tu Allah ya kawo su lafiya ga mame ta ce zaku gaisa"Anty Kubra ta faɗa tana miƙawa mame wayar.......


******************


 ```BALARABE```

Gama cin abincin sa yayi dai-dai da saukuwar Huda,

zama tayi kusa da Ammy tace "Yaya kasan me tun shikaran jiya nake so kazo na nuna maka irin motar da zaka siya min,tunda kace sai nayi graduation na makaranta zaka sake min,bari ma kaganta wallahi Yaya ko kai sai ta burge ka,sabuda me kyau ce duba kagani"tafaɗa tana miƙa masa wayar,karɓa balarabe yayi yana gani yace"kai gaskiya tayi kyau sosai dole nasiyawa Auta wannan mota ke dai ki dage ki fito da sakamako me kyau"cikin farin ciki tace" nagude Yayana Allah ya kare mana kai"da ameen ya amsa yana duba agogon hanunsa yaga lokacin magariba ya fara gabatuwa yace"Ammy in Abey yadawo kifaɗa masa gobe zanzu da takadunan ya duba nakira wayarshi ɗazu be ɗauka ba"Ammy tace "tu zan faɗa masa kasan yau suna taro da wakelan shugaban ƙasa akan harkar tsaro tayuyu yasa wayar a silent" sai sanan ya tuna shima wayarsa tana silent dauko ta yayi yana cewa "shaf na manta wallahi Allah dai ya kawo mana ƙarshin wannan rashin tsaron da ƙasarmu ke ciki" Ameen" Ammy da Huda suka faɗa.



duba wayar shi yayi yaga anyi mishi misscall kusan ashirin ga saƙoni kusan nawa suma duba so ya fara yi nan yaga kiran Asiya ne sai wasu nambobi da ake yawan damunsa da kira da so wanda daya ɗaga sai yaji kawai 'yan'matan dake nacin suna son shine,wanda shi basa gabanshi dumin shi dai ko aure zai kuma yi tufa ba zai kuma auren macen da ta taso gidan sangarta ba waɗanda ba'a kwaɓar so dan gasunan yana tare daso amma basa amfana mai kumai sai bacin rai.


"Ammy banaje sai goben","Allah ya kaimu kagaida su Asiyar" Ammy tafaɗa tana mikewa,"zasuji"balarabe yace yana nufar ƙofa,Huda ce tace "Yaya agaida su Ayiman da Ammy ƙarama" zasuji"ya faɗa yana ficewa yanufi harabar gidan inda yayi perkin ɗin motarsa.





@***



  *maman nabeela* ...✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol