Free chapter · Read without an account
Chapter 17-18
🪴 *GIDAN BALARABE* 🪴
BY
🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴
***
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
💃💃💃💃💃
*AUTAR MANYA*
_Ramadan bononza_
*AUREN BARE*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*
*RABON WANI*
*H A S K E*
*KOBA SO*
All in 1500 for more infor chat me up ***
*DEDICATED TO GIDAN BALARABE FAN'S*
INA *ƘAUNAR KO A DUK INDA KUKE* 🥰🥰🥰🥰
🅿️1️⃣7️⃣↔️1️⃣8️⃣
.............Abdussamad Balarabe Ya tashi da Wani hali na rashin Yawan Magana, Yana da fara'a Wadda ko da Magana aka yi Masa lokuta da dama Sai dai yayi Murmushi' Ba Shi da faɗa ko kaɗan Yana da matuƙar haƙuri Amma kuma baya ɗaukar raini, be yarda da a Wulaƙanta Shi ba, kuma Shima baya wulaƙanta Wani!
Yana gama Matakin sakandire Mahaifinshi ya tura shi ƙasar London inda ya ci gaba da karatunsa a chan, kafin ya bar Nigeria Sai da ya Sauke Al'ƙur'ani Me girama tare da Littatafan adini, yana da riƙon ibada dan baya bari Sallah ta Wuceshi kumai rintsi.
Ya kammala karatunsa cikin Nasara inda ya karanci Kasuwanci Shi ma ,Dawowarsa Nigeria Mahaifinsa ya ɗora shi Matsayin Manager na companyn da ya gina cikin Shikarun da suka Wuce,
Ɓangare guda kuma ƴan'mata su ka yo masa Cha kowace tana burin ya karɓi tayin Soyayyar ta, Wanda Shi basa gabansa duk da ya kai Matakin da ya kamata ya ajiye Iyali duba da larurasa ta yawan ciwon Mara Wanda in ya fara Sai anyi Masa Alura Sanan ya ke jin dama-dama dumin ƙwaya ma ta daina yi Masa aiki kuma Abokinsa Haidar da ya zama likita yana yawan gaya masa tana da ila ya kamata ya yi Aure,
Sai dai kawai ya yi Murmushi yacie Zaiyi in lokaci ya yi Cikin haka Allah ya yi Wa Baffa tsoho me ran ƙarfe rasuwa' Mutuwar da ta gir-giza Ahalin Su Balarabe Da Jama'ar gari kowa Faɗin irin halin Baffa yake nagari Wanda Abby da jin Mahaifinsa ya rasu nan ya yanke jiki ya faɗi inda Ana kaishi hospital Suka Shaida Musu jininsa ne ya hau nan aka yi masa tai makon gagawa aka Shawo kan Matsalar.
Balarabe da Shima ji yake kamar ya faɗi jin Batun rasuwar Kakan nasa Haka ya daure ya ringa Zirga -Zirga na ganin Abby ya samu lpy, yayin da idanonsa Kana kalonsu zaka gane tsantsar tashin hankalin daya ke ciki Sunyi Wani bala'in ja,
Abby na far faɗuwa a kayi discherge ɗinsu daga asibiti Mota suka shiga Wanda dama tun daga yin rasuwar duk ƙanen Balarabe Hassana da Husaina da sukayi Aure Suka zo jin Mahaifinsu na hospital yasa Suka ran kayo Asibitin gida Suka kuma in da Nan Suka ɗauki Babbar Mota Suka tafi airport,dama Hassana da Hussaina da Shirin tafiya Yola Suka zo nan jirginsu ya ɗaga Sai Yola.
Bayan anyi Sadakar uku nan kowa ya fara haramar kumawa gida inda nan Dada ke Shaida wa Mahaifin Balarabe cewa " kafin Baffa yarasu yana ta zancin yaushi Takwaransa zaiyi Aure,kaga Allah beyi zai ga Auren bama"cikin ƙasa da kai Abby yace"Dada Wallahi nima ina tayi masa zanchan Auren Sai yace Bashi da Buduruwa Shi baya kula kowa"
"In dai haka ne basai Ayi masa Auren Zumunci ba Kar nima na faɗi na Mutu ba tare da naga Auren Me gidana ba!"ta faɗa tana fece majina da gefin zani tana me Share ƙwalla,"Insha'Allahu Dada zaki gani har ƴa'ƴansa"
"toh'indai hakane nidai a ganina kawai a haɗashi Aure da Asiya ƴar Wajen Halime kaga Shikenan tuwona maina"
"toh'Dada zan yi masa magana inson dai-daita Shikenan"
"Wanne irin in sun dai-daita kasan halin Me gidan nawa Wallahi Sai yace bata yi masa ba,toh Mukuma haka zamuyi ta zama ina da tabbacin ba ƴan matan ne bashi da So ba iya Shige ne kawai kaga yanzu Abinda za'ayi kawai zaka ce kayi Masa Mata yayi Shirin Aure kaga ba zaiyi jayaya da kai ba, ko ya kace!"
"toh Dada za'ayi yadda kika ce" "toh Allah yayi maka albarka ya ƙara rufa Asiri" "Amin"ya amsa yana fita daga cikin ɗakin, Haɗuwa Sukayinda ɗan'uwansa Abdurrashid nan yake Shaida Masa abinda Dada tace Shima guyon bayan Maganar Dada yayi yana cewa"ka duba fa kaga Sa'ansa Hamza yaransa biyu Shi kuma ko Auren yaƙe yi ko dai bashi da lpy ne!" ya faɗa yana kallon ƙanin nasa "lafiyarsa ƙalau na dai rasa me yasa Sam be ɗauki Maganar Auren da Mahimanci ba"
"Kaga yanzu abinda Za'ayi kawai ranar Sadakar Bakwai ɗin Baffa a ɗaura Masa aure kaga ai ba yadda zaiyi"
"Amma Yaya baka ganin kar Asami Matsala Zumunci ya Samu tazgaro"
"Kai dai kayi musu fatan alkairi,nikuma yanzu Zan nemi Haliru muyi magana dashi"
"Yaya da ka bari ko bayan Ar'ba'in ɗin Baffa ne kaga yanzu ai yayi kusa da yawa"
"Baffa kafin ya Rasu ba Shida burin da ya Wuce yaga ranar Auren Baffa ƙarami kaga ya zama kamar Muncika Wasiyarsa ne!"
"toh Yaya Shikenan bana gayawa Mahaifiyarsa" nan suka rabo Abby ya koma cikin gidan Shi kuma yayi Waje.
Abby ya Samu Ammy inda Yake faɗa mata Abinda yake faruwa Ba yadda za tayi haka ta bishi da Adu'a da fatan Zaman lpy amma taso Ɗan nata ace Shi ya kawo Matarsa da kansa,amma ko ba komai tasan Ɗan nata Me biyaya ne a Wajen Iyayinsa ba zai basu kunya ba tana da tabbacin Zai amince.
"amma a gani na Baban Yara ai da am faɗa masa ina da tabbacin Zai amince"Ammy ta faɗa tana duban Mijin nata.
"eh' Zan faɗa Masa duk da Yaya Abdurrashid ya nuna kawai a kyaleshi amma a faɗa masan shi yafi kar yaji abu Sama taka"Abby ya faɗa.
"ina da yaƙinin bazai ƙi amincewa ba" Ammy ta kuma faɗa "toh Allah ya tabbatar Mana da alkairi Abby ya faɗa yana tashi yace"ba na leƙa Shagon ko yana ciki Sai muyi maganar!"
"toh"amsa cike da tausayin Ɗan nata.
Abby bayan ya samu Ɗan nasa nan yake Shida Masa ɗaurin Aurensa ranar Juma'a Wadda tayi dai-dai da ranar Sadakar Bakwai,tamkar Saukar arado haka yaji Maganar Mahaifin nashi Wanda bashi da yadda Zaiyi face ya amince dan baya fatan mahaifinsa ya nemi yayi Wani abu ace ya kasa mudi be kaucewa Shari'a ba,magamar Mahaifinsa ta dawo dashi daga tunanin daya faɗa ywna cewa"Son ba kayi magana ba in baka Sonta Sai a fasa"
"Abby duk abinda koka yanke akaina ni me biyaya ne a gareko Allah yasa haka Shine Mafi alkairi"cikin farin ciki Abby yace"amin amin Allah yayi maka albarka yasa kaima ƴaƴanka Suyi Maka biyaya kamar yadda kake mana" da Amin ya amsa.
Ranar Sadakar bakwai bayan Saukowa daga Massalacin Juma'a Shaido Suka Shaida ɗaurin Auren Abdussmad Abdallah Abdussamad tare da Asiya Halliru,Wanda duk wanda ya kali iyayin ƴaƴan zai tabbatar da Suna cikin farinciki Saɓanin Balarabe da idanonsa Sukayi Wani ja Sakamakon Wani azababin ciwon kai da yayi masa Mugun kamu.
Ɓan garen Amarya Asiya Ma tana cikin ƙawayinta da suka zo taya ta Murna Sai Washi baki take cike da farin cikin ta Samu cikar burinta,dumin ita ta jima da ɗan'uwanta a ranta.
Abby da iyalinsa sun koma Kano inda yace da ƙanwarsa kuma Mahaifiyar Amarya da ga baya in Sun gama Shirye-Shiryensu A kawo ta ɗakin Mijinta,Mahaifinta yaso kawai So tafi da ita Abby Shi ya nuna ya kamata A baso dama Suyi Shirye-Shiryensu na Mata.
Bayan Sati biyu aka kawo Asiya ɗakinta inda da farko nan gidan Mahaifanshi a ka kaita Wanda Ganin yanayin Zamansu yasa Ammy tace ya ɗau Matarsa Su kuma gidan su ko Sa Samu jituwa Susai,
Bayan Sun kuma Tudun Yola Ma Sun ɗau lokaci Kafin Balarabe Wani Abu ya haɗashi da Asiya,Shikara ɗaya kuwa Asiya ta Santalo kyakyawan ɗanta Me kama da Mahaifinsa inda nan Balarabe yasa ka Masa Sunan Abby Suke kiransa da Aiymar Shikara biyu bata cuka ba ta kuma haifu Me Sunan Ammy Wadda Suke cewa Meme cikin haka kuka Asiya ta fara baiyana Wasu irin halayi ƴaƴan ta tamkar ba ita ta haifisu ba basa Samun kulawarta Shima Mijin Sai Sanda taga dama take kulawa dashi Wanda ya fara haifar musu da Saɓani bana kaɗan ba,cikin haka kuma Laila ta Shigo cikin rayuwarsu Wanda ita ɗin Wata rana tazo gidan So Balarabe Mahaifiyarta ta aiko ta gurin Ammy tunda ta kyalla ido a kansa ta ce itafa Alam fur Sai Shi nan Suka Shiga Suka fita ita da Mahaifiyarta Wanda yasa Saida ta Shigo gidan.
TO fa Shiguwar Laila gidan Wadda ta kasance irin ƴaƴan Masu kuɗinan Waɗan da ba'a Sa su ba'a hana su, Mulki Wanda take zubawa a gidan yanda kasan itace Uwar'gida Mugunta idan yaran Asiya Suka je inda ta ke haka Za su fito da kuka Wanda Me gidan baya Sanin Me ya ke faruwa tunda ba zam yake gida ko yaushi ba ga company da ya buɗe da gidajen mai nasa na kansa Wannan yasa yau yana chan gube yana chan,inda ita kuma Asiya idan taji kukan yaranta nan zata fito Suyi ta bala'i gida ya Zama kamar filin dambe cikin haka Bussiness ɗin da Laila ke yi ya fara ƙarfi Wanda ta fara Safarar yara Suna kaicsu ƙasar Waje ita da Wata ƙawarta Merry Wanda ya ke kawo musu kuɗi Sosai inda ya zamana itama yanzu bata zama,inda tace wa mijinta order kaya takeyi daga Dubai inda ta shigo da Wannan kasuwancin Saboda kar mijin ya gane.
Asiya ta kuma haihuwa inda ta haifi Nimrah Wanda daga ita ta ce ita Wallahi ta gaji da haihuwa Wanda yasa Sai da Suka Sami Matsala ita da Balarabe Wanda Har iyaye Su ka Shiga ciki Sanan Suka Samu dai-daituws.
Bayan Nana, Wata tafiya da ta samu Balarabe ya bar ƙasa cikin Wanan lokacin tayi ammfani da Wannan damar ta je ita da ƙawarta hospital Aka juya mata mahaifa ba tare da Sanin mijin ba....
Waɗɗanan Su ne kaɗan daga cikin irin Matsalar da Balarabe ke fama da shi a gidansa Wanda ko Wane Bawa baya iya kaucewa ƙaddarasa.
ME _KUKE TUNANIN ZAI FARO GA KAHADIJA TA SHIGO RAYUWAR BALARABE_ _WANDA DA ALAMA ITA ƊIN HASKE CE A GARESHI,WANDA_ _MUKE KYAUTA ZATON ZATA KAWO SAUYI A GIDANSA_
_WADDA AKANTA ZAIYI AUREN SOYAYYA,YA_ _SIYAYYARSO ZATA KASANCE ?_
SHIN *ME ZAI FARO IDAN BALARABE YASAN ASIYA JUYA MAHAIFARTA TAYI ?*
SHIN *ME ZAI FARO IDAN ASIRIN LAILA YA TUNO?*
KO *BIYU NI DUMIN JIN AMSOSHIN NAN* 👆
*MU DAWO LABARI....*