Free chapter 路 Read without an account

5&6

by Binta Umar Abbale 路 Matsalar Mu A Yau

MATSALAR MU A YAU!*

 _(Labarin Surayya)_


*NA*

*BINTA UMAR ABBALE馃崚*

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION馃馃徎*

____________________________




 *MAR'ATUS-SALIHA*

_(Itace Cikakkiyar Mace)_


*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu馃懌 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*

1- Maganin Sanyin mara

2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa

4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba

5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa

6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa

7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)

8-Maganin Basir mai tsiro

9-Maganin Basir mai kulle ciki

10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)

*11- Maganin Karin Ni'ima

12- Maganin K'iba mai kyau

13- Maganin Cikar Nono (Breast)

14- Maganin Hips

15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!

16- Maganin Matsi mai kyau

17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)

19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba



*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*

*****

*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*

Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp


  *SADAUKARWA NE GA:*

 _(Surayya Dee馃グ)_



Free Pege

 *5&6*

Yaro ya samu a kofar gidan ya bashi abincin da kudi kimanin dubu biyar yace ya shiga ya kai. bayan yaga shigar yaron gidan sai ya juya ya bar gurin cikin yanayin tafiyarsa ta gwarazan maza irin wanda ba'a nuna su da yatsa.


Suna zaune jugum-jugum! abin duniya ya dame su gabad'ayansu Yunwa ce take sasakarsu dan dai kawai sun saba da ita ne shiyasa basu galabaita sosai ba amma a zahirin gaskiya ita Surayya daurewa kawai take dan har ta fara 'kananun hawaye kawai dai bata so iyayenta su lura shiyasa ta shiga daki ta kwanta kan ya mutsatstsiyar katifa tana share hawaye.


Jin sallamar yaro a gidan yasa tayi shuru tare dasa kunnenta. Yaro yace."Wai gashi in ji wani ." Innah ta kalleshi ta kalli kwanakun abincin dake hannunsa tace." Aminu Anya kuwa anan aka tura ka."?


Yaron yace."Eh Innah nan ya turo ni kin ga ma har da kudi yace na bawa Malam." Yafada yana mikawa malam kudin.


Malam Habu ya mike zaune yana kallon kudin dake hannun yaron yace."Aminu baka sheda mutumin da ya turo ka ba."



Yaron yayi shuru yana tunani Yace."Na sheda mutumin shine mai zama a kofar gidan Alhaji Sabo  yana karatu."


Malam Habu yayi murmushi da fadin."Dama ai tunda naji yace zai dawo nasan hidima zai yi mana babu komai Aminu jeka abinka."


Yaron ya kama hanya zai fita Innah ta kira shi da fadin."Zo ka kar'bi naira goma kasha alawa." Yace."Aa Innah ki barshi nagode." Sai ya ruga da gudu ya fita Murmushi tayi tace."Aminu kenan babu ruwansa da son kudi irin na yara wasu yaran kuwa koda iyayensu ne zasu aikesu sai sun biya su sannan za suje.


Malam Habu ya kalleta da fadin."Habiba kin ga hidimar da yaron nan yayi mana ko."?


A sanyaye tace."E na gani wallahi malam ni mamaki ma ya hana ni nayi magana Yaron nan Nura yana da kirki ya dauko halin mahaifinsa dama mahaifiyarsa ce mara san mutane.



Malam Habu yace."Allah kenan shine yake had'a mutum da mutum haka kawai yaron nan yake kaunata hakika da ina da wani abu mai muhimmanci da zan bashi to dana dauka na bashi domin alkairinsa a gare ni."


Innah Habiba tace." Gaskiya kam Nuraddin ya cancanci ko wace irin kyauta amma bamu da abin da zamu biya shi face muyi masa kyakykyawar addua kaga yanzu muna zaune cikin halin damuwa da tunanin abincin da zamu ci gashi ya kawo mana harda kudi."


Yace."Kudin kuma masu yawa dubu biyar ne." Innah ta rike baki tana mamakin al'amarin Tace."Allah ya saka masa da alkairi ya biya masa bukatunsa yanzu gobe idan Allah ya kaimu za muje kasuwa ni da Surayya sai mu siyo kayan abinci idan yaso sai aji dana cefane."


Yace."Eh kwarai wannan shawarar taki tayi kyau amma zan dauki dubu daya a ciki domin na siyawa yarinyar nan littafan makaranta."


Tace."Malam daka bari an siyi abinci daga baya sai a siyi littafan." Ya girgiza kansa da fadin."Habiba kina wasa da karatun yarinyar kina kallo yau ma saboda rashin littafan ya hanata zuwa makaranta bamu da wani abu da  za muyi mata a duniya face mu bata Ilimi a rayuwata inaso Surayya tayi karatu mai zurfi sai dai kuma bani da arzikin da zan tallafe ta." Murya na rawa ya kare maganar



Innah Habiba jikinta yayi sanyi tace."To shikkenan Malam na amince da hukuncin daka yanke Allah ya taimaka ya bata ilimi mai amfani.'' Ya amsa da ameeen ya Allah.



To duk wannan zantukan da sukeyi tana jinsu ita gabad'aya ma ba karatu ne a gabanta ba tunaninta ya tafi kan maganar da taji suna yi akan Masoyinta wai suna cewa basu da abinda zasu bashi ita kam wallahi da zasu dauketa su bashi da tayi tsalle tayi dara a duniya bata da wanda take so kamarsa ita kanta bata san irin kauna da son da take masa ba.



Hawaye ta share tana wani tunani tana ganin kawai zata samu babanta da maganar watakila ya amince da tunaninta duk da tasan Shi d'in ba tsaran auranta bane amma tana ganin idan babanta ya bashi ita ba zai qi kar'ba saboda yanda yake ganin girmansa. 



Tana tsaka da wannan tunanin taji Innah na kwala mata kira. A sanyaye ta amsa ta mike jiki a mace ta fito tsakar gidan.


 A sabule ta zauna kusa dashi tana ya mutse fuskarta ya kalleta cike da tausayawa yace."Kin ga Allah ya dube mu ko." Tace." Nagani Baba Allah ya saka masa da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen ya Allah kin ga yanzu a cikin kudin zan baki dubu daya sai ki sayi littafan.'' Zumbura baki tayi tace." Baba ai kudin littafan dubu daya da dari bakwai ne." Shuru yayi yana nazari yace."To ki fara siyan masu muhimmanci a ciki insha Allahu cikin satin da zamu shiga zan baki dari bakwai din sai ki sayi sauran.'' Shuru tayi domin ba taso hakan ba.


Ya kalli Innah da fadin "Ki zuba mana abincin muci gobe idan Allah ya kaimu idan kun tashi tafiya kasuwar sai ku shiga gidan Alhajin Sabo ku gaishe dasu.


Innah Habiba ta kalleshi da fadin." Aa Malam kasan fa ni bana san wulakanci mai zai kaimu wannan gidan da ba'a son talaka."


'Bata rai yayi yace."Habiba Umarni na baki bana so kuma kiyi min gardama duk wanda ya wulakanta wani kansa ya wulakanta kuma ba dan kowa za ku shiga gidan ba sai domin wannan yaro."


Tace."To shikkenan Malam Allah ya kaimu goben lafiya." ya amsa da "ameeen ya Allah. kwanukan abincin ta fara budewa a take kamshi ya cika musu hanci Shinkafa ce fara tas da ita da miyar kifi manya-manya sai 'kamshi miyar take da alama suna amfani da tafarnuwa da sauran kayan gyaran kirki.


Jin kamshin tafarnuwa yasa zuciyarta tashi abin da ta tsana kenan a rayuwarta. Hanci ta toshe tana kakarin amai."


Innah tace."To sarkin iyayi da sanabe nasan dai kamshin tafarnuwa ne yasa ki toshe hanci.


Kamar za tayi kuka tace."Allah Innah amai nake ji ki rufe miyar nan."


Innah Habiba tace."Idan kakan amai za kiyi sai dai kiyi amma ba zan rufe abinci nan ba.....Da sauri ta mike daga gurin ta nufi bakin rariya ta tsuguna.


Malam Habu ya bita da kallo yana girgiza kanshi Innah tace."Malam dan Allah ka rabu da yarinyar nan kaci abincin ka tsirfa ce kawai gashi kiri-kiri ta hana ni girki da tafarnuwa a gidan nan."


Yace."Habiba ki rabu da abinda mutum ba yaso ba tsirfa bace ba taso ne saboda haka maza zuba mana abincin ki dauke kwanukan daga wurin."



Tana tsugune a bakin rariya tana tofar da yawu har suka gama cin abincin Ya kalleta da fadin."Taso kizo ki fada min abinda kike so kici ma fita na siyo miki.


 Ta yunkura ta mike tsaye ta nufi inda yake hannunta ya rike da fadin." Me zaki ci tunda da akwai kudi sai a siyo miki." Tayi jim tana tunani tace."A wara nake sha'awa." Innah Habiba tace"Surayya bana san shashanci a gidan uban wa zaki samu awara yanzu ga abinci mai rai da lafiya amma saboda tsirfa kina gudu."


Tana marairaicewa tace."Can karshen layi Ummiyo tana soyawa dan Allah ki bari naje na siyo." Tace." Ba zaki je wannan gurin ba awarar Ummiyo maza ne suke cika a gurin.


Kuka ta fashe dashi da fadin."To ni Innah ina ruwana da maza kawai ina zuwa zance ta bani idan kuma da layi sai na shiga gidansu gurin kawata Samira kafin azo kaina."


Innah Habiba tace."Ban yarda ba sai dai ki nemi yaro a waje ya siyo miki."


Malam yace."Eh hakan shi yafi Surayya kar'bi kudin ki nemi yaro a waje ki bashi ya siyo miki ta yanda kike so."


Hawayen ta goge ta kar'bi kudin daki ta shiga tasa hijabi ta fito. Innah tace."Kada fa kije gurin nan." Kai kawai ta daga tasa takalmanta ta kama hanya ta fita daga gidan.




 _*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_

*****

*****

*BINTA UMAR ABBALE*


*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE  KU NEMI WANNAN NUMBER......._*

*22790899076*

*HAJIA FATIMA MUSA  (MOMMY NIJAR)*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol