Free chapter · Read without an account

14 and 15 last free page

by Rahma Kabir · ƘADDARARREN AL'AMARI

[7/2, 10:19 PM] Rahma Kabir: *ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


14


Abuja


Su Safna sun isa Abuja lafiya suka isa gidan Haj. Hauwa driver yayi parking a harabar gidan suka fito gaba daya, Haj. Hauwa tayi gaba Safna tana biye da ita a baya har suka shiga babban falo, hajiya ta kai ta wani daki mai dauke da gado mirror da Waldrop komai tsaf, sai ta kalli Safna da take ta kama jiki saboda ba kunta ta ce.


Mu shiga bayi na nuna miki yadda zaki yi amfani da shi sai kiyi wanka.


To tace tabi bayanta suka shiga, hajiya ta kwatanta mata yadda zata hada ruwan wanka kana ta fito, safna ta shiga kallon kyawun toilet din. Hajiya ta haura sama ta shiga dakin Seema ta samowa Safna wasu kaya riga da siket yan kanti ta sauko ta kai mata kayan ta ajiye kan gado, ta bude murya yadda Safna zata ji ta.


In kin fito ga kaya nan ki sanya ina zuwa


Sai fice ta nufi dakinta itama wankan tayi cikin sauri ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga ash color saita yane kanta da gyalen rigar, bata tsaya yi kwalliya ba turare kawai ta shafa saboda tana sauri. Ta zo ta samu Safna ta shirya itama siket din ya dameta dan pelcil ne kuma na roba ga shegen tsagu har kaurinta yana bitowa, a ido kamar ba zai shigeta ba amma da yake na roba ne ya zauna daram a jikinta, rigar kuma mai guntun hannu ne tayi sa'ar bai kamata sosai ba, hajiya Hauwa ta kare mata kallo ta saki murmushi domin tayi mata kyau, kayan kamar dan ita aka yi su don duk surar jikinta sun bayyana, danma babu wani kulawa sosai data samu ta san zuwa nan gaba kadan in ta wanke mata dattin talauci ta sha ac sosai komai nata zai dawo na ajebota. Ta zo ta kama hannunta ta isa da ita jikin mirror ta warware mata gashinta da yake tufke ta dauki kum ta taje shi sosai, ganin ma gashin tsaf yake ba datti sai ta daure mata da rebom ta kitse mata jelar gashin, Safna ta fito ras kamar wata yar tsana.


Ya kika ganki kinyi kyau ko? Duk da ba ki yi makeup ba


Murmushi kawai Safna ta saki bata ce komai ba, hajiyar ma bata kuma magana ba taja hannunta suka fice har zuwa jikin motarta ta bude gefen driver ta sanya Safna a ciki ita kuma ta zauna mazaunin driver ta sa key, Safna ta kalleta cike mamaki ganin zata fita da ita haka kai ba dan kwali.


Ummm hajiya bari na dauko dan kwalina


Hajiyar ta waigo ta kalleta cike da kulawa


Haka zamu tafi tunda cikin mota muke, sannan ba kida wasu dan kwali ko hula da zaki using dan ba zaki sake sanya wancen kodaddun kayan ba, yanzu kasuwa zamu zan miki siyayyar kaya. Bana son musu da kardama duk abinda nace shi za kiyi 


Safna ta gyada mata kai alamar to saita kwantar da bayanta jikin seat tana nazarin irin sabon rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, addu'ar tsari kawai take jerowa a cikin ranta, har suka isa babban wani super market na boutique suka yi parking suka fito Safna sai kama jikinta take kamar tana jin sanyi gani take kamar ita kadai ake kallo, hajiya da ta ga haka sai ta kama mata hannu suka shiga ciki, Hajiya ta shiga kwasar mata kaya, English wears, dogayen riguna ready made, gyale, takalma, kayan kwalliya, turaruka, dan kunnaye passion da abin hannu, ta kashe mata kudi kimanin dubu dari da hamsin, Safna tsoro ya gama cikata sai hakan ya tuna mata da Haj. Uwale yadda ta dinga kashe mata kudi ashe da walakin goro a miya, ta shiga tunanin kar dai itama wannan hajiyar hanyar banza zata daura ta, ita da tazo aiki me yasa zata siya mata kaya irin wannan. Haka suka dawo gida da kaya niki niki, hajiyar tasa mai aikinta ta gyarawa Safna kayan ta jerasu a Waldrop ta kuma bata umarnin ta jera musu abinci a dinning, ta amsa da to ta fice.


******   ******

Washe gari


Safna ta kwana bisa lallausan gado, tayi barcin da bata taba yin irinsa ba, duk da tayi aiki a gidan masu kudi da dama amma bata taba samun wurin kwana mai kyau da aka karrama ta irin haka ba, har saida ta makara wajen tashi sallar asubahi sai misalin karfe bakwai na safe ta farka. Bayan ta idar da sallah sai ta shiga ta hadawa kanta ruwan wanka kamar yadda hajiya Hauwa ta karanta mata jiya, ta fito ta samu wata doguwar riga maroon ta sanya sai ta daura dan kwalin, ta shafa mai ta koma ta kwanta, sai ga mai aikin gidan ta shigo tare da gaya mata hajiya tana jiranta a dinning. Haka ta fito ta samu hajiyar ta tsuguna ta gaisheta ta amsa fuska sake kana tayi mata umarnin ta zauna su karya da sauri dan fita za suyi.


Bayan sun gama karyawa suka koma falo zuka zauna bisa Cushing, hajiyar ta shiga tambayar Safna.


Shekarunki nawa yanzu? A ina kika tsaya a matsakin karatu?


Inada shekara sha takwas, a JS 3 na tsaya zani SS 1, islamiya kuma nayi sauka.


Good, yanzu kinga shekarunki ya wuce matakin secondary zan sanya ki a lesson school na biya miki jamb da waec dan an soma biya, in yaso da kin samu result mai kyau sai na saki a jami'a. Sannan zan saki a makaranta koyan kwalliya da dressing, duk a yanzu za kiyi su, da safe zaki lesson da yamma makarantar kwalliya duka driver zai rika kaiki.


Nagode hajiya Allah ya saka da Alkhairi ya kara miki budi


Safna tace cike da rawar murya har kwalla ya cika mata ido za tayi kuka.


Karki damu fa taimakon ki zanyi sannan duk yadda da kula da ke nima zai amfane ni sosai, dan haka ki saki jikinki kiyi komai kamar gidanku, yanzu in mun fita zan biya na siya miki waya da layi wanda zaki rika gaisawa da yan uwanki, daga nan mu wuce nayi miki register, ni dai dan Allah ki mai da hankali 


Insha Allahu nagode sosai 


Safna ta fada cike da murna, hajiya ta mike rike da jaka da waya safna tayi sauri zuwa ta amsa sai ta hanata.


Ba wannan aikin na dauke ki ba, ke dai ki zama mai min biyayya zaki samu yadda kike so a guna.


Safna ta gyada kai alamar to kana suka fice. Kamar yadda Haj. Hauwa tayi lissafi haka duk ya faru ta kammala mata duk rigistan komai kana ta barta a makarantar koyan kwalliya ta dawo gida. Zuwa yamma driver ya dauko safna cike da murna ta dawo. A daren ranar tayi waya da Baffansu da kannenta. Safna ta su kanta cikin matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ta ji kamar an sauyata ne zuwa sabon mutum, nan da nan rayuwar ta yana niman sauyawa a cikin second, lallai yanzu ta tabbatar da Allah ya gama amsar addu'an ta data jima tana yi.


Bangaren hajiya Hauwa kuwa ta gama tsara yadda komai zai zo mata cikin sauki, dama ta dade tana niman yarinya kamar Safna, mai kuruciya, kyau, diri wacce talauci yayi musu kanta sai yanzu Allah yayi mata gamdakatar, tunda ta hadu da Safna tana ganin burinta na duniya ya kusa cika. Tayi alkawarin zata kiwata ta da kyau ta inganta rayuwarta domin cimma wani burinta da ta barwa zuciyarta, shiyasa kwata kwata bata ga asarar kudin data kashe akan Safna ba saboda tana hangen nan gaba kadan zata fanshe kudinta harda tsabar riba cikin kwanciyar hankali.


******     *******

Kaduna 


Bangaren su Najwa kuwa sai misalin karfe goman safe suka farka, suka duba Safna a daki har zuwa toilet suka rasa ta, sai suka fito a hauka zuwa gun mai gadi suka tambaye shi ya tabbatar musu da fitar ta, wani irin ihu Najwa ta saki ta isa mota ta shiga, Billy ma ta shiga suka fita gidan a haukace kamar zasu tashi sama, gidansu Safna suka nufa sai suka samu a rufe da kwado, hakan ya tabbatar musu da ba gidan ta je ba sai ta wuce gidan Haj. Uwale nan ma ba safna ba labarinta. Suka bawa uwale labarin abinda ya faru, ta girgiza sosai domin bata yi zaton Safna zata basu wahala haka ba, ta shiga basu hakuri tare da yi musu alkawarin zata sanya yaranta su bincika safnar a badarawa tunda akwai gidan kawunta a nan kila can ta nufa, haka suka rabu Najwa jiki a mace, ko da suka dawo gida sai da taci kuka mai isarta sosai saboda ta kwallafa ranta akan Safna, dan har tana hango irin kyakkyawar rayuwar da zasu shinfida tare, a rayuwar tana mugun bakin ciki sosai akan rasa muradinta, sai hakan ya sata shiga wani hali saboda a duniyarta ita bata san babu ba. Haka tayi ta jinyar zuciyarta har washe gari, su Billy nasu ido dan ko lallashi taki basu fuskar da zasu yi mata, inda sabo sun saba da halinta shiyasa suka zuba mata ido har ta huce dan kanta.


******  ******  ******


Bayan mako guda.


Abbansu Akram ya gama yanke lokacin biki nan da wata guda mai zuwa za a daura, gaba daya dangi da mutanan arzikinsu sun san da wannan gagari min biki na yayan Senata Tahir. Gaba daya iyayen da yaran sun shiga shirin biki ba kama hannun yaro. Bangaren Abida kuwa murnan ta ba zai misaltu ba, iyayi kala kala da rawar kai, haka ta shirya ta dawo Abuja dan hada wasu kayanta na amfani wanda zata gidan mijinta da shi. Bangaren Akram dai shirinsa sai dai ayi masa, dan Amir ya barwa komai, ya mai da hankali sosai wajen business dinsa sam baya farin ciki da wannan auren, amma babu yadda ya iya dole ya yiwa iyayensa biyayya. 


Bangaren Amarya Humaira da Ango Auwal suma suna ta nasu shirin ko ta wani bangare. Musamman Abba yasa aka soma gyaran gidan har zuwa side din da Akram zai zauna duk a cikin gidan, dama ya jima da ware masa bangarensa dan baya so yayi nesa dasu. Bangaren Teema, Meena, Anty Meemi suma shiri suke da tsara irin rawar da zasu taka a wannan biki domin shine biki na farko da za'a fara yi a gidan shiyasa suke son yin shiri na ke ce raini.


******  ******


Biki saura sati biyu


An gama bugo kati, mutanen Abuja sun hallaro zuwa Kaduna dan yin shagalin biki, ba zasu koma ba sai an gama. Anyi free wedding pic da sauran souvenirs da za a raba a bikin, kafafen radio, tv, social media babu inda zancen aure bai kai ba ko ina hirar bikin ake, ga hadaddun hotunansu dake yawo a duniya, wannan abu ba karamin bakanta ran Akram yayi ba, yasan duk wannan aikin Amir ne amma shi sam ba shida tsarin yin free wedding pics. Amir ya samu hotunansa masu shegen kyau ya sanya Abida taje ta dauki wasu masu kyau ya kai aka hada hotunan, babu wanda zaice ba a tare suka dauka ba.


*****


Najwa tana zaune a falo Billy ta shigo da gudu ta isa gabanta kamar zata fada jikinta har saivda ta tsorata ta tashi zumbur.


Dalla meye haka zaki fado min a jiki, mutsss aikin banza


Sai ta zauna fuska daure, ta daura kafa daya kan daya tana karkadawa.


Bebeee good news na samo miki fa shiyasa kika ganni a rikice.


Na me fa? 


Tayi maganar a cikin ya tsine fuska. Billy ta mika mata wayarta da hotun su Akram ke kai, Najwa ta amsa.


Mutumin ki ne zai angonce da wata kyakkwawa beb


Najwa ta gyara zama tana karewa hoton kallo tare da lip din Abida daya mugun burgeta. Sai ta shafa hoton dai dai lips din ta saki murmushi.


Dan iska wato ya bata min shiriya shi zai angonce? Karya kake Akram wallahi wannan karan sai nayi fito na fito da kai, sai na nuna masa Najwa nake, sai na k'unsa maka bakin cikin daka kunsa min. Billy ki bincika min wace ce? a ina take?


Karki daga hankalinki dan ba sai mun hawala ba, an ce cousins dinsa ce, dan bikin gaba daya a gidansu za ayi, kuma a nan gidan zasu zauna sai dai part dinsu daban.


Kyakkyawan labari, wallahi sai na sha zumar ta, sai na maidata wajen hutawa ta, kisa min ido a duk movement dinta ina son haduwa da ita a cikin satin nan.


An gama bebee ki kwantar da hankalinki tamkar kin sameta kin gama. Dole ne mu mara miki baya domin yanzu ne dai dai lokacin daukar fansa.


Najwa tayi wani murmushin kasaita ta jingina bayanta a Cushing, ta cigaba da karkada kafa cike da kwanciyar hankali.


Rahma ce


#comment

#vote

#follow

#share

[7/2, 10:21 PM] Rahma Kabir: *ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


15


*Biki saura kwana uku.*


Biki wan shagali, gidan Alh. Tahir Ali ana ta shagalin biki babu kama hannun yaro, dangi na birni dana kauye harma da abokan arziki sun hallara zuwa wannan babban taron auren 'ya'yan tsohon gomnar jahar kaduna kuma senator mai ci a yanzu. Bangaren abinci kuwa na musamman aka sanya wasu restaurant har guda uku suke kawowa tun safe har dare babu wani girki da ake yi sai dai mutane su ci su sha sannan su goge wuya da nama. 


Amare kam shiga suke ta yi na alfarma wanda tun lokacin suke sanya sabbin kaya masu tsada, haka ma su teeyma ba a barsu a baya ba. Yau ne zasu je saloon kamar yadda suka sanya a katin programs of events, saboda gobe in Allah ya kaimu akwai mothers day da iyayensu suka shirya a babban holl din Arewa house dake kan titin Minister, wannan taron zai hada manyen matan yan siyasa tare da matan alhazawan Nigeria, shiyasa suke ta kokarin shirya komai a yau dan gobe ya zamana shirin mothers day din ne zai rage musu. Jibi kuma akwai Babban walima da aka shirya musu na Maza da mata a holl din multipurpose wanda suka gayyaci Babban Malam Aminu daurawa dan ya gabatar da lecture akan aure. Sai jibi Ranar Juma'a daurin Aure wanda za a daura a babban masallacin Sultan Ballo dake unguwar sarki bayan an idar da Sallah, zuwa dare kuma Dinner da aka shirya a Hamdala hotel.


Angwaye ma suna ta nasu shirin, wanda Amir da Umar sune kan gaba akan komai, Auwal ma yana ta nashi shirin iya karfinsa wanda tuni ya tanadi gidansa dake yan majalisu unguwan dosa inda za'a sauke Amaryansa Humaira, tun kwana uku da suka wuce aka je aka yi mata jere da italian bed da kujeru, fadin tsadan kayan bata lokaci ne haka ma ta bangaren kayan kitchen. Bangaren Akram kuwa na shi dai ido ne, dan babu abinda yake yi, sai ma kara kokarin kebe kansa da mutane yake, hakanan yake yawan jin faduwar gaba, kwata kwata baya son auren yana fargaban faruwan hakan, ji yake kamar ya gudu ya bar kasar amma hakan ba mai yuwuwa bane soboda kar ya bawa iyayensa kunya sannan kar zumuncinsu ya samu matsala. 


****


Billy sai da ta san yadda tayi ta samu programs of events din bikin, ta duba inda su Abida za suyi saloon, saboda sun boye wasu abubuwa ko a tv daurin auren kawai ake sanarwa, haka ta dawo gida ta sanarwa Najwa. Farin ciki sosai tayi ta tashi cikin sauri ta shirya suka nufi Waseela special saloon, wurin saloon ne na musamman wanda ba dai dan talaka ba sai masu kudi da suka tada kai da naira, wurin yana a can cikin Gari, babban plaza ne da yake dauke da shaguna daban daban a ciki.


Najwa sun isa wurin da misalin karfe sha daya na safe, suka samu ba kowa sai mai wurin da ma'aikatanta, wuri suka samu suka zauna suka gaisa kana Najwa tace a yangace.


Nazo a gyara min kai ne?


Haj. Waseela ta ce.


Ayya aiko yau wurin nawa da akwai Amaren da suka kama duka. Sai dai ko zaki bari gobe ki dawo.


Nawa suka biya ki na rib'anya miki kudin ki wanke min? domin naji labarin kin iya aiki dalilin zuwana kenan.


Kudi mai yawa suka biya kuma Amaren da kawayensu za muyi wa aikin


Gyaran kaina ba zai hana nasu ba dan haka ki wanke min ga budu dari biyu nasan ya isa ki wanke min.


Haj. Waseela ta sauke ajiyar zuciya dan harga Allah tana son kudin dan haka sai ta amince, sai dai Najwa akwai kitso a kanta, nan ta sanya wata yarinyar aikinta ta fara kwance mata kitson. Ita dai Billy tana jinsu sai karkada kafa take yi hankali kwance duk ta kosa su Teema su karaso.


Bayan kamar awa daya wajejen karfe sha biyun rana, an gama kwance kan Najwa ana kokarin wankewa sai ga motar su Teema ta shigo cikin plazan tayi parking a harabar wurin suna takowa dai dai kamar wasu yayan sarakuna. Meena, Teema Abida da kawayenta guda biyar wanda suka zo daga Abuja. Sune suka fara zuwa kafin karfe biyu Humaira ta tawo tare da tana kawayen. Suna shiga gurin Ma'aikatan suna musu sannu da zuwa itama haj. Waseela ta amshe su fuska sake, sai duk suka samu samu wuri suka zauna babu wanda ya tanka wani tsakaninsu da su Najwa. Haj. Waseela ta fara wankewa Najwa kai, dan sama wash and set zata ji, yaran haj. Waseela suka fara sanyawa su Teema, Meena da sauran yan mata biyu mai a kai kafin ta gama wa Najwa ta kama kan amarya Abida. Sai hira suke wanda gaba daya hirar nasu na bikin ne, Najwa tana ta tunanin yanda zata yi magana da Abida sai saka take a zuciyarta tana warwarewa har dai aka gama mata wanke kai aka sanya mata rollers ta shiga tukunyar saloon, Billy dai sai danne danne take a waya zuciyarta tana tsuma ta kosa taji hanyar da Najwa zata bi dan tayi magana da Abida. Haj. Waseela tace Abida tazo ta sanya mata mai sai Abinda tace.


Gama da kawaye na tukuna nawa ya zama karshe saboda ana gama min mu wuce.


To mai saloon din tace, sai d'aya daga kawayenta ta isa kujera ta zauna ta soma sanya mata mai, Najwa tana jin haka saita dan bude murya tace.


Yan mata hala dai kece Amaryan? dan naga zanen lallan jikinki yafi na sauren kyau.


Abida ta dago kai suka hada ido da Najwa tana murmushi cike da zumudi da son a san ita ce Amaryan ta ce.


Eh ni ce,


Ohhh Abida ki bari mana mu fada sarkin rawar kai 


Cewar Meena tana zolayenta.


Hey respect, kin san dai ni matar yayanku ce, ki san me zaki rika fada min, dan na zama antyn ku 


Sai duk suka kwashe da dariya 


Su matar Yaya Manya za muga iko a gunki, amma fa ki sani in zaki mana wulakanci ba za ki dinga kanin kafarmu a gidan ki ba


Cewar Teema tana murmushi.


Haba ai kun san kune abokan hirana dole ku rika zuwa, in kuma baku zo ba ni nazo side din ku tunda gidan ba bako na bane 


Ohhh wannan amarya ba kunya, bakin wasu yana mutuwa amma ke naki kamar ana kara masa taki, sai zuba kike kamar kanya 


Cewar daya daga cikin kwayenta. 


Kuma kwa fada, amma mu rabu da ita yaya Akram sai ya gyara mata zama 


Cewar Meena sai duk suka sanya dariya, Suma su Najwa suka murmusa da yake tana niman hanya sai ta tace. 


Wacece tayi miki lallen? nima ina so a min zanen, dan mun kusa bikin wata sister dina.


Zeeza henna design aka mana, plazan dake kusa da murtala square. 


Wow ashe sun iya, aiko zan leka gurin na gode. Amma da kin gayya ce ni bikin da nazo miki dan na kula kina da kirki, ina son mutum very friendly haka


Ayya ai bakomai ina gayyarki Dinner dinmu, ga get pass din a hamdala hotel za ayi.


Wow aiko zan zo, ga Friend dina itama a bata ta min rakiya


Abida ta ce ok sai taso ta zo kusa da Najwan ta mika mata get pass din guda biyu, Najwa sai tayi amfani da wannan damar ta mika mata wayarta.


Pls bani digit dinki 


Abida ta ce to sai ta amsa tayi dialing number ta sai ta kira ya shiga wayarta sai ta mikawa Najwa wayan zata juwa sai Najwan tayi saurin cewa.


Me zanyi saving 


Abida ko kisa Mrs Akram


Ok, ni kuma ki sanya Baby N


Meaning 


Zan gaya miki amma ba yanzu ba


Najwa tace tana kanne mata ido daya, murmushi kawai Abida tayi ranta fes bata kawo komai ba ta koma mazauninta, Su Meena suna can suka hirar su basu san me su Abida suka tattauba ba. Sai wajen karfe daya aka gama wa Najwa komai ta yi sallama dasu cike da fara'a a fuskarta da alkawarin sai ta zo dinner, saku wuce Billy sai dariyar mugunta take saki har suka isa mota.


Amma fa ke ba karamar makira bace sai kuma kije Dinner din ko?


Zanje ko ba zan je ba, ba shi ne matsala ta ba, kawai ni yanzu yadda zan shawo kan wannan Amaryan mai rawar kai, na samu mu hadu gobe ko jibi ta yadda zan fasa budurcinta da kaina, na mai da ta cikakkiyar yar harka kafin taje dakin Akram, kinga sai dai ya samu fanko ni na rigashi samunta, daga nan kuma na cigaba da kwasar gyara kin ga ya aura mata ni da shi, duk da dai bana son mace tana harka da maza amma a wannan karan zan yarda muyi sharing ni da shi, wanda in so samu ne har shinfidar aurensu na rika kasancewa da ita.


Kai babee wlh ke bala'i ce duk wanda ya shiga tarkonki ya shiga uku, wato kin Riga da kin gama hada komai. To ni dai ina bara a barni na lasa nima tunda na taya ki fighting akan hada ki da ita.


Najwa ta bankara mata harara, tare da jan tsaki ta maida kallonta kan titi bata ce mata uffan ba dan ta san shuru ma magana ce.


Fitansu Najwa ba dadewa Humaira tazo wurin salon din da kawayenta.


******* ******


Abuja


Da yamma Haj. Hauwa ta fito cikin shirin fita, dan yanzu bata kawo abokan hurdanta gidan, saboda bata so ta bada kofar da Safna zata ga wani abin ashsha a gareta, tana so ta saki jiki sosai da ita sannan ta rika mata kallon matar kwarai ta haka ne zata cimma burinta akan ta. Ta samu Safna zaune bisa Cushing tana kalon tashar Arewa24, sai ta zauna tana kare mata kallo gaba daya a sati uku zuwa cikin na hudu da tayi a gidan ta sauya, fatarta ta goge har dan kiba tayi na kwanciyar hankali.


Allah yayi halitta a wajen nan, lallai zan kwashi dami a kala saura kiris na samu cikar burina a kanki


Tayi zancen zuci tana murmushi Safna ganin ta kafe ta da ido sai ta shiga kallon jikinta, hajiyar ta wayence.


Safna kinga yadda kika yi kyau kuwa? Gaskiya masha Allah diyar tawa tubarakalla 


Safna ta sunne kai cike da jin kunya.


Yauwa Safna zan fita sai zuwa anjima ki kula da kanki. 


To sai kin dawo


Haj. Hauwa ta mike kenan tana shirin daukar jaka sai aka shiga ran gada guda a tv, ta kai kaoonta ga tv hoton Akram da Abida ya cika allon tv, wani irin mugun faduwar gaba tayi wanda ya haddasa faduwar jakar hannunta kasa, ta koma ta zauna tana kallon ikon Allah, bangaren Safna kuwa mutuwar zaune tayi a Cushing zuciyarta ya wani irin bugu, faduwar jakar hajiya shi ne ya dawo da ita hayyacinta ta shiga zancen zuci.


Dama aure zai yi? Yanzu yana kaduna, ko yaushe zan kara haduwa da shi?


Nan take ta shiga wani irin yanayi mara misaltuwa, bata gane me zuciyarta take nufi ba, wani abu ke kai komo wanda bata taba jin irinsa ba.


Me hakan ke nufi?


Tayi tambayar a zuciyarta.


So ne


Wani bangare na zuciyarta ya bata amsa. Nan take ta shiga girgiza kai alamar a'a, sai dai gangar jikinta ne ya amsa hakan amma zuciyata taki amsawa, ita dai tasan Akram yana matukar burgeta tun farkon ganinsa da tayi, tasha jin labaran Hikaya wanda ake yi a redio bata taba cin karo da irin yanayin da take ji ba, wanda so tari a yadda ake bayyana so ba irin yadda take ji game da shi ba. Haka dai tayi ta kallonsu tana jin haushin Abida a cikin ranta tana mata kallon bata dace da shi, kama yayi ace matar da zai aura tafi haka. 


Bangaren Haj. Hauwa kuwa, shagala tayi da kallonsu zuciyarta yana harbawa da sauri da sauri, har sai da aka dauke sanarwan bikin kafin ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, zuciyarta ta shiga mugun kunci gaba daya ta manta da lamarinsa tun haduwarta da Safna, ganin burinta yana gab da cika shiyasa ta manta da babinsa, amma wannan ganin da tayi masa komai ya dawo sabo a zuciyarta, ji take da za a bata damar kisa da shine mutum na farko da zata fara raba shi da numfashinsa. Sonsa da sha'awarsa da take yi a da yanzu ya zama babban kiyayya a zuciyarta, ba tada makiyin daya fishi a rayuwarta.


Wato aure ma zaka yi hankalinka kwance ni ka sanya min yarinya ta a gidan yari. Wannan auren ba zai dauru ba sai na lalata shi na kunsa maka mugun bakin cikin da sai kaji gwanda mutuwarka


Ta yi zancen zuci tana huci ta mike a fuska ce ta dauki Jakarta, uffan bata cewa Safna ba ta fice, Safna ta bita da Addu'an dawowa lafiya. Safna hakanan taji zazzabi yana shirin kamata, ranta duk a dagule, dan farin cikin data ke ciki sai duk ya yaye, ji take dama tana Kaduna ko zata kara ganinsa, tana son su kara haduwa koda fada ne yayi mata kila hakan zai sa ta samu salama akan abinda take ji a cikin zuciyarta, sai ta mike ta wuce daki dafe da kirjinta wanda ya sanya fitar wasu hawaye masu zafi ya sauka kuncinta, kwanciya tayi taja bargo ta rufe duka jikinta. Hoton fuskarsu Akram ne kawai ke yawo a idonta tana kara jin haushin Abida.


Haj. Hauwa mota ta shiga mai gadi ya bude mata gate ta fice da gudu sai gidan bokan ta da yake zaune a Suleja, dan ta fasa zuwa inda tayi niyya saboda so take ta Kawar da matsalar Akram a gabanta.


Dole ne na lalata auren nan 


Tace da karfi tana buga sitiyarin mota da karfi, tana wani huci kamar gumurjin maciji.

_____________


A rayuwa ba sai lallai na kusa da kai yake zama makiyinka ba, ko kuma ayi maka zagon kasa ko nuna kiyayya akan arzikin ka ko wani daukaka da Allah ya yi maka, kowa ma yana iya zama makiyinka muddun ka zama mai gaskiya, ka kasance mai hulda da mutane mabanbanta halayya.


Kun ga dai yadda wasan ya fara, Akram ya taso bai da abokan gaba ko mahassada, bai rasa komai ba na jin dadin rayuwa bai kwana da kowa a ransa, amma bisa ga gaskiyarsa yasa cikin kankanin lokaci ya samu manyan makiya wanda suke farautar ganin sun lalata masa jin dadin rayuwarsa, suna ta farautarsa bai san suna yi ba.


*ƘADDARARREN AL'AMARIN* a zane yake cikin kundin ko wani bawa, sai dai yana zuwa a fuska daban-daban, sai wanda Allah ya nufe shi da cin nasara shi ne zai iya jure duk kan ƙaddarar da ta tunkaro shi.


Labarin dai yanzu aka fara akwai babban tashin hankali, tsantsar tausayi, rikici, damuwa, wahala, ƙunci, rashin ƴanci, cin zarafi, rikitacciyar soyayya, cakwakiya, hargishi, tijara, rashin mutunci, illar lesbian, illar yadda aka zubar da rayuwar marayu, illar rashin tarbiyya, sakacin iyaye. Babban kalubale, ilmantarwa, nishadantarwa, fadarkawa.


*Ya rayuwar Safna zata kasance? wani irin buri ne haj. Hauwa take da shi akan Safna? Shin tana samun nasara?


*Yaushe Safna zata kara haduwa da Akram? Anya zasu kara haduwa kuwa?


*Haj. Hauwa da Najwa suna samun nasara akan Akram kuwa?


Akram yace Auren sa da Abida kamar tonan asirinsa ne, shin wani irin abu ne yake boyewa?


Tambayoyin da yawa...


Don samun warwarewar zaren wannan labari ku biya akan farashi mai sauki. N200 kacal.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol