Free chapter · Read without an account

Part 3

by Safiyya Haruna · Part 1

Dr. Laylah


03


"Affuwan yallab'ai bayarda zanyi ne domin ban iya k'arya ba."


Ma'aikacin ya furta bakinsa na rawa.


"Tafi amma ka shirya amsar hukunci dan alamu ya nuna za'a iya hada baki da kai ayi kisan kai."


"A'a yallab'ai wallahi nasan shi dan uwanka ne kuma kun saba zuwa tare wannan dalili yasa na sanar masa da gaskiyan inda kake amma wannan shi ne na farko kuma na k'arshe sabida kiyayewar tsaro."


Harara ya watsa masa ya koma ciki Saifullah ya d'oki kafadar ma'aikacin tare da furta masa wata kalma cikin rad'a, ya gyad'a kai tare da barin wurin da sauri, murmushi Saifullah ya sa ki ya shige ciki tare da kullo k'ofar.


"Brother me ka ke shirin yi? Shin wai ko kana da sa hannu a barinta gida ne?"


"Saifullah bansan komi a kai ba, ka yarda da ni."


"Idan ka tabbatar da hakan gaskiya ne yanzu ka taho muje ka kare kanka domin kowa na family ya dora zargin alhakin tafiyarta akan ka."


"Ya salam ni Mahi na ga ta kaina kam."


"Brother wannan zancen ba ita ce mafita ba domin ka gama b'atawa kowa rai, Umma ta yi fushi da kai ainun haka Baba Alhaji ya fusata da lamarin kai hatta momy da ta ke bayanka na hango b'acin rai a idanun ta ga Hajiya ta hana kowa sukuni da rigiman sai an nemo mata jikanta, Ammi da Ummi tare da su Abba dik suna cikin damuwa, kai kowa hankalinsa a tashe ya ke barinma da ake ta kiran layinta bai tafiya, wannan dalilin ya sa na zare jiki na fice a wurin taron batare da sanin kowa ba nazo tafiya da kai."


"Waya sanar maka da ina nan?" Ya cillo masa tambayar idanunsa jajur.


"Kunna wayarka ya bani damar gano mafakarka."


"Saifullah ba zan bika ba domin na yiwa kaina alk'awarin nemo musu diyarsu ko aina ta ke dan na tabbata bata bar Nigeria ba."


"Kana da tabbacin tana k'asar nan?"


" Eh."


" Ok sai ince Allah ya baka nasarar gano inda ta ke, ni zan koma amma ka tabbatar da ka rage damuwa kuma ka kunna wayoyinka ka kira su Baba Alhaji domin wanke kanka."


"Insha Allah zan kira."


"Ok."


"Nagode da kulawa brother."


"Ka da ka damu hakkin na ne kula da zumunci."


Murmushi suka sakarwa juna sannan suka rungume juna cikin tarin k'auna mara misaltuwa.


Bayan fitar Saifullah, Mahi ya zauna shiru zuwa can ya tashi ya fice ya yi sallama da hotel din ya shiga motarsa ya dauki hanayar Zaria sai da ya fice garin Kano sannan ya sa ki ajiyar zuciya ya doki steering cikin furta "Saifullah kenan sarkin wayau to na hasko dibarar ka, kafin su Baba Alhaji su ritsani na san inda dare ya yi min."


Ya shafi beard nasa ya kuma kaiwa steering duka tare da jan tsaki mai k'arfi. "Damuwa dai damuwa dik akan wacce bata isa ba." Ya furta hakan cike da takaici wasu kwalla suka taro cikin kwqrmin idanunsa, ya shafosu zuciyarsa na kuma d'aukan zafi, cikin cije lips ya girgiza kai tare da k'ara speed.


***

Saifullah ban sanka da karya ba amma sai gashi yau ka aika tamin, me ya sa?"


"Baba Alhaji wallahi yanzu muka rabu da shi a d'akin nan kuma bai nunamin zai tafi ko ina ba, shi yasa na zare key din d'akin batare da ya sani ba, wallahi Baba kayarda da ni ba zan yi ma karya ba."


" Shi kenan na ji amma na dora maka alhakin kawomin d'an uwanka gabana daga yau zuwa gobe domin rigimar Abdul waheed ya soma isa ta wallahi daren jiya ban iya barci ba musanman ganin yarda Hajiya ke kuka da hawaye dik sabida abinda yaron nan ya aikata."


"Baba Alhaji ku yarda da Mahi wallahi bai da sa hannu a tafiyar Laylah."


" Me ye hujjarka na ambatar hakan?"


"Ya sanarmin bai san ko...


" Yimin shiru Hassan! Ban son jin komi a bakinka tunda ka sanja hali ka na bayar k'arya, maganata na k'arshe shi ne ka kawomin dan uwanka gabana gobe kafin rana ta fad'i." 


Yana ambatar haka ya fice Saifullah ya rufa masa baya da sauri tamkar zai kifa. Suna kan hanyar komawa gida ya dubi Baba Alhaji ta mirror suna had'a ido ya girgiza masa kai cikin cewa "Hassan ka natsu ka samowa kanka mafita ko kaima ka shiga cikin zargin."


' Nashiga uku! Ni kam ina zan nemo ka Mahi? Hak'ik'a ka jefani cikin tsaka mai wuya.'


" Ka maida hankali kan kanya ya Hassan, ka da asami matsala." 


Maganar Baba Alhaji ya dawo da shi hayyacinsa ya gyad'a kai tare da rike steering da kyau.


***

Mahi kam tafiyar rabin awa ya yi cikinsa ya kulle ya yi parking a gefen hanya dafe da gefen cikinsa, yafi mintoci goma rik'e da cikin zuwa can yaji ciwon ya lafa ya fito yana kallon wani shago da ke gefensa wurin ya isa ya sami madara ta ruwa guda biyu aka bude masa ya sanye a ta ke yana maida numfashi ya biya kudin ya juya a hankali ya koma ciki motarsa ya jingina da seat zufa sai karyo masa ya keyi, yana fidda numfashi cikin jin k'irjinsa na yi masa zafi, zuciyarsa tamkar and'ora masa dutse.


"Ulcer dik a dalilita." Ya ambata cikin k'aramin murya hannunsa dafe da k'irjinsa.


"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un." Shi ne kalma da ya yi ta maimaitawa tsawon lokacin daga bisani ya natsuwa ya ziyarci shi ya sami kuzarin kunna motar ya koma d'aya hannun domin komawa gida ya fasa zuwa inda ya yi nufin zuwa sabida baida kuzarin iya tuki mai nisa, yana driving a hankali, ruhinsa cike da cin alwashin kala-kala idan sun had'u.


***

"Laylatu ansoma zama 'yar gari." Mama zainabu ta ambata cikin zolaya.


"Mama ai ni can dama yar gari ce."


"Anya kuwa na aminta da zancen nan naki kuwa?


"Mama ki amince kawai dan yanzu na san hanyar zuwa kogi da fadamu inda ake shukar rake."


"Wato kicemin kinzo yawon bude ido kauyenmu kawai, abinda baki samu damar aiwatarwa ba a shekarun baya shi ne kike fanshewa yanzu."


Murmushi ta sa ki ta juya idanun tare da yin jim zuwa can ta ce "Kusan haka ne Mama kuma yau zan soma zaga lungu da sak'o na garin idan mukayi sallar la'asar Maryam zata rakani bayan gari ga koramu da idanuna na shiga fadama na samo rake da hannuna sannan da dare na fita dandali na bawa idanuna abinci, na yi hira da su ina cin gyad'a suyar ruwa, na kalli sabuwar al'ada da bansan da ita ba kamar hiran samari da 'yan mata cike nishad'i, hak'ik'a ina son rayuwar jama'an garin nan sosai Mama."


"Ke yarnan ki rufamin asiri in mutu mazaje su kai, yanzu dik inda kika lisssfa da izinin wa zakije su?"


"Kaina." Ta amsa kai tsaye tana mai hade rai.


"To ba garin mahaukata kika zo ba, dan haka ba inda zaki je kinji dai na fad'a miki, zunubi komi kankantarsa zunubi ne balle naki na fita batare da izinin mi...


K'ara hade rai da Laylah ta yi yasa Mama Zainabu yin shiru tana hasko wani lamairi wanda da alama shi ne dalilin zuwarta wurinta.


"Eh kin dad'e baki fashe fa karshen fuskan shanu kenan kuma ki sani in har baki sanarmin da abinda ya kawoki garin nan ba gobe zan dauki hanyar Kano da kaina na kai musu rahoto in yaso a can na sami labarin komi."


" Wallahi Mama kina tafiya ni kuma zan bar garin nan in nausa inda ba mai sa ke jin labarina har abada." Ta furta cikin tabbatarwa.


"Na shiga uku ni Zainabu! Na bar zancen Laylatuna, muyi zamanmu kuma Allah ya kaimu anjima ki fita ki kashe kwarkwatan idonki ki more ba mai hanaki, kinji jikallen alkhairi." Mama ta ambata cikin sigan rarrashi.


Juya kai gefe ta yi alamun bata sakko ba.


"Kin gane Laylatu wallahi na bar zancen tunda kikaga yau kwanarki biyu bansa an nemomin mahaifiyarki a waya ba kema kinsan ina tare da ke."


Murmushi ta yi kad'an ta kalli Mama sannan ta juya kai gefe ta ce "Mama matsalar ni da shi ne bai shafi kowa ba amma idan zuciyata ta yi sanyi zan koma na bawa su Dady hakuri dan na san ban kyauta musu ba."


"In jin ba rabuwa kukayi batare da sanin kowa ba?"


Da sauri ta kalli mama, ganin duban da ta key mata mai cike da zargi sai ta yi saurin wayancewa ta sa ki murmushi tare da matsowa ta kwantar da kanta a jikin Mama ta soma magana a hankali k'irjinta na harbawa gudun ka da Maman ta ki aminta da zantukan.


"Mama ba wani abu babba ba ne na dai taho nan ne dan in sami iska kuma nan da sati daya zan koma."


Shiru Maman ta yi tana nazarin fuskanta ya yin da ita kuma ta lumshe ido cikin doka murmushi dan yiwa Maman basaja sabida tuno lamarin ya b'akanta ruhinta.


"Kin tabbata da gaske kike yi Laylatu?"


"Eh Mamana." Ta amsa cikin rungumo hannayen Maman cike da shagwaba.


"Alhamdulillah, har naji hankalina ya kwana domin mutuwar aure babban tashin hankali ne musanman naku na zumunci mai k'arfi."


"Haka ne kam Mama." Ta amsa a hankali.


Tsira mata ido Mama Zainabu ta kuma yi cikin shakkun lamari amma dik kwakwarta ta kasa gano komi domin Laylah mai shegen wayau ce ta yarda kafin agano karatun zuciyarta da kamar wuya..


Bayan la'asar Laylah ta shirya cikin shigar doguwar riga maroon ta yi rolling da gyalen rigar, ba'abinda jikinta ke fitarwa sai k'amshin kuraruka masu tsada na companin oriflame domin komi nata na daban ne bata amfani da abu local shi yasa tayi rik'o da kayan companin har ta koyawa su Ramla soma amfani da kayan suma. Plat shoes ta sanya black da ratsin maroon ta gefensa, hannunta rik'e da black pose ta yiwa Mama sallama ta fice cikin takun kasaita matan gidan suka rakata da idanu cike da jin sha'awarta sam bata da girman kai irin na masu kud'i, kwanarta biyu har ta soma sabawa da mutanen gidan, gata da son yara bata da k'yan-k'yaminsu, a kullum cikin yi musu kyautar chocolate ta ke sai dai bata son hayaniyarsu dan haka iyayensu ke kiyaye bugunsu, hakan na faranta ran Mama Zainabu ganin yarda suke daraja muradin Laylah. A k'ofar gidan dattijai ne suke hira a shimfidar Malam (Mijin Mama Zainabu) wurinsu Laylah ta nufa ta russuna ta gaisar da su suka amsa cikin fara'a, ta wuce suka raka ta da ido cike da yabawa tarbiyyanta.


Uhm Laylah kenan hawainiya saninki hakikaninki sai anyi da gaske.


Sun fice wajen gari tare da Maryama da zugan kawayenta, hananiyarsu dik ya cik'awa Layla kunni amma ta kasa yi musu magana sabida yarda zuciyarta ta yi mata nauyi sakamakon faduwar da gaban ta keyi, tarasa gano dalilin faruwar hakan, tazo samun natsuwar ruhi amma a maimakon samun natsuwar sai gashi damuwa ya kuma dabaibayeta.

Haka nan ta cigaba da binsu, sun sakata a tsakiya wasu a gabanta wasu a bayarta tana takawa a hankali tamkar Sarauniya, ko da ya ke dama sarauta gadonsu ne.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol