Free chapter · Read without an account

Part 12

by Safiyya Haruna · Part 1

Dr. Laylah.


12.


Baiko ganin gabansa ya fice, a tsakanin sashin iyayen nasa ya tsaya yana bin ko wani part da kallo yarasa wanne zai shiga domin ba zai koma part din Baba Alhaji ba dan ya san b'acin randa Hajiya ta dasa masa ba komi ba ne akan wanda ya karanto Baban zai shuka masa.


"Kai Muhammad." 


Ya tsinkayi muryan Dady ya doki kunninsa. Kallon volcany ya yi ya hangosa tsaye hannayensa goye a bayansa, kallon a gogon hannunsa ya yi yanzu kusan k'arfe goma na dare.


'Tabbas Dady ni yafito nema.'


"Shigo ka sameni."


Maganarsa ya katse masa zancen zucci. Ba musu ya nufi k'ofar da zai sada shi da gidan Dady zuciyarsa na harbawa amma dik da haka yana jin kwarin guiwa.


Sallama ya yi a falo Momy ta amsa masa tana k'are masa kallo ya zube gabanta kafin ya furta kalma ta mik'e da sauri ta haye sama, zamewa ya yi ya zauna a saman rug wasu hawaye masu zafi suka biyo cheek nasa domin wannan alama ne na baida nasara ta ko ina domin dik wanda ke ganin zasu fahimce shi sun juya masa baya.


"Allah na tuba." Ya ambata cikin raunanniyar murya.


"Muhammad zuwa yanzu na amince ba ka san inda Laylah ta ke ba amma ina umurtanka da ka nemomin ita ba dan wani manufa sai dan kai din jininta ne, Yaya ka ke gareta, a kan wannan matsayi na ke son ka nemo inda ta ke ka dawomin da ita gida, idan kayi min haka k'ullin da ke tsakanin mu na kwance shi daga ranar zamu dawo fiye da can baya."


"Zan nemo ta Dady a dik inda ta b'oye daga nan kuwa har wajen Nigeria fatana ka fahimci dalilin faruwar lamarin."


"Nayima alk'awarin fahimtarka Muhammad, kuma zan saurareka dan jin dalilinka."


"Nagode Dady, yanzu zan dauki hanya, idan gari ya waye ka bawa Baba Alhaji hakuri wallahi bazan iya ganin b'acin rai a fuskansa ba kuma wai ni ne silar samuwan lamarin, itama Hajiya ka bata hak'uri zan cika umurninta insha Allah bazan dawo gidan nan ba sai da Laylah. Kai da Momy ina neman gafararku na tarin laifukan da aikata muku bayan haliccinku gareni, zan gyara ko ma ince na gyara, su Baba K'arami dik a ce su yacemin natuba."


Yana gama fad'ar haka ya mik'e ya fice jiri na dibanda. Da ido Dady ya raka shi yana mai jin tamkar ya dakatar da shi amma ya kasa samun kuzarin yin hakan domin fuskan d'iyarsa kawai ya ke muradin gani.


Ta k'aramin gate ya bi ya fice bai bi ta kam motocin da ke harabar gidan ba haka bai damu da ya kira Saifullah ba balle ya koma ya dauko motarsa burinsa ya bar garin Kano ciki daren nan. Yana jin maganar Baba Ali mai gadi da ke yi masa ya ki kulashi wanda hakan ba halinsa ba ne share na gaba da shi, yana isowa bakin titi ya hau napep ya sauke shi a tasha drop na taxi ya dauka sabida babu fasinja ko daya a cikin motar kuma ba zaiyi iya zaman jira ba. Ba b'ata lokaci driver ya ja shi suka dauki hanyar Zaria sai dai Abuja suka nufa wanda a k'iyasi nan da zuwa k'arfe ukun dare zasu shiga garin Abuja.


Sun isa lafiya sai dai suna isa bakin gate din gidan Mama Mariya securities da su je wajen gate din suka sanar masa dazun da safe mutanen gidan suka wuce Kano, umurtan drivern ya yi ya kaishi hotel su kwana washe gari su juya. Washe gari da kyar Mahi ya iya shan ruwan tea shima dan jin yana shirin mutuwa ne, kafin su wuce sai da ya koma gidan Mama Mariya cikin sa'a saiga Asiya ta fito, ganinta ya tabbatar masa jiya raina masa wayau securities din sukayi.


"Mahi kai ne da safiyar nan?"


Lashe busassun lips nasa ya yi ya amsa "Ni ne aiki ya kawo ni, daren jiya na zo gidanku amma securities suka tabbatar da kuna Kano, babu kowa a gidan."


"Mamace ta tafi amma mu muna nan kuma ina jin sunyi hakan dan tsaro sabida kwanaki irin hakan yafaru cikin dare abokin Yaya Abdul ya zo neman shi a she had'a baki ya yi da yan fashi suka shigo Allah ya taimaka kafin suyi ta'asa cikin security d'aya ya gano su kafin a ankara suka gudu shi ne Abba ya ce ko waye ya zo da dare ka da abarshi ya shigo, ci kuwa har danginsa da mu yayansa sai gari ya waye sun tabbatar da gaskiya sannan subari."


"Ikon Allah, to Allah ya tsare gaba."


"Amin."


"To bari in koma dama Mama nazo gaisarwa."


"Ka jika da wani zance ai tunda na ganka sai ka shigo kun gaisa da Abba sannan mutumiyar Laylah na gari na san taji kazo baka shigo ba na shiga uku da mita."


Jikinsa ne ya yi sanyi ganowa da ya yi Laylah bata zo nan ba. Sallaman driver ya yi da kudi mai tsoka wanda ya ninka abinda ya ne ma ya biya sau biyu. Baki har kunne drivern ya sunkuya yana zuba masa godiya.


"Ni ke da godiya Malam da ka iya biyo ni batare da tsoro ba." Ya ambata masa hakan cikin kirkiro murmushi.


A falon saukan baki na musanman Asiya ta yi masa masauki, yana nan zaune cike da fargaba ta dawo dauke da tire mai girman ta jera kayan saman table da ke falon zata soma had'a masa tea ya dakatar da ita.


"Kaini in gaisa da Dady domin ina sauri ne ana jirana."


"Dady bai tashi ba amma na san zuwa sadda zakagama karyawa zai fito."


"Ina Amira?"


"Itama tana barci."


"Wato ke ce sarkin sanmako?"


Murmushi ta yi kadan "Nima dole ne ya sa na tashi akan lokaci sabida Yaya Kabir na daf da isowa shi ne zanje dauko sa."


"Uhm ki ce Angonki zai dawo shi ne ki ka kasa barci sabida murna."


Dariya ta yi cike da jin kunya.


"To yanzu abinda za'ayi mufita tare ki sauke ni a hanya na k'arasa inda zani in yaso anjima sai na dawo cin abincin dare kinga lokacin kowa ya nan k'ilama har da mama ta dawo."


"Ok amma ka kammala karyawa tukunna."


"Na k'oshi dan saida na karya sannan na fito."


"To dan jirani inzo."


Da kai ya amsa yana latsa wayarsa cike da ya bawa kirkin Asiya wanda tun can baya a haka ya santa da iya karrama mutum sama da yayanta Amira.


Tana ficewa shima ya fito ya tsaya a harabar gidan sabida ya san waye Amira wurin saurin gano abinda mutum ya b'oye a ruhinsa. 'Gara ta ganni a tsaye cike da uzuri akan ta ganni zaune cikin damuwa.'


"Oh yallab'ai a she kaine a Abuja tamkar wanda ya zo neman abu mai mahinmanci."


Dam! K'irjinsa ya harba jin kalaman Amira sadda ta iso. Ganin ta kafeshi da ido sai ya yi tunanin kila ma ta san inda Laylah ta ke.


"Barkanki da warhaka Mrs Jalal dafatan kin iso lafiya?"


"Lafiyalau ina mutumiyata da rigimarta?"


"Lafiyalau."


"Anya lafiya kuwa?"


"Me kika gani mai gani har hanji." Ya furta tare da maida hankalinsa kan wayarsa yana kirkro murmushi, bai jira amsarta ba ya kara wayar a kunni shiru ta yi tana kuma karantar yanayinsa.


"Muhammad gayu." Ta furta cikin dariya sai ya ji dik ya muzanta dan tunaninsa hango k'azantarshi ta yi sabida ko wanka bai samu yi ba suka baro hotel d'in.


"Kalaman Laylah na tuna a lokacin baya da ta ke tsokanarka kana shan kunu wai ta rainaka." Ta ambata cikin dariya. 


Murmushin dole ya yi a daidai lokacin ya gama wayan ya kalleta da kyau sai lokacin ya lura da cikin jikinta da ya soma tasowa. Idanu waje ya nuno cikin sai ta juya masa baya dariya ne ya kubce masa jin sautin dariyarsa ta nufi cikin gida da sauri tana cewa "Ka gaishe min da su Rahma ka cewa mutumiyar ta bud'e wayoyinta ina son magana da ita."


Bai amsa ba ya koma ya jingina da mota yana hasko wani lamari sai kuma ya ja tsaki ya fice gate batare da ya jira Asiya ba. Maimakon ya koma Kano kamar yarda ya yi nufi sai kawai ya hau taxi zuwa wani private hospital sabida jin kansa ya yi masa nauyi tare ciwon k'irji. 


A asibitin dik yarda yaso likitan ya rubuta masa magani ya wuce ya k'i saida ya bashi gado sabida yarda ya gano yana buk'atar hutu dan gujewa kamuwa da hawan jini mai illtana sassan jiki.


Yini ya yi yana barci sai da la'asar ya tashi dik da jikinsa ba k'arfi amma nauyin da zuciyarsa ta yi masa ya ragu, haka shima nauyin kan din ya nemeshi ya rasa. Salloli ya rama sannan ya ci abinci mai rai da lafiya wanda likitan ya siyo masa. Yana kammalawa likitan ya shigo ya dubeshi ya sa ki murmushi "Yallab'ai Mahi Magajin Gari sannu da ta shi."


Murmushi ya maida masa da martani "Yawwa Doctor Noor, hak'ik'a na gode da kulawa domin ga shi inajin abinda ke damuna babu kaso saba'in cikin dari."


"To alhamdulillah yanzu zaka amshi allura zuwa gobe sai na sallameta."


"A'a yanzu zan tafi sabida...


" Ka da ka damu daga yanzu zuwa ko wani lokacin 'yan uwanka na saman hanya sabida Saifullah ya kiraka na sanar masa baka da lafiya haka Baba karami shima ya kira dik na sanar musu."


Shiru ya yi yana kallon likitan tamkar wanda ke shirin gano nak'arsa.


"Affuwan abokina idan hakan baima dadi ba, na tsorawa ne da ganin halin da ka ke ciki sabida zuciyarka na harbawa da sauri kuma hakan babban matsala ne ga lafiyar jikinka shi yasa da suka kira na sanar musu dubi da yarda na fahimci neman inda ka ke sukeyi."


"Bakomi nagode da kulawa." Ya sami kansa da furta masa hakan.


"Hakkina ne baka kulawa Abokina."


Murmushi suka sakarwa juna.


Bayan ya yi masa allurar sai ya zauna suna hira tamkar sun jima da sanin juna, haka nan jinin likitan ya ji ya hadu da na Mahi barinma da ya ga sunar family nasa ya tabbatar da ba daga k'aramin gida ya fito ba babban dalilin kenan da ya bashi kulawa na musanman sabida ya san zai samu sallama mai tsoka.


"Wa ye Laylah Abokina?" Dr. Noor ya jefo masa tambayar tare da tsareshi da ido.


Tamkar saukan gaton dutse haka tambayar ta daki k'irjinsa.


"K'anwata ce." Ya ambaci hakan cikin tsare gira.


"Lallai ta mori Yaya mai son farin cikinta, ni kam idan ka nemota ina son kabani aurenta dan nasan ita din sarauniya ce dubi da yarda kake ambatar halin da ka shiga a rashin sanin inda ta ke wanda sanadin hakan ya haifar maka da ciwo.


Runtse ido ya yi Dr. Noor ya kyalkyale da dariya ya doki kafanta cikin cewa " My in-law zan kula maka da ita fiye da yarda kake zato just give me a chance."


"Doctor zanyi barci." Ya furta cikin kulle ido.


"Ok bari in barka ka huta nima zanje gida amma anan zanyi magrib so sai na dawo."


Kai ya gyad'a.


"Me kake son in taho ma da shi?"


"Tuwo."


"Angama domin wanna mutumin Kaka ce na tabbata idan ka ci tuwonta sai ka mance sunar My Love Laylah."


Bude ido ya yi a hanzarce ya raka Dr. Noor da kallo yana jiyo harbawan k'irjinsa. Dafe saitin hagunsa ya yi inda halittan zuciyar ke a jiya "Nagode miki Umma da ki tursasani sai na aikata." Ya ambata tare da maida hannunsa saman goshinsa yana fatar zuwan barci ya d'auke sa amma sabanin haka fuskanta kawai keyi masa gizo, yunkurawa ya yi ya tashi zaune batare da tunanin komi ba ya lalibo number Fatima ya bude volume sannan ya koma ya kwanta ya kafe wayar da ido yana dakon ta d'aga kiran ko ya sami sauk'in abinda ya ke ji.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol