Free chapter · Read without an account
Part 1
by Safiyya Haruna · Rumasa'u
*RUMASA'U* (The Innocent girl).
Page 01.
Allahumma salli ala sayyidina Muhammadun wa sallim S.A.W.
*Note.* RUMASA'U k'agaggen labari ne dan haka ban yarda ajuyamin shi ta wani sigar ba. Idan anci karo da wani abu yazo dai-dai da naki ko naka wannan salon rubutu ne kawai amma ba'ayisa dan cin zarafi ko farantama kowa ba.
*Shimfid'a*
Uwa da d'iyar rayuwarsu cike ta ke da k'alubale, sun shak'u da juna ainun ta yarda suka zamo ko wani sashi jigon rayuwar d'an uwansar ne, hakan shi ne silar haifar da dank'on k'aunar tasu mai sosa ruhi sannan tafiyar nasa cike ta ke da tausayi. Kowa yasan Soyayya irin ta uwa da d'iyoyinta shi ne ake kira da dashen Allah S.W.A wanda Ubangiji ke sanyawa a zukatan kowani sha-shi na halittar amma dik da hakan gwanin iko da baiwan kan kuma juya lamuran a bisa yarda ya rubuta cikin k'udirarsa wanda babu mai iya sauyashi dik kuwa k'i ko so da bawa ke yiwa al'amarin. Tabbas yabo da dikkan godiya tabbatattu ne a garesa, Ya Rabbi muna rok'onka da ka k'aramana tsoronka a dikkan halin da muka tsinci kanmu, Amin. Bari dai ku mu tsunduma cikin labarin RUMASA'U.
*
A k'asar busas-shiyar itaciyar d'orawa wacce tabushe k'ayau babu alamar tohon ganye a samanta. A nan ta ke kwance cikin turb'aya ta yi matashin kai da jijiyar itaciyar sai shak'ar barci ta ke yi abinta hankali kwance, hak'ik'a dik wanda ya gitto ya ganta kwance cikin rashin galihu sai lamarin ya tab'a masa zuciya amma ga mai wadatuwar imani.
Hasken ne na wayewar gari daga duhun subahi ya takurata ga k'udaje sun soma hanata sukuni sai kai masu duka takeyi idanunta kulle amma da zarar ta sauke hannu zasu dawo suna cigaba da yi mata ihu cikin kunni. A kan dole ta tashi daga barcin badan ya isheta ba, mik'a ta yi tare da sauke hannunta gefen damarta dan lalibo d'iyarta kamar yarda ta saba dik in ta tashi barci ita ta ke soma tab'awa kafin komi, sai dai maimakon ta tab'o d'iyar sai k'ullin kayansu ta kamo, a zabure ta kalli wurin idanuwa nan nata masu razana jama'a a waje, shiru ta yi na 'yan second sai kuma ta soma kaima k'ullin kayan bugu da iya kacin k'arfinta, ganin hakan baiyi mata ba sai ta mik'e tsaye ta k'walla ihu ta d'iba a guje ta nausa cikin unguwa.
Gudun ta keyi cikin ihu sai ta kai k'arshen layin sai ta dawo farkonsa dik cikin ihun kuru-ruwan mai tada hankali wanda da kaji kasan bana lafiya ba ne. Dik wanda ta had'u da shi babba ko yaro sai ta kama hannunsa ta zube saman kneel nata tana d'aga hannaye sama alaman rok'o,wasu su tureta ya yin da wasu kuma d'auketa da mari sukeyi, masu tausayi ne ke janye jikinsu subarta batare da sun hantareta ba, yara kuwa in ta rik'e sai su fashe da kuka sabida tsoro dan gani su ke dukansu zatayi dubi da halin da ta ke ciki na tab'in hankali.
Haka ta kasance cikin wannan hali tsawon lokaci amma ba wanda ya kula da ita alhalin al'umma sun fahimci taimako ta ke nema tunda bata tab'a yin hakan ba dik tsawon zamanta tare da su. Cike da gajiya ta zube a k'asa cikin turb'aya ta yi ta juyi tana d'iban k'asar tana watsama kanta, ta kuma yin butun-butun da datti. Zuwa can ta yi shiru na 'yan mintoci tana zare ido sai kuma ta zabura ta cigaba da bin mutane tana rok'on su cikin sigan kurumta domin ba wanda zaice ya tab'a jin maganarta. Nan ma ta yi mai isarta ba wanda ya kulata sai ta samu gefen bishiya da ke kan hanyar ta zauna ta yi ta kuka numfashinta na ciccira tamkar zai bar jikinta.
Sai kuma a lokacin ta zamewa al'umma abar kallo cikin k'an-k'anin lokaci mutane suka zagayeta ganin jama'ar baisa ta yi shiru ba saima sauti da ta k'ara tana kaiwa goshinta duka tamkar ba'a jikinta ya ke ba. Ganin wannan abinda ta keyi sosai ya karya zukatan wasu dan al'umma da yawa a wurin sharan hawaye sukeyi musanman ma da suka ga jini na fita a hancinta amma dik da hakan an rasa mai bata taimakon sabida tsoron kada ta shak'e mutum dik da sun san hakan ba d'abi'arta ba ce.
"Alhaji Bala wai taron me akayi a can? wanda da k'yar na samu hanyar wucewa."
"Ni ma tambayar da zanyi maka kenan Alhaji Ahmad."
"Ikon Allah tabbas ba lafiya kuwa wurin."
"To Allah ya kyauta."
"Amin, lallai kam ya kamata muje wurin dan najiyo ihu mara dad'in amo a wurin kuma da alamu muryan mace ce."
"To in ko haka ne ina zaton mahaukaciyar nan ce ta ke yinsa dan naji Hafiz ya shigo yana ihu wai ta rik'e masa hannu zata cije shi d'an uwansa na musawa tare da bawa Umminsu labarin irin ihun da ta ke zabgawa, ina shirin tambayarsu dalilin faruwar lamarin naji sak'on isowarka."
"To in haka ne muje mana muga abinda ke faruwa Alhaji, kafin mutattauna batun da ya kawoni."
"Ok muje d'in sarkin tausayi Ahmadu."
Dariya Alhaji Ahmad ya yi jin sunar da abokin nasa ya bashi.
"Yes kayi dariyarka amma kasani ba zan shige gaba ba dan bana shiri da mahaukata domin yanzu zasu nemi illatani, abanza."
Dariya Alhaji Ahmad ya kuma sanyawa yana cewa "Wannan gaskiya ne mutumina dan bazan manta wata mahaukaciya da ta tab'a biyoka ba har ka sami targad'e garin gudu."
"Ai Abokina har kwanar gobe in na tuno lamarin tsigar jikina tashi ya ke yi."
"Uhm Allah dai ya kuma tsarewa."
"Amin dai."
Zuwansu Alhaji Ahmad sukayi nasarar korar jama'an wurin suka ja baya, ya motsa gabanta ya sunkuya bakinsa d'auke da addu'a ya ce "Baiwan Allah me ya faru?"
Shiru bata d'ago ba sannan kuma a ta ke ta yi tsit ta bar ihun da ta ke kwara-rawa, sai ajiyar zuciya ta ke saukewa cikin jan numfashi.
Ya kuma mai-maita tambayar nan ma shiru tamkar yana magana da dutse. Ya juyo wurin mutanen da ke kallonsu, Alhaji Bala ya yi hanzarin ja da baya aikam mutanen suka rintuma da gudu, ganin ba abinda ya faru sai suka dawo suna lek'e daga nesa.
"Jama'a ko kunsan abinda ta ke so?" Alhaji Ahmad ya ambata muryansa na rawa sabida tausayinta da kamashi a lokaci d'aya.
Wani matashi ya bud'e murya daga can baya ya amsa. "Alhaji ina zaton d'iyarta ta ke nema dan bamu ganta tare da ita ba."
"Matso nan samari kayimin bayani, shin d'iyar nata babba ce ko jaririya?"
"Matsashiya ce dan zatayi shekaru sha biyu zuwa sha uku."
"Hasbunallah, me ye sunar ta?"
"Ba wanda ya sa ni, mukan dai kirata da d'iyar mahaukaciya."
Juyawa Alhaji Ahmad ya yi ya tsirawa mahaukaciyar ido wacce kanta ke sunkuye har lokacin ta yi shiru bisa alamu sauraren bayanin su takeyi ko wani tunanin. Cikin dakiya ya mik'a hannu ya d'ago fuskanta batare da k'yan-k'yamin daud'an da ke jikinta ba domin tashin warin jikinta kad'ai ya isa sanya mutum yin amai.
Kafeshi ta yi da manyan idanunta farare tas wanda ke razana mutane har suke jin tsoronta dik da bata duka hasalima ita kanta tsoro mutanen ke bata musanman jinsin maza.
Haka nan yasamu kansa da sakar mata da murmushi, tausayinta na k'ara ninkuwa cikin ruhinsa. Ihu ta k'walla mai k'arfi da d'imauta brain da hanzari ya ja baya har yana fad'uwa ya buge hannu amma ko a jikin sa, ganin haka al'umman wurin suka dare wasu har da kwasawa da gudu.
"Kaga Alhaji Ahmad taho muje wannan lamarin ba namu ba ne."
"A'a Alhaji Bala taimako namu ne tunda muna da halin yinsa."
"To ni kam kaga inda na bi inka gama ma had'u wani lokacin dan yanzu fita zanyi wani sabgar bazan lalace wurin mahaukaciya ba wacce bata da amfani." Yana gama fad'ar haka ya bar wurin da hanzari yana waiwayen Alhaji Ahmad da ya yi sukuti na binsa da kallo, cikin ransa jinjinawa rashin imanin abokin nasa ya ke yi musanman akan talakawa da musakai.
Matsowa Alhaji Ahmad ya kuma yi gabanta ya murza yatsunsa a fuskanta sukayi k'ara ta d'ago akaro na biyu ta kuma watsa masa idanu. Cikin tsoro yasoma yi mata maganar kurame inda ya ce "Me ke damunki?" Bisa mamakinsa sai ta amsa da alamar bada nono ya juya ga jama'ar wurin ya ce "Wa yasan inda d'iyarta ta je?"
Wannan karan wani dattijo ne ya amsa "Babu wanda ya sa ni ranka ya dad'e domin dik inda ka gansu tare su ke da juna yau ne kad'ai bamu gansu tare ba."
Kallonta ya kuma yi ta had'a hannaye sama alaman rok'o ruwan hawaye na gudu saman kumatunta sai kuma ta sa ke fashe da kuka mai sauti tana buga goshinta a k'asa, hab'on d'azun ya dawo sabo, kama kafad'unta Alhajin ya yi da k'arfi hawaye na bin fuskansa lamarin da ya kuma raunata zuciyoyin dubban al'umman da ke wurin barin ma da suka ga ta rik'e hannayensa tana mai son yin magana amma bakinta yak'i fitar da furucin komi sai k'arar ihu.
"Ya isa haka nan, ki natsu yanzu zamu dubo miki d'iyarki bisa taimakon jama'an da kike gani." Ya ambata a hankali yana mai nuna mata mutanen wurin.
Kai ta motsa tare da goge majina da bayan hannunta. Lamarin ya kuma jefa mutanen wurin cikin mamaki dan basuyi zaton tanajin magana ba d'aukansu kurmace kuma bebiya.
"Jama'a kuyi taimako dan Allah dan manzon Allah domin samun taimakon mahaliccinmu lokacin da babu tsimi da dabara sai nashi shi kad'ai." Alhaji Ahmad ya ambata cikin raunin murya.
Jinjina kai sukayi hakan ya bashi k'arfin guiwa cigaba da cewa "Dan Allah ina kuke ganin zamu nemo mata d'iyarta?"
"Yallab'ai mu kam bamu sani ba dan yarinyar kullum tana tare da mamanta yau ne kad'ai bamu gansu tare ba kamar yarda Baba Liman ya sanar ma ka." Wani mutum ya fad'i haka.
"Ya Salam, yanzu ina mafita jama'a?"
Basu kai ga bashi amsa ba suka jiyo ihun wata mata tana fad'in. "Jama'a ku kawo d'auki kada ta mutu!"
Kalamar da ya diro kunnuwar su Alhaji Ahmad kenan. Kafin ka ce kwabo jama'a sun nufi wurin da matan ke ihun akawo d'auki ciki har da Alhaji Ahmad tare da mahaukaciyar wacce ta riga kowa isa bak'i kangon da matan ke tsaye bata jira komi ba ta ture matar gefe tare da kutsa kai ciki sabida hango d'iyarta da ta yi kwance cikin jini. Zama ta yi dirshan a k'asa ta kamota ta rungume ta soma kyal-kyala dariya dagani dai hauka tuburan. Dik wanda ya yi nufin zuwa kusa da ita domin amsar yarinyar sai ta rarimi dutse kamar zata jefo shi tana gunguni, dole suka tsaya tsirko-tsirko suna kallon ta. Ita kam ta k'an-k'ame d'iyar gam wacce babu alamun numfashi a tare da ita.
Ta cigaba da kwasan dariya har da hawaye. Alhaji Ahmad ya kalli matar da ta yi sanadin ganin d'iyar cikin tambaya da ido domin bakinsa ya yi nauyi. Ta ke ta d'auki haske tasoma koro masa bayani.
"Yanzu ne nazo wucewa sai na tsinci wannan agogon ko da na sunkuya dan d'auka sai naji kamar nishi a ciki ina lek'awa na hango d'iyar mahaukaciya kwance cikin jini anyi mata fyad'e."
Salati wurin ya d'auka, wasu suka soma tsinewa wanda ya aikata lamarin ya yin da masu ilimin ciki ke nema masa shiriya wurin Allah.
Muhsin ya matso ya na kallon agogon hannun matan tare da tsira masa idanu. 'Tabbas na Abid ne.' Ya ambata cikin ransa zuciyarsa na zillo. Ganin Idanun Alhaji Ahmad na kansa yasa shi ja da baya ya fakaici idanunsa ya silale ya bar wurin cikin rashin kuzari sannan ruhinsa cike da tsanar d'abi'ar d'an uwarnasa wanda kullum ya ke yi masa wa'azi akai amma tamkar k'ara ingizashi ya keyi.
Ran Alhaji Ahmad ya yi mugun b'aci da jin labarin abinda ya sami yarinyar. Da k'yar cikin dibara ya samu Mahaukaciyar ta yarda aka sanya yarinyar amotarsa suka nufi asibiti da ita bisa rakiyar police guda biyu wanda wani bawan Allah ya kirasu suka zo gudun kada a sami matsala wurin amsarta a asibitin.
A harabar asibitin nanma da kyar aka shawo kanta ta yarda aka d'ora yarinyar a gadon d'aukan marasa lafiya, jikkinta rufe ya ke da babban rigan Alhaji Ahmad sabida kusan tsirara ta ke dan mara imanin ya yage mata kaya shi yasa tun a wurin ya cire babban rigarsa na shadda ya rufeta da shi.
A bakin k'ofar d'akin da aka shiga da ita ya tsaya dafe da goshinsa yana jin wayarsa na ringing amma ya kasa dubawa, ya yin da mahaucakiyar ta ke jikin window tana hango abinda akeyiwa d'iyarta tana kwasan dariya wai ita nan murnan ganin d'iyarta ta ke yi.
Matar da ta rakosu ta dubi Limamin unguwar wanda akazo tare da shi ta ce "Baba Liman zan koma gida sabida mijina bai san na taho ba."
"To baiwar Allah angode, Allah yabiya ki."
"Amin." Ta masa tare da juyawa zata tafi Alhaji Ahmad ya kirawo ta, ta dawo kudi ya mik'a mata ta hau abin hawa, ta amsa cikin godiya ta fice, zuciyarta cike da tausayin lamarin, ba abinda ta ke hangowa sai kyaky-kyawan fuskan yarinyar da akaciwa zarafi.
'Oh ni Hanne inda ace d'iyata Abuwa akayiwa haka ko ya zanji a raina?' Haka dai ta yi ta auna lamarin cikin ranta tana zancen zucci har ta k'arasa bakin titi ta sami abin hawa.
Awa d'aya da mintoci arba'in da biyar da shiga da ita likita ya fito nurses biye da shi. Kafin ya k'araso Alhaji Ahmad ya tareshi.
"Doctor ya...
"Biyoni office Alhaji." Likitan ya katse shi.
Shi da Baba Liman suka rufa masa baya jikinsu a sa ke sakamakon ganin fuskan likitan babu annuri.
*Mrs j moon.*