Free chapter · Read without an account
15
...Rumanah🕊️
(Zabin Iyaye)
©️ Aisha Machika
*Page~15*
Tun daga wannan ihun da Jamila ta yanka ban sake jin komai ba, har lokacin zuciyata bata daina harbawa ba ga Al'amin maƙale jikina, ganin anba minti goma baya banga fitowar ko ɗaya daga cikinsu ba yasa naja hannun Al'amin muka shige ɗaki, duk yarda naso in hana kaina tunanin su Saraki hakan ya gagara, dana yakice sai tunanin ya sake gittawa cikin zuciyata, shin da gasken mu'amular aure suke kamar yarda yace? Nayi maza na hau girgiza kai ina ƙaryata tunani na, daga baya nayi matuƙar ƙoƙari wajen bawa kaina magana, inma abinda suke kenan Rumanah miye naki, matarshi ce kamar yarda kike, matar ma ta fari uwar gida.
Sai can wajen taran dare Saraki ya shigo ɗakina a lokacin har Al'amin yayi bacci, ni kuma ina zaune kan gado daga gefe na jingina bayana da gadon inata latse-latse waya, amma a zahiri damuwa ce tab a cikin zuciyata ta tunanin rashin ganin Sarakin, na bishi da kallo ganinshi cikin farar lallausar jallabiya sai ƙamshi ke tashi a jikinshi da ganinshi dai wanka yayi da yammacin nan, wani irin baƙin ciki da takaici ya rugu da gudu yayi masauki a cikin rayuwata.
Na dinga banka mashi harara ganin wani annuri saman fuskarshi, baima san ina yi ba, sai da ya gama shafa kan Al'amin sannan ya kalleni yana faɗin madam ya jiki-jikin? Nayi ƙasa da kai tare da mashi banza, bai damu ba ya miƙe yana faɗin sai da safe toh tunda ba za'a man magana ba, ya fita na rakashi da harara ina jan tsaki.
Kwana ɗaya, biyu, uku banga ko giccin Jamila ba, sau biyu kuma ina taba ƙofarta ina jinta a kulle alamar dai bata cikin gidan, Saraki baice man komai ba game da ita, nima kuma ban tambayeshi ita ba, sai da akai sati guda cur sai gasu da ƴan'gidansu mutum uku wajen sha ɗaya na safe, ina ɗaki naji motsinsu, na fito domin inga su waye, ganinsu yasa muka gaisa ina kallon Jamilar da duk ta rame man a ido, ban dai ɗora daga gaisuwar ba na koma ɗaki.
Bayan kwana biyu da hakan, duka muna zaune falon sai sallama muka ji, dukanmu cikin mamaki muke kallon waÉ—anda suke shigowa falon, Baba Sarki ne a gaba sai mahaifin Jamila Ibrahim Ningi yana bayanshi, cikin girmamawa muka gaishesu tare da dawowa kan kafet mu duka, su suna kan kujeru, nina kawo masu kayan motsa baki bayan Ć´ar fira kaÉ—an, Baba Sarki ya gyara murya ya soma magana kamar haka; nasan zakuyi mamakin ganinmu a gidan nan yau, musamman ma da bamu taba zuwa ba, toh yau ma dalili ya kawo hakan, kai Saraki shekaru fiye da takwas kenan dayi maka auren fari, wanda na yi shi ne a bisa ra'ayina na zaba ma yarana abokan rayuwar aure, toh abin mamaki kaine kawai ba'a samu yarda ake so ba.
Nayi tunanin ince ka sakar masu ƴa, sai kuma naga shi uban yarinyar ba zai ji daɗi ba, shiyasa duk tsawon shekarun nan nayi shiru, amma shekaranjiya na samu shi Ibarahim na shaida mashi irin zaman da kuke yi kai da Jamila, ba wanda yasan gawar fari, kada mu da muka haɗa auren mu bar duniya kunga an ƙwareku, yanzu mun zo dai gareka ne, idan kana son matarka toh ka barta, in kuma baka sonta maza rubuta mata takardar saki.
Ibrahim Ningi yace ma Baba Sarki, wallahi Alhaji ban taba zaton irin rayuwar da Ć´a'Ć´a na keyi kenan ba, ashe basu ganin mutuncin kowa a duniya sai ni, kofa mahaifansu mata basu isa da su ba, toh har yaushe za'a so auransu dama, Allah ya sani ni dai ina bakin iyawata a kansu, sai kuma ya soma share hawaye, Baba yace ah'a Alh ba laifinka bane, kai da baka zama a Nigeria gaba É—aya, kasan yanzu ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba.
Ba ni kaɗai ba da nake ganin rashin dacewar zamana a wajen ba har Saraki jikinshi yayi sanyi, Jamila ko Allah kaɗai yasan halinda ta ke ciki, dan kanta na a ƙasa, Baba yace Saraki kai fa muke jira kayi shiru, a sanyaye ya ɗauko biro da takarda ya soma rubutu, ban san meya rubuta ba ya dai gama ya miƙa ma Baba, Baba ya karanta ya yi murmushi sannan ya miƙa ma mahaifin Jamila, shima ɗan murmushin ya yi ya linketa ya sanya a aljihu, Baba Sarki ya ce toh Allah yasa haka shi ne mafi alheri muka amsa da amin gaba ɗaya, mahaifin Jamila ya kalleta yace ke Jamila maza haɗo kayanki mu tafi gida, kinga sai ki je ki auri rashin mutunci ko?
Ta miƙe jiki ba lakka, ashe kuka take sirfa, duk da bansan zafin saki ba amma yau na tauasaya ma Jamila, ganin irin ƙaunar da take ma Saraki, amma duk ita taja ma kanka da tun farko tayi haƙuri tayi biyayya shikenan, dama ance abinda ka shuka shi zaka girba, ni da Saraki munyi shiru sai su Baba keda keda firarsu kamar wani abu bai faru ba.
Ta ɗauki aƙalla wajen minti talatin sannan ta fito ɗauko da akwati guda ɗan babba, ni da ita ba wanda yace ma juna ƙala suka yi mana sallama suka wuce, Saraki kuma ya fita maida Baba Sarki.
>>>>>>>>>>>
Wai Allah dare gari ya waye, na haifi ɗiyata mace wadda taci sunan mahaifiyata SAUDAT, ba wani inkiya da mukayi mata Saudah muke ce mata, rayuwa taci gaba da tafiya ba daɗi yanzu gida sai ni kaɗai ba Jamila, Saraki kam idan ya janye yaranshi suka shige gari sai na gansu koba ranar aiki ba ko, ga aikina na asibiti gana gida, dole wani lokacin na rinƙa dawowa gida da rana inyi abinci in koma, shidda na dawo gaba ɗaya sai in ana nemana kuma ayo mani waya inje, ba shiri na samo ƴar aiki daga kura, yarinya ce mai tsabta da ladabi ƴar shekara goma sha huɗu mai suna Saratu, ita ke man shara da wanke-wanke da sauran aiyukan gida, abinci dai nike yi da kaina wai wani lokacin tana masu ita da ma'akata.
Hankalina ya yi matuƙar tashi jin ina ƴan ciwace-ciwace kamar cikin Al'amin, ba shiri na binciki kaina sai gani da ciki na sati uku, ga Saudah duka watanta huɗu, da farko kuka na zauna ina yi shikenan ni kuma da antaba ni sai ciki kamar ina sha a ruwa.
Ban yarda ma Saraki yasan da shi ba naje aka zuƙe man shi, kwana biyu ina zubar da jini ya ɗauke, na sake zuwa aka yi scanning na gwajin jini dan tabbatar da cewa ya gama fita, muna zaune da sister Aina'u ina jiran result Saraki ya mani waya inyi maza inzo gida ya dawo dasu Al'amin zashi wani waje, dole na barma sis Aina'u sallahun idan result ɗin ya fito ta kirani kota aiko man da test ta waya ina jira.
Koda na isa gidan tsaye na iske shi cikin shiri, yana ganina ya miƙo man Saudah, yana faɗi man Abuja zashi amma yau zai dawo komin dare, nayi mashi Allah ya tsare hanya, har na gama abincin dare ba waya ko massage ɗin sis Aina'u, ina zaune a falon wayar na gefena naji kukan Saudah daga ɗaki, nasan Al'amin na ɗakin shi yayi mata wani abun, ɗakin na nufa inga meke faruwa, ina shiga na ganshi zaune gabanta ita kuma sai tsala ihu take, yana ganina ya sauko ya nufo wajena yana magana.
Mummy inga ace Baby ta taci aga bacci cine ake kuka, na É—auketa ina rirrigawa na kalle shi dake man bayani nace Al'amin ba'a hanaka tashinta daga bacci ba bakaji ko?
Ya yi narai-narai da ido zai kuka, nace toh maza jeka falo kace ma Saratu ta kula da wayata idan an kira ta kawo mani, ya juya ya fice, ni kuma wanka nayi ma Saudah nima na watso ruwan sannan na fito falon, nace Saratu har yanzu ba'a yo wayar bane? Tace Mummy aini ban ma ga wayarki ba tun É—azu muke nema da Al'amin, haba kan kujera fa take, ba dai ku duba da kyau ba ya za ace ba........shigowar Al'amin da gudu ya katseman maganata.
Al'amin bana hanaka shiga ɗakin Daddy ba idan baya nan, Mummy aya nan ace na kira Mummy, na kalli Saratu nace yaushe ya dawo? Mummy kina shiga ɗaki ya dawo, na miƙa mata Saudah na juya nanufi ɗakin ina mamakin shine ya dawo bai shigo ya shaida mani ya dawo ba, zaune na sameshi kan gado da murmushi na na isa inda yake, na zauna kusa dashi, Saraki ashe ka dawo?
Shi ne kaƙi zu---kallon da yayi mani ne yasa nayi shiru, ya miƙo man waya ta, gata ko ba ita naji kina ma waccan yarinya magana ba? Ki duba ma tun ɗazu akayo maki massage ganin babu kowa falon yasa na ɗauka na karanta, wai ko sister Aina'u kowa, duba dai ki gani, hannuna na rawa na amsa na hau dubawa, ga abinda ta aiko.
Dr. Rumanah result É—in ya fito and congrate cikinki ya fita duka ba saura, gobe idan kin shigo kya amsa.
S. Aina'u
Zuciyata tayi mummunan faÉ—uwa, na kasa É—ago kai in kalli Saraki da nike jin idanuwanshi a kaina, na shiga uku ni Rumanah yau me zance ma Saraki, tabbas nasan dai ya karanta tunda ya faÉ—i da bakin shi, amma ai tabarmar kunya da hauka ake naÉ—eta, Sarakin ne ya dawo dani daga tunani na.
Rumanah manyan likitoci sannu da aikin zubar mani da ciki, nasan kinyi ne dan inji haushi, toh hankalinki ya kwanta kinyi nasara, naji haushin harda ciwo sosai ma, sai dai babu abinda zan iya yi tunda aikin gama ya gama, yanzu sai hankalinki ya kwanta kin zubar da cikin maƙiyinki, ya ɗanyi tsaki a hankali, Rumanah kinfi kowa sanin ina son ƴa'ƴa ko zasu kai ɗari ne ina son abina, Ummu kiyi tunani idan ba irina ba akwai ɗan'iskan namijin da zai biye ma matarshi yayi duk abinda ta ce mashi?
Amma ni wane irin tashin hankali ne ban gani ba kafin in samu Al'amin, amai, bacci, dariya, kuka, farin ciki da baƙin ciki duk nayi su akan Al'amin, har aikina na kusa rasawa saboda rashin zuwan da bana yi kamar da, amma duk haka baisa kinji tausayina ba sai da kika zubar mani da jini yabi rariya.
Ba abinda zan iya maki, Allah kika yi ma laifi can tsakaninku dashi, ya miƙe ya tsaya saman kaina, na kalleshi nace nifa ba dan komai nayi ba naga duka watan Saudah huɗu, ace na samu wani cikin kaima kayi tunani ma...........hannu ya ɗaga mani, Rumanah ni fa ba sakarai bane kamar yadda kike zato, Rumanah na gaji da waɗannan halayen naki, kullum abu ɗaya babu canji kamar dai ki kaɗai ce mace a duniya.
Nima na tashi fuskata a É—aure, Saraki fito sarari ka gaya mani cewa Rumanah na gaji da zama dake kaga idan zan sake mintuna a gidanka, dama waya nace ma wani?
Koka taba jin nace ni Rumanah ina sonka?
Toh bari kaji abinda baka sani ba, daman dan Baba Sarki nake zaune da kai da tuni kowa ya kama gabanshi, Baba yace inyi haƙurin zaman ƴan watanni da kai, innaji bana sonka inzo ya raba auren, sau biyu ina zuwa yana ban haƙuri, biyayya tasa ka ganni har yanzu, amma tunda abin haka ne in Allah ya yarda gobe zan bar maka gidanka, tunda bani kaɗai ce mace ba sai a auro huɗu mu gani.
Rumanah ni kike gaya ma magana haka ba kunya balle shakka? Nayi tsaki toh ka wuce a gaya maka ne? Gida dai nace zan barshi, daga yau aure ya ƙare tsakaninmu, zanje in samu wanda ya haɗa ya raba, saukar mari naji a kumatuna, a firgice na kalli Saraki idanunshi babu sauran annuri a cikinsu, na ce nika mara Saraki?
An mara zaki rama ne? Maza zo ki fice man a ɗaki, idan kin tashi tafiya dan Allah kada ki tsaya garin Kano, kima bar Nigeria gaba ɗaya matsalarki, igiyar aure kuma sai inga wanda zai sa na saki, Allah baka isa ba sai ka sake ni, nace bana sonka ko ana d.....wani marin ya sake mani, fitar mani ɗaki nace kafin kisa zuciya ta ɗeboni na canza maki kamanni, ganin yarda ya hasala yasa naja jikina na bar ɗakin dan ba ƙaramin aikinshi bane ya naɗa man na jakin.
Kayana na hau haÉ—awa ga Al'amin ya tsareni da surutun Mummy angowa caki nima cani Mummy, nace mashi toh kawai dan babu inda zani dasu zan bar mashi yaranshi harta goyen, Saratu ta shigo da Saudat wai tana kuka, na amsheta na bata nono sannan na kwantar da ita ina tunanin abinyi gobe.
Da safe ni kaÉ—ai na sulale na bar gidan, dama akwatuna na cikin mota suka kwana, sai da na soma biyawa asibiti aiki har aka tashi kana na wuce can gidan Baba Sarki.