Free chapter ยท Read without an account
Episode 5&6
FARAR MACE* ๐
*By*
```Ummu Sumayya```
*(Baby Bintu)*
Vote me on wattpad
#Bintubaby
*Elegant Online Writer's*
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*PAGE THREE*
Cike da kunya ta janye nata idanun tana bashi hanya alamun yashigo, wani kyakykya-wan handsome guy ba fari ba kuma ba ba'ki ba amma fatar shi dai tafi ta Mufeeda haske k'arasa wa yayi cikin palourn cikeda girma mawa yaduk'a yagaisar da Mom,
Cikin kula ta amsa ta'kara da cewa
"Ka zo gaishe mu ne ya Hajiya Sarah take hope lafiya dan kwana biyu tarabu da Kira na nikuma abubuwa sun min yawa ban tab'o taba"
Kanshi yad'an sosa yana satar kalon Mufeeda dake tsaye kanta a'kasa yace "Uhm ta na lafiya yanzu Dr yakira ni wai baijin dad'i shine naxo duba shi na biyo naigaisar da ke"
"Innalillahi wa-enna ilaihirraji'un yanzu dama Muneef baida lafiya shine bai gaya min ba ai yamai kyau muje side d'in nashi dama chan na nufa Mufeeda muje daga chan saiki gaida shi ko" Mom ta'karisa maganan tana nifan corridor da zai kaita side d'in Muneef
Badan taso ba tabi bayan Mom dan ita yanda bai k'aunar ta itama ba k'aunar shi take ba daidai zasu fita ne ta tsinkayi muryan ba'kon yana cewa
"Y'an Mata ba gaisuwa?"
Baki tad'an tura tace "Umm am sorry barka da safiya fatan katashi lafiya"
Dariya yad'an yi cikeda wani farin cikin da baisan dalilin saba ya amsa da "Alhamdulillah amma fa nafiki lada dan ni na ro'ki gaisuwar"
Baki tad'an tab'e kawai batare datace mai komai ba kuma adaidai nan suka iso part d'in shiga sukai ba kowa a palourn sai air condition daketa aiki ga k'amshin turare daya cika palourn gunun dad'i ganin Mom ta nufa bedroom ne yasa suma suka rufa mata baya Dr Fahad fa gaba d'aya yagigice dan sosai Mufeeda tatafi da shi jira kawai yake yayi abunda zaiyi yakafa kanshi a zuciyar ta Allah dai yasa wani bai rigashi ba ajiyar zuciya yasauke harsaida tad'an kalle shi da many'an idanun ta wanda hakan ba'karamin tafiya dashi yayiba.
Akan bed Mom tasame shi yana k'udundune yanata famar rawar sanyi cikeda damuwa ta'karisa gareshi tace "Ayya Son meyasa kake b'oye min rashin lafiyar ka ne" ta'karisa maganar tana zame blanket d'in daya lullub'e dashi ta'ba wuyan shi tayi taji rau
Shiko Muneef da yasamu barci yasake kwashe shi jin sanyin hannun Mom yasa yabud'e idanun shi karaf suka sauka akan fuskar Mufeeda dake tsaye daga chan bakin k'ofa
Lumshe idanun shi yayi yasake bud'e su akanta hannun Mom yasake ji ajikin shi hakan yasa yad'an kalle ta cikin shagwa'ba da zafin zazza'bi yace
"Mom" sai kuma yayi shiru yana kallon yanda Dr Fahad ke kallon Mufeeda cikin takaici yad'an ja tsaki sai kuma yace "Idan ka gama iskancin zaka iya zuwa kaduba ni ko meye abun kallo ajikin k'waila ohoo mtssss" ya'karisa maganar dajan tsaki dan sosai yaji haushin kallon da Dr Fahad ke mata gani yake kamar zaiga abunda yagani ne jiya d'an sake kallon su yayi yaga ita tama juya shikuma Dr Fahad yayi kichin kichin da rai batare dayayi magana ba ya'kariso yafara duba shi
Mom kuwa kallon su tayi saikuma tami'ke tana fad'in "bara na sallami Mufeeda na dawo ke Mufeeda bakimai ya jiki ba"
Batare data juyo ba tace "Allah ya'kara sau'ki yasa kaffara ne" tana fad'in haka tai waje dan sosai taji zafin cemata k'waila da yayi
Direct side d'in Mom suka koma inda tabata two k tana ta gargad'in ta akan karta dad'e gudun kar Abban ta yazo har compound tarako ta tana bama driver umaranin yakaita *GWARIN FA* sannan ta'kara da cewar "ki gaida Umman taki kice ta'kara ha'kuri komai zai wuce insha Allah"
"Tom Mom Nagode insha Allah kuma zan gaya mata"
"Yawwa ki dawo da wuri fa"
"Insha Allah Mom byeee" ta'karasa maganan tana weaving d'in Mom d'in sannan tashiga motan Mom na weaving d'in ta itama.
Mom ko saida taga wucewar su sannan tanufa side d'in Muneef d'in,
Tana isa ta iske Dr Fahad na mai allura tsayawa tayi har aka gama sannan yace zai wuce anjima inya tashi zai kawo mai magani,
Kallon shi Mom tayi tace "amma meke damun shine haka?"
D'an sunkuyar dakai yayi amma kafun yayi magana sai suka tsinkayi muryan Muneef nace wa
"Mom karfa kiwani damu kawai chanjin weather ne wallahi shiyasa kinsan da naje kano ruwa yad'an dake mu ahanyar dawowa"
Cike da gamsuwa Mom tace "Ayya Allah yakyauta gaba lallai soyayya tayi riba tunda gashi anfara cin Karo da many'an abubuwa"
Lumshe Ido yayi yana hamdala da Mom bata ramfo komai ba,
Dr Fahad kuwa cike da mamakin k'aryar daya girba yake kallon shi sai kuma yakad'a kai yama Mom sallama sannan yafuta.
Bayan fitar shine Mom takalli tea cup da fatan lemon tsami guda uku dake wajen alamun a tea d'in akasa tace "waye yasha Lipton ba ko madara ga lemon tsami?"
Shiru yayi kamar me barci dan dama idanun shi alumshe suke, jin shiru ne yasa tayi tunanin barci ne yad'auke shi dan haka tajuya ta futa tana mai fatan samun lafiya.
*GWARIN FA*
Gida ne d'an daidai ginin talakawa amma da ganin sunada rufin asiri ahankali tashak'i wata iska tana kallon k'ofar d'an madaidai cin gidan sauka tayi amotan tana ma driver godiya sannan tanufa cikin gidan cikeda zumud'i dan tunkan ta'karisa ainihin tsakar gidan take ta fad'in "Maami na Maami na kina ina ga d'iyar ki Maami na kina ina ne" ta'karisa maganar da k'arfi adaidai nan kuma ta'karaso ainihin tskar gidan da baida wani girma sosai d'aki d'aya ne agidan tsaf dashi duk daba siminti amma an share shi k'al daga gefe ga randunar k'asa nan guda biyu atushen wata k'atuwar banana data mamayen wajen tayu luf luf
Wata mata ce ta fito daga d'akin wacce bazata haura shera talatin zuwa da biyar ba aduniya sosai suke kama da Mufeeda da alama daga barci tatashi duba da yanda take mutsitsike idanu da sauri Mufeeda tayi hugging d'in ta gamida yamata peck a forehead tana cewa "I miss you Maami na"
D'an ture ta tayi daga jikin ta tana fad'in "Oh ni Zulaikha wai yaushe zaki girma ne Yarinya! Sai kace baki ta'ba ganina ba kin tadani abarci na dama banjima da kwanciya ba Allah yashirya ki"
Cikin murmushi tace "Ameeen Maami na ko bakiyi farin cikin ganina bane?"
Ta'karisa maganar tana d'an b'ata rai dan dama sun saba itada Maami d'in kasantuwar ta y'ar fari juyawa tayi kamar zata futa aiko dasauri Maami ta chafko ta tana fad'in
"Kefa baki da ta ido abunda nake nufi shine kidinga saka natsuwa a lamarin ki ke mace ce mushiga ciki nan akwai rana"
Cike da farin cikin datake ji duk sanda tazo wajen Maami d'in tabi bayanta tana ta murmushi wanda yaba ma beauty points d'inta daman lotsawa abun gunun kyau domin ita d'aya ne agefen bakinta d'aya wajen kumatun ta ta sama wato wajen idanun ta.
D'aki ne d'an madaidaici babu komai aciki sai katifa da kujera three sitter zama Mufeeda tayi tana fad'in "wash Maami na nagaji yasin"
Cikin kula irin ta d'a da mahaifi tace "sannu ya hanyar amotan haya kikazo?"
Idanu ta jujjuya tana cire hijab d'in ta kasantuwar rana harta k'wallaro saida tacire sannan tace
"Wallahi driver Mom tasa yakawo ni tace na gaishe ki wai kik'ara ha'kuri wataran sai labari"
D'an kauda fuskar Maami tayi alamun bata son maganar batare data tanka ba tami'ke tafuta,
Da ido Mufeeda ta rakata aranta tanajin wani iri "shin kome ye tsakanin Abba da Maami da yasa suke takun sa'ka oho ita kanta abun nabata mamaki domin Abba ma idan tamai maganar Maami shima haka yake dan akwai ranar data k'ure shi har marin ta yayi akan ta tambaye shi meyasa be son Maami" ajiyar zuciya tasauke daidai lokacin da Maamin tadawo hannun ta ri'ke da cup d'in silba na ruwan sanyi d'ayan hannun kuma plate d'in taliya ce dafa duka dataji manja tayi dahuwar kyau,
Agaban Mufeeda ta aje sannan takoma tazauna a bakin katifar ta tana cema Mufeeda "Bismillah ko, nasan baki karya ba kika fito"
Murmushi Mufeeda tayi sannan takalli Maamin nata tace "Nagode"
D'an hararan ta tayi sannan tace "bazaki daina min wannan d'abi'ar ba ko?"
Cikin tura baki alamun shagwa'ba tace "to Maami idan bance Nagode ba mezan ce?"
Hararan ta tayi sannan tace "idan nabaki abu kidaina min godiya domin kin wuce komai agare ni Yarinya saina maki abu innaji kin gode sai inga kamar bai maki bane kina sa inajin wani iri araina da zuciya ta"
Jikin Mufeeda ne yayi sanyi da'kyar ta bud'e baki tace "kiyi ha'kuri Maami bazan sake ba amma kuma idan akamin abu ne ban yi godiya ba sainaji wani iri nariga da nasaba"
"Uhm Yarinya kenan duk sanda nabaki abu kice Allah shi amfana yafi Nagode so dubu kuma sai kiga Allah yasa nasibi acikin abun"
Kai tajinjina alamun gamsuwa sannan tafara cin taliyar tana lumshe idanu alamun tamata dad'i ayangan CE take cin abincin kamar batason ci wanda haka d'abi'ar ta yake tun tana k'arama,
Bayan tagama ne suka ci gaba da fira da Maami sama sama wanda yawancin firar ma kan karatun tane.
Sai bayan azahar rana tafara sanyi sannan tafara haramar tafiya kamar zatai kuka domin ita harga Allah bata wani son gidan Mom saboda yanda y'ay'an ta ke nuna mata k'iyayyar su afili da nuna wariyar launin fata inama ace Abban ta zai yarda tabbas da tayi zamanta awajen Maami don zaman gidan ta sai tafi farin ciki duk da chan zataci mai kyau tasha me kyau amna in wula'kancin Samraat yatashi maida ta take tamkat y'ar aiki dan kawai Mom d'in su ke biyan mata kud'in makaranta jiki asanyaye Maami tarako ta har bakin titi saida ta tabbatar tahau taxi d'in sannan itama tajuya cikeda kewar y'ar tilon y'ar tata da aka rabasu k'arfi da yaji.
__________________________________________________________
Daga lumshe idon da yayi barci yayi awon gaba da shi,
Sai wajen k'arfe d'aya yafarka da wata yinwa da'kyar yayi sallah jikin kam da sau'ki adaddafe yayi wanka yafito yashirya cikin kayan shan iska yanufa side d'in Mom,
A palourn k'asa yasame ta tana waya directly dining area yanufa kujera yaja yazauna sannan yazaro wayar shi yad'auyi y'an dane dannen da zaiyi yakara akunne yace "kizo palourn k'asa kisame ni" abunda yace kenan yakatse wayan,
After like two minutes saiga Samraat ta sakko sanye da Arabian gown dayai matu'kar yimata kyau wayan tane ahannun ta tana ta dannawa harta k'arasa sauka daidai nan Mom tagama wayan kusan atare suka isa dining d'in Samraat nace wa
"Barka da war haka Bros yajikin hope ka warke"
Baki yad'an tab'e sannan yace
"Alhamdulillah samin abinci am hungary ko break fast banyi ba"
Cikin d'an tausayin Yayan nata tace "ayya sannu bros bara na had'a maka coffee firstly kafara warware hanji"
Bai tanka ta ba sai charting d'in da yake yi da Khalisat datake ta mai k'orafin tun jiya ya'ki d'aga wayar ta,
Coffee tahad'a mai tatura gaban shi sannan tazuba mai fried couscous dayaji vegetables da hanta shima tura mai tayi sannan itama tayi serving d'in kanta da Mom,
Gaba d'aya ahankali suke cin abincin babu mai magana acikin su sa k'aran spoon da ac daketa tashi awajen.
Sun rigashi gamawa dan haka suka mi'ke Samraat tanufa sama Mom kuwa kitchen tanufa wajen Mama me girki,
Yajima yana cin abinci wanda baima wani ci dayawa yaji yafiatar mai aka bakin shi yagoge da tissue yami'ke ya'kara so palourn yazauna gaban bowl d'in dayake shak'e da fruit pawpaw yad'auka ya yanka dakanshi sannan yasaka fork yana chaka yana ci ahankali yanata lumshe idanu ahaka Mom tadawo tasame shi d'an zama tayi kusa dashi tana fad'in
"Ya dai jikin da sau'ki ko?"
Kai yajujjuya mata kafun yace "Alhamdulillah k'arfi ne kawai banda shi"
Murmushi tayi tace "Masha Allah shima zuwa gobe zaka dawo normal Allah ya'kara sau'ki"
"Ameeen ya hayyu ya qayyum Mom d'ina"
Mik'ewa tayi tanufa sama tana fad'in "bara na d'an kwanta kafun la'asr"
"To afito lafiya Mom"
"Allah yasa" tafad'i tana haura step d'in k'arshe tanufa bedroom d'inta,
Saida yaji yayi dam yayi gyatsa yace "Alhamdulillah bi-ni'emati tatimmu salihat" sannan yami'ke cikeda wata kasaala yanufa side d'in shi yana zuwa yakira Khalisat suka fara zancen love kamar zasu cinye juna ta wayar at d-end yau tagabatar mai da k'udurin ta nason yaturo iyayen shi sunema mai auren ta,
Ajiyar zuciya yasauke cikeda gamsuwa yace "Masha Allah kice nakusa zama angon Khalisat kenan?" Dariya tayi daga chan side d'in takashe waya tatashi tafara tik'a rawa.
Shiko murmushi yayi danshi Allah yasani kunyar Khalisat ba'karamin burge shi take ba yanada ga cikin abubuwan dayasa yake matu'kar sonta sannan uwa uba tarbiyya yakan jinjina ma iyayen ta domin awannan lokacin ba ko wacce yarinya xaka samu da irin tarbiyar Khalisat ba, to shima dai ayanzu kam yasan yana son aure dan tundaga jiya zuwa yau yafahimci wani abu akanshi amatsayin shi na Dr tabbas yasan inbaiyi aure ba komai na iya faruwa dashi, shi gani yake ma kamar wani asiri tamai amma babu yanda za'ai kamar shi ace wata ba'kar mace taburge shi mtssss yaja wani shegen tsaki da wannan tunanin barci yayi awon gaba dashi.
Ana kiran sallar la'asr tana shigowa gidan agajiye take saboda abakin layi taxi d'in ya ajeta ta'karaso da k'afa kasantuwar babu tree cycle a unguwar tasu sosai bata taradda kowa ba a palourn dan haka tashiga d'akin ta direct cire kaya tayi tafad'a toilet wanka da al-wala ta yi sannan tafito tazura dogan riga tatada sallah.
Muneef kuwa cike da b'acin rai yatashi domin still mafarkin yana sex da Mufeeda yayi gaba d'aya kayan shi sun lalace kamar zaiyi kuka haka ya watsa ruwa yachanza kaya yanufa masjid aranshi yanata tunanin anya ba wani abu Mufeeda tamai ba ahaka dai yayi sallah yajima yana ro'kon Allah ya yayemai abunda ke damun shi akan Mufeeda dan kwata kwata ba type d'in shi bace.
________________________________________________________
*KANO*
The following day da Khalisat ta koma aka mata wankin inji yauma ba'karamin azaba tasha ba dan harda hawaye amma saboda tsaban son abun duniya bata ha'kura ba haka tafuto tana wani fitinannen k'amshin mai jikin ta gaba d'aya yafara sauyawa kasantuwar yau ita kad'ai tazo driver yakawo ta haka tazo tashiga mota tanufa gida skin d'inta sai rad'ad'i yake mata tana zuwa gida tayi barci kamar yanda suka tsara mata sai wajen uku tafarka tayi wanka da sabulan ta sannan tafito tashafa mayukan dasuka bata sallah tayi azahar da la'asr da yanzu aka kirata bayan tagama komai tanufa palour kasantuwar yau week end mahaifinta na gida
Tana zuwa palourn sama ta same shi yana zaune suna fira da Mommy da gudu ta k'arisa tafad'a jikin shi kamar wata Baby, bayanta yashafa sannan yad'an d'ago ta yamata peck agoshi yace
"Babyn Dad tun d'azun nake expecting ganin ki shiru Mommy ki tace kina chan kina barci hope lafiya dai ko?"
Cikin shagwa'ba data fara zame mata jiki tace "Am fine Dad wajen kama nazo fa!"
Dawo da hankalin shi yayi kanta kachokan yace "ina jinki babyn Dad mekike bu'kata?"
D'an juya idanun ta tayi tagyara zamanta tana jin gina da Dad d'in cikin farin ciki tasauke idanun ta akan Mommy dake ta kallon su tunda tashigo d'an fari tayi da idanu kafun tace
"Dad dama nasamu mijin aure ne har mun gama magana zai turo magabatan shi"
Kallon ta yayi cikin farin ciki da fara'a yace "Kai masha Allah Khalisat d'ina takusa girma Allah yasanya alkhairi d'an waye? ko ince d'an wani gari ne?"
Dariya tayi cikin fara'a tace "sunan shi Muneef d'an Abuja ne sunan mahaifin shi Alhaji Omar Fate"
D'an jujjuya kai Dad yayi cikin tarin al-ajabi da kad'uwa kafin yace
"Alhaji Omar Fate to ai........โ๐ป
*wannan littafi na kud'i ne inkina so kikaranta cikin salama tura naira 200 cikin wannan asusun bank d'in 4210014214 lawal Shamsiyya Eco bank saiki tura shaidar biyan ki ta *** y'an VIP group kuma zasu tura 400 ta account details d'in da na fad'i y'an Niger kuma saiku tuntu'be *** danjin yanda zaku biya maza kuhanxar siyan naku akasuwa domin bazaku nadaman hakan ba๐๐ป siyan nagari maida kud'i gida*
*Ga masu son littafina wato paid book akwai HANGEN DALA inkina son siye tare da wannan ne zaki tura 300 kachal don samun littattafan guda biyu*