Free chapter 路 Read without an account

Episode 15&16

by Babybintuu 路 FARAR MACE KO MAYYA CE

馃崅 *FARAR MACE* 馃崅


        *BY*


 *Ummu Sumayya*

```Vote me on wattpad ```

    *#Bintubaby*


*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




         *PAGE EIGHT*



Ranshi a'bace da yanda Mubarakatu take kallon tsiraicin su yadaka mata tsawa yace 

"Baki da hankali ne zaki shigo mana d'aki gaba gad'i ohya get out" 

Itako dama Zulaikha tunda taganta ta b'oye ajikin shi tsawar da yayi kuma yasa tasake shigewa kamar zata b'ula fatar shi tashige,

Gaba d'aya idanun Mubarakatu yarufe gani take Alhaji Abubakar yaci amanar ta tunda ya had'a makwanci da wata cikin wani irin azababben kishi da yataso mata tace "asirin ka yatono maci amana annamimi munafuki ashe amanata kake ci wallahi yau KO ni ko kai agidan nan bazan yarda ba" kawai sai gani yai tayo kansu,

Cikin azama yatare ta hankad'ata tayi baya tafad'i a'kasa war was, sake tasowa tayi aiko yami'ke yacire Zulaikha ajikin shi yaja blanket yarufe ta sannan yad'auka boxers d'in shi yasa yakama Mubarakatu yafalla mata wasu lafiayyun maruka har biyu dasuka sa tadawo cikin hankalinta sannan yabar d'akin da ita da tsiya da fad'a ya wurgata waje yakullu k'ofar yabarta tan ta bugawa tana zagin shi da maci amana shiko yayi banza da ita yanata lallashin matar shi,

Dakan shi yama Zulaikha wanka bayan yagasa ta sai shimata albarka yake, itako gaba d'aya jikin ta yayi mugun sanyi ganin da Mubarakatu tamusu ko da safiya tayi bayan Alhaji Abubakar yafuta aiki ta lallab'a domin taba Mubarakatu ha'kuri amma saita tadda d'akin ta akulle bata nan,

Haka ta wuni daga ita sai masu aikin su kad'ai agidan koda yadawo tagaya mai bata nan bai wani damuba dama yagaji da halinta haka yadinga kula da Zulaikha harta warke Mubarakatu bata dawo ba,

Dan haka suka dasa sabuwar soyayya abunsu gunun ban sha'awa KO tamai maganan Mubarakatu yakan nuna baya so wani lokacin har fushi yake yi,

Saida Mubarakatu tayi wata d'aya bata gidan rannan kwatsam tana zaune sai gata tadawo tana janye da akwati da murna ta tare ta itama haka kamar wani abu bai faruba amma aran Mubarakatu cewa take "zaman ki agidan nan yakusa k'arewa yarinya"

Har dare suna tare suna fira ko da Alhaji yadawo yagansu sai baice komai ba kuma bai wani nuna farin cikin shi akan dawowar Mubarakatu ba,

Awannan lokacin ne aka raba girki kwanaki biyu biyu sosai zama yami'ka amma me tunda Mubarakatu tadawo zama yafara yalalacewa tsakanin ta da Alhaji ahaka suka koma kamar da baya son ganin ta kwata kwata tayi kuka tayi kuka kamar me amma bata da wanda zata gaya ma damuwar ta dan y'an uwan mamanta da na babanta dama basu damu dasuba tun iyayen ta nada rai kuma tunda suka mutu babu wanda ya waiwaye ta, Khadija (Mom) dake bata shawara tuni basa k'asar suna California dan Omar dama bai cika zama ba,

Kwatsam ciki yabayyana ajikinta batare data fahimta ba sai Mubarakatu ne tagane aiko hankalin ta yayi mummunan tashi tasake bazama tabar garin to kafin tadawo ne wataran Zulaikha na zaune saiga Alhaji yashigo afujajan yana shigowa yarufe ta da duka bata san hawa ba batasan sauka ba yakuma mata koran kare haka takwashe kayanta daya watso mata tanufa gidan iyayen ta dababu kowa aciki tun bayan mutuwar su arufe yake tabud'e tagyara tazauna ad'akin mahaifiyar ta aranan tayi kukan maraici da rashin dangi kamar me haka tazauna agidan mak'ociyar su ita ke bata abinci domin tana matu'kar tausayin ta sannan ga lalurar ciki dataganta dashi, tsayin lokaci batare da tasan ciki gareta ba tadaiga cikinta sai girma yake gashi duk tabud'e amma bata ta'ba kawo wa ciki gareta ba, Kwatsam su khadija (Mom) suka dawo Nigeria taje gidan domin taduba KO lafiya batazo mata sannu da zuwaba dan Mubarakatu tazo amma data tambaye ta Zulaikha saitace batasan inda Zulaikha take ba to datazo ne tasamu duk kanin labarin abunda yafaru awajen y'ar aikin su itama iya wanda taga Alhaji yama hajiyar ne aiko hankalin ta yatashi tanufa gwarinfa dake tasan gidan kuma tasan tabbas can zata nufa, kallo d'aya tama Zulaikha tafashe da kuka saboda yanda taga takoma ga ciki yafito ga uban rama tayi gashi dama chocolate ce saita koma ba'ka k'irin Cikin jimami Zulaikha ta tarota ta amsa jaririyar datagani ahannun Mom (Samraat) kenan lokacin tana da wata shida aduniya Yayan ta Muneef yananda shekara goma sha tara aduniya danshi ne ma yakawo Mom amota yajuya yace inta gama takira shi. bayan sun natsa ne tabama khadija labarin tiryan tiryan akan abunda yafaru abun takaicin ma shine har lokacin bata zargin Mubarakatu,

Ajiyar zuciya khadija (Mom) tasauke sannan takalle ta dakyau tace "saiki dage da addu'a zan zo on monday nakai ki kifara ganin likita watan ki nawa rabon ki da al'ada?"

Sai alokacin zuciyar ta taimugun bugawa kenan ciki gareta tabbas ita wawiya ce kanta a'kasa tace "kusan watanni biyar kenan" gaba d'aya muryan ta rawa yake alamun kuka,

Lallashin ta tadinga yi har yamma sannan tama Alhaji Omar waya tamai bayanin komai tace yasiyo kayan abinci da komai da komai na bu'kata, shikan shi da yazo ba'karamin tausaya ma Zulaikha yayiba alokacin yaso yad'auke ta yakaita can gidan amma khadija tanuna hakan ba mafita bace kawai sudinga kula da ita annan inba hakaba hankalin Mubarakatu zai dawo kansu take duk sukai na'am da wannan shawarar,

Haka sukaita d'awainiya da ita har ta haifi Mufeeda wacce akasa mata sunan kakarta ta wajen uba wato (Fatima) khadija kuma tamata lak'abi da Mufeeda wato mai amfani haka taita rainon Mufeeda batare dako ubanta yasake waiwayarta ba balle yasan ma tana da yarinya ba itakuma tasaka dangana aranta kuma har lokacin bai saketa ba kawaidai yakoreta wanda amusulunce saki yashiga amma sai yafad'i ko saki nawa yayi,

Alhaji Omar dakanshi yasamu d'an uwan nashi cikin lumana yadinga mai wa'azi akan Zulaikha sannan yanuna mai abunda yayifa bai dace ba sosai jikin shi yayi sanyi amma al'amarin shi daban tsoro saboda sai yaji yana son ganinta yana son zuwa yabata ha'kuri abisa abunda yamata amma daya nufi inda take saiyaji kamar ana hura mai wuta kokuma yaga duhu ya mamaye hanyar wani lokacin yarasa inda ma zaije dole yadawo gida kuma azuciyar shi yana muradin ta ajiyar zuciya yasauke kafun ya kwashe kaf abunda yakeji agame da ita yashaida ma k'anin nashi yana kuka yana gaya mai yana matu'kar son matar shi amma bayason ganin ta,

Cike da mamaki dakuma al-ajabi yake kallon d'an uwan nashi kafun yadafa shi yace "tabbas kayi sakaci da azzkar sannan kana barcin asara mai zaisa bazaka raba darenka biyu ba d'aya kai barci d'aya kagayama Allah damuwar ka wallahi inkayi yau kayi gobe kayi jibi indai damuwa ce Allah zai kawo maka mafita sannan yanzu bayanin danake maka matarka tahaihu tasamu d'iya mace kuma nasa ma yarinyar sunan mahaifiyar mu yanzu haka watan yarinyar uku tashiga na hud'u amma kadage da addu'a in akwai alkhairi azamanka da Zulaikha Allah yakad'e shaid'anin dake kawo muku wannan bala'e inkuma babu alkhairi kasake ta kawai taje tai auren ta dan akwai cutar wa"

Ajiyar zuciya yayi sannan yashare hawayen dasuka zubo mai yace "Na gode d'an uwa kuma insha Allah zanyi yadda kace"

To bayan wannan maganar nasu ne bawani dad'e wa Alhaji Omar yayi hatsarin jirgi kuma take yarasu saidai gawar sa aka kawo gaba d'aya sun girgiza da mutuwar shi fiye da tunanin mai karatu haka akaita koke koke har aka share makoki kowa yakama gaban shi alokacin Muneef shekarar sa Ashirin a duniya dan haka take yaci gaba dajan ragamar dukkanin companies d'in mahaifin shi da yaso aje karatu amma Mom tace bazai yiywuba yayi k'arami akula da companies yadinga zuwa makarantar shi yana dawowa ita zataji da komai kasantuwar itama tana da master afannin kasuwanci yasa batasha walaha ba anan suka had'u da mahaifiyar Fahad sunje wani taro a Dubai nankuwa suka k'ulla k'awance domin ita Hajiya Sara mijinta rik'akk'en d'an kasuwa ne yamutu yabar uban dukiya kuma d'an su d'aya k'wal kuma tana bala'en jida shi duk abunda yakeso itama tana sonshi koda bai mata ba sosai suke aminta da Mom domin takai takawo har sharing problem sunayi da junan su kuma babu wanda yata'ba jin kansu sosai itama Mom takeson Fahad inda inbata da lafiya ko Samraat yakanzo yaduba su agida,

Mufeeda tataso agaban mahaifiyar ta Yarinya black beauty komai na mahaifinta tad'auko illa kalar fatar mahaifiyar ta data kwaso tataso cikin kula da gatan Mom domin komai ita ke musu harta kai shekara goma alokacin ne asirin dake jikin Alhaji Abubakar yad'an sake shi domin Hajiya Mubarakatu takamu da ciwon suga yau lafiya gobe rashin ta hakan yasa tad'an jinkirta ma zuwa wajen bokan aganinta Alhaji yamanta da maganan Zulaikha balle cikin dabai san dashi ba acewarta tunda bata haihu dashiba babu wacce ta isa tahaihu dashi balle gado yazamto nata ita da dukiyar ma na mahaifinta ne ace wata tazo tacinye ita tazama y'ar kallo to bazai yiywuba ba *(wa iyazubillah tamanta Allah shike da iko akan kowa da komai)*

Koda yaje sosai yaji tausayin inda suke take yayi yink'urin maida Zulaikha gidan ta tace ta amince amma yaraba musu gida da Hjy Mubarakatu sosai yayi na'am da hakan ranan sunsha fira kamar bazai tafi ba da'kyar yatafi amma da Mufeeda dantunda yad'aura idanun shi akan yarinyar Allah yad'aura mai sonta mai tsanani haka yad'auko Mufeeda badan Zulaikha tasoba amma ganin baita'ba ganin yarinyar ba sai yanzu yasa ta'kyale shi yad'auke ta tsakanin mata da miji akace sai Allah,

Bayan yazo gidan kallo d'aya Hjy Mubarakatu tama yarinya take tagane KO y'ar wacece batace mishi komaiba takira bokanta tace yamata sabon aiki akan Zulaikha,

Boka babu b'oye b'oye yagaya mata cewar "Hjy inkika matsa akan wannan yarinyar allura zata tono garma saidai asake mai firraq tsakanin shi da matar shi wanda hakan zai shafi yarinyar Alhaji bazai maida ma uwar itaba sannan komai zakima yarinyar agabansa bazai tanka ba k'arshe dakanta zata gudu tabar gidan"

Take tai na'am da hakan tatura mai kud'in komai ta waya,

Aiko Alhaji tunda yad'auki Mufeeda ya'ki maidata, itama farkon zuwa gidan tanajin dad'i amma ak'arshe sai aka maida ita y'ar aiki dan duk ma'aikatan gidan Hjy ta salleme su ita keyin komai,

Hjy Zulaikha dataga shiru bashi ba Mufeeda takira shi awaya amma ya'ki d'agawa dataje office d'in shi yamata korar kare yakuma ce in akwai wadan zata turo ya amshi Mufeeda taturo yana jira, daga wajen shi tanufa gidan Mom tana kuka tazayyana mata dukkanin abunda yafaru,

Anan ne takwantar mata da hankali tace zata rok'e shi yabata Mufeeda inyaso ita saitaci gaba da ri'kon ta har aure,

Badan Hjy Zulaikha tasoba ta amince dahakan domin tasan zaman Mufeeda acan komai na iya faruwa dan yanzu tagane wacece Hjy Mubarakatu sosai taji ta tsanesu dikkan su daga Hjy Mubarakatu har Alhaji Abubakar d'in,

Haka Mom tarok'i Alhaji da'kyar da jib'in goshi yabata ita bayan yakafa mata munanan dokoki akan Mufeeda takuma amince koda aka kawo Mufeeda gidan nan ma tafara fuskantar wula'kanci awajen Samraat KO kad'an Samraat bata k'aunar ta gashi Mom tana bala'en sonta kome zata mata bata iya tsawatar mata da d'aki d'aya suke kwana kuma komai tare take musu bata nuna banbanci kwatsam Wataran tadawo sch taga kayanta abakin palour ga Samraat agefe tace "inkina son side d'in masu aiki kikoma can inkuma BQ kike so saiki zab'a amma ni bazan zauna dake kishafa min ba'ki ba nonsense kawai black gorilla kuma kikace ma Mom nina kaiki can saina miki duka kuma kikoma gidan Abban ki Mom Mubarakatu takashe ki muhuta da ba'kar fata mtssss " tabarta awajen takoma ciki tanata zage zage,

Bata damu ba dan tasaba da kalan hayalayyan ta haka takwashe kayan takai side d'in masu aiki cike da takaicin halin Samraat d'in domin duk abunda mom Mubarakatu take mata wani lokacin agaban tane hakan yasa tamugun raina Mufeedan koda Mom tadawo ranta yayi mugun b'aci ganin Mufeeda a'kasa ahalin su suna sama, take Mufeeda tace "ai k'afan ta na ciwo ne yasa tadawo nan d'in zatafi walawa dama can kamar tana takura Samraat"

K'wafa kawai Mom tayi dan tasan Samraat ce takorota haka ta'kyale ta tafara booking kaya daga wani furniture nakusa dasu zata zuba ma Mufeeda aiko Samraat tabuga tsalle tadire tace ba'a isaba saidai akai mata can gwarinfa takoma can d'in da zama amma bazai yiywuba komai adinga daidaita suba haka taita hauka tana fushi dole Mom ta'kyale ta akaci gaba da zama ahaka kwatsam saiga Muneef yadawo k'asar yakammala kratun shi yazamo cikakken likitan zuciya inda k'asar dayai karatu suka bashi aiki gida da mota ga albashi mai tsoka koda yadawo yazo yaga Mom ne sannan yaduba companies d'in su dake tasamun cigaba afad'in arewacin Nigeria har wasu k'asashe na sa hannun jari sun bunk'asa sosai hakan yasa Omar fatee investment products yayi suna kuma kayan su masu inganci ne tundaga kan blues jewels shoe bag clothes electronic na kitchen da duk wani abun bu'kata na rayuwa companies d'in su yanayi sannan sukanyo order daga k'asashe daban daban kuma su sayar kan farashi mai sau'ki,

Tunda yazo baiga Mufeeda dan bai cika zama ba ranar dasuka fara had'uwa tana wanki abaya yahango ta tujaya tana shanya shape d'inta kawai yatafi da shi gaba d'aya yak'osa tajuyo dan arayuwar shi yana matu'kar son mace mai diri baison siririya juyowar da zatai kawai yaganta black take yaji duk duniya babu abunda yatsana irinta sabida shi baya k'aunar ba'kin fata aganin shi fatar su bata da qualities 馃馃ぃ 

Duk da kirjin ta sun susuta shi hakan baisa yaji yana sonta ba amma tundaga ranar kullum sai yayi mafarkin yana sex da ita haka yad'aure har yakoma batare dayasan KO wacece ba,

Alokacin dayasake dawowa ne hankalin shi yatashi daya sake ganin ta komai yacika masha Allah nan ne Mom tagabatar mai da ita.itama aka gabatar mata dashi Mom taso Muneef yaso Mufeeda amma direct yace mata shi bazai aure ba'kar mace ba sai fara KO a ina ne zai nemo ta tundaga nan Mom tashare shi tazuba mai eyes tana ta ma Mufeeda addu'a akan Allah yabata miji nagari,

Shiko Muneef hankalin shi kwance watarana yaje skyline university ziyara saboda zaima surgery student lecture akan zuciya kwatsam yayi gamo da Khalisat fara sol duk acikin students d'in tafi burge shi sabida tana da dad'in murya ga k'ok'ari to bayan yagama musu lecture ne suka bu'kaci daya bud'e musu group koda ta WhatsApp ne yadinga musu lecture inyasamu lokaci kasantuwar shi mutun mai matu'kar son karatu yasa yaji sun burge shi take yamusu al'khawari,

Bayan yakoma California ne yabud'e group d'in bayan yamusu gargad'i mai k'arfi akan kar wanda yad'auki number sa dan yadinga takura mai bayason damuwa, Khalisat da sauran y'an matan aji dasuka gama susucewa akanshi jikinsu yayi sanyi kowacce taja kanta itako Khalisat tana nan tana lura dashi dataga alamun yana son mutun mai maida hankali akan karatu take tafara shishshige mai akan karatu tun baya kulata har yafara kulata takan tura mai hotunan ta wani lokacin ya yaba wani lokaci yayi shiru ahaka tashak'u da soyayyar shi amma shi bai san tanayi ba 馃ぃ


*_Wahala for wanda yake son maso wani haswa sukace k'oshin wahala_*



*_How to subscribe 馃憞馃徎_* 

_200 for normal paid post once a day 400 for VIP group post twince a day, 4210014214 lawal Shamsiyya Eco bank and send the evidence of payment via *** or mtn card with this number ***_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol