Free chapter · Read without an account
Chapter 10
Da safe karfe bakwai Zaina ta wuce makaranta don lecture da take dashi 8-10am. Ba ta ga Moses ba hakan yasa ta wuce cikin class, tasan da ma zai yi wuya zuwa yanzu ya zo.
...
Moses kam bai farka da wuri ba sai tara, shima dom tunawa da yayi da Zaina, ga bai san lokutan da take da aji ba.
Wanka kawai yayi ya fito falon, zai wuce Momy ta tsayarshi ta hanyar cewa. "Musa!"
Juya yayi ya dubeta alamar tambaya. Momy ta tashi tace. "Ina za kaje da safe haka ko breakfast ba ka yi ba."
"Bana buƙata." Yace ya fita ya barta tsaye. Ta jima kafin taja kafarta ta bar gurin ta koma dining, kasa cigaba ta yi da cin abincinta ta miƙe ta koma ɗakinta tana jin haushin kanta duk ita ta jawo musu hakan.
Amma kuma yanzu me laifinta da ita ma ta gane gaskiya, shi ma ya kamata ya fahimci hakan ya dawo hanya maidaidaiciya.
...
Moses School ya wuce kai tsaye, har bakin department ɗinsu Zaina yana dubanta ko zai ganta har karfe goma sha ɗaya ba ita ba labarinta.
Wayarshi ya jawo ya ƙirata, yana ta ringing ba ta ɗauka ba, ya tura mata saƙo yana jiran amsarta.
Har sha biyu yunwa da ya dame shi ya sashi barin cikin makarantar, a eatry ya tsaya ya nemi abinci ya ci kafin ya koma cikin makarantar, ya tsaya inda yasan zai ganta, ai kuwa ganinta yayi ta fito ɗauke da jakarta da hijabinta kamar kullum.
Da sauri ya fito a motar ya isa wajenta. Zaina ta bishi da kallo, ganin haka yace. "Kin san damuwar da ki ka saka ni, ba ki ɗauki call ɗina ba na miki message ba reply why?"
"Wayar tana silent ina lecture ne." Amsar da Zaina ta ba shi tana yin gaba.
Moses ya bi bayanta ya ce. "Kin gama karatun yau."
Kai ta ɗaga masa, suka ci gaba da tafiya, ta yi gaba shi kuma tsaya wajen motarshi ya shiga ya kunna, ya sameta kamar jiya ya buɗe mata yace. "Muje in sauƙe ki gida."
Zaina ta ɗauke kanta ta ce. "Bana buƙata."
"Please Zaina. I said believe me." Ya faɗa cikin kwantar murya.
Ba musu ta shiga suka bar filin makarantar, abun mamaki yau ba kiɗa cikin motar amma ba ta tambayeshi dalili ba, ta juyar kanta kawai.
So take ta mishi tambaya amma ta rasa ta ina fara. Nutsuwa da jarumta ta saka zuciyarta ta dubeshi tace.
"Moses right?"
"Yes!" yace mata yana ɗaga kanshi ya ƙara da cewa. "Moses Abdul."
Zuciyar Zaina ta buga jin sunan shi. Da ƙyar ta ce"Christian or Muslim?"
"Christian." Ya ce hankalinshi yana ga titi.
Jin haka shi ya ƙara rikita zuciyar Zaina da ƙwaƙwalwarta, ta kasa masa magana har yayi parking inda ya sauƙeta jiya, ya juya ya kalleta ya ce. "My father was a Muslim, and my mother too."
Fasa fita a motar Zaina tayi, ta kalleshi tace. "But me yasa kai ka zamto daban cikin su? Why?"
Yatsine fuska ya yi ya ce. "Saboda na tsani musulunci da mai yi, kaf cikin musulmai ke kaɗai na fara mu'amala da ita bayan tsawon lokaci, wanda ni kaina ban san dalili ba."
Zaina rai ta ɓata ta ce. "Ka daina fadar haka, ka daina cewa ka tsani addinina in ba haka ba za ka daina gani na. Addinina shine addinin gaskiya, addinina bai yarda na aibata addinin wani ba don haka ka daina aibata min addinina."
Murmushi yayi ganin ta ɗauki zafi ya ce. "Na fiki sanin addininki tunda na taso cikinta, kuma kinji na faɗa miki iyayena shi ne addinin su."
Zaina kallonshi take da mamakin kalamansa da suke ba ta, ya ɗaga kai yace. "Yes mahaifina musulmi ne ya auri mahaifiyata a Christian, bayan haihuwata da na ƙanwata Esther na so bin addinin mahaifina, Momy ta hanani karshe ta rabani da shi ta tura ni wani ƙasar, wanda bayan dawowata na samu itama ta zama musulma.
To me yasa za ta min haka? Ni ne ba ta son na musulunta? Ko na mata wani abun da za ta hanani musulunta? Tun lokacin na tsani musulunci da kuma mai yinta."
Shuru Zaina tayi bayan gama sauraronshi, maganganunsa suka kashe mata jiki, iyaye musulmai ɗa ya zamto Christian, wanda duk fushi ne ya jawo masa. Hakan yasa ta ji sai tayi ƙoƙarin rabashi da shi idan har tana raye suna tare.
"Zaina." Moses ya ƙirata, ta dubeshi da sauri. Ya ɗaga mata gira alamar tambaya, ta girgiza kai ta buɗe motarsa ta fita tace. "Na gode Musa."
Rai ya haɗa yana yamutse fuska. "Bana son sunan nan."
"Ni kuma daga yau shi zan dinga ƙiran ka da shi." Zaina tace tana murmushi da sai yau ya fara gani a fuskarta.
Shi ma murmushin yayi yace. "Shikenan din ke ce."
Murmushi tayi ta juya ta kama hanyar gida, zuciyarta tarin neman hanyar da za tayi ta kawar da fushin zuciyarshi take.
Da tunane tunane ta isa gidan.
Inna ta dubeta tace. "Ke da nake jiranki tun karfe sha biyu ga shi har biyu saura."
"Inna ban samu abun hawa da wuri ba." Ƙaryar da Zaina tayi tana wucewa bangida, ta kama ruwa da yin alwala ta fito ta shiga ɗaki.
Ta idar da sallah ta duba agogo ta ga uku saura, hakan yasa ta zauna jiran sallar la'asar.
Aka ƙira ta miƙe ta gabatar, da ta idar ta nemi abinci taci ta tashi tayi aikace aikacen gida, ta ɗaura abincin dare.
Inna na zaune tana lura da ita da wani lokaci kawai sai taga ta yi tagumi, amma ta bar abun a ranta akan daga makaranta ne hakan.
Karfe takwas na dare Zaina ta hau saman shimfiɗarta, ta jawo wayarta ta shiga gurin ƙira, rabonta da waya da Hashim tun shekaran jiya da rana, har za ta ƙirashi ta fasa ta ƙira Moses kawai.
Yana zaune cikin falon yana kallon wrestling, ya hana Jawad kallon cartoon, yaron yakai ƙara wajen Momy ta ce ya rabu da shi.
Wayarshi dake hannun Esther tana dannawa ta miƙa masa, ya karɓa yaga mai ƙiran.
Ya yi mamakin ganin ƙiranta, ya ɗauka yace. "Zaina how was night."
"Fine." Tace ta rasa me za tace mishi kuma.
Hakan yasa yayi murmushi ya ce. "Gobe karfe nawa kuke da lecture, kar ki bani wahala wajen jiranki."
"Gobe bani da lecture, lecturer ba zai zo ba." Ta faɗa a hankali.
"Oh God zan yi missing ɗinki." Ya ce yana hararan Esther da ta kafeshi da idanu jin yana hira da mace.
Daga ɓangaren Zaina ta c."Zamu haɗu ai ran Thursday by 10am nake da lecture."
"Ok to muga lokacin da rai." Ya faɗa mata.
Zaina ta ce. "Ameen." Ta kashe wayarta tana dafe kirjinta, don jin ta mishi karambani.
...
"Bros who's she?" Esther ta tambayi Moses bayan ya kashe wayarshi, ya mayar da hankalinsa kan Tv.
"My girlfriend." Ya ce ya tashi yabar falon, Momy da Esther suka bishi da kallon mamaki. Musamman Momy da ta ji kalmar budurwa a bakin ɗanta.
Moses yana shiga ɗakinshi kan gadonshi dake hargitse ya faɗa ya shiga tunani.
Son Zaina yake amma zuciyarshi ta ka sa ba shi yardan haka? Ko don ta kasance cikin addinin Musulunci ya ka sa yarda da hakan oho?
'Me yasa sai ita zuciyarshi za taso? Bayan ƴan mata da yawa da suka kasance cikin addininshi.' Ya tambayi zuciyarshi.
Dole ya nemawa kanshi mafita a kanta, don baya jin zai iya rabuwa da ita.
....
Washegari ranar laraba Zaina ba ta je makaranta ba, hakan yasa bayan ta gama ayyukanta wajen karfe sha biyu ta kama hanya zuwa gidan Ado.
Ta samu baya nan, da ma ba ta tsammaci samunshi yanzu ba, suka gaisa da matarshi Surayya. Zaina ta zauna don jiranshi tana kallon film din da ake haskawa a Tv.
Surayya ta fita taci gaba da aikinta ganin haka ya saka Zaina tashi ta fita don taya ta, suna yi suna hira sama-sama Surayya tana mamakin da ma Zaina haka take, yadda cikin dangi ana yawo ana zaginta sai ta ga duk ba haka bane.
Karfe uku Yaya Ado ya dawo gidan, lokacin su Surayya sun gama aikinsu sun gyara gidan.
Bayan ya shiga ciki yayi wanka, yayi sallah ya fito falo suka gaisa da Zaina yana tambayarta gida da makaranta, ta ce duk lafiya ƙalau.
"Ya mai jikin, ashe Hashim bai ji daɗi ba." Yaya Ado ya tambayi Zaina.
Cikin ruɗewa Zaina ta ce. "Ya Hash ɗin? bai sanar da ni ba."
"Ina ga baya so hankalinki ya tashi shi yasa bai sanar dake ba." Ado ya faɗa mata don kwantar da hankali.
Kai kawai ta ɗaga mishi, ta ɗauki jakarta tace. "Yaya zanje gida sai wani lokaci."
"Daga jin Hashim ba lafiya." Ya faɗa yana murmushi.
Kai ta iya girgiza mishi ta fita, ganin haka yace. "To ki gaishe da Inna zuwa gobe zan leƙo mu gaisa."
Ba ta iya bashi amsa ba, ta ciro wayarta jaka ta ƙira numbern Hashim yana ta ringing bai ɗauka ba, kawai sai ta fashe da kuka ji take kamar tayi tsuntsuwa ta sameshi ta ga halin da yake ciki.
Kwana biyu yau ba suyi waya ba, bai ƙirata ba ita kuma ba tayi tunanin ƙiranshi ba, Ya Hash ba lafiya amma ba ta da labari sai dai taji bakin wasu, me yake damunta ne haka.
A haka ta isa gida bayan ta tsaya ta share hawayenta.
Inna tana ganinta tace. "Lafiya kuwa, ko kunyi faɗa da Surayyar."
"A'a Inna lafiyansu lau." Zaina ta faɗa rai a dagule.
"To me ya same ki?" Inna ta ce tana tsareta.
Zaina kuka ta sanya ta ce."Inna Ya Hash ba lafiya amma ba wanda ya sanar ni hatta Yaya Tahiru."
Hararar Inna ta mata ta ce. "Au da ma shine ya sakaki kuka, to nima bani da labari sai ɗazu a bakin Tahiru, zazzaɓi yayi har ruwa aka saka mishi ya ce."
Kwanciya Zaina tayi taji ita ma zazzaɓin na neman rufeta, ta kasa magana ta ci gaba da ƙiran layinshi, ƙarshema aka ce mata a kashe.
Har dare Zaina tana gwada ƙiran layin Hashim a kashe, wanda kafin ta kwanta wani mugun ciwon kai ne ya kamata.
Ta shiga tashin hankali da ruɗanin rashin samunshi a waya. Ba ta iya runtsawa ba sai ɓarawon bacci da ya kwasheta.
Sukuku Zaina ta farka, har asuba ta gwada ƙiran numbern a kashe, bayan tayi breakfast da kosai ta ka sa shan koka da Inna ta dama, tasha magani ta koma ta kwanta Inna ta dubeta. "Ba za ki je makaranta ba ko ba ki dashi."
"Ina da shi kawai bana jin daɗi ne." Zaina ta faɗa daga kwancen da take.
"Tunda kinsha magani ki ɗaure ki tafi kar kiyi asara." Faɗin Inna.
Zaina ba ta so haka ba ta miƙe tayi wanka sama-sama ta fito, doguwar riga kawai ta saka sai hijabinta ta ɗauki jakarta tare da wayarta tama Inna sallama ta fita.
Adaidaita ta shiga ya kaita har makaranta, ta ba shi kuɗinshi ta sauƙa ta nufi department. Ji ta yi an ƙira sunanta ta baya, juyawa tayi ta ga Moses fuskarshi ɗauke da murmushi, ta amsa da ƙyar tana ƙoƙarin tafiya.
Ganin haka ya ce. "Are You okey?"
Kai ta ɗaga mishi tana ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta, ta wuce ciki.
Moses ya bita da kallo kafin ya koma motarshi don jiran fitowarta.
Kasa nutsuwa Zaina tai ta fahimci karatun, hakan yasa ta ɗauki excuse ta fita waje ta zauna ta ƙira numbern Hashim still a kashe, gaba ɗaya ta kasa sukuni ta shiga damuwa da zullumi.
Da taga zaman ba zai mata komai ba ya sakats tashi ta fita a department ɗinsu, tayi gurin Moses da ya hangota ya fito.
"Ka mayar da ni gida." Zaina tace da shi.
"Kun tashi ne?" Ya tambayeta da mamaki.
Kai ta ɗaga mishi, ta zagaya ta shiga motar. Shi ma ya shiga yaja suna barin gurin.
Lokaci zuwa lokaci yake dubanta. Ba ta ankara ba ya ɗaura yatsarshi saman hannunta yaji da zafi, ta kalleshi ta ɗauke hannunta. "Me haka? Bana so." Ta faɗa tana ɓata rai.
"Ba ki da lafiya ne da ma ba ki sanar dani ba." Ya faɗa da damuwa.
Har lokacin ranta a haɗe ta ce. "Lafiyata ƙalau, kar ka ƙara taɓa ni."
Shuru ya mata, ta ga ya canza hanya ta kalleshi ya rigata cewa. "Zamu je a duba min ke."
"Nace maka lafiyana ƙalau." Zainata faɗa mishi fuska a haɗe.
"Ban yarda ba sai na tabbatar." Ya ce yaci gaba da tafiya, haka har suka tsaya bakin pharmacy ya fito yace ta fito, ba ta so ba ta fito suka shiga ciki, ya sakata zama mai kula da gurin yazo yace. "Waye ba lafiya?"
"Ita ce ka duba min ita." Moses ya faɗa mishi yana nuna Zaina.
Kallon Zaina mai gurin yayi yace. "Me ke damunki?"
"Babu ciwon kai ne kawai." Zaina ta faɗa.
"Babu komai bayan shi."
Kai Zaina ta ɗaga. Ya miƙe ya haɗo mata tarukucen magunguna ya ba ta.
Moses ya biya suka fito suka shiga motarshi suna barin gurin. Bai tsaya bakin titin ba ya gangara har kofar gidansu, ba ta yi mamaki ba don ya taɓa zuwa.
Bayan ya parker motarshi, ya miƙa mata ledar magunguna yace.
"Ina miki fatan samun sauƙi, ki kula da kanki sosai sai gobe mun haɗu a school."
Kai kawai ta ɗaga mishi ta karɓa tana fita, ta wuce gida kafin yaja motarshi yana barin gurin.
Tafiya yake yana tunanin halin da ya barta. Baya jin zai iya daɗewa ko ɗaukan lokaci bai sanar da ita cewa sonta yake ba.
Keep liking and commenting ❤️
Pharty BB