Free chapter · Read without an account
Part 13
by Safiyya Haruna · Rumasa'u
RUMASA'U
BY SAFIYYA.
WATTPAD @Mrsjmoon.
Page 13.
"Ai gara da ka kora mana sokon banzan, dan Allah ya dawo d'akin nan saina fal-falla masa maruka."
"Kai Umma ke da Mahmudun ki, akejin kanku yau?"
"Wa! Ai tuni na sallama shi ya tafi can ya k'arata da rashin mutuncinsa, shi yasa kaga ko gidana ya daina zuwa dan baya son gaskiya, da ansoma yi masa nasiha ya juya gyeya ni kuwa bai isa ba dan ko Yusufa darajar Zuwaira ya ci har na zuba masa ido ya yi dik kan iskancinsa yagama batare da na tanka ba dan haka wannan tatsi-tsin bai isa ba kuma in bai dawo natsuwarsa ba ina daf da mik'asa gidan horo ba damuwata ba ce nasa a hukuntashi har sai yafi fulawa laushi."
"Kai Umma dan Allah ki daina tad'o da abinda ya zama tarihi, abinda tafi ki tsakaya kan Mahmud tunda ya fita zakka."
"To nabari Ahmadu ko dan d'iyar albarka Aminatu. Mahmudu na zaka ya fita ba tarihi ne ya ke mai-maita kansa."
"Wayyo Umma ki barri haka nan." Ya ambata cikin kallon Hajiya Aminatu wacce kanta ke sunkuye kafin Umman ta kuma magana ya d'ora "Kuma Allah Umma kune ba kwabinsa ta lalama yarda da zai saurareku sai kuga kun rabu lafiya da shi dan yana da fahimta."
"Ank'i a yimasa ta lallamin, kaga Ahmadu zan sab'a maka akan goyon bayan rashin gaskiya."
"Yawwa Umma gara dai da kika gano da kanki goyawa Mahmud baya ya ke a dik abinda ya keyi." Hajiya Aminatu ta ambata cikin saukewa mijin nata kallon dama ina cike da kai.
"Haka zamuyi da ke ko Madam?" Ya ambata a hankali.
Kama baki ta yi tana kallon Umma "Au Umma Mahmud d'in ne baijin magana sam, Dadyn Hamid ka d'ai ke iyawa da shi ni...
Kallon da Umma keyi mata yasa ta datse magana ta kulle baki tana dariya.
" Aminatu na Ahmadu har yanzu dai baku canjaba wurin kare juna."
Sai dik suka sauke kai k'asa cike da jin kunya.
"Allah ya yi muku albarka."
"Amin Umma." Suka amsa a tare.
"Wannan d'iya kuma da Allah yabaku, Allah ya tayaku rik'o."
"Amin."
"Shi kuma Mahmudu Allah ya shirya shi hankalinsa ya dawo jikinsa ya bar shaye-shaye nan babbar illace ga lafiyar bil Adam sannan hanyace ta zubewar mutunci."
"Amin ya Rabbi."
"Ahamdu ga RUMASA'U nan dan shi ne sabon sunar da na bata bisa amincewar Aminatu da fatan bamu shiga hakkinka ba wurin zartar da hukunci."
"Hakan ya yi Umma Allahu ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta ya yaye duhun dake baibaye da ita haske ya maye gurbinsa."
"Amin ya rabbil Alamin."
"Umma zo in kaiki gida ki huta."
"A'a kai Aminatu dai wacce lafiya bai wadaceta ba, zuwa dare sai Hafizu ya maida ni."
"To Umma. Madam taho mutafi kisha magani." Ya yi magana yana kallon Hajiya Aminatu.
"Ni fa ina tare da Umma, kaje ka tahomin dashi nan."
"A'a Aminatu bishi ku tafi inyaso gobe kya dawo, ga jikin ki nan ya soma zafi."
Ba dan taso ba ta wuce sai dan bata son yin musu da Umma.
"Hubby Allah da dare tare zamu dawo in kwana da d'iyarta." K'orafin da tasoma yi masa kenan bayan sun hau titi.
"Angama Dear sai dai kafin mu taho sai kin yi aikin lada kuma biyan bashi zakiyi, dan kin san kin tara carry over."
Gyeya ta juya masa ya janyo jelar kitsonta ta waigo da hanzari ya kyal-kyale da dariya.
"Dadyn Hamid cin zalin."
"Ke kika siyo da kud'inki."
"Uhm muje gida ka lalibo mana Hamid tun da akayi rasuwarnan bamu gaisa ba."
"Aikam d'azu munjima muna waya ya ce nan da sati biyu na nan tafe ya sami hutu mai tsayi, zaizo taya Momynsa jimamin rashin da akayi."
Murmushi ta sa ki cike da murta ta ce "Masha Allah, rabbi ya kawo shi lafiya."
"Amin. Kinsan sabida bai son jin muryan ki cikin damuwa ne yasa bai nemeki ya yi miki ta'aziyyar ba."
"Allah sarki yaron albarka, ai ni zan nemesa da mun koma gida dan na yi kewarsa ainun."
"Kin ganki da iya nuna bambanci, shi yasa Mahmud ke fushi da ku."
"Ya dad'e baiyi fushin ba, in yaso ya fashe k'arshen fushi kenan."
"Oh Aminatu sam kin kasa fidda damuwa akan lamuran Mahmud, anya bakya ganin hantarar da kike yimasa ke kuma sanyashi yin abinda bakya so?"
Shiru ta yi fuskanta a had'e ganin haka sai shima ya kame bakinsa.
"Hubby ina ganin a nemawa Mahmud wata school a waje." Ta katse shirun.
Kallomta ya yi kad'an ya cigaba da deriving kamar ba zaiyi magana ba zuwa can ya ce "Yau da kanki kike ambatan hakan? Ba cin kin haka yin hakan a baya."
"Wannan ma na dole ne."
"Me ke faruwa Haskena?"
"Nothing but ban son zamansa tare da Rumasa'u sabida na hango tsanarta a idanunsa, ina tsoron haukansa ta motsa ya halaka baiwar Allah dan kasan ba tsorona y keji, to gara ya bar k'asar har zuwa lokacin da komi zai dai-daita."
"No ki daina raya bad things irin haka akan Mahmud kawai kiyi ta addu'a insha Allah ba a binda zai faru sai khairan."
"Allah yaso hakan."
"Amin, Amma hak'ik'a Mahmud bazai tafi ko ina ba domin ina son gina rayuwar sa fiye dana Hamid, insha Allah da ya kammala service zan dank'a masa shugaba cin company ina ga in yaga nauyin wasu ya hau kansa zai natsu tunda fad'a da nasiha sun gazayi masa komi."
"Bana bayanka akan wanna k'udirin amma in ka dage akai sai na ce Allah ya taimaka."
"Ami. Domin na sanar masa kuma insha Allah wannan sanadin zai samar da natsuwarsa, tunda ya nace yana son kammala karatun sa na tabbata burin yin aiki ne a ransa."
"To." Ta furta a tak'aice, ganin ta d'auke wuta yasoma lalibo labarai masu sanya nishad'i yana bata tun tana sharewa har ta sa ki suka cigaba da hira cike da farin ciki. Da dare bayan isha'i suka koma asibitin. Alhaji Ahmad yana tare da su sai k'arfe shad'aya ya baro su ya dawo gida wanda har lokacin Mahmud bai dawo ba samun kansa ya yi da kasa kwanciya ya dawo bakin volcany ya tsaya yana tsimayen dawowar nasa zuwa can ya lalibi number Hafiz suka soma tattaumawa akan cigaban da masana'antar shi ke kan samu. K'arfe d'ayan dare dai-dai ya shigo ta k'aramin gate batare da motarsa ba bayan ya kulle k'ofar ya nufo ciki, tamkar mara gaskiya haka ya ke tafiya cikin sand'a sai da ga zo daf da k'ofar part d'in su Alhaji Ahmad ya yi gyaran murya aikam wani zabura da ya yi ya wuntsila ya fad'i tim ya k'walla ihu jikinsa na rawa fad'i ya ke "Natuba iblis wallahi ban k'ara yin dare, wayyo jama'a akawo d'auki na yi gamo da shed'anu jinin iblisai!."
Dik yarda Alhaji Ahmad yaso gintse dariyar ya kasa. Jiyo dariyarsa Mahmud ya yi tsit tare da tashi da sauri ya isa wurinsa ya rungume shi.
"Dan Allah Dady yimin add'u,a karanto min suratul Jinn da Rahman har ma da Bak'ara dik had'a gudun kada su shigeni na haukace dan ance haukan namiji bai da kyau, yafi na mata muni."
Dariya sosai Dady ke yi mai gadi na tayashi domin ihun Mahmud ya tasoshi.
"Kai natsu banson shirman banza, na wani gamo da kayi."
"To Dady na natsu soma karatun, na soma jin kaina na yamutsa."
Kallon mai gadi Alhaji Ahmad ya yi cike fushi ya nunasa "Malam Ayuba kada ka sa ke barinmin gida a bud'e dik inda k'arfe shad'aya zuwa shabiyu ya yi ka kulle k'ofofi dika, kai a kullum na ke buk'atan samunsu kulle din wanda zai shigo sai yanemi izini sannan banda bawa sha-shan abokanan Mahmud damar shigowa da fatan ka fahimce ni."
"Eh, Alhaji dama Yallab'ai Mahmudu ne yakemin fad'ar baison ina kulle masa k'ofa, shi yasa na ke barin k'aramin a bud'e in ya shigo sai na kulle."
"Daga yau na soke barin k'ofar a bude kuma dik wanda ya wuce shad'aya a waje ko da kuwa ni da kai na ne ka da abud'e min."
"Angama Alhaji insha Allah hakan za'ayi, Allah dai ya k'ara girma."
"Amin, yi tafiyarka Malam Ayuba, mu kwana lafiya."
"To Alhaji."
"Kai kuma wuce ka kwanta."
"Tsoro na keji Dady kabarni na kwana a d'akin Momy."
"Kai bansan shirme wuce ka tafi ka kwanta ko in sab'a maka."
"Allah bazan iya kwana ni kad'ai ba."
"Ikon Allah ashe kai d'in ba jarima ba ne?."
"Ai dama Dady ni da mace bambancin suna ne kawai ke tsakaninmu."
Harara Dadyn ya watsa masa amma cikin ransa dariya ce ke cinsa.
"Please ka taimakeni na kwana tare da kai na yau kad'ai kafin gari ya waye ayimin rukiyya dan na tabbata banrasa tsarabar aljannu a tare da ni."
"Oh ni Ahmadu nagama ganin abinda ya isheni yau, kaga illar da shaye-shaye ke janyowa kenan mai da k'aramin abu babba mutum yarik'ayi dabi'ar tankar na mahaukata, yanzu wannan abin kunyar da kakeyi meye amfani sa, ka koma sakaran k'arfi da yaji."
Ko a jikinsa saima k'ara shigewa Alhaji ya keyi yana cewa "Wallahi kam Dady lamarin sai an had'a da saukan Qur'ani dan jin jikina na keyi a sa ke kamar ana zaremin b'argon cikin k'ashina."
"Kai Dalla shige muje ban san haukan banza."
Da sauri ya wuce Dady ya shige parlourn yana dariya "Thank you my Dad." Ya ambata kamar mara hankali.
"Shiga kayi wanka kazo muji inda ka je kayo uban daren nan."
"Ai wannan simple explanation ne Dady just club na lek'a amma wallahi banyi komi na d'aukan zunubi ba dan ko sigari ban sha ba." Yana gama fad'a ya shige bedroom da sauri. Girgiza kai Alhaji Ahmad ya yi ya mik'e zuwa bedroom d'in Hajiya Aminatu ya kulle, jallabiyar jikinsa ya cire ya haye gadon cike da tarin gajiya ba jimawa barci ya yi gaba da shi.
Washe gari misalin k'arfe 8:30am Alhaji Ahmad yafito rik'e da basket shak'e da kulolin abinci wanda ya girka da kansa domin ya iya girki masu ban sha'awa ga d'and'ano tamkar wanda ya ziyarci catering school. Yana ajiye kayan a back seat ya tsinkayi sallama a gefensa, juyowa ya yi ganin Muhsin ne sai ya mik'a masa hannu yana cewa "Kai ne tafe a bazata Malam Muhsin?".
"Eh Alhaji, dama na kawo maka d'an uwana Abid ne abisa alk'awarin danayi maka kwanaki."
"Ayya ai ina ganin mubar zancen tunda ka tabbatar bashi ya aikata ba."
"A'a Alhaji dik da na aminta bashi ya aikata ba amma ina da alamar tambaya akansa sabida yana tarayya da abokan banza, ina son ka tuhumeshi cikin siyasa wata k'ila ba zai rasa sanin wanda ya aikata ba cikin abokansa."
"Tam shi kenan yanzu asibiti zani anjima mu had'u a office."
"Tam shi kenan muma bari mu bika muga ya jikin nata dan jiya da naje d'aukan Umma bansamu na shiga ba."
"Ok ku muje d'in."
Yana gaba suna biye da shi. Dik tambayoyin da Abid ke jerawa Muhsin akan dalilin da yasa ya d'aukosa zuwa gidan Alhaji Ahmad bai samu amsaba har ya gaji ya kame bakinsa cike da takaicin shareshin da ya yi.
Suna isa asibitin Muhsin ya fito da sauri ya amshi kwandon hannun Alhaji Ahmad suka jera zuwa ciki ya yin da Abid ya gyara zama cikin mota ya rakasu da idanu har suka b'acewa ganinsa. Tsaki ya ja yafito ya jingina da mota yana mai gyara zaman bak'in gilashin idonsa tare da k'arewa nurses da ke kaikawo a haranar wurin kallo.
*Mrs j moon.*