Free chapter · Read without an account

5&6

by Babybintuu · WAYE SANADI!? PART TWO

🌺🌺 *WAYE SANADI..!?* 🪦🪦

        *PART TWO*


           *Story & Written*

                 *By*

            *Oum Sumayya*

              #Babybintuu



BINTU KITCHEN AND INCENSE*


*Ina kuke ma'abota son k'awata girke girke da sinadaran girki masu k'amshi da sa dad'in girki uwar gida kai harda amarya kuna ina ku masto kusa ku mallaki Bintu curry powder ingantaccen sinadarin girki mai sa girki k'amshi da dad'i curry powder mu yasamu had'i na musamman daga ingantattun kayan k'amshi masu sanya girki d'and'ano har lau Bintu curry powder basu tsaya anan ba sun kawo muku had'add'en yaji dayaji kayan k'amshi mai k'ara lafiya ajiki dakuma had'in daddawa mai sanya miya k'amshi da sa oga santi muna da kitchen ingredients kamar haka*


Curry powder

Garin citta kanin fari dan lipton

Hadd'd'en yaji mai kayan k'amshi 

Had'add'en yaji mai tafarnuwa

Had'add'iyar daddawa mai kayan k'amshi

Duka akan farashi mai sau'ki muna turawa ko ina afad'in arewacin nigeria kayan ki su iso cikin salama uwargida amarya maza ku hanzarta siyan *Bintu kitchen ingredients* sai angwada akan san na kwarai! Zaku iya tuntu'bar mu akan wannannumber ***


*abun bai k'are haka ba akwai ingantattun turarukan mu masu sanyin k'amshi da dad'i munada turaruruka kamar haka*



Farar humra

Ba'kar humra

Ja humra

Kulacca

Humra ta fuska

Turaren wuta na kaya

Turaren wuta na jiki

Turaren wuta na tsugunno mai matse mace taciki da waje 


*Kuna ina amarya uwar gida kai harda y'an mata ma don k'amshi shine mace muna saida d'aya d'aya muna bada sari akan farashi mai sau'ki uwargida amarya karku bari abaku labari zaku iya tuntu'ban mu akan wannan number *** koda kud'in ka saida rabon ka*




*PAGE FIVE AND SIX*




Ahankali take bud'e idanun ta da sukai mata mugun nauyi dishi dishi tafara gani kafun dasauri tamaida ta kulle saka makon ganin haske bau a idanun ta k'ok'arin motsawa tafara taji muryan wani yana fad'in "she's wake up go and call Dr"

Dasauri tasake k'ok'arin bud'e idanun ahankali tana k'are ma wajen kallo bataga kowa ba hannunta tafara k'ok'arin motsawa taji kamr ad'aure ga wani mugun zafi dasauri takalli hannun bandage tagani da y'ar siririyar igiya, igiyar tabi da kallo har kan d'an k'arfen da ruwa ke sak'ele yana d'iga zuwa jikinta "hos....pital" tafurta ahankali kamar me koyan magana dasauri tawani zabura tana zare idanu tunawa da abunda yafaru daidai nan Dr da nurse biyu mata suka shigo sai wasu mutane uku masu k'irar samudawa dake sanye da kayan sojoji dukkanin su rik'e da gun fuskokinnan kamar an aiko musu da mutuwa kowanne amurtuke, 

Jikinta ne yafara tsuma bakinta na wani irin makyarkyata take kallon su cike da fargaba da tsoron abunda zaije yadawo tace afisge "where's my husband and my ilow innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dr waye yakawo ni nan? Ina mijina meya same shi? Karkuce min naras shi" Tayi maganar tana wani irin sauka agadon kamar zata kife k'asa jikin ta sai b'ari yake, 

Dasauri nurse d'in suka rik'eta ganin cannula yafuta jini yayi tsartuwa yana d'iga ak'asan tiles d'in cikin lallashi d'aya daga cikin nurse d'in tace "so sorry Madam be careful jikin ki babu k'wari kinji calm down please" tayi maganan suna k'ok'arin maida ta gadon

Cikin wani irin numfashin tsoro da tashin hankali tace "i said again where's my husband and my ilow too"

Cikin wani tsawa d'aya daga cikin sojojin yace cikin hausar shi da bata futa Shegae azzalumi bayan ka bashi poising ne zaka zo kana mana shouting this will be the last time idan ba haka ba i will short you d'an banza kawai duk son da oga yanuna maka saida kayi k'ok'arin kashe shi butulu"

Wani irin sauti cikin ta yabada k'uuuu dasauri tarik'e cikin nata jikin ta na wani irin kyarma tafurta "nooooooo......" Sai kuma numfashin ta yad'auke lokaci d'aya jikinta yawani saki kamar gawa, 

Cikin azama likitan ya k'araso yabasu umarni dasu maida ta gadon su kwantar kafun yajuyo ga sojojin cikin harshen turanci yace musu "Please sir wai......" Dasauri suka d'aga mai hannu suka juya suka bar room d'in, 

Juyowa yayi yaba ma nurse umarnin takawo mai wasu injection kafun yaduk'ufa akanta cikin k'ank'anin lokaci yashiga bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah numfashin ta yadaidaita ajiyar zuciya yasaki yana share zufan fuskan shi yamata wasu injection acikin drip sannan yafuta daga room d'in. da mamaki nake kallon harabar d'akin ganin sojoji sama da goma kowanne da bindiga arataye a wuyan shi nace lallai akwai wata kitimurmurar acikin hospital d'in nan.


Cikin tsananin b'acin rai Aunty Saudat ke kai kawo acikin room d'in idanun ta k'ur akan Dija dake ta sharb'ar kuka cike da nadama tace "Dan Allah Mom kiyi hak'uri wallahi ban san abun zaikai haka ba shiyasa ni yanzu shike nan da zaran yafarfad'o kashina yabushe kenan dan nasan kashe ni za'ai dan Allah Mom kitaimaka min nabar k'asar nan ban son inmutu yanzu ban shirya mutuwa ba kitaimaka min dan Allah" tak'arisa maganar wani sabon kukan na kubce mata cikin rashin sanin madafa, 

Wani irin iska Mom taja ta fesar dawani irin zazzafan huci cikin b'acin rai tace "Khadi bansan baki da hankali ba sai yanzu ban san cewar nono na dakika sha kin furzar ba sai yau meyasa kike abu babu shawara meyasa zaki jefa rayuwar mu cikin garari why ni dakin gaya min abunda yafaru tun adaren kece da tuni munbar Nigeria inata murna taimusu muguwar sakayya ashe ba ita bace kece yanzu to gaya min yakikeso ayi alhalin yanxu muma suspect ne kina ganin sojojin da aka zuba abakin ko ina na part d'in nan alamun babu sauk'i gaya min yazamuyi yanzu eye?"

Tayi maganar tana share zufan fuskanta hankalin ta duk atashe dan tunda Dija tagaya mata itace tasa poising a coffee d'in tad'auka Haulat d'inne zata sha sai reshe yajuye da mujiya hankalinta inyayi dubu to atashe yake kimanin kwanaki hud'u kenan da faruwar abun amma kodaidai da parking lot anhanasu futa ance babu wanda zaifuta agidan sakamakon binciken da akeyi hatta da wayoyin su duk ank'wace hakan bak'aramin tayar musu da hankali yayi ba window tasake lek'ewa tana k'ara kallon sojojin dake zagaye akowani lungu da sak'a na gidan fuskokin su sam babu imani sakin labulen windon tayi cike da tunanin mafita dan tana tsananin son Dija bazata so rayuwarta yak'are akurkuba sake kallon ta tayi akaro na barkatai kafun tazauna gefen gadon tabuga uban tagumi tana dana sanin turo Dija gidan gashi komai ya lalace mata.



Ahankali Dr daya shiga operation d'in yad'an zame mask d'in dake fuskan shi yakalli d'ayan Dr d'in bayan sun fito yace "Nice to meet you Dr" yayi maganar yana ba d'ayan hannu, 

Gaisawa sukai cikin murmushi yace "thank you sir" rabuwa sukai kowa yakama hanyar office d'in shi yayin da wasu nurse maza suk gunguro Hamza kamar gawa akan wani gado zuwa d'akin hutu numfashin daya keyine kawai ke tabbatar da rayuwar shi wani had'add'en room dabaiyi kama da amenity ba aka kaishi aka d'orashi akan gadon room d'in sannan nurse d'in suka futa akabar sojoji biyu acikin room d'in, 

Dr ne yashigo yasake yimai allura acikin ruwan da ake k'ara mai sannan yafuta yashiga d'akin da Momma take itama yazuba ruwan alluran acikin ruwan sannan yafito yakoma office yazauna yana y'an rubuce rubuce.

Many'an jeep bak'ak'e guda uku da motan sojojo guda biyar ne suka shigo asbitin da mugun gudu yayin da gaba d'aya jiniya ke tashi acikin asbitin tako ina ka kalla sojojine ke kai kawo kafun motocin su parker awajen adana motoci sojojin suka futo dagudu wasu suka shiga hospital d'in wasu suka tsaya awaje bud'e mai motar akayi kusan mintuna uku kafun yafito yana sanye da kakin sojoji babban mutum ne sosai dan zaikai sheka hamsin aduniya kakkaurane bak'i cikin isa yake takawa yana kallon kaiwa da kawowar sojoji acikin reception d'in tafiya yake yana sake studying hospital d'in har zuwa office d'in Dr d'in batare da knocking ba yashiga kanshi tsaye likitan na ganin shi yamik'e gamida sara mai shima d'an k'amewa yayi kafin yacema Dr d'in batare daya zauna ba cikin harshen nasara "nazo duba general ne zan iya ganin shi kuwa?"

Cikin girmamawa Dr yace

"Yes you can't follow me" yayi maganar yana futa daga office d'in shima yamara mai baya kallon Hamza yake cike da tausayi ganin yanda na'ura ke zagaye dashi g oxygen ahankali yakad'a kai yace "ina d'ayar da suka sha guban tare?" 

Batare dayasake magana ba Dr d'in yafuta shima yasake mara mai baya duba Momma yayi itam yafito suka sake komawa office d'in bayan sun zauna ne yakalli Dr d'in yace "yanzu awani condition suke ciki?"

Ajiyar zuciya Dr yasaki yace "they are all safe insha Allah domin anyi operation d'in cikin sa'a ankwashe gubar dan batai ma kayan cikin su lahani ba daga yanxu zuwa kowani lokaci zasu iya farkawa"

Kaii yad'an jinjina kafun yamik'e yace "that's good Dr all the best nizan tafi daga zarar yafarka kakirani kasanar min"

"Okay sir but another patient da ake zargi she's unconscious"

"Ayya sorry she's general wife but yanxu zargin mu ba'a kanta yake ba duk da itama tana under suspect ne muna nan muna kan bincike ta CCTV cameras na gidan insha Allah komai zai warware bara na dubata anjima Salimat zata zo wajen ta Allah yabasu lafiya"

Da amin Dr ya amsa suka futa zuwa d'akin da Haulat take yaduba ta kafun yatafi.

Cikin kwanakin sosai take yawan munanan mafarkai akan Haulat hakan yasa take yawan kiran ta amma shiru no answer tswon kwanaki hud'u kenan sosai tashiga damuwa hakan yasa takira Salma domin ta tambaye ta kosuna waya nan fa taji itama tana hospital tana labor cikin azama tatafi asbitin inda kafun ma takaii asbitin nasarawa Salma tahaifi d'anta namiji tana keke napep Sulaiman yakira yake shaida mata itakuma ta kira kawu ta sanar mishi inda sukaima juna barka koda ta isa asbitin har ankai Salma d'akin hutu ga Sulaiman da Fatima sai mahaifiyar su fuskokin su duk awashe nan sukaima juna barka tad'auki jariri tubarkalla dashi tana mai tsiya Fatima na fad'in kodai yamata ne bata son tabaada kud'in toshi shine take d'an waken zagaye, Mama tayi dariya tana fad'in "A'a mezan yi da wannan abun fuska jawur kamar k'osai akai kasuwa saidai in hajiya nikam badani ba" nan dai suka dinga barkwanci kafun Dr yazo yasake dubasu ganin babu wata matsala ne yasa yasallame su, 

Gaba d'aya tare suka taho inda mahaifiyar Sulaiman tabashi umarnin daya wuce dasu gidan Mama zaiyi musu tad'aga mai hannu dole yajuya kan motar zuwa gwammaja badan ranshi yaso ba, 

Sosai hakan yama Mama dad'i domin harta fara tunanin ya wankan Salma xai kasance dan taga sirikarta y'ar boko ce da wuya tagasa ta yanda yakamata 😂😱

Koda suka isa gidan sosai Fatima data jima rabonta da gidan tayi mamakin canzawar sa gida yasha get ga interlock tundaga bakin get har zuwa cikin gidan bata sake mamaki ba saida suka shiga parlour taga wasu had'add'un royal cushion ga k'amshi sai tashi keyi komai neet ga mai aiki sai kai kawo take sosai tayi mamakin sauyin da gidan yasamu kamar bashi ba, 

Bayan sun zauna ne sun huta Mom d'in Sulaiman tace yamaida ta gida tunda taga Fatima bata da niyyar tafiya sai snapping suke ita da jariri masu shigowa barka ma dak'yar take basu, 

Sosai Mama tama Mom d'in Sulaiman godiya da karamcin data nuna mata takuma rakasu har bakin mota Sulaiman dai fuska acunkushe dan ba haka yaso ba kawai anhanashi jin d'umin Babyn shi da matar shi gashi yana matuk'ar jin kunyar Mama balle yadinga zarya damaa Mom d'in shine sallama yama Mama kan zai dawo anjima yakawo sauran kayan Salma dana baby, 

Saida Mama tad'an natsu ne mutane sunyi sauk'i Fatima ma taje gida kwaso kayanta sai anyi suna zata koma acewar ta Mama takalli Salma tace "Wai kunyi waya da y'ar uwarki kuwa acikin kwanakin nan?"

Wani irin bugawa zuciyar Salma yayi batare da tasan dalili ba tabud'e baki da niyyar yin magana sukaji sallaman Ammi..........✍🏼





Don't forged to

Share it fisabilillah

Comments, vote and

Follow me



#Babybintuu on wattpad

#Babubintu on arewabooks

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol