Free chapter · Read without an account
Page 9-10
by autararewa101 · ZAFIN KISHI
ZAFIN KISHI
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI .
PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣
📝Da asubar farko ta farka zame jikinta tayi zuwa dakinta.alwala tayi kafin ta tayar da sallah.shiko saida aka tada kabbara kafin ya tashi da a gaggauce yayi alwala kafin ya nufi dakin su Ahmed.taddawa yayi mai aikin ta tayar da su sunyi alwala,Dan haka ya kama hannun su suka nufi masallacin cikin unguwar.zulaihat tana idarwa kitchen ta shiga dan hada kayan breakfast.karfe bakwai aka tafi da su Ahmed islamiyya.shiko yahau Shirin office kasancewar ranar laraba ne.yana gyara maballin riganshi ta shigo dakin cikin kwalliyar kananun Kaya wandon jiens da shet mai dogon hannu,sai Dan siririn mayafi data dora bisa kanta.karasa saka mai maballin tayi tana murmushi shima mayar mata yayi Yana kollan cikin idonta.hannunshi ta kama zuwa falo akan dinning area ta zaunar da shi tana zuba mai breakfast.kallonta kawai yake yi ganin yadda ta Kara kyau,shi harga Allah Banda larura mezai saka shi neman matan waje?Amma Yana Addu'ar Allah yasa ta daina halinta.baisan ta gama zubawa ba saida ya ji tana hura mai iskar bakinta a idonshi kafin ya dawo tunanin shi.da haka suka fara cin abincin harya karasa.ganin har karfe tara ta kusa.har bakin motar shi ta rako shi saida ta tabbatar ya fita kafin ta daina daga mai hannu ta wuce cikin gidan.
Shiko A S P Habib derect gidan Mama ya nufa, kasancewar bayan layin su ne yasa dandanan ya karasa.shiru ya ji gidan ganin Bata a falonta yasaka shi karasawa a kuryar dakin ya risketa Kan abin sallah ga kayan fruits a gaban ta.
"Assalamu Alaikum"cewar A S P Habib Yana karasawa kusa da ita.
A hankali ta juyo tana amsa sallamar ganin shi ne yasa ta ce "Habibu harka fito?"
"Eh Mama na fito,Ina kwana?"
"Lafiya Lau,ya iyalin naaku?"
"Duk suna lafiya,yaran sun tafi isalamiyya".
"To Masha Allah,Ina maganar da muka yi da Kai?"
Dan Kara sadda kanshi yayi,Yana jin faduwar gaba dan ya rasa amsar da zai bata.
"Da Kai nake Habibu ko banida amsa ne?"
"A a Mama Allah ya huci zuciyar ki,kidan karaman lokaci insha Allah a wannan karon baza'a sake samun matsala ba,zanyi kokarin ganin kin samu duk abinda kike so daga gareni"
"To Bari kaji na fadama wannan shi ne dama na karshe da zan baka idan ko ba haka ba zaka Sha mamakin hukuncin da zan dauka akan ka"tana cire glass din dake fuskarta.
Wata zufa ce ya ji ta karyo mai,hannun shi ya saka Yana gogewa cikin sanyi ya ce "insha Allah komai zai wuce,ki Kara hakuri ni kaina bana jin dadin abinda Zulaihat take aikatawa,Amma Insha Allah a wannan karon zan Bata mamaki"mikewa yayi "Bari na wuce office,idan akwai abinda kuke da bukata anjima da yamma zan dawo,saina taho maku da shi"
"A a muna da komai sai danyun kayan Miya da suka rage,Dan Naga kaman sun kusa karewa"cewar mama tana saka ayaba a bakinta.
"Tau zan kawo insha Allah"Yana fita daga gidan.a daidai bakin kofa ya gamu da Asabe mai yiwa mamanshi aiki.cikin girmamawa ta gaishe shi kafin ya fice daga gidan.
Office ya wuce har kusan karfe ukku Yana can kafin ya nufi gidan su Habiba Dan Kara duba jikinta,sannan ya tattauna da Babanta.
Bayan ya fita Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin tausayin danta Yana Kara ratsa jikinta,Dan ta fahimci kullin matsalar matar shi karuwa take yi ba raguwa ba.ga shi duk lokacin da yayi yunkurin Kara aure sai a samu matsala.karo ukku kenan ana saka ranar bikin shi ana fasawa.Daya yarinyar ta ce bata sanshi tun ana sauran sati biyu,saboda sunji labarin matar shi ta mallake shi sai abinda ta ce mai,ta biyun kuwa kawai an wayi gari ta rasa Wanda har yau an rasa sanadin mutuwar ta.duk iya binciken likitoci sun kasa ganowa,Dan Babu wani rauni ko wata alama da zata nuna kasheta akayi.hakan yasa suka hakura.cikon ta ukkun kuwa har saida aka saka Rana Diyar kanen Mama ce da yake a unguwar dosa,Bayan saka Rana da wata daya yarinyar kwatsam ciwon hauka ya sameta,Wanda tun daga lokacin ake faman neman magani har yaunzu ba'a dace ba.tun daga nan Mama take zargin akwai saka hannun matar shi a cikin wannan al'amarin.shiyasa ta dage da yimai addu'a,ta Kuma tsaye akan saiya Kara aure.Danta fahimci matar shi tana wahalar da shi,Kuma ta hana ya Kara aure.ajiyar zuciya ta Kara saukewa a karo na ba adadi tana goge hawayen da ta ji suna zubomata.dan ita abinda yafi bata takaici yadda Zulaihat ta rainata kwata-kwata bata girmamata,Dan ita a ganinta itace take saka Habibu Kara aure.ita ko wannan dalilin yasa ta kafe akan saiya Kara auren danta ga yadda zatayi da ita.da haka Asabe ta risketa tana wannan tunanin kayan break ta aje Mata kafin ta juya tana girgiza kanta.
Tun bayan fitar Habib daga gida zulaihat itama ta fita,sai yanzu karfe ukku take dawowa,Wanda ni kaina bansan inda taje ba.
A S P Habib kuwa gidan su Habiba ya wuce.a kofar gida ya iske Malam mahaifinta.wurin shi ya karasa a bisa tabarma cikin girmamawa suka gaisa "yaro ban wayeka ba dukda na ganka da Kaya irin na jami'an tsaro Allah yasa lafiya"cewar malam musa Yana sauraren shi Dan jin amsar da zai bashi.
"Eh Baba baka sanni ba,nine Wanda ranar na kawo Habiba.wallahi bisa tsautsayi na kadeta inata sauri Naga na koma gida.to a lokacin Dana zo Innajo taceman kana kasuwa,shiyasa na Kara dawowa Dan ganin ya jikin nata yake?"cewar A S P Habib Yana kar tonkwashe kafar shi.
"To to Alhamdlillah kwarai Habiba tayiman bayani,ba komai shi tsautsayi ai baya wuce ranar shi haka Allah ya kaddara saidai muyi fatan Allah ya kiyaye gaba.inji Malam.
"To nagode Baba Bari na karasa gida insha Allah zan Kara zagayowa"Yana mikewa tsaye.kudi ta ajemai kafin sukayi sallama ya wuce dukda dakyar ya amsa.
Zulaihat ce a kitchen tana ta kokarin ganin ta kammala girki kafin mai gidan nata ya Kara so.dan tasan yanzu Yana Kan hanya.a hankali ta kaga kular data zuba Miya a ciki wani kulli ne ta dauko daga cikin wata loka,koncewa tayi kafin ta barbada Dan kadan tana juya miyar sa spoon .kafin ta rufe tana mayar da maganin wurin data dauko shi.
A gajiye ya shigo gidan Dan haka da sauri ya dauki kayan shi Yana shiga cikin gidan.ko sallama baiyi ba jin motsi a kitchen yasaka shi bin hanyar abinda idon shi ya hango yasaka shi saurin komawa da baya Yana jin jiri Yana daukar shi.
Ita ko zulaihat ji tashi kaman hucin mutum a bayanta da sauri ta nufo jikin kofa ganin shi tayi dafe da kanshi Yana Jan numfashi.cikin bakinciki ya fara nunata da yatsa Yana cewa .............
By
AUTAR AREWA
✍️✍️✍️✍️✍️.