Free chapter · Read without an account

Free page

by Zainab410 Zainab410 · Maraicina!

🔥🔥🔥🔥🔥


MARAICINA!


🔥🔥🔥



Labari

Da

Rubutawa


Zainab Ibraheem

🌹Momy



🔔📚

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

***

*⚜️©J.A.W📚🖌️*



_WANNAN LITTAFEN NA KU'Di NE Ki BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI_






🆓 page 7&8



Kiran da Baba ta k'wallamin ne yasa na d'auko "Yar bagen kayana da sauri nafito. duk'awa nayi a gaban su tare da sunkuyar da kaina k'asa wasu hawaye masu zafi kebin kuncina. Baba ta ce "Toh Laraba ga ta nan dan Allah ki samu inda za'ayi biya mai kyau kowane irin aiki ne zatayi. kallo na Labara tayi "Ta ce kiyi hak'uri wannan aikin ba ke kadai ce keyi ba akwai "Yan mata irin ki da yawa. Talatu ce tayi caraf "Ta ce karma ta hak'ura idan aka kai ta ta dawo. "Nima dai shi nagani cewar Baba, murmushi Laraba tayi tare da "Cewa ai duk bazata kai haka ba, " Bara dai mutafi kar dare ya yi mana a hanya, tashi ta yi "Ta ce to sai kun jini zuwa jibi insha Allah. "Suka amsa da Allah ya kaimu, tashi na yi nabi bayan ta. muna fita suka fashe da dariya da tafa hannu tare da "Fad'in mun yada d'an Mangwaro mun huta da k'uda.....




Tun da muka kama hanya nake kuka dagani har Laraba ba wan da ke magana ganin kukan nawa ya yi yawa ne ya sa "Ta ce kiyi hak'uri wannan aikin zakaje insha Allah zai zamemiki alkairi ki kwantar da hankalin ki zan nema miki gidan da bazaki samu matsala ba. shiru nayi da kukan da nake har muka iso tashar da zamu shiga mota batare da na tan kata ba. ruwa ta siyo guda biyu kallona ta yi cike da tausayi "Ta ce amshi ga ruwa kisha ko zuciyar ki zatayi sanyi, amsa nayi cikin disasshiyar muryata da ko fita batayi sosai saboda kuka "Na ce nagode, ba komai "Ta ce tare da cewa ya sunan ki, "Aisha na ce da ita, daganan ba wan da ya koma magana har motar mu ta tashi.ina kallo har muka fita garin mu a zuciyata "Na ce shikenan yanzu sun rabani da garin mu mahaifata, munyi tafiya mai nisa kafin muka iso inda za'a sauke mu Laraba ce "Ta ce ya isa bayan mun fita. adaidaita ta tsayar muka shiga nidai banji ina ta ce a kaimu ba shiga mukayi bamuyi tafiya sosai ba muka iso k'ofar wani had'add'en gida tun a waje zaka san gidan ya amsa sunan sa..




K'wan k'wasawa tayi wani soja ne yazo ya bud'e kad'an kallon Laraba ya yi sannan ya mai da kallon shi gareni ganin yasan Laraba ne yasa ya bud'e mana. shiga mukayi tana gaba ina binta a baya kalle kalle kawai nake a zuciyata "Na ce anya ko ba siyar dani sukayi ba. wata k'ofa mukazo "Yar ma dai-daiciya amma tsayawa mukayi Labara ta k'wan k'wasa wani mutum ne yazo ya bud'e mana muka shiga, ni dai sai kalle kalle nake amma a b'angaren zuciyata kuma cike nake da tsoron kar dai ace siyar dani suka.....



Ban gara tsurewa ba sai da muka shiga wani Babban palour. yanzu ne nadawo asalin bak'auya dan duk kallon da nayi a waje ashe banga komai ba sai yauzu nake kallo. wani k'aton palour ne da kujeri sat biyu da wani kafit a tsiyar shi idan ka taka kamar ka taka katifa a gefa ga matakaiyan da zaka taka kayi sama. idan "Na ce nafad'a muku tsaruwar gidan to wan nan page bazai d'auka ba amma ku tsara a zuciyar ku....



Wata "Yar budurwa ce tafito ta wata k'ofa "Ta ce sannun ku ku zauna dan Allah hajiya na sama kubari a kira ta.. k'ofar da tafita ta koma sai gata d'auke da kaya nik'i_nik'i zuwa ta yi ta ajiye a gaban mu tare da bud'e tiren. abinci ne mai rai da lafiya gefe d'aya kuma kayan marmari ne kala_kala komawa tayi ta d'auko ruwa ta kawo mana san nan ta taka saman bata jima ba ta dawo "Ta ce tana zuwa wata k'ofa naga tabi.....



Laraba ce ta sauko k'asa ta zubamin abincin amsa nayi nafaraci hannu baka hannu k'warya dama yunwa nakeji rabona da abincin tun safe wani irin dad'i abincin yayi har na cinye batare da nasani ba sai naje d'iba naji wayam ruwa nasha. san nan Laraba ta k'aramin da kayan marmarin suma sai da naci sosai san nan naji nak'oshi hamdalah nayi a zuciyata ina tunanin yau she rabon naci abinci nokashi sai yau, Laraba ma abincin ta ci da kayan marmarin san nan ta koma kan kujera. yariyar d'azun tazo ta kwashe kayan ta mayar san nan ta k'ara goge wurin ta koma k'ofar danake tunanin d'aki ne.......




muna nan zau ne wata matashiyar mata da bazata gaza shekaru hamsim ba a duniya ta fito cikin shiga ta k'asaita da aji daka ganta kasan hutu da jindadi sun zauna sau kowa tayi d'auke da murmushi a fuskar ta suka gaisa da Laraba bayan sun gama gaisawa. "Ni ma na gaida ta "amsawa tayi cike da fara'ar ta "Ta ce Labara kinsa mu yarinyar kenan, "Eh Hajiya nasamu itama d'in da k'yar ta yar da. kallona Hajiyar tayi tare da "Fad'in ya sunan ki, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da ya tsun hannu na "Na ce Aisha, Masha Allah " Ashe dai babban suna ne da ke, kallon Laraba ta yi "Ta ce Laraba ya zamuyi dake nawa kike ganin zan biya ta?.



shiru Laraba ta yi san nan "Ta ce to hajiya gata nan dai duk abin da kikaga zaki iya bata shikenan.. "Toh shikenan zan bata dubu hamsin duk wata, cike da murna Labara tafara godiya sannan "Ta ce amma kud'i iyayen ta za'a ringa bawa duk wata, nan ma hajiya "Ta ce ba matsala ai "Ni ma godiya nayi duk da bani zanci kud'in ba. tashi hajiya tayi ta saura sama ba jimawa ta dawo d'auke da k'atuwar leda da kud'i bawa Laraba tayi Ta ce gashi wannan ki kai wa iyayen ta kud'in kuma naki ne nagode .Ita ma Laraba godiya tayi san nan ta tafi. Kallona Hajiya ta yi "Ta ce bara nasaka akai ki d'aki. wani abu daga ta danna a gefen gini nan take sai ga wan nan budurwar tazo kallon ta tayi san nan "Ta ce kije da ita d'aki kafin nasan yadda zanyi, da toh ta amsa san nan muka tafi. har muka shige k'ofar d'akin hajiya na tsaye tana kallona....



Muna shiga d'akin nafara "Yan dube_dube a raina na ce kai gaskiya gidan nan ya had'u wai wan

nan d'akin "Yar aiki ne maganar da takemin ne ta dawo da ni daga duniyar tunani kallon na yi batare da nace komai ba. ita ma kallona take can kuma "Ta ce kije kiyi wanka ki huta, "Na ce toh, band'akin ta nunamin nashiga sai dai duk abin da ke ciki ba wan da na iya amfani da shi.fitowa nayi "Na ce banga ruwan wankan ba dariya tayi sannan "Ta ce muje na nuna miki yadda ake amfani da shi, shiga mukayi sai da ta nunamin komai ta tabbatar da na ita san nan ta fito ta barni nayi wankan wani .sanyi da dad'i nakeji a jikina saboda a gida sai nayi sati d'aya biyu banyi wanka ba koda zamuzo ma banyi wanka ba.


Bayan nagama nafito gaban madubi ta nunamin zuwa nayi na tsaya ina kallon kayan dake wurin. tasowa tayi tana dariya ta nunamin mayukan shafa da turare da mayukan gashi da sauran su shafawa nayi san nan na bud'e "Yar bagen kayana na d'aukoh wata kod'ad'd'iyar doguwar riga nasaka sai ga ni nafito fes kamar bani ba ,kallon kaina nayi a madubi "Na ce Masha Allah ashe inada kyau haka amma duk daud'a ta gama kasheni, tasowa tayi tana dariya "Ta ce gaskiya kam kinada kyau Masha Allah......



Cike da farin cikin da na dad'e banji irin shi ba. dariya nayi san nan "Na ce Anty na manta ban tambaye sunanki ba, cike da farin cikin tasamu "Yar uwa "Ta ce hajara kefa, "Ni kam Aisha, haka muka wuni ranar cikin farin ciki....




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol