Free chapter · Read without an account
Page 43-44
by autararewa101 · ZAFIN KISHI
ZAFIN KISHI!!!!!!!!!!!!!
Written story
By
AUTAR AREWA
Bismallahi Rahamanir Rahim
PAGE4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣
📝........................Cike da tsoro Zulaihat ta bude baki ta ce "Ke kuma wacece?daga ina kike? Meye alakarki da ni?"
Murmushi Ihsan tayi kafin ta kara harde hannuwanta a kirji cike da izza ta fara bata amsa "my name is IHSAN BUKAR SADA ni haifafiyar garin Maiduguri ce,ina fatan yanzu kin gane ni"
Da sauri Zulaihat ta kara matsowa kusa da ita tana Kara karemata kallo zuciyarta cike da tsoro,dan sosai ta ji jikinta yayi sanyi ganin wannan gogagiyar yarinyar a gabanta.
Mamace ta ce "Bayin Allah ince dai lafiya ko?" Tayi tambayar tana kara mayar da kallanta gare su .
Sai a sannan Hannatu tayi magana da cewa "kiyi hkr mama mun san zaki ji babu dadi akan abinda ya faru da danki, Amma duka laifin yana wurin wannan munafukar sarakuwar taki,sanadin ZAFIN KISHINTA ya Kaita ga hallaka wanda yanzu mun tabbatar koda ta kasa mijinta a cikin tray to ba wanda zai siya........
Murya cike da rudani mama tayi saurin tare numfashinta da cewar "Haba bayin Allah ya kamata ku yimana cikakken bayani ta yadda zamu fahimci akan abinda kuke magana,saboda kun fara saka ni cikin rudani.ta kai karshen maganar tana jin zuciyarta na kara nauyi.
Ita dai Zulaihat still haryanzu tana tsaye sororo tana binsu da kallo,tuni hankalinta baya jikinta ta lula duniyar tunani,dan idan bata manta ba lokacin suna fada da IHSAN a wayar Habib akwai wasu maganganu da ta fadamata masu rikitarwa,dukda bata daukesu da mahimmanci ba,Amma yanzu ta fara tsorata da lamarin su.
Da sauri Hannatu ta ja hannun IHSAN suna kokarin fita daga dakin ganin Dr ya shigo.
Cikin azama Zulaihat ta ce "Ku dakata baku sanar da mu abinda kuke san fada ba?"
A tare suka juyo Hannatu ta ce "Uhm me kike ci na baka na zuba,ki kwantar da hankalinki tunda ga Doctor nan zai sanar da ku,idan kina da bukatar ƙarin bayani sai ki nememu ta waya domin mu wayar Maki da kai,but ki sani mu duk wanda ya ci tuwo da mu to fa miya ya sha".tana gama fada mata haka suka yi saurin ficewa daga dakin.
Hankalinsu suka mayar ga Doctor lokacin da yake cewa "Ina matar shi da mahaifiyar shi"
Zulaihat kasa magana tayi sai mama ce ta ce "Ni ce mamar shi,wannan kuma matar shi".
"Ok Ina san ganinku a office dina yanzu"cewar Doctor Yana fita dan komawa office din shi.
Mamace ta fara bin bayanshi tare da kawu Aliyu.
Zulaihat ganin da gaske sun fice kafin ta samu damar jan kafafunta ta bi bayansu tana jin kanta yana wani irin sarawa.
Bayan sun zauna gaban Doctor gaba daya hankalinsu yana gare shi.saida ya cire farin galashin dake manne jikin fuskarshi kafin ya mayar da dubansu gare shi yana kara nazarin halin da suke ciki.tsawon wasu dakika suna haka kafin yayi karfin halin cewa "Ku kwantar da hankalinku ita cuta ba mutuwace ba,sannan yana bukatar addu'ar ku a matsayinku na makusantanshi,sannan ita rayuwa kowa da irin kaddarar rayuwar shi,Amma ya zama dole duk wani mumuni ya yadda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau".
Saida ya nisa kafin ya dauko wata takarda da aka sakata cikin emblance ya mikawa Kawu Aliyu yana cewa "Wannan shi ne result din da aka kawo mana dazu,ance shi ne gwajin wanda aka yi masu tun baya da kwana biyu akan auren da zai yi,To muma mun dauki jinin shi tare da kara yin wani gwajin dan tabbatar da gaskiyar abinda ke damun shi to alhmdl duka result din ɗaya ya nuna da wannan,dan haka yanzu zamu dora shi akan magani insha Allah zai samu sauki".
Cikin sauri kawu Aliyu ya fara ware takardar tare da addu'ar Allah yasa yaga alkhairi.
Tunda ya warware result din idon shi yakai kan sakamakon gwajin nan take ya ji zuciyar shi ya bada wani sautin dammmm.....dammmmm kasa cewa komai yayi lokacin daya gama karantawa sai kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"yake maimaitawa.
Cikin tsoro Zulaihat ta anshi result din tana cewa "Kawu ka sanarmana da abinda yake faruwa daidai tana kai kwayar idonta kan rubutun.kawai sai ji suka yi ta fasa wani gigitaccen kara tare da zubewa kasa a sume.
Gaba daya suka yo kanta,itama Mama kuka ta saka ganin wannan sabon al'amari yana tunkaro su.
Da sauri Doctor yayi Kiran wasu Nursing Mata guda biyu,a gadon tura marasa lafiya aka ɗauki Zulaihat zuwa emergency Dan bata taimakon gaggawa.Banda kuka babu abinda mama take yi kawu Aliyu shi ne mai dauriyar baya hakuri.
Bayan fitar su IHSAN kuwa bushewa suka yi da dariya harda tafawa kafin suka karasa jikin motar,A guje suka ja suka fice daga harabar asibitin.
A dakin da aka kwantar da Habib kuwa daga Fatima kanwar shi sai ikilima kawar Zulaihat.sunyi jugum suna jiran dawowar su kawu Aliyu sai ganin wata Nurse suka yi ta shigo tana cewa "Ina Fatima ki kira waya gidan su Zulaihat ki ce su zo asibiti yanzu Doctor Yana san ganin su".
Mikewa Fatima tayi cikin sanyin murya ta ce "To amma yanzu suna ina tun dazu muke jiransu"
Har nurse din takai bakin kofar fita ta ce "Zaku iya zuwa tana emergency".
Ai da sauri ikilima ta fita da gudu tana cewa "Innalillahi Allah yasa dai lafiya".
Lokacin da ta je wata Nurse tana sakamata ƙarin ruwa.bakin gadon ta karasa tana tambayar abinda ya faru,ita dai Nurse din cewa tayi bata sani ba kawai sun daukota ne a sume.
Haka duk suka yi jugum bayan Fatima ta kira momyn su Zulaihat ta sanarmasu da abinda yake faruwa.Momy bata wani damu sosai ba saboda tasan wannan ZAFIN KISHIN na diyarta bazai haifa da mai ido ba,Amma a zuciyarta ita kadai tasan ciwon da take ji.
Da haka ta sauko babban falo inda ta sanar da abokiyar zamanta,nan take suka saka hijaf dinsu driver ya daukosu Dan zuwa asibitin.
A bangaren amaryar Habiba kuwa ta dade a dakin ita kadai baka jin karan komai sai fanka da AC wanda yasa ta takure wuri ɗaya saboda sanyin da ta ji yana ratsa ta.Haka tayi ta faman sake-sake a zuciyarta "Yanzu da Habib ne tasan daya bata kulawa ta musamman,Amma yanzu shi wannan tasan kila ya rinka wulakanta ta "da sauri ta kawar da tunanin jin alamar motsi kamar ana nufo dakin da take.
Ƙarar bude kofa ta ji hakan yasa ta kara tsorata,kada ta je a saceta.
A hankali Mukhtar ya turo kofar bedroom din ya shigo bakin shi dauke da sallama.
Can kasan makoshi ta amsa,dan yanzu ta gane shi saboda hasken daya gauraye dakin.
Bakin gadon ya karaso yana cewa "Sorry Amarya na barki ke dai,wallahi su Aminu ne suka bataman lokaci"
Ita dai "Uhmm"kawai ta ce tana kara rufe fuskarta da mayafi.
Ledojin daya shigo da su ya aje bisa kafet din da aka shimfida gaban gadon,kafin ya dubeta yana cewa "Ki shiga toilet ki yi wanka ki dauro alwala yanzu zan dawo"Bai jira jin amsarta ba ya fice daga dakin.
Saida ta tabbatar ya fita kafin ta cire mayafin tana kara karema bedroom din kallo tana mamakin irin kudin da aka narka,wai yau ita Habiba ita ce a irin wannan gidan cab haka Allah yake ikon shi.
Da wannan tunanin ta nufi toilet din kasancewar Habiba ba laifi da wayewar ta shiyasa bata sha wahala ba ta fahimci yadda ake amfani da kayan toilet din.cikin lokaci kalilan tayi wanka tare da yin brosh sai kanshi take na sabulu.Alwala ta yi kafin ta fito daure da towel.wata doguwar riga ta ciro daga akwatinta marar nauyi da sabin enerwest ta saka,sosai ta shafa turare da humra masu dadin kanshi wanda kanwar mahaifiyarta ce ta kawo su.
Tana kokarin saka hijaf ya kara turo kofar ya shigo a karo na biyu.Inda take ya kalla kafin ya shimfida abin salla.Itama bayanshi ta bi suka gabatar da sallar raka'a biyu tare da yin addu'o'i,Anan yayi mata wasu tambayoyi game da addini kuma alhmdl yayi mamaki sosai jin yadda take ba shi amsa,Yayi tunanin yarinyar bata da ilimi irin haka.
*Please masoya kuyi hkr na jina shiru da kuka yi,kunsan uzirin yawa yake yi 🙏,Amma yanzu insha Allah na dawo zan kammala maku wnn book kafin mu shiga sabon book dina Mai taken...................😄 Basai na fada ba ku dai ku kasance tare da ni Autar Arewa dan nishadantar da ku* 👏🤝.
Pls follow, vote, comment, and share 👏
BY
AUTAR AREWA.
✍️✍️✍️✍️✍️