Free chapter · Read without an account

Chapter 8

by Maryam Umar · MASARAUTAR FADAKATAM

*_MASARAUTAR FADAKATAM_*


*_Na Maryam Umar Abdullahi_*

( _Maman yusuf_)



*____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***



*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


***


*____________________________________*


🅿️age_8


*_BAYAN SHEKARA GOMA SHA UKKU_*


.......................Acikin wad'an Nan shekarun Masarautar fadakatam ta k'ara girma da k'arfi inda sunanta ya watsu a dukan sassan Africa da kewaye , Sarki ZULAIMU yanada hatsabiban mayak'a kimanin mutum dubu ashirin , Wanda duk Masarautar da ya kaima Hari cikin k'ank'anin lokaci suke gamawa da ita ,an Basu wani irin horo inda aka horar dasu rashin Imani da rashin tausayi haka zasuyiwa masarauta kaca-kaca suyiwa matansu fyade sannan su kwashe Yara kanana da matasa a matsayin ganima , Wanda mutanen da ake kamowa ake azabtar dasu ta hanyar sasu aikin hak'ar zinari da azurfa , sanadiyar hakan sarki ZULAIMU ya samu gawurtaccen arzik'in da Babu wani sarki daya ta'ba samun irinshi a tarihin Masarautar, haka maza da Mata da k'ananan yara ke wannan aikin wahalar ba dare ba Rana , sanadiyar hakan kusan kullum sai wasu daga cikinsu sun mutu ,Amma Sam wannan Bai damu sarki ZULAIMU ba don suna mutuwa ne ana kawo wasu , duk Masarautar da ya ci da yak'i zai tattaro sauran mazansu da matansu ne akawosu a zube cikin k'angin 'bauta, haka za'ayi ta bautar dasu da azabtarwar da ko dabba ba za'ayiwa ba , 


Wannan al'amari fa yasa gaba d'aya sunan sarki ZULAIMU ya tamfatsa a duniya inda yayi nasarar Sanya tsoronshi Mai tsanani a zukatan al'ummar nahiyar dama wajenta Baki d'aya, Wanda dama burinshi kenan a cewarshi da sannu sannu sai ya mulki duniya wannan shine burinsa 


Yarima ZILLAK'I ne zaune bisa wata karagar mulki wadda akayi da d'anye zinari da azurfa Yana sanye da riga da wando rigar irin Mai d'an Tsawon nan ce don har ta kusa kaiwa ga gwuiwarshi ,sai wando irin Mai fad'in Nan dukkansu anyi masu kwalliyar sak'i irin na 'ya'yan sarakuna ,wuyanshi sanye da wata k'atuwar sark'a Mai tsawo ta zallan zinari tana d'auke da zanen tambarin Masarautar fadakatam, yayinda faratanshi ko wanne ke dauke zoben d'anyen gwal, ayi mashi nad'i Hawa d'aya Mai kyau wanda ya Kara fito da yarintarshi Wanda yake da shekara goma Sha takwas a yanzu, yayinda dakaru guda ashirin ke tsaye a bayanshi da gefe-gefenshi suna bashi tsaro ,sai Kai da kawo suke a wajan kamar zasuci Babu, gefe d'aya bayi ne mata a jere reras su goma Sha biyar, Wanda dukkansu bazasu wuce shekara 15, 16, 17, ba kallo d'aya zakayi masu kasan cewa a matuk'ar firgice suke , kowacce kanta a k'asa ko numfashin kirki basa iya ja sai jikinsu dake rawa sosai Wanda zai tabbatar maka zukatansu acikin tsoro da firgici suke , a hankali yarima ZILLAK'I ke yawo da idanunshi akansu Yana k'are masu kallo d'aya bayan d'aya , cak ya tsaida idanunshi akan wata kyakkawar yarinya Fara Tass lokaci d'aya yanayin siffar yarinyar da yanayinta na Kamar shagwa'ba ya fisgeshi akanta , ba tare da yayi magana ba ya lumshe idanunshi kawai , cikin hanzari wasu tsaffin Mata biyu bayi suka nufi yarinyar nan ,suna zuwa inda yaran suke suka zak'ulo yarinyar suka fito da ita inda suka bawa sauran umurnin subar wajan, aikuwa kamar zasu tserewa k'afafunsu haka suka bar wajan cikin d'akikun da Basu wuce biyar ba, yarinyar da aka fitar kuwa tuni wani irin kuka ya k'wace mata ba tare da wani musu ko jayayya ba tabi wad'an Nan tsaffin suka nufi sashen yarima ZILLAK'I, 


Kasancewar yarima ZILLAK'I na samu tsananin horo yasa lokaci d'aya jikinshi ya bud'e a kallo d'aya zaka dauka yakai shekara ashirin da biyar ne saboda yadda komai na jikinshi ke nuna mazantaka ,shekara d'aya kenan da yarima ZILLAK'I ya Fara ke'bewa da mace kasancewar shi jarababben yaro yasa tun Bai Kai ko'ina ba yake lalube 'yan matan dake kawo mashi abinci ,abun takaici abun bak'inciki sunaji suna gani yaro k'anen bayansu zai dinga lalube masu jiki yadda yakeso baka Isa kayi magana ba ,don sa'bawa yarima ZILLAK'I dai dai yake da daukewar numfashinka ,tun baya haik'e masu iyakacinshi ya lalubesu har ta Kai ya Fara Kai masu Hari , ai kuwa tunda ya Fara sanin dad'in mace shikenan kusan kullum sai yasa an kawo mashi yarinya d'aya daga cikin yaran bayi ,tun abun Yana iya kan 'ya'yan bayi yanzu har yaran gari ma ya shafa ,duk yarinyar daya ga tayi Mai babu ruwanshi ko Yar uban waye zaisa a dauko mashi ita , wad'an Nan tsaffin sune suke tafiya da yarinya suyi Mata wanka Mai suna wanka a gyara Mata gashi da duk wani abunda ke buk'atar gyara ajikinta , zasu shiryata cikin sutura ta alfarma cikin k'amshi da kwalliya sannan suje su kaiki har d'akin yarima , haka yarima ZILLAK'I zai k'eta mutumcin yarinyar yayi Mata kaca kaca sannan yasa azo a fita dake , wannan abun da ke faruwa Yana matuk'ar yiwa Yan garin da bayi ciyo , sunajin ciyon abunda yarima ZILLAK'I ke yiwa 'Ya'yansu fiye da da ciyon da sukejin akan ubansa sarki ZULAIMU, sunajin tsanarshi sosai fiye da tsanar da sukayiwa sarki ZULAIMU, wannan yasa gaba d'aya iyayen yara dama yaran ke matuk'ar Kama kansu da duk wani abunda zai had'asu da yarima ZILLAK'I , ganin hakan yasa yarima ZILLAK'I fito da sabuwar hanyar samun duk yarinyar da yaso ,inda ya bada umurnin adinga fito ya 'ya'yan bayi ana jera masa su a gabanshi ta hakanne zai ga yarinyar da tayi mashi,


Kuka take Mai matuk'ar ta'ba zuciyar Mai sauraro , ganin yadda tsaffin Nan sukayi mata tunbur suke wanketa ciki da Bai d'inta , ba su damu da kukan da takeyi ba don in da zabo sun Saba tun sunajin tausayi har zuciyarsu ta bushe Akan hakan , duk da acan k'asan zukatansu abun na tsinkararsu sai dai fad'an da yafi k'arfinka maidashi kakeyi wasa , haka suka gama Mata wankan suka daukota kamar jaririya suka fito da ita , Nan d'aya daga cikinsu ta Fara tsane mata ruwan kanta yayin da d'ayan ke faman murza Mata wasu irin turarruka masu wani kalar k'amshi irin na gidan sarauta,Bayan ta gama murza Mata turarrukan ne sukaci gaba da gyara Mata gashin kanta ,suna gamawa sukayi Mata kwalliya da wani yadi Mai ratsin ja da fari tayi kyau sosai sannan suka yafa Mata Zane d'aya na yadin , ya kasance mayafinta da tufafinta iri d'aya ne sai da suka gama gyarata tsaff sannan d'aya daga cikinsu ta dube yarinyar tace " kiyi hak'uri ki daina kukan Nan don ba amafnin da zai maki, idan har kika kuskura kikaje turakar yarima kina kuka Zaki iya rasa iyayenki a dalilin hakan , ko kuma ke in ya Gama abunda zaiyi da ke yasa a kasheki ,don haka muna Mai gargad'inki da kiyi hak'uri komai Daren dadewa Allolin zinari zasu kawo Mana mafita ,ba zamu dawwama a hakan ba , 


Babu yadda ta iya haka Nan wani mugun tsoro ya sake mamaye zuciyarta tuni wani zazzafan zazza'bi ya sauko Mata jin cewar zata iya rasa iyayenta wannan abune da bazata iya jura ba , zata hak'ura kawai sai dai tasan har ta mutum ba zata sake farinciki a rayuwarta ba , haka Nan tsaffin Nan suka Kai yarinyar Nan Mai suna feeyaa har cikin turakar yarima , nan suka ajiyeta a k'asa suka juya suka barta cikin wani irin yanayi Mai wuyar fassara, 


Tayi a k'alla sa'a biyu a wajan a zaune kamun yarima ZILLAK'I ya bayyana cikin d'akin, tana ganinsa gabanta yayi wani masifar fad'uwa sai dai ba damar nunawa maimakon haka ma duk'awa tayi ta Fara gaisheshi da yi mashi kirari irin Wanda bayi ke mashi, lumshe idanunshi yayi jin yadda zak'in muryarta ke sake kashe mashi jiki, ba tare da wani 'bata lokaci ba yayi Mata nuni da gadonshi Wanda yasha shimfid'u na alfarma ,ba musu ta tashi ta nufi gadon inda ya Mara Mata baya,


Tabbas yarima ZILLAK'I ya cika bak'in bugu azzalumi kuma marar tausayi , gaba d'aya feeyaa ta fita hayyacinta hasalima Bata san Wanda yake kanta ba saboda azaba ,wani irin k'arfi yake sakewa mace ba tare da damuwar komai ba kamar wani dabba , sai da ya samu yadda yakeso sannan ya sa k'afa yayi shuri da ita ta fad'o daga saman gadon inda kanta ya bugi wani k'arfe take ta saki wata k'arar azaba kamun numfashinta ya tsaya cak , ta antaya duniyar suma , 

Ba tare da damuwar komai ba ya baje akan gadonshi ya Fara baccinshi hankali kwance,



********************************


Da gudu take ratsa mutanen dake wajan tana nufar tsakkiyar filin , bakinta a washe kana ganinta kasan tana cikin tsananin farinciki, ba zato ba tsammani taji an rik'o hannunta ,cak ta tsaya kamun ta d'ago da sauri don ganin Wanda ya rik'e Mata hannu, ganin mahaifiyarta yasa ta shagwa'be fuska kamar zatayi kuka tace "UMMI wajan Yarima zanje fa, " 

Harararta uwar tayi tace "bakida hankali ne ,bakiga wasan gwaji akeyi ba ,sai kinje wajan shegen kaud'in ki kibiya ta Huda maki tsakkiyar Kai ,muje can gimbiya HIDAYA tun d'azu take nemanki, ba don ranta yaso ba tabi Bayan uwar Tata tana 'yan k'unk'uni irin na Yara, 


Tun daga nesa gimbiya HIDAYA ke sake Mata murmushi ,inda itama AZIZA ta sake Mata murmushinta Mai kyau da shiga zuciya Wanda har saida gefen kumatunta duka biyu suka lo'ba gwanin sha'awa , hak'ik'a AZIZA ba k'aramar kyakkawa bace wannan yasa gimbiya HIDAYA ke matuk'ar sonta da k'aunarta , tana zuwa kusa da gimbiya HIDAYA ta d'ane Mata kafafu tare da furta 

    "Maaa Kinga ummi ta hanani zuwa wajan Yarima ko "ta fad'a tana tura bakinta irin na sagartattun Yara, 

Murmushi gimbiya HIDAYA tayi tace " to ke yarinyata bakiga ana tsaka da wasan gwaji bane ko so kike su lahantamun ke ba tare da saninsu ba , Kinga yanzu da yayanki za'ayi zo ki zauna kusa Dani kidinga mashi addu'ar Allolin zinari su bashi nasara Kar wani abun ya sameshi , "

Cikin zumud'in ance yanzu yarima ne zai fito ta k'ara gyara zamanta ta zubawa filin wasan Ido bakinta kuwa sai motsi yakeyi alamar tana mashi addu'ar ne , 

Shafa kanta gimbiya HIDAYA tayi cike da soyayya tace "Allolin zinari su cikamun burina akanki ya ke yarinya ta, kamun ta maida hankalinta ga filin Wanda fitowarsa kenan , 


Cikakken jarumi ke nan yaro Mai jini a jika kyakkawa ne na bugawa a jarida ,kallo d'aya ya isa ka shaida cewa shid'i jinin sarki KUNTARU ne saboda tsananin kamar da sukayi fari ne Tass Wanda ya gado daga mahaifiyarshi gimbiya HIDAYA wadda ta kasance Fara Tass kuma kyakkawa ajin farko , 


Sanye yake da riga da wando sai rawaninshi akanshi Wanda aka nad'a mashi shi Hawa d'aya Wanda wannan saka rawanin Al'adar Masarautar fadakatam ce , shiga ce da 'ya'yan sarautar kawai ke yin ta, yayin da wuyanshi yake sanye da asalin sark'ar da magadan Masarautar fadakatam ke sanyawa ,duk Wanda aka bawa wannan sark'ar to shine zai zama magajin masarautar , rigar silki ce a saman rigarshi wadda mayak'a ke sakawa a saman tufafinsu lokacin da suke filin daga tsaye yake rik'e da shar'be'biyar takobi sai kyalli yakeyi ya zubawa jarumman sadaukan da suka k'ware wajan harbi dake kallonshi Ido Yana jiran ko ta kwana , yarima ZAHIRR kenan yaro d'an shekara goma Sha ukku Wanda yake samun horon yak'i da salo kala kala tun yanada shekara hudu a duniya ,


Filin yayi tsin ana jiran bada umurnin Fara gwajin da za'ayi wa yarima ZAHIRR yayin da gefe d'aya zuciyar gimbiya HIDAYA ke cike da tsananin fargaba da tsoro don tasan kuskure d'aya zai iya hallaka Mata jarumin d'anta har lahira , 

Jin an buga gangar dake nufi bada umurnin yasata dasowa hayyacinta ta zubawa d'an nata Ido , 


Maharba ne wajan mutum d'ari suka zagaye shi sukayi mashi zobe ,kowanne da kwari da baka a hannunshi ,inda suka d'anata tsaf suka saita yarima ZAHIRR , Wanda shi kuma akeson yayi amfani da takobinshi ya dinga Kade kifiyoyin nasu ba tare da ya Bari d'aya ta shiga jikinshi ba , Wanda yin wannan kuskuren dai dai yake da rasa numfashinshi, , dukkansu lokaci d'aya suka gyara tsayuwarsu kamun su Fara Yi mashi ruwan kifiyoyin ,aikuwa cikin wata irin jarumta da tsananin zafin nama da k'wararren horon da ya samu ya dinga wani irin tsalle Yana juyi gabas da yamma kudu da arewa Yana kwa'be kifiyoyin suna fad'uwa k'asa , kamun kace mi tuni duk ya kwa'be su ba tare da d'aya ta samu nasarar Shiga cikin jikinshi ba , aikuwa take filin ya d'auki ihu da sowa na murnar wannan jarumta da yarima ZAHIRR ya nuna Wanda ko manyan jarumai ba kowanne yake iya tsallake irin wannan had'arin ba, 


Sarki da gimbiya HIDAYA harma da matar Malamin duba sai murna da farinciki sukeyi da tunanin zuwa gaba Basu San inda kwazon yaron nasu zaije ba............


*Kuyi hkr da rashin jina wlh ko inji nan ya barni Akan yawan hidindimu ayukkane sukamun yawa , Amma insha Allah Zan Kara maida hankali akai*


*Zanyi aike kano kudin motar kyauta ne Maison kayan Mata tayi magana ngd*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol