Free chapter · Read without an account
PAGE 1
🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF(GIMBIYA AYSHU)
ELEGANT ONLINE WRITERS 📚
WHATPAD NAME
*AISHAMAARUF*
📚📚 PAID BOOK 📚📚
BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM.
*FREE PAGE*
PAGE 1
________________Tsauri take tagama sharan datake, taji mama ta kwala mata kira kafin ta amsa, taji tana cewa dan ubanki bazaki yi tsauri ki gama ba,"ko so kike yayi kwante" a shegiya mai suffan mayu, uffan bata ce ba taci gaba da sharanta, bayan ta gama, ta kwashe takai bola, ta dawo ta ijiye sinsiyan da pakan, ta dau bucket ta nufi rijiya ta debo ruwa, ta zuba a roba, ta dau kwandon wanka ta wuce bayi bayan ta fito, ta shiga dakinta ta shafa mai, "ta shirya chikin wani kodadden riga da skirt" kalan sky blue da fari dadan rasin peach, tana gama sawa ta dauko hijabinta sky blue tasa, tana gama shiryawa tafito tasa slipas dinta taje tayi sallama a kofan dakin mama, mama tace waye, tace nasreen ce, nagama mama, tace gashi chan kusa da murhu je ki dauka na dubu dayane a wurin kuma kisiyar da duka, "in kika rago kinsan tsauran" tace "toh" ta juya ta nufi murhu ta dauki tiren da a ka sa abincin ta fita gidan, da ganan bata zarce ko ina ba sai bakin kasuwa, in da take haduwa da abokan tallan ta, bayan ta kai, ta sauke tiren, ta nemi wuri ta zauna suna dan hira da kawar tata mai sunna maijidda, tana hira tana siyar da abincin ta karfe biyar da rabi ta siyar da komai tana jiran kawar ta, ta gama siyar da nata tunda Saura kadan, shida da kwata suka kama hanyyan gida tunda hanyya dayane, ba nasreen ta kai ba sai shida da rabi ta shiga gidan da sallama, ta samu mama a tsakar gida tana girki, "tace ina wuni mama", tace daban wuni ba zaki ganni, taja tsaki ni ba wannan bane damuwana, kin siyar koko tace na siyar "tace toooo" Allah ya taimakeki, da kinci na jaki, nasreen batace komai ba, ta matso ta bata kudin dubu daya cip, ta ijiye tiren a gaba da wurin murhu inda take wanke wanke, ta shiga daki ta cire kayan jikinta, tayi daura kirji tasa baby hijab ta fito, taja ruwa arijiya ta dau kwandon wanka ta shiga bayi ta wasa ruwa bayan ta fito, mama tace iyyen tsabta Wato kinje kinyi tanbadan ki kenan, I banga laifin ki ba gado kikayi, shegiya dangin mayu tsintar ciyar mage, hawayen dake kokarin zubo mata ta hadiye, tanemi buta tayi alwala, ta shiga daki ta shafa mai tanemi wani kaya tasa, tayi sallah tafito tsakar gidan ta zauna,tana sauraron hiran da suke da en matan ta, suna cikin hiran salmanu ya shigo yana tafiya kaman wani dan daba, yana zuwa ko gaisuwa babu yace "ladi" sannu da gida ba abinci ne tace akwai dan Albarka, yace to asa mun tace to, k bakiji mai yayanku yace ba, jikinta na rawa ta tashi, ta shiga dan kitchen dinsu ta dauko kwano mai dan zurfi ta fito ta dauriye shi ta diba tuwo tasa, sannan ta zuba miya takai mai, ya amsa ya fara ci ko wanke hannu babu, sa'ade tace k nima samin, lauratu ma tace samin nima, toh! tace ta juya ta shiga kitchen ta dau kwano uku ta fito ta dauriye, tasama sa'ade da lauratu ta kai musu, sannan ta dawo tasa ma mama ta kaimata, takara komawa kitchen ta dau plate tasa ma kanta dama ka'ida ne sai ansa ma kowa ake samata, ko tasa dan cewa suke su ba bayin ta bane "sai dai ita tazama baiwar su", "abin nan na mata ciwo" amma babu yanda ta iya, bayan ta gama cin tuwo, taje tayi sallah, ta dawo ta hada kan kwanoni ta fara wanke wanke, mama da yaranta na tsakar gida ko sallah ba'ayi ba, suna na suna surutun da baze an fane su ba, suna cikin hiran baba ya shigo mama ta mai sannu dazuwa "yace yauwa" yaran duk suka gaishe shi ya amsa, mama tace nasreen tasa ma baba abinci, "tace toh "ta tashi tasa mai abinci ta kawo da ruwan wanke hannu da ruwan sha, ta ajiye shi ta koma wurin wanke wankenta, bayan ta gama ta kai kwandon kwanonin kitchen, ta dawo ta share wurin ta koma ta zauna a kofan dakinta, ta na tsauraren hiran da suke ita dai bata sa musu baki ba, ta fada tunani, basu suka tashi awurin ba sai sha daya dan babu halin ta tashi sai kowa ya tashi, tashiga daki ta kakkabe dan katifan ta ta kwanta.
Aban garen salmanu bashi ya dawo ba sai 12, ya kulle kofan ya shiga dan akurkin dakin shi dake zaure, ya kunna sigari, yana busawa sai daya sha sanda uku Kafin ya kwanta bacci.
Washer gari tun karfe biyar ta tashi, "tayi sallah" ta fara aikinta, shara, kunna murhu, wanke bayi har sharan dakin mama ita keyi ta share ta gyra, taje ta debo wake da shinkafa duk ta gyra su ta ijiye, bayan wutan yakama tasa tukunya, ta zuba Ruwa, bayan ya tafasa, ta wanke "waken" ta zuba ta koma gefe ta zauna tana jiran su mama su tashi, waken na nuna ta wanke shinkafan tazuba tasa gishiri ta kulle tukunyyan, ta debo tattasai da tumatir da albasa...........
COMMENT IS NEEDED
KU CIGABA DA BIN ALKALAMIN GIMBIYA AYSHU, DAN KARANTA CIGABAN LABARIN.
🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡
❤❤❤LOVE AND DESTINY STORY❤❤❤
Ladi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi"
Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye".................
Sai dai abin da mama bata sani ba shine in Allah ya kaddara abu bawa bai isa ya chanja shi ba.
Zuwan safwan rayuwan ta a matsayin dan talaka tukuf ya zeme mata Alkairi, dan ganin shi a haka da mama tayi ta zata ba dan kowa bane kuma ba komi ba face kaskan tance, talaka irin Wanda takesan Nasreen ta aura, ba batasan tayi kuskure ba ta kaita in da bataso............
Toh! Masu karatu ku biyo ni dan karanta wannan labarin.
Duk zaku sami wannan littatafan daga taku Gimbiya Ayshu marubuciyar "LAILAH" and now "ZUBAR HAWAYE NA" a farashi mai tsauki dan jin dadin ku.
Kada ku tsake a baku labari dan it gonna be like 🔥🔥🔥. Gamai buka tan littafan, the payment are as follow:
Daya:150
Biyu:250
Uku:350
Hudu:400
Biyar:500
In kina bukatan duka zaki biya daribiyar(500) ta wannan bankin:
Aisha Nura Murtala
GT bank
Account number
0623151889
Evidence of payment ta wannan number
***
*NIHLAH
*IDAN ZUCIYA TAYI WAKE
*TUGGU BIYU
*ZUBAR HAWAYE NA
*MATA A YAU
Kar ku bari a baku labari, kuyi hanzarin siya dan ku nishadan tu.
Ga matsu turo kati kuma sai ku turo ta wannan lanban
***.
Karku manta zafafa ne sai kunzo ❤❤❤
Ga mai bukatan ZUBAR HAWAYE NA. Ga
Account name
Zainab Yahaya
Fcmb
Account number
7410207015
Evidence of payment
***
Ga mai bukatan NIHLAH. Ga Account number
2215749011
Name
Saratu kabir
UBA Bank
Evidence of payment
***
Ga mai bukatan MATA A YAU. Ga Account name
Hafsat Yahaya
First Bank
Account number
3140418863
Evidence
***
Ga mai bukatan IDAN ZUCIYA TAYI WAKE. Ga
Account name
Halima Nuru Murtala
ECO Bank
Account number
3090183528
Evidence
***
Ga mai bukatan TUGGU BIYU. Ga
Account name
Aisha Idris Abdullahi
Wema Bank
Account number
0241707861
Evidence
***
Kuyi hanzarin tsiya insha Allah zakuji dadin littattafan kuma zaku wa'azan tu, nishadan tu da dai tsauran su...........
Bye GIMBIYA AYSHU💞💞💞.