Free chapter · Read without an account

Chapter

by Maryam Umar · MASARAUTAR FADAKATAM

*_MASARAUTAR FADAKATAM_*


*_Na Maryam Umar Abdullahi_*

( _Maman yusuf_)



*____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***



*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


***


*____________________________________*


🅿️Age _10



💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐

*_INFECTION BABBAN CIYO NE_*


Ciyon da yake shiga tsakanin ma'aurata ya hana masu zaman lafiya. Da kwanciyar hankali a zamantakewarsu ta aure , ciyo ne da yake kassara martaban mace harma da mazan Kansu , ciyo ne mai hadarin gaske Wanda duk take dashi to ba ita ba jin dadin aure , saboda yana dauke ni'imar mace gaba daya yana hana mace jin sha'awar mijinta yana saka ciyon Mara mai tsanani idan yayi yawa , Wanda zuwa gaba yake hanawa mace daukar ciki. Ko kuma yawan 'barin ciki Sannan duk abunda mace zatayi domin gyaran kanta to bazai mata wani amfani ba saboda wannan ciyon wannan zaisa mace taga tana ta faman shan maganin mata amma baya mata aiki, 


*KADAN DAGA ALAMOMINSHI*

Bushewar gaba

K'aikayin gaba

Fitar kuraje agaban mace

Fitar farin ruwa mai kamar madara ko mai kamar majina 

Ko fitar ruwa mabanbanta kala 

Rashin sha'awa 

Rashin jin dadin kwanciyar aure 

Yana haifar da budewar gaba,

Ciyon Mara da sauransu ,


wannan yasa mukazo maku da sahihijn 

maganin sanyi wato infection yana wanke duk wani dattin Mara yana maganin sanyi sosai tareda saukowa mace niima maganin 3in1 ne na sha da sabulun tsarki da Wanda zaki dafa kina tsarki dashi , akwai kuma maganin sanyi na maza daban Wanda yanada kyau duk wacce ta siyama kanta to ta siyawa mijinta don kar ayi badi babu rai don ko kinji sauki in shi mijin yanada zai iya shafamaki .......*

*** mmn Yusuf mai kayan mata sokoto🥰🥰




......................... Kuka takeyi har tana shid'ewa jikinta wani irin rawa yakeyi , ga zafin ciyo ga azabar da takeji a k'asanta ga kuma tsananin tashin hankalin da take ciki na faduwar iyayenta lokaci d'aya , tana son ta tashi Amma ta kasa ,haka Nan ta dinga Jan ciki har zuwa inda randan ruwansu take ,d'ebowa tayi ta koma janyo jikinta zuwa inda iyayen suke ta kwara masu ruwan tana Kiran sunayensu ,Amma har lokacin ba alamar numfashi a tattare dasu. Nan ta Fara jijjiga uwar tana kuka sosai , tana haka k'awarta Talatu ta fad'o gidan ,don tun jiya ta kasa sukuni akan kaddarar da ta fad'awa k'awarta , sosai hankalin Talatu ya tashi ganin halin da k'awarta da iyayenta suke ciki , a guje ta fita don shaidawa iyayenta halin da suke ciki, Basu dauki lokaci ba kuwa sai ga iyayenta acikin gidan nan suka Fara Basu taimakon gaggawa kasancewar dama mahaifin Talatu ya na bada magani, cikin k'ank'anin lokaci ya fahimci mahaifin yarinyar ya rasu ,inda ita kuma uwar suma ne tayi , ya Jima sosai kamun ya samu numfashin ta ya dawo ,aikuwa a firgice ta farka tana ambatar sunan mijinta , Akan gawarshi ta Dora kanta ta sake wani irin kuka Mai amsa kuwa inda itama yarinyar da rarrafe ta k'arasa wajan iyayenta ta fad'a Kan gawar Babanta tana sakin nata kuka, 


Cikin Dan lokaci mutuwar ta zaga cikin masarautar da ma wajenta ,inda mutane sukayi ta jajen abun kasancewar sun riga sun San ko minene dalilin mutuwar tasa ,don ba yau aka Saba irin Haka ba , haka aka taru akayi mashi bikin jana'iza kamar yadda Al'adar garin ta tanada , haka aka Gama komai aka binneshi inda aka bar matarshi da 'yarshi cikin mawuyacin Hali, 


Wannan abun da ya faru ya matuk'ar k'arawa mutanen Masarautar fadakatam tsanar yarima ZILLAK'I fiye da zato sai dai tsananin tsoron da aka dasa a cikin zukatansu ya hanasu wani motsi bare daukar mataki , haka sunaji suna gani ya ci gaba da ketawa 'ya'yansu mutunci ba abunda suka iya, abubuwan da suke gudana a masarautar fadakatam sun k'ara tsananta mutane sun Shiga Hali na matsi da takura suna cikin Hali na k'angin 'bauta Wanda a kullum suke fatan Allolin zinari su kawo masu dauki akan zaluncin da suke fuskanta,


..................................



Kwance yake ya k'urawa sama Ido ,idan ka ganshi zaka dauka Yana kallon taurarin da suka yi wa sama'u k'awanya ne , sai dai Sam ba haka bane Sam baya tare da wannan duniyar ,duk da k'arancin shekarunshi kallo d'aya zaka mashi kasan cewa Yana cikin alhini da matuk'ar damuwa , idonshi yayi ja sosai saboda damuwa da rashin bacci, tun da ya yi arba da Malamin duba da halin da ya ke ciki ya ke cikin d'acin zuciya ,ya damu sosai da dattijon haka nan ya ke jin wani irin tausayinshi da kuma tausayin Aziza wadda a kullum batada burin da ya wuce ta ga mahaifinta , furucin Malamin duba na jiya ya firgitashi sosai Sam ba zai so ace tsohon ya mutu ba tare da ya had'u da tilon 'yarshi ba, 

Mik'ewa ya yi ya Fara zagaye a cikin lambun cikin tsananin fushi da tsanar sarki ZULAIMU ya Fara magana ,

    "Sai Naga bayanka ya Kai wannan azzalumin sarki kuma da izinin allolin zinari sai na k'wato Malamin duba daga hannunka, sai na cikawa Aziza alk'awarin da na Jima ina yi Mata , tabbas sai na cika alk'awari... Ya fad'a Yana wani irin huci ,


Tun daga lokacin yarima ZAHIRR ya Fara shiri Shirin da ko Mah Bata san da shi ba, sati d'aya ya dauka Yana tunanin mafita akan Shirin shi kamun ya yanke shawarar da yake ganin zai taimaka Masa , wannan yasa yau ya shirya ya nufi sashen gimbiya HIDAYA don shaida Mata hukuncin da ya yanke,


Tun da ya doshi inda take fad'awa ke fad'uwa suna gaisheshi ,sai dai da yake Sam baya cikin dad'in rai ya sa ko kallonsu bayayi haka ya dinga ratsasu har ya isa inda mahaifiyarshi take ,

Tunda ya doso ta take k'are mashi kallo ,inda ta hango damuwa sosai akan fuskar yaron nata ,ganin yanayinshi yasa ta d'agawa bayin dake tare da ita hannu, nan take duk suka mik'e suka Fara fita don basu waje,


Zama yayi kusa da ita tare da gaishe ta , Bata amsa ba sai Ido da ta Sanya mashi , cikin damuwa ta Fara magana , "mi ya ke damunka yarima ? yanayinka ya bayyanamin da irin damuwar da kake ciki ,ba iya yau ba Tsawon sati d'aya kenan da na fahimci kana da damuwa , Kar ka ji komai ka fadamin minene damuwar , in kuma wani abun kakeso ka gayamun ko miye shi zanyi maka don farin cikinka shine nawa Yarima,"

Kan shi ya d'ora akan k'afafunta kamun yace " Mah akwai abun da nakeso ki mun duk da nasan zakiji ba dad'i Amma Ina son ki mun wannan alfarmar , "


K'ureshi tayi da Ido na tsawon lokaci kamun ta lumshe manyan idonta ta bude tace "mi kakeso yarima na ? duk abunda kakeso zanyi maka shi matuk'ar ba zai cutar da Kai ba" 

"Mah Ina son na 'boye Kai na ne har na Tsawon shekarun da muke jira , Ina son na 'boye kaina na Tsawon shekara bakwai ,Ina son kamun cikar wannan lokacin na samu tsananin horon da sani Akan lak'unnan tsafi Ina son na Zama gagara badau a fagen k'arfin damtse da kuma k'arfin tsafi , ta yadda ko zuwa gaba wani Mai irin halin sarki ZULAIMU bazai ta'ba sha'awar mulkar Masarautar fadakatam ba, Ina jin ciyon a cikin zuciyata , Ina jin ciyon abun da akayi Mana Mah , Ina jin zafin halin da mutanenmu suke ciki ,an mayar da Masarautarmu sansanin k'angin Bauta, tabbas sai na hukunta ZULAIMU da mafi girman hukunci , " ya fad'a ya na wani irin huci sai kace wani babban mutum , 


Gimbiya HIDAYA ta jima tana kallon d'an nata cikin alfahari ,tana mamakin wasu hallaya na shi ,tabbas ya nuna cewa shi d'in jinin sarki KUNTARU ne , sai dai ta fahimci yaron nasu yafi mahaifin nashi zafin zuciya tabbas ta na alfahari da jarumin d'anta Wanda ga dukkan alamu zaiyi adalci a k'asarsa duba da irin damuwar da yakeyi akan halin da talakawanshi suke ciki tun Yanzu , 


"MAH" ya fad'a yana d'an matse Mata hannu ganin tayi shiru ta zuba mashi Ido , 

Firgigit tayi tare da sauke numfashi ta ce " na baka dama yarona hak'ik'a Ina matuk'ar alfahari da Kai , ka je kana tare da sanyawar albarka ta , da izinin Allolin zinari burinka zai cika , "


Cikin matuk'ar mamakinta ya d'ago kai Yana kallonta fuskarsa na bayyanar da farin ciki don Sam Bai dauka zata yarda da zancan shi ba ,sai gashi cikin sauk'i ta amsa mashi bukatarshi , rungumeta yayi Yana Mata godiya kamun ya mik'e don zuwa wajan sarkin RIGASA da kuma shaida mashi shawarar da ya yanke,


Hak'ik'a sarkin RIGASA ya ji dadin shawarar da yarima ZAHIRR ya kawo kuma yayi na'am da ita d'ari bisa d'ari , sosai ya yabawa hikimar yaron ,don in har ya kadaice kanshi na Tsawon shekara bakwai tabbas ba mutum ba ko aljani sai yaji tsoron arangama dashi ,kuma zai samu makamin yak'ar duk wani azzalumin da zai tunkarosu da niyar zalunci , Nan take sarkin RIGASA ya sa aka Tara mashi manyan dakaru inda ya bawa shugaban dakarun umurnin tafiya da yarima ZAHIRR *masarrafar horo* Nan da kwana biyu , *masarrafar horo* waje ne na sirri kuma tsafaffen waje Wanda ba kowa ya San inda yake ba sai amintattun sarkin RIGASA, 



Bayan kwana biyu yarima ZAHIRR yayi shirin tafiya inda gimbiya HIDAYA ke matuk'ar damuwa da kewar d'an nata tun bai tafi ba tana tunanin yadda zata shekara bakwai ba tare da ta sanyashi a idonta ba , gefe d'aya ga Aziza ta d'aga Mata hankali a kwana biyun Nan har zazza'bi tayi Banda kuka ba abunda takeyi tayi lallashi har ta gaji , 

Zaune suke yarima ZAHIRR Yana k'ara kwantarwa da gimbiya HIDAYA hankali aka zo tafiya dashi , haka nan cikin matuk'ar kewar junansu sukayi sallama inda ya hau doki suka Kama hanya , a wannan lokacin gimbiya HIDAYA har da kuka saida ta yi , tana ganin kamar shi kenan ba zasu sake had'uwa ba, tanaji kamar ta rabu da d'an nata kenan...............



Agurguje don ina son mu shiga asalin chakwakiyar dake cikin *Masarautar fadakatam*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol